Showing 72001 words to 75000 words out of 75226 words

Chapter 25 - Exiled Princess Book 1 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

297

ni ba zan sake shi ba , babu inda zan je "

Da sauri Abdoul ya dafa kafadun ta ya na fadin " auta ki yi hakuri ki bari a duba shi " ya fada cikin rarrashi

Ba dan ta so ba ta tashi da ga jikin shi ta fada jikin shi Abdoul ta rungume shi sai kuka ta ke
Shi kuma doctor ya shiga duba Zayd

Sai da ya dauki wajen two minutes ya na yi mishi wasu gwaje gwaje kafin ya juya ya kali Moussa ya na murmushi ya ce " Gaskia abu ya yi kyau, ban san yadda a ka yi ba , wajen kwana hudu mu na neman mu saita bugun zuciyar shi , amma ga shi lokaci guda bugun zuciyar shi ya dawo dai'dai , ku ci gaba da yi mishi adu'a , in sha Allah zai tashi " ya na gama fadar haka ya juya ya fice dakin

Murmushi Moussa ya yi ya shiga jerowa Allah godiya da ya sa Zayd bai mutu ba

Inaya kuma ta na ganin doctor ya fita ta saki Abdoul ta koma jikin Zayd ta konta ta na sauke ajiyar zuciya ta lumshe idanun ta


Shi kuma Abdoul ya juya ya ficewar shi ya koma wajen Malam
Ya na isa bakin A&E room din doctor ya fito

Da gudu Abdoul ya nufe shi ya na fadin " Doctor ya jikin na shi "

Dafa kafadar shi doctor ya yi kafin ya ce " i'm sorry ya riga mu gidan gaskia "
Ya kai karshen ya na janye hannun shi ya yi gaba

Sumar tsaye Abdoul ya yi ya kassa wani kwakwaran motsi har a ka fito da gawar malam a ka tafi da ita morgue ya na nan tsaye ya kura wa waje guda ido


Ya dauki wajen good ten minutes a haka ko kifta idanu ba ya yi
Kamar da ga sama ya jiyo Muryar mama ta na fadin " Abdoul lafya ka tsaya a nan , mun ga tun dazu ba ka zo ba , shi ne Nesrine ta ce mu shigo Taxi "

Ba ta kai karshen maganar ta ba Abdoul ya fada mata a jiki ya rungume ta ya na sakin kuka kamar karamin yaro


A rude mama ta dago shi ta na fadin "Abdoul lafya ka na kuka kamar yaro haka da girman ka , me ya yi zafi haka "

Cikin kukan ya ce " mama komai ma ya yi zafi , sun kashe Abba , sun kashe shi"

Dum mama ta ji zuciyar ta ta buga , nan take jiri ya debe ta ta sume a wajen

Da sauri ya Zube saman guyiwowin ta talabo kan mama ya na kiran nurse
Da gudu wasu nurse guda biyu su ka yo kan shi , har gudar ta juya za ta je ta dauko gadon jinya , gudar ta tare ta ta ce mata ta debo ruwa kawai jiri ne ya debe ta


Da sauri nurse ta bar wajen, jim kadan ta dawo rike da glass dauke da ruwan sanyi
Karbar glass din nurse ta yi , ta zuba kadan a hannun ta, ta shafawa mama a fuska

Ta na yin hakan mama ta sauke ajiyar zuciya , ta na karanto kalmar shahada

Dan lumshe idanun shi Abdoul ya yi ya na sauke ajiyar zuciya kafin ya kali nurses din ya yi musu godiya

Jinjina mishi kai kawai su ka yi kafin su mike su ka yi tafiyar su

Su na barin wajen mama ta mike zaune ta na kallon Abdoul ta ce " Abdoul , ina malam ya ke , don Allah ka bar min irin wannan wassan " ta kai karshen hawaye na zubo mata

Shi ma wasu hawayen ne su ka zubo mishi ya na sunkuyar da kai ya ce " mama ta ya zan yi miki irin wannan wassan , ina shirin tafiya dauko ku , Inaya ta shigo likitar wani soja na biye da bayan ta , ya na dauke da Abba a kafada , bayan doctor ya duba shi ne ya ke ce min wai ya rasu , mama ko ni ban san abun da ke faruwa ba "

Lumshe idanun ta mama ta yi kafin ta mike tsaye ta na kallon Abdoul ta ce " mu je na gan shi don Allah " ta kai karshen kuka a kubce mata

Da sauri Abdoul ya mike ya riko ta , su ka nufi morgue dan su ga gawar malam

A takaice dai ranar wannan ahalin sun ga ta kan su , sai da su ka ji duniyar su ba ki daya ta ruguje dan malam shi ne duniyar su
Nesrine da mama sun sha kuka kamar za su mutu , har shi Abdoul da ya ke namiji sai da ya yi kuka
Bangaran Inaya kuma ko digon hawaye ba ta yi ba , ba yin da mama ba ta yi ba a kan ta yi kuka ko da sau daya ne amma ina ta ki , sai dai ta yi zaune ta zuba wa waje guda idanu babu ko kiftawa
In muka leko Zayd kuma jiki alhamdoulilah ya samu sauki sosai, sai dai har yanzu bai dawo cikin hayacin shi ba


After some days


Sati biyu yanzu kennan da rasuwar malam , har an yi jana'izar shi , an kai shi gidan shi na gaskiya , Mama kuma ta shiga takaba

Tambayar duniyar nan Abdoul ke yi ma Inaya a kan ta fada mishi wanda ya kashe malam amma ko bude baki ba ta yi
Tun ranar da ta dawo ta yi wa Zayd magana , tun da ga ranar ba ta sake bude baki ta yi magana
Ko tambayar ta ka yi sai dai ta bi ka da ido amma ba ta cewa komai
Tun abun na damun mutanan gidan , har sun daina damuwa su ka mika komai a hannun Allah
Ita kuma Inaya, duk abun da su ke kar ta ke kallon su amma ta share , dan duk hankalin ta na wajen Zayd
Kullum sai ta likita ta yi one to two hours tare da shi kafin ta koma gida , haka gobe ma za ta dawo
Moussa dai kallon ta kawai ya ke , cikin ranshi ya na kara yabawa soyayyar da ta ke yi wa Zayd , dama a ce Nesrine za ta so shi a hakan
Zayd kuma jiki sai kara sauki ya ke dan har an cire mishi dress din da a ka yi mishi a kai ,
A cikin sati biyun nan Moussa ya kira ahalin Zayd ya fada musu halin da a ke ciki ya kuma sun ce su na nan zuwa


Misalin karfe 10 na safe


Konce Inaya ta ke saman jikin Zayd sai faman surutai ta ke zuba mishi kamar ba ita ba ce in ka yi mata magana sai dai ta bi ka da ido

Ta na a haka har barci mai dadi ya de ta a jikin shi
Moussa dai tun safe ya bar likitar kuma bai sanar da kowa inda zai je ba



❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥


( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )



STORY & WRITTEN BY : ANISH


Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 30 ❤🔥


Misalin karfe 12 na safe

Zayd

A hankali yar yatsar shi ta fara motsi , ta na yin sama
A hankali ya dinga sauke ajiyar zuciya ya na girgiza kan shi

Idanun a lumshe ya bude bakin shi a hankali ya ke furta sunan " mimi " ya kai sau biyar

A dubu dari ya bude idanun shi ya na kallon ceiling sai juya su ya ke yi , ya na bin wajen da kallo
Ya na kokarin tashi ya jiyo yauni a saman shi

A hankali ya lumshe idanun shi , ya sake bude su a hankali kafin ya sauko da kan shi ya kali jikin shi

Idanun shi ba su sauka ko ina ba sai saman ta , ta na konce a jikin shi face din ta dauke da wani dan karamin murmushi da allamun barcin ya yi mata dadi

Dan zaro idanu shi ya yi ya na kallon ta , ya ma rasa bakin magana , ya na dawowa cikin hayacin shi ita ce mutun ta farko da ta fado mishi a rai , ga shi kuma ta na konce a jikin shi abun sai da ya bashi tsoro


A hankali ya fara dago da hannu shi me sanye da catheter ya daura a saman bayan ta
Ya dago gudan hannun ya daura saman kumatun ya na kallon din ta
Kassa kassa ya ce " mimi "

A hankali ta fara bude idanun ta cikin magagin barci ta ce " na'am "

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya meda kan shi ya lumshe idanun shi
Wani irin dadi ne ya ji cikin zuciyar shi lokaci guda , bai San lokacin da ya rungume ta tsam a jikin shi ya na sumbatar forehead din ta

Yar karamar dariya ta yi kafin ta ware idanun ta da kyau ta dago kai ta na kallon face din shi

Zaro idanu ta yi ta na kallon cikin na shi ta , ta saki wani kyawatencen murmushi ta ce " yaya Zayd da gaske kai ne "

Jinjina mata kai ya yi kafin ya daura hannun shi saman kumatun ta ya ce " mafarki ne na yi kennan "

Nan take yanayin face din ta ya sauya ta koma ta konta a kirjin shi
Da sauri ya ce " mimi why did you cry , ba abun da ya same ki dai ko ? "

Kuka ne ya kubce mata ta na fadin " ba abun da ya same ni yaya Zayd, amma Abba , Abba ya tafi ya bar ni " ta kai karshen ta na kara sautin kukan ta

Dum ya ji zuciyar ta buga , har sai da ya lumshe idanun shi da karfi dan su na shirin kawo ruwa , duk da ba shi da wata alaka da malam da farko , amma yanzu shi ma ya zama familyn shi , ya san duk duniya ba wanda zai yi mishi abun da malam ya yi mishi


A hankali ya ware idanun shi ya na kallon ta ya ce " please stop crying , i'm here with you forever , don Allah ki daina kukan nan so ki ke ciwo na zama biyu "

A hankali ta fara rage sautin kukan ta ta na fadin " shikenan yaya Zayd ka yi hakuri "

Dago kai ya yi ya sumbaci forehead din ta ya ce " yi hakuri kin ji , Allah ya jikan shi , ya sa ya huta "

Da amine ta amsa mishi kafin ta lumshe idanun ta , ta na sauke ajiyar zuciya
A hankali shi ma ya lumshe idanun shi ya fara shafa bayan ta a hankali a haka har barci ya yi gaba da su a tare



Misalin karfe 2 na yamma

A hankali Moussa ya turo kofar dakin kai a sunkuye ya na sallama kafin ya koma geffe ya tsaya ya na fadin " Bismillah "


Ya na gama fadar haka a ka bude kofar , wani dattijon ya shigo dakin ya na sanye da manyan kaya masu bala'in kyau farare kal
Kamanin shi sak da na Zayd ba dan gemun shi ba da kuma shi ya na da dara daran idanun amma har colour din su hazel irin na Zayd ne a kila a shekaru zai kai 55 haka
Bayan shi kuma wasu matane biyu , su na sanye da gown ma su bala'in kyau sun daura wata Alkyaba da ga sama , sun saka hular ta
Gudar ta dan lattijantaka dan a kila ta kai 48 to 50 years haka amma kyakyawar gaske ce da ga ganin fatar jikin ta kassan ta na samun hutu
Dayar kuma yar budurwa ce a shekaru za ta kai 23 years ta so ta yi kama da Zayd , amma ita idanun ta bakake ne ta yi simple make up , ta saki wani lalawsan curly hair din ta ya zubo mata ta cikin alkyabar ta


A hankali Moussa ya dago kai ya kali saitin Zayd
Dum ya ji gaban shi ya fadi , sam bai san da cewa Inaya ta na cikin dakin ga shi kuma ta na konce a jikin Zayd , kuma ya na rungume da ita

Su ma mutanan da ke tare da shi sai da su ka sha mamaki
Macen sai da ta kali Moussa ta ce " Diya wacece wanan a jikin Amir kuma ? " ta fada cikin harshen larabci

Sunkuyar da kai Moussa ya yi kafin ya ce " Ran ki shi dade , ina ga Amir ya kamata ya baki wannan amsar " shi ma ya fada da larabci

Medo da kallon ta matar ta yi kan Zayd kafin su ida shigowa cikin dakin
Dattijon da ke tare da su ne ya karaso bakin gadon ya na kallon face din Zayd da larabci shi ma ya ce " Amir , tashi mu koma gida don Allah " ya kai karshen kamar zai yi kuka


Kamar da ga sama su ka jiyo Muryar shi da larabci ya na fadin " ni babu inda zan je "

Duka sai da zuciyoyin su su ka buga , a iya sannin su Zayd ya yi doguwar suma ya a ka yi ya amsa musu

Tun lokacin da Moussa ya yi sallama ya farka da ga barcin shi , amma bai motsa ba , sai da ya jiyo Muryar matar nan ta na tambayar Moussa wacece a jikin shi

Duk duniya ba zai iya manta wannan Muryar ba, amma ya shanye bai motsa ba

Su na a haka yar budurwar da ke tsaye ta karaso wajen ta na fadin " Akhie ! " kamar za ta yi kuka


Slowly ya bude wadanan hazel eyes din na shi ya na kallon mutanan da ke cikin dakin

Bai ce da su kami ba ya kali Moussa ya matse fuska ya ce " why za ka fada musu da sai ka bari har in tashi sai mu tarda su a cen "

Murmushi Moussa ya yi ya na sunkuyar da kai dan a halin yanzu ba ya da bakin magana

Zayd na ganin haka ya ja dan tsaki ya kauda kan shi gefe
Dattijon da ke tsaye bakin gadon ya ce " Amir kenan da ba mu so ba ba za ka je ba , Amir tsawon Shekara shida ka na raye amma ko so guda ba ka yi tunanin ka koma gida ba , ba dan Diya na kiran mu na gaya mana halin da ka ke ciki , da ba mu san cikin halin da za mu kasance ba "

A dubu dari Zayd ya juya ya na kallon Moussa da ya sunkuyar da kai, ya ma rasa bakin magana

Kawai sai ya ja tsaki kafin ya ce " please ya isa haka Abbi , ni ban ce ba zan koma ba , amma ai yanzu ku na ganin halin da na ke ciki kun iya bari na one minutes please " ya kai karshen ya na juyawa da Inaya a jikin shi ya ba su baya

Yar budurwa nan ta fashe da kuka ta je ta fada saman bayan shi ta na fadin " Akhie don Allah ka tashi mu koma gida wlh na ki kewar ka sosai "

" Amira , kontar da hankalin tare za mu koma kin ji ko " ya fada ba tare da ya juyo ba

A hankali ta sake shi ta na murmushi ta koma gefe ta tsaya
Dai'dai lokacin da Inaya ta bude idanun ta , ta tashi da ga barcin ta

Ita ba ta lura da mutanan da ke cikin dakin ba, kawai sai ta mike zaune ta sauko da ga saman gadon

Ba ta yi taku daya ba, jiri ya debe ta ta yi baya za fadi
Da sauri Zayd ya mike ya taro ta , ta fado jikin shi , ya na kallon face din ta ya ce " are you okay ? "

Jinjina mishi kai tayi ta na dan karamin murmushi ta ce " yaya Zayd , ina lokacin sallat ya yi zan je na yi "

Ta na gama rufe bakin ta Abdoul ya shigo dakin ya na sallama Nesrine na bayan shi ta na rike da wani basket

A hankali Inaya ta juyo ta kali saitin kofar , sai yanzu ta lura da mutanan da ke cikin dakin
Ba ta san lokacin da zuciyar ta ta buga ta juya da sauri ta rungume Zayd ta boye fuskar ta a kirjin shi

Gaishe su Abdoul da Nesrine su ka yi duk da ba su san ko su wanene ba sannan Abdoul ya yi sauri ya je ya rungume Zayd ya na fadin " Bro , sannu ya jikin na ka "

Dan bubuga bayan shi Zayd ya yi kafin ya ce da sauki sannan ya kali Inaya ya ce " To madam sa ke ni ko , They are my family , our family "

Da sauri Abdoul ya sake shi ya juyo ya na kallon mutanan da ke tsaye cikin dakin , ba karya kallo daya za ka yi musu ka san abun da ya fada gaskia ne

Yarinyar da ya kira da Amira ta ce cikin harshen larabci " Akhie su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login