Showing 63001 words to 66000 words out of 75226 words

Chapter 22 - Exiled Princess Book 1 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

305

sakin dan karamin murmushi ya na daga mata gera guda ya ce " to na mine ki na yi min irin wannan kallo kuma , ko na fadi ba dai'dai ba ? "


Girgiza mishi kai kawai ta yi ba tare da ta janye idanun ta da ga cikin nashi ba

" okay , yanzu tashi ki je lokacin sallat ya yi " ya kai karshen ya na janye hannayan shi da ga saman kafadun ta
Sannan ya juya ya na kokarin sauka da ga saman gadon
Ya koma bakin gadon ya yi tsaye ya na kallon ta fuska dauke da murmushi


Ita dai ta tsaya ta na kallon shi ta rasa dalili

Daga mata gera guda ya yi ya na fadin " ko sai na taimaka miki ? "

Da sauri ta girgiza mishi kai ta sauko da ga saman gadon , a hankali ta fara takawa ta na jan kafa ta na rumtse idanun ta dan fa har yanzu zafi wajen ke yi mata


Da kallo ya rakata har sai da ta shiga toilet sannan ya saki wani cool murmushi ya sa kafa shi ma ya bar dakin


Bayan sallar isha


Zayd

Zaune ya ke cikin harabar gidan saman wasu chair irin na shan iska , ya daga kan shi sama ya na kallon stars


Ya na zaune a hakan Moussa ya karaso wajen ya na yi mishi sannan sannan ya zauna saman daya chair din da ke fuskantar ta Zayd


Cen kassan makoshi Zayd ya amsa mishi sallamar shi ba tare da ya sauko da kai ba


Hannu Moussa ya kai ya bugi cinyar Zayd ya na fadin " kai dan Allah malam sauko da kan ka , kar ya yi maka ciwo "

Ko sauraron shi ma Zayd ba ya yi ga Dukan allamu ya yi nisa cikin tunanin shi

Murmushi Moussa ya yi ya na fadin " tunanin mi ka ke yi haka ne Amir ? "

Sai da ya dauki dan lokaci kafin ya ce " Diya , ina ji a jiki na wani mumunan abu na shirin faruwa da ni "

Da sauri Moussa ya katse shi da cewa " kontar da hankalin ka ba abun da zai faru da kai da yardar Allah "


Lumshe idanun shi Zayd ya yi kafin ya ce " zan iya yi maka wata magana , please be serious "


Gyara zaman shi Moussa ya yi kafin ya ce " ina jin ka mai martaba " ya fada dan yau ya ga allamun na mulkin ke sama


Jinkirtawa Zayd ya yi kafin ya ce " ka na ganin zan iya komawa gida da wannan yarinyar "

" me zai hana ran ka ya dade , na ga ai matar ka ce ta sunna dole ne ka tafi da ita , ta ga ahalin ka , su ma su ga sirikar su "

" but ba na tunanin uncle zai yarda , it's not sure idan na je za su yarda su karbe ta a matsayin gimbiya , she is so small "

" ran ka shi dade idan har kai ka karbe ta a matsayin matar ka , dole za su karbe ta "

Dan tsaki Zayd ya yi ya na bude idanun shi ya sauko da kan shi ya na kallon Moussa ya ce " please Diya , ni fa yanzu friend di na , na ke bukata , kai daina cewa ranka shi dade , i don't like that "

Murmushi Moussa ya yi ya na kallon abokin nashi ya ce " Amir na san ba wannan maganar ka ke son yi min ba , ka fi kowa sani , idan har ka koma Daular saudiya da ita ka ce matar ka ce , babu wanda ya isa ya ce a'a har shi Malik , kamar yadda ka ce friend's din ka ka ke bukata , zan yi maka magana a hakan , Nawfel , fada min gaskia ka na son yarinyar nan ko ba ka son ta "


Ajiyar zuciya Zayd ya sauke kafin ya sake daga kan shi ya na kallon sama ya ce " i don't know "

" you lie , ka sani sarai kawai dai har yanzu zuciyar ka ta ki yarda da hakan ne dan har yanzu kallon yarinya ka ke yi mata "

Sauko da kan shi Zayd ya yi ya matse fuska ya ce " Diya ni ka ke cewa karya na ke ? "

Da sauri Moussa ya mike tsaye ya nufi hanyar shiga falon gidan ya na fadin " e na fada karya ka ke "

Da gudu Zayd ya mike ya bi bayan shi da gudu su ka shiga cikin falon gidan


A cikin falon kuma Malam, mama da Abdoul su na zaune su na hira su ka ga Moussa ya shigo da gudu kamar an koro shi

Da sauri malam ya ce " Moussa lafya ka ke wannan gudun "

Bai kai ga rufe bakin shi ba ya ga Zayd shi ma ya shigo da gudu ya bi bayan Moussa su ka Haye stair

Da kallo malam ya bi su ya na sakin dan karamin murmushi ya ce " Allah dai ya shirya tun da haka ne "


Bangaran Zayd kuma , Moussa na Hayewa stair ya nufi part din Zayd

Har ya kai bakin kofar ya tsaya ya juyo , ya na kallon Zayd da ya tunkaro shi da gudu


Zayd na karasowa wajen ya kai hannu zai damko shi

Da sauri Moussa ya gauce gefe , sai ga Inaya tsaye a bayan shi ta sunkuyar da kai ta na gyara hijabin jikin ta

Zaro idanu Zayd ya yi ya na kallon ta , ya na kokarin ya dakatar da kan shi amma ina sai da ya fada mata , su ka yi fuuu baya su ka fadi


Yar siririyar kara ta saki ta na datse idanun ta da karfi

Gumshe dariya Moussa ya yi ya na sa kafa ya bar wajen , dama ya na shirin shiga dakin ya ga Inaya ta fito da ga cikin bedroom kai a sunkuye , kawai sai ya tsaya har ta karaso dan ya yi ma Zayd tarko , kuma ya fada


Ya na barin wajen Zayd ya sa hannayan shi biyu ya mike ya mata runfa da kirjin shi ya na kallon face din ta , har yanzu ta na lumshe idanun ta


Slowly ya bude baki ya ce " Mimi ba ki ji ciwo ba ? "

A hankali ta fara ware idanun ta , sai cikin nashi
Shiru ta yi ta na kallon shi cikin ido babu ko kiftawa ta kassa cewa komai


Daga mata gera guda ya yi ya na fadin " me ki ke kallo ? "

Da sauri ta dawo cikin hayacin ta , ta kauda kai gefe ta ce " ba komai yaya Zayd "

" shikenan to , ai yanzu sai ki tashi ko " ya fada da allamun ya manta shi ne ya hana ta tashi

A hankali ta juyo da kan ta, ta na kallon shi , kassa kassa ta ce " yaya Zayd tashi to "

Daga mata gera guda ya yi ya na fadin " in tafi ina ? "

Dan murmushi ta yi mai sauti kafin ta ce " yaya Zayd ka tashi da ga sama na na fara gajiya da koncin nan "

A hankali ya dan lumshe idanun shi , sannan ya koma geffen ta ya zauna

Ya na sauka da ga saman ta , ta tashi ta mike tsaye ta juya ta koma cikin part din

Da kallo ya rakata har sai da ya ga ta zauna saman sofa sannan ya tashi , ya na taku a hankali ya shiga falon ya na sallama kassa kassa


Kamar ta san ya yi sallamar a fili ta amsa mishi ta na kallon Tv

Geffen ta ya karaso ya zauna ya na kallon Tv din shi ma

A hankali ta juyo ta kaleshi cikin sanyi murya ta ce " yaya Zayd , yaushe zan koma school , na gaji da zama a gida "

Ba tare da ya kale ta ba ya ce " okay gobe ki shirya , sai mu je ki ga college din da na zaba miki "

Cike da murna ta washe baki ta na murmushi ta ce " da gaske gaske yaya Zayd ? "

Jinjina mata kai kawai ya yi , bai kai ga bude bakin shi ba ya ji ta fado mishi a jiki ta rungume shi ta na fadin " nagode yaya Zayd "

Tsit ya dauke na wucen gadi , dan bai shirya wa hakan ba da ga gare ta

Ajiyar zuciya ya sauke ya lumshe idanun shi slowly ya bude , ya kai hannu shi saman bayan a hankali ya dan bubuga cen kassan makoshi kamar mai rada ya ce " okay Ya isa haka "



❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥


( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )



STORY & WRITTEN BY : ANISH


Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 26 ❤🔥


A hankali ta dago da ga jikin shi ta na kallon face din shi ,
Da sauri ya kauda kai gefe dan ba ya son ya kali face din ta

Murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta mike da ga jikin shi ta koma gefe ta zauna ta na kallon Tv


Washe gari

Misalin karfe 8 na safe

Tsaye Inaya ta ke cikin falo, ta na sanye cikin wata gown mai bala'in kyau navy blue da na da wani madauri a tsakiya
Ta saka wani dan karamin hijab zuwa kirji sky blue ta yi kyau over


Sai kai kawo ta ke yi kamar mai jiran wani abu
Ta na tsaye a haka , zayd ya fara saukowa da ga stair
Ya na sanye da jeans Baki da t-shirt navy blue shi ma

Ta na ganin shi ta tsuke fuska , tun bai karaso wajen ba ta ce " yaya Zayd tun dazu fa na ke jiran ka " ta kai karshen cikin shagwaba

Dai'dai ta da ya karaso gaban ta ya tsaya ya na kare mata kallo da ga sama har kassa cikin zuciyar shi ya na kara yaba kyaun da ta yi cikin wannan rigar

( WAI NI KADAI CE NA LURA DA TSADADUN KAYAN DA INAYA KE SAKAWA TUN SU NA KANO , GA SHI BA TA TABA FITA TA SAYO KAYAN BA KO DAI ALJANAI KE KAWO MATA SU 🤔🤔🤔 )


Gaba ya yi ya na fadin " waya ta na manta , mu tafi yanzu "
Murmushi ta yi ta na bin bayan shi su ka fice falon


Su na barin wajen Nesrine ta fara tako stair a hankali za ta saukowa
Har ta kai tsakiyar stair ta tsaya ta na meda nunfashi dan har yanzu ciwo ta ke ji in ta taka

Ta na tsaye a haka Moussa da Abdoul su ka fito da ga cikin bedroom din Moussa dan shi ma Abdoul yau Zayd ya bawa Moussa kudi a kan su je su ga university da ya yi wa Abdoul a biya mishi ya ci gaba da karatun shi


" Nesrine me ki ke yi a nan kuma ? " ta jiyo Muryar Abdoul ya na fada

A hankali ta juyo ta na kallon shi ta saki dan karamin mais ta ce " Ina kwana "

A tare shi da Moussa su ka amsa mata da lafya kafin Abdoul ya sake maimaita tambayar da ya yi mata

Dan murmushi tayi kafin ta ce " yaya Abdoul dama zan je falo ne na gaji da zama ni kadai cikin daki "

Abdoul na shirin magana Moussa ya riga shi cewa " da sai ki kira ni na zo na taya ki hira ko , tsaya ma , me ya tseda ki saman stair "

Dan sunkuyar da kai ta yi ba tare da ta ce komai ba

Da ya ke Abdoul bai San abun da ke damun Nesrine ba sai ya yi gaba ya na fadin " shikenan sauko yanzu ko "

Wasu yawu ta hadiye kafin ta juya ta daga kafa a hankali ta tako stair din ta na rumtse idanun ta da karfi

Ba shiri ta ji an dauke ta cak kamar baby har sai da ta dan razana

Shi kuma ya na daukar ta ya sauko stair din da ita , sai kallon shi ta ke yi , shi kuma ya na kallon gaban shi

Sai da ya nufi doguwar sofa ya zaunar da ita sama sannan ya kali face din ta ya saki dan karamin murmushi ya ce " ki daina wahalar da kan ki in ki na bukatar wani abu ki kira ni kawai "

Ya na gama fadar haka ya mike ya yi gaba ya fice falon

Duk abin da ya yi a kan idon Abdoul , dan dama bai fita ba , ya shiga dining room ne ya sha ruwa , ya na fitowa ya ga Moussa dauke da Nesrine ya ajiye ta saman sofa


Da sauri Abdoul ya bi bayan Moussa shi ma ya fice su ka bar Nesrine nan zaune ita kadai

Abdoul kuma ya na fitowa ya ga Moussa cikin mota bakin kofar shigowa falon , ya na jiran shi

Geffen mai zaman banza ya nufa , ya bude kofar ya shiga, sannan Moussa ya tada motar su ka bar gidan cikin konciyar hankali


Su na fita gidan Abdoul ya kali Moussa ya ce " na lura kwana biyun nan ka na yawwan zama tare da Nesrine , ko kai ma ka fada in sa malam ya baka ita " ya fada cikin zolaya

Dan karamin murmushi Moussa ya yi ba tare da ya kale shi ba ya ce " kar ka bawa kan ka aiki , already dama ta wa ce "


" ni fa da gaske na ke yi maka "

Kallon shi Moussa ya yi kafin ya ce " ni ma da gaske na ke maka ai , ko malam bai fada maka ba ya aura min ita ? "

Dan zaro idanu Abdoul ya yi ya na kallon Moussa ya ce " wait ! Are you serious ? Abba ya aura maka ita ba tare da sanin mu ba , ita ta sani ma ? "

" ba ta sani ba , ban shirya fada mata ba yanzu gaskia , na fi son har ta manta abun da ya faru, duk da na san zai dauki lokaci "

Cike da shakku Abdoul ya ce " ban gane ba , wane abu kuma ka ke magana a kai ? "

Kallon shi Moussa ya yi kafin ya juya ya ci gaba da kallon titi ya ce " ban gane ba Amir bai fada muku Raping din ta a ka yi ba ? "

Dum Abdoul ya ji zuciyar shi ta buga , har sai da ya fara ganin wani dishi dishi
Ya na dafe saitin zuciyar shi , ji ya ke kamar an aiko mishi sakon mutuwa

Dafa kafadar shi Moussa ya yi ya na fadin " Abdoul lafyar ka kuwa "

Shiru Abdoul ya yi ya kassa cewa wani abu sai zaro idanu ya ke ya na kallon gaban shi

Daga kafadun shi Moussa ya yi kafin ya janye hannun shi ya meda saman steering ya ci gaba da tukin shi


Inaya

Tafiya su ke cikin motar su, babu mai ce ma dan uwan shi uppan , har sai da su ka karaso wani babban private college

Ya na shigowa ya nufi parking space ya yi parking din motar , sannan ya kashe ta ya kali Inaya ya ce " mimi , ki jira ni a nan ba zan dauki lokaci ba "

Da to amsa mishi ta na murmushi , shi kuma ya bude kofar ya fice ya nufi hall din school din

Da kallo ta raka shi har sai da ya kure wa ganin ta sannan ta juyo ta fara bin wajen da kallo

Sai ganin yan mata da samari ta ke su na wucewa su
Matan su na sanye da skert pink colour ya wuce guyiwa da kadan , da Shirt fara mai dogayen hannu , sai da karamin hijab zuwa kirji shi ma white colour
Mazan kuma , wando navy blue da Shirt white , su na sanye da tie navy blue ita ma
Tsarin school din ya yi matukar burge ta , kawai sai ta ci gaba da kallon su , car Zayd ya dawo ya shigo motar ba ta sani ba
Kawai sai ji ta yi ya tada motar

A razane ta kai duban ta gare shi ta na fadin " yaya Zayd wlh ka bani tsoro "

A hankali ya juya motar su ka bar parking space din , su ka kama hanyar fita school din sannan ya ce " tunanin mi ki ke yi da har ba ki ji shigowa ta ba ? "

Dan karamin murmushi ta yi cikin shagwaba ta ce " yaya Zayd, wlh school din nan ya na da kyau sosai "

Da sauri ya katse ta da cewa " ya yi miki kenan "
Gyada mishi kai kawai ta yi, ta na cije

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login