Showing 54001 words to 57000 words out of 75226 words

Chapter 19 - Exiled Princess Book 1 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

304

gidan sun yi zugum kamar an turo musu mutuwa


A tare su ka dago kai su na amsa sallamar shi
Malam na ganin Zayd ya mike da sauri ya nufe shi ya na fadin " Zayd an gan ta ne ? "


Riko hannun shi Zayd ya yi ya dawo da shi inda ya tashi ya ce " uncle zauna zan yi wata magana "

Ba musu malam ya koma ya zauna dan shi fa yanzu ba ya cikin halin yin jayyaya da shi a kan wani abu


Tsaya wa Zayd ya yi ya na rike da hannayan shi a baya ya zuba musu idanu ta cikin glass din shi


Sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " ku kontar da hankalin ku uncle an gan ta , amma sai dai ku yi hakuri ta samu hatsari dalilin da ya sa ma ta kassa dawowa gida , yanzu haka na sa an wuce da ita Abuja za a ci gaba da kula da ita a cen , ina son ku shirya kayan ku nan da two hours zan sa a zo a dauke ku tare za mu koma Abuja da zama "


Da sauri malam ya mike shi da Abdoul ya na fadin " Zayd mu fa ba mu da gida a Abuja idan mun je ina za mu zauna , karatu na da aiki na duk na yi yaya da su ? "


" duk ba damuwa ba ne , ka fadi duk makarantar da ka ke so a Abuja ka fada min zan nema maka admission, batun gida kuma a gida na za ku zauna , ku shirya nan da two hours za a zo daukar ku " ya na gama fadar haka ya juya ya na taku cike da nitsuwa ya bar gidan


Ya na fita Abdoul ya kali malam ya ce " Abba ya za muyi ne , haka za mu bar gidan nan lokaci guda ? "


Malam na shirin magana mama ta mike da sauri ta ce " e tafiya za muyi , wlh duk inda yarinya ta , ta tafi sai na tafi bazan kyale ta wani abu ya sake faruwa da ita " ta kai karshen kuka na kubce mata ta juya da sauri ta shige dakin ta


Ta na barin wajen malam ya kali Abdoul ya ce " to ba yadda za muyi , la shiga kawai ka shirya kayan ka sai mu tafi "

Da to Abdoul ya amsa mishi sannan kowa ne ya kama hanyar dakin shi dan su shirya kayan su


Zayd


Bayan ya baro gidan malam kai tsaye gidan shi ya nufa

Bakin shi dauke da sallama ya shigo falon gidan , kai tsaye ya nufi doguwar sofa ya zauna ya jingina a bayan sofar ya daga kan shi sama sannan ya sa hannu ya cire glass din shi ya ajiye gefe shi ya lumshe idanun shi


Ya na zama Inaya ta fito da ga kitchen ta na rike da tray dauke da kwanonin abinci ta nufi dining room ta ajiye


Ta na juyowa ta ga Zayd a zaune har sai da ta ji tsoro dan ita sam ba ta san lokacin da ya shigo gidan ba


A hankali ta fara takowa ta karaso inda ya ke , ta zauna geffen shi ta na kare mishi kallon cikin ran ta , ta na fadin lalle akwai abun da ya ke damun shi dan yanayin shi ba haka ya ke kullum ba


A hankali ta gyara zaman ta ta konta ta tada kai da cinyar shi ,

A razane ya sauko da kan shi ya bude idanun shi ya na kallon ta , shi sam bai san lokacin da ta iso wajen


Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mayar da kan shi ya sake lumshe idanun shi , ta kai hannu saman kan ta slowly ya fara shafawa


Ta na jin saukar hannun shi saman kanta ta saki dan karamin murmushi ta ce " yaya Zayd me ya ke damun ka ne ? "


Ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce " me ki ka gani ne ? "

" yadda ka fita ba haka ka dawo ba , duk yanayin ka ya sauya , me ya ke damun ka ne "


Gaskia maganar ta ba karamin dadi ta yi mishi cikin zuciyar shi , kennan har ta iya gane yanayin da ya ke ciki lokaci guda haka


" ba komai , ba abun da ya ke damu na kar ki damu "

Da sauri ta katse shi da cewa " a'a yaya Zayd ni na san akwai wani abu da ya ke damun ka amma ba ka son ka fada min "


A hankali ya bude idanun shi ya sauko da kan shi ya na kallon face din ta ya ce " shikenan fada min ta ya ki ka san akwai wani abu da ke damu na ? "


Gyara konciyar ta tayi ta juyo da kan ta yadda su na iya fuskantar juna

Dan murmushi ta saki kafin ta ce " yanayin face din ka ya sauya, ba kamar yadda ka fita ba , yanzu kuma duk ka yi sanyi kamar ba kai ba "


Hannun shi ya kai saman face din ta ya shafa a hankali kafin ya janye ya daura shi saman cikin ta ya koma ya daga kan shi ya lumshe idanun shi ya ce " don't worry ba abun da ke damu na , kawai dai na gaji ne , tashi ki je lokacin sallat ya yi , Idan kin Kamala ki shirya kayan ki za mu koma Abuja da zama har da su uncle "


Da sauri ta dago kan ta ta na sakin wani kyawatencen murmushi ta ce " da gaske yaya Zayd za mu koma Abuja da zama "


Jinjina mata kai kawai ya yi ba tare da ya bude idanun shi ba

Da sauri ta tashi da ga jikin shi ta nufi corridor ta shiga bedroom din shi

Ta na shiga wayar shi ta fara ringing
Ko bai duba ba ya san wanene ke kiran shi
Hannu ya kai ya ciro wayar da ga cikin aljihun shi ya daga kiran sannan ya kai kunne ya yi shiru bai ce komai ba


A daya bangaran kuma, Moussa ya na jin ya daga kiran ya ce " please ka shirya min kaya na zan bi ambulance din mu tafi Abuja tare da ita "

" okay " Zayd ya bashi amsa a takaice , sannan ya sauko da wayar ya kashe kiran

Sannan ya tashi ya shiga bedroom din Moussa ya wuce toilet ya yi wanka ya dauro da Alwalla sannan ya fito ya shirya cikin kayan Moussa , wandon jeans brown da t-shirt fara yi gabatar da sallar shi nan cikin dakin


Bayan ya gama sallar shi ya shiga shirya kayan Moussa cikin trolley biyu sannan ya fito da su falo ya koma ya shiga bedroom din shi

Nan ya tardo Inaya ta shirya musu kayan su da na shi da natan duka cikin trolley guda hudu dama nata yawancin cikin trolley su ke so aïkido bai yi mata yawa ba


Ya na shiga dakin bai bi ta kan ta ba ya janyo trolley din ya fitar da su falo sannan ya dauki trolley din daya bayan daya ya saka su cikin motar shi sannan ya gewaya ya bude babbar gate din gidan da kan shi


Sannan ya dawo cikin gidan inda ya tardo ta , zaune cikin falo saman sofa

" tashi ki jire ni bakin gate ina zuwa " ya fada ya na wucewa corridor ya shiga bedroom din shi


Ya na shiga ta tashi ta fito waje ta fita gidan ta tsaya baki kofar kamar yadda ya ce


Ta na fita ya fito shi ma ya na rataye sa wata purse ya fito gidan ya shiga motar shi ya tada ya fice

Ya na fitar da motar ya tsaya ya like gidan
Ya na shirin shiga cikin motar shi wani dattijo ya iso wajen shi ya na mishi sallama

Cen kassan makoshi ya amsa sallamar shi sannan ya mika mishi keys din gidan ba tare da ya ce komai ba ya shiga motar shi ya bar wajen da gudu


❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥


( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )



STORY & WRITTEN BY : ANISH


Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 23 ❤🔥

Inaya


Bayan ta fito gidan ta tsaya ta na jiran shi , ta dauki wajen five minutes ta na tsaye a wajen sannan ta hango shi cikin mota ya tunkaro ta


Gaban ta ya tsayar da motar ba tare da ya ce mata komai ba , bai kuma fito da ga cikin motar ba


Ganin hakan ya sa ta tako a hankali ta zagayo geffen mai zaman bazan ta bude kofa ta shiga ta zauna

Ta na shiga ya ja motar su ka yi gaba

Sai da su ka yi tafiya mai dan nisa kafin ta kaleshi ta ce " yaya Zayd ba tare da yaya Moussa za mu tafi ba "

Sai da ya dan jinkirta kafin ya ce " ya riga mu tafiya ma "

Gyada kan ta kawai ta yi ta medo da kallon ta kan hanyar su

Tun ta na ganin gidaje har ya kai ta daina ganin komai bayan itace
Sannu sannu har barci ya dauke ta ba ta shirya ba


After one hours


A hankali ta fara motsi ta na son tashi da ga barcin ta
Slowly ta faro karanto adu'ar tashi da ga barci ta na ware idanun ta


Ta sha ruwan mamaki jin ta konce saman gado al'halin ita a sanin ta cikin mota ta ke

A hankali ta fara bin dakin da kallo
Dakin babba ne gaskia komai na cikin dakin white colour ne , har closet da ke fuskantar dressing mirror duk white ne

Gaban gadon dakwai wani carpet sky blue me ratsin white gwanin burgewa , gadon ya na fuskantar wasu sofas guda uku suma white , biyu one seater su na fuskantar juna sai three seater a tsakiyar su , da ga tsakiya kuma akwai wata table ta glace mai kyau

Geffen gadon na hagu dan nesa kadan dakwai wata door wadda ina kyautata zaton toilet ce


Sai da ta karewa dakin kallo da kyau kafin ta mike zaune ta sauko kafafun ta kassa , ta mike tsaye ta fara takawa a hankali ta nufi wata kofa da ta gani bude a geffen dama na bed din


Nan ta fito parlour na sama mai bala'in kyau ya sha fournitures da ga gani kassan tsadadu ne , sai kofofi biyar na bedroom , amma ta karshen ta yi nessa da sauran

Ba ta tsaya bin ta kan falon ba ta nufi daya da ga cikin stair din da ta gani ta sauko kassa

Ni fa gaskia ban iya description ba dan haka kowa ya yi tunanin yadda falon na kassa zai kassance yawwa 😌😌


Ta na saukowa ta hango shi cen zaune saman sofa three seater ya daga kai sama ya lumshe idanun shi


A hankali ta karaso inda ya ke ta tsaya gaban shi ta ce " yaya Zayd ? "

Slowly ya medo da kan shi ya bude idanun shi ya na kallon ta
Sai da ya dauki lokaci ya na kallon ta kafin ya mika matta hannu a kan ta zo

Ba musu ta daura hannun ta saman na shi ta fara takowa gare shi

Zaunar da ita ya yi saman cinyar shi , sannan ya daga mata gera guda allamun minene


" yaya Zayd wannan gidan wanene ? " ta tambayeshi ta na karewa wajen kallo
Cen bayan sofar da su ke zaune ta hango dining room dauke da dining table zagaye da chair goma sha biyu , sai wata kofa ta kitchen amma ta glass ce


Ta yi nisa cikin duniyar ta, ta tsinci Muryar shi ya na fadin " ya dai ? Bai miki ba ne ? "


Girgiza mishi kai ta yi kafin ta ce " ya na da kyau sosai yaya Zayd "

" shikenan tashi ki je ki yi wanka , ki yi sallat , sai ki sauko ki ci wani abu na san ki na jin yunwa na sa a shirya miki lunch "


" to amma yaya Zayd ina ne bedroom din nawa " ta fada cikin shagwaba

" duk wanda ki ke so , amma bedroom din da ki ka fito cen na saka kayan ki , in bai miki ba zan sa a sauya miki "

Da sauri ta ce " a'a yaya Zayd wannan ma ya na da kyau " ta kai karshen ta na kai mishi kiss saman kumatu sannan ta tashi da sauri ta Haye stair ta koma bedroom din da ta fito


Da kallo ya rakata har sai da ya ga ta shiga bedroom din sannan ya koma jikin sofar ya daga kan shi saman ya lumshe idanun shi


After two days


Bayan malam da ahalin shi sun dawo gidan Zayd da zama duk sai da su ka sha ruwan mamaki ganin gidan Zayd musaman mama sam ba ta yi tunanin haka gidan ya ke ba
Bangaran Nesrine har yanzu dai shiru ko yatsa ba ta daga ba , amma an maido ta word room na gidan, nan Zayd ya dauko doctor musaman wanda zai kula da ita amma har yanzu malam da mama da Abdoul ba su san abun da ya same ta ba su dai a tunanin su accident ne ta yi dan haka Zayd ya fada musu
In muka leko Inaya kuma bayan barci da kallon cartoon ba abun da ta ke , ko girki akwai yan aikin da su ke kula da komai na gidan da ga mopping har girki akwai ma su yi
Kwana biyu bayan zuwan su gidan , Zayd ya nemawa Moussa auren Nesrine
Malam ya yi farin ciki sosai shi da mama , a ranar a ka daura auren duk da Nesrine ba ta cikin hayacin ta
In mu ka leko Zayd kuma bawan Allah kullum cikin damuwa ya ke har ya yi wata yar rama , tambayar duniyar nan Moussa da Inaya su ke yi mishi amma ko wane lokaci sai ya ce ba komai , kullum ya na zaune cikin bedroom din shi ya lumshe idanun shi amma ba barcin ya ke ba , a takaice ko dare in ya yi da wuya barci ya ke dauke shi wani lokaci har sai an yi kiran sallar asuba ya na farke ,
Ko me ke damun shi ?




Misalin karfe 12 na dare

Zayd


Konce ya ke saman daguwar sofa a falon kassa, ya daura hannun shi daya saman ciki, dayan kuma saman forehead din shi


Ya na konce a hakan ya ji a na takowa stair a hankali
Slowly ya ware idanun shi ya na kallon ceiling amma bai motsa ba


Ko bai duba ba ya San ko wanene , dan ya san bayan ita ba wanda ke saukowa a irin wannan lokacin

A hankali ya sauko da kafafun shi ya mike tsaye , sannan ya nufi hanyar dining table ya na taku a hankali cikin ranshi ya na fadin yau sai ya ga wainar da ta ke toyawa cikin daren nan


Cen kassan makoshi ya yi sallamar shi , sannan ya tsaya bakin kofar kitchen ya zuba mata idanu , ya nade hanayan shi a kirji


Sanye ta ke cikin kayan barci kanana pink colour , ta na tsaye gaban counter ta na yankar fruits


Slowly ya fara takowa inda ta ke ya na yi mata gyaren murya

Da sauri ta juyo ta ga ko wanene dan ita ba ta ji shigowar mutun cikin kitchen din ba

Ta na ganin shi ta saki murmushi ta ce " yaya Zayd har ka bani tsoro " ta kai karshen ta na juyawa ta ci gaba da yankar fruits din ta


Takowa ya ci gaba da yi har ya karaso geffen ta ya tsaya ya na kallon kananan hanayan ta , ta na yankar fruits cikin konciyar hankali


A hankali ya kai hannun shi ya riko nata da sauri ta dago kai ta kali face din shi , yayin da shi kuma hannayan ta ya ke kallo


Cikin sanyi murya ta ce " yaya Zayd me ya faru ? "

Sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " ba ki jin tsoron ki ji tsiwo da wadanan kananan hannayan na ki ? "

Dan murmushi mai sauti ta yi kafin ta janye hannayan ta da ga cikin nashi slowly ta ci gaba da yankar fruits din ta


Sai da ta Kamala sannan ta dauki tray din ta juya ta bar kitchen din ta bar shi nan tsaye

Sai da ta fita sannan shi ma ya fara takawa ya fice falon
Nan ya hango ta zaune saman sofa ga table gaban ta , ta daura tray din fruits a sama sai ci ta ke a hankali


Geffen ta ya karaso ya zauna , a hankali ya kai hannu saman tray din ya dauki barin Apple guda ya kai baki


Ba tare da ta kaleshi ba ta ce " yaya Zayd , don Allah ka fada min abun da ke damun ka "


Shiru ya yi bai amsa mata ba, sai ma konta wa da ya yi a jikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login