Showing 27001 words to 30000 words out of 75226 words
girgiza kan shi ya ce " no ! No ! Impossible bazai yi yu ba "
Ya na gama fadar haka ya mike tsaye da sauri ya shiga corridor kai tsaye ya wuce bedroom din shi cikin zafin nama ya bude kofar dakin ya shiga
Cak ya tsaya bakin kofar ya na bin dakin da kallo , duk wajen a tirje ya ke , ga pillow duk an zubar da su kassa , an zare bedsheet an tila shi gefe guda
Cen ya hango Inaya zaune a kassa ta saka kan ta tsakanin cinyoyin ta, ga jakar school din ta cen gefe ta tila ta
Tsaya wa ya yi ya na bin dakin da kallo ya na son ya ga Moussa amma ita kadai ya gani
Abun da bai sani ba shi dama Moussa wassa ne ya ke yi mishi dan ya san abokin shi da mugun kishi nan take zai fara bibiyar Inaya duk wane abu da za ta yi sai ya Ankara da shi , dalilin da ya sa ya ke yi mishi wannan abun amma shi gaskia ba son Inaya ya ke ba ko yanzu da ya shiga corridor din bedroom din shi ya shiga ba na Zayd ba
A hankali ya fara takowa cikin dakin har ya karaso inda ta ke zaune shi ma ya zauna gaban ta ya yi irin zaman cin tuwo ya zuba mata idanu, da allamun ba kuka ta ke ba
Sai da ya gaji da kallon ta sannan ya kai hannu shi ya kyasta mata dan yatsun shi biyu saitin kunnen ta
Da sauri ta dago kan ta ta na kallon shi dan ita ba ta ji shigowar shi ba cikin dakin har lokacin da ya zauna gaban ta , duk ta yi nisa cikin tunanin ta
Dan murmushi ta saki kafin ta gyara zaman ta, ta yi irin zaman da ya yi ta sunkuyar da kai ta riko tafin kafarta guda da hannayan ta duka biyu
Ganin ba ta da niyar yi mishi magana ya sa ya kai hannu ya dago habar ta ya na kallon face din ta , sam babu digon hawaye a kai , to me ya faru kennan ?
Ita kuma murmushi kadan ta saki kafin ta ce " yaya Zayd me ya faru ? "
Janye hannun shi ya yi kafin ya girgiza mata kai sannan ya kai hannu ya nuna nata sannan ya mata allamu da hannu " me ya ke damun ki ? "
Sunkuyar da kan ta yi kafin ta ce " yaya Zayd wlh Nesrine ta na yawwan takura min wai na auri kurma kuma makaho duk cikin mazan da ke cikin duniyar nan wai shi na zaba, ban San minene matsalar ta ba , ni na fada mata ina son ka a hakan amma ta ki jin magana har wasu classmate din ta ta fadawa yanzu duk sun bi sun takura min a school , ni wlh in ba ta bani lafya sai na fadawa Abba , shin minene matsalar in baka gani ko baka magana na ga kai ma mutun ne ka na da tsoron Allah , ka na sallat ka na azumi ka yarda da Allah da manzon sa , kuma ka na da zuciya mai kyau , amma ita duk ba ta ganin wannan , wlh ina jiye mata duniya ba ta san abun da zai faru da ita ba nan gaba , sam ba ta ganin darajar mutane , duk abin da na ke son na gwada mata ta ki gani amma a haka wai ta ke ce maka makaho al'halin ita a bata gani "
Tun da ta fara magana ya tsare ta da idanu ya na kallon ta cikin ranshi kuma cewa ya ke " Moussa ya yi gaskia she is so innocente , her heart is so pure , duk zaman da na yi a Nigeria ke ce mace ta farko da ta ce min ta na so na a matsayin makaho kuma kurma al'halin ba haka ba ne , ina ga zan yarda da maganar Moussa na amshi soyayyar ta , muyi sabuwar rayuwa nassan bazan samu wadda za ta zauna da ni tsakanin ta da Allah kamar ke ba "
Kawai sai ganin kan shi ya yi ya saki wani kyawatencen murmushi ya mike tsaye ya juya ya fara takawa ya fice dakin
Ya na fitowa falon ya isko Moussa ya na konce saman sofa ya na latsa wayar shi
Ya na ganin Zayd ya fito ya mike zaune ya na murmushi ya ce " har ka ida rarrashin baby na "
Ko kallon shi Zayd bai yi ba ya sa kai ya fice falon, ya bar gidan baki daya
Tafiya ya ke cikin konciyar hankali ya na taku cike da izza har ya karaso bakin kofar gidan su Inaya, ko me ya zo yi oho !
Ya na shirin shiga gidan Malam ya fito da cikin gidan ya yi shirin tafiya massalaci dan lokacin sallat ya yi
Ya na ganin Zayd ya saki wani kyawatencen murmushi ya mika mishi hannu su ka yi musbaha sannan ya ce " a'a malam Zayd yau kai ne a gidan na mu haka , ina fatan ba dai laifi autar tawa ta yi maka ba "
Girgiza mishi kai Zayd ya yi kafin ya ce " no ba maganar ta ba ya kawo ni gidan nan uncle ! "
" toh , lafya kuma ? Maganar mi ta kawo ka in haka ne ? " malam ya fada ya na tsare shi da ido
Sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " uncle ina so in san dalilin ka na aura min Yarinyar nan al'halin ba ka san ko ni wanene ba ka san kowa nawa ba za ka dauki d'iyar ka ka bani ita haka kawai "
Dan murmushi malam ya yi kafin ya ce " Zayd na fada maka in lokacin ya yi za ka sani amma tun da ka matsa bara na fada maka wani dan karamin abu saman ta , Inaya da ka ke gani ba kamar kowane mutun ba ta ke , akwai wata baiwar da Allah ya yi mata wadda ko ita ba ta san da ita ba , a kan wannan baiwar a ke bibiyar rayuwar ta , abu guda ne zai iya sa ta iya gane ta na da wata baiwa har ta iya anfani da ita shi ne ta hanyar aure , kafin mu baro kaduna wasu azaluman mutane sun so su yi anfani da ita wajen mugayan manufar su , dalilin da ya sa na aura maka ita kenan, dan kar su samu damar cin ma manufar su , ni nassan har yanzu su na bibiyar rayuwar mu su na neman inda mu ke amma ka ga cikin wani ikon Allah har yanzu ba su gano inda mu ke ba , kai baza ka dalilin hakan amma ni na sani abu guda zan roke ka , ka kula min da yarinya ta dan rayuwar ta na da matukar mahimanci musaman a cikin rayuwar ka "
Jinjina kan shi kawai Zayd ya yi ya na son ya ji wace irin baiwa ce haka wadda za ta sa ka a dinga bibiyar rayuwar mutun haka , to su da su ke bibiyar ta me su ke so da ita ? Ko kuma wannan baiwar da malam ke fada ita ce dalilin da ya sa ta ke wasu abubuwa kamar karamar yarinya ? Ya kamata ya ji micece wannan baiwar
" uncle zan so na ji wace irin baiwa ce wannan wadda zai sa a dinga bibiyar ku haka ? " Zayd ya tambayi malam
Murmushi malam ya yi kafin ya ce " Zayd bazan iya fada maka ba , amma zan so ka sani , Inaya ba ta tune da rayuwar mu ta baya , ko za ka bude baki ka tambaye a ina mu ka yi rayuwa kafin mu dawo kano baza ta iya fada maka ba , amma idan ka tambaye ta wani abu saman ka, ko da abun ya yi shekara 20 sa wucewa za ta fada maka shi har ma wanda ba ka sani ba , amma hakan bazai yiyu ba har sai kun zama abu guda "
Daga gera guda Zayd ya yi cikin zuciyar shi ya ce " kennan madubiya ce ko kuwa ? "
A fili kuma ya ce ma malam " amma uncle ya za ayi ta manta rayuwar ta, amma ta san rayuwar wasu ko kuma amnesia ce ? "
Dariya malam ya yi kafin ya ce " yo malam Zayd kai ka san minene hakan dan ni ban yi boko ba, yanzu dai mu tafi lokacin sallat ya yi kar mu rasa jam'i "
Malam na shirin tafiya Zayd ya yi saurin cewa " uncle ina son nayi magana da Nesrine kafin mu tafi "
Juyowa malam ya yi ya na kallon cike da tambaya, ko dalilin mi ya ke son magana da Nesrine ? Ya tambayi kan shi
Shi kuma Zayd ya tsaya ya zuba mishi idanu ta cikin glass din shi ya kassa yi mishi magana
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 12 ❤🔥
Murmushi kadan malam ya yi kafin ya juyo ya nufi cikin gidan ya na fadin " mu je to bara na kira maka ita "
Ba musu ya bi bayan shi su ka shiga cikin gidan malam na sallama , dai'dai lokacin da Abdoul ya fito da ga cikin dakin shi sanye da jallabiya fara allamun shi ma massalacin za shi
Ya na ganin Zayd ya saki murmushi ya ce " a'a yau ango ne a cikin gidan na mu " ya fada cikin zolaya
" kai dan Allah ya isa haka je ka kirawo min Nesrine ya na son magana da ita " malam ya fada mishi
Ba musu ya taka ya shiga bedroom din Nesrine ya na sallama
Ya na shiga mama ta fito da ga cikin toilet ta na rike da buta
Ta na ganin Zayd a tsaye geffen malam ya rike hannayan shi a baya ya na kallon gaban shi
Ta saki murmushi ta karaso wajen ta na fadin " malam Zayd sai yau a ka yi niyar dawowa gidan na mu ? "
Ko kallon inda ta ke bai yi ba ya ci gaba da tsayuwar shi
Ta na gama rufe bakin ta Abdoul ya fito da ga cikin bedroom din Nesrine ya karaso geffen mama ya tsaya ya na fadin " ga ta nan " ya kai karshen ya na nuna kofar dakin
Ya na rufe baki Nesrine ta fito da ga cikin dakin ta na sanye da hijab blue har zuwa kassa ta karaso ta tsaya gaban shi dan nesa kadan ta na fadin " gani Abba lafya ya ke nema ta ? "
Daga kafadun shi malam ya yi kafin ya ce " ni ma ban sa ni ba , Zayd ga ta an kira maka ita " ya kai karshen ya na dawo da kallon shi kan Zayd da ya zubawa Nesrine ido
Shi kuma Zayd sai da ya dauki lokaci kafin ya tako a hankali cike da izza ya tsaya gaban Nesrine ya zuba mata ido ta cikin glass din shi
Sai da ya dauki wajen good two minutes kafin ya kai hannu slowly ya zame bakaken glass din shi
Dum Nesrine ta ji gaban ta ya fadi dan ba karamar razana ta yi ba da ganin wadanan hazel eyes din na shi ga shi sai wani kyali su ke saboda hasken rana
Ta na a haka ta jiyo wannan zazzakar Muryar ta shi ya na fadin " ban san abun da na yi miki ba da ki ka tsane ni haka , a sani na tun lokacin da ku ka shigo gidan nan ko kalma daya ba ta taba shiga tsakani na da ke amma yau sai da ki ka sa na yi miki magana ba da so na ba , kamar yadda ki ke ji ni ba kurma ba ne ina magana kamar yadda ki ke magana sannan kuma ina ganin ki kamar yadda ki ke gani na a tsaye gaban ki , ban zo gidan nan dan na fada muku ko ni wanene ba , na zo ne dan na fada muku dalilin da ya sa ku ke min kallon makaho da kuma kurma , shekara biyar kenan da na zo Nigeria kuma a nan kano na sauka , Lokacin da na shigo Garin nan ba na jin haoussa da ga turanci sai larabci kuma ba kowa ba ke jin su dalilin da ya sa na dinga yin shiru dama cen ni ba ma'abocin magana ba ne shi ya sa duk wata magana da zan yi sai dai na yi ta da hannu in kuma tambaya ce na girgiza kai a haka har mutane su ke min daukar kurma kuma kuka zo ku ka same ni a hakan, sannan kallon makahon da ku ke min na san ya samo nasaba ne da bakaken glass di na da na ke sanye da kullum, ina saka su ne saboda nassan a nan Africa ba kowa ba ke da colour din idanu na hakan na tsoratar da mutane su na yi min wani kallo cen daban dalilin da ya sa na ke saka su , sandar da ki ka ga ina yawwan rikewa kuma "
Ya kai karshen ya na sa hannu shi cikin aljihun shi ya fido wani dan abu kamar remote
Ya na danna shi nan take abun ya yi wata kara ya kara tsayo ya koma kamar sanda
Sannan ya sake danna button din sandar ta koma kamar da farko
" ba sanda ba ce kamar yadda ki ke tunani , duk wani mumunar zato da ki ke yi a kai na yau na tabbatar miki da ba gaskia ba ne , zan so nan gaba ki fara sannin wanene mutun kafin ki kaskantar da shi , da zan fada miki ainahin wanene ni to za kiyi mamaki ki tambayi kan ki abun da ya kawo ni nan amma bazan fada miki ba nassan wannan karamar kwakwolwar ta ki baza ta dauka ba amma ki sani ba sunana Zayd ba duk ranar da ki ka samo sunana na gaskiya ki zo ki fada min zan baki kwatar dukiyar da ko jikokin jikokin ki sai sun ci albarkacin ta " ya na gama fadar haka ya meda bakin glass din shi ya juya ba tare da ya ce komai ba ya bar gidan
Nan ya bar Nesrine baki sake tun lokacin da ya fara magana ta na zaro idanu
Sai da ya fita sannan ta kali mama ta kali malam
Ta na shirin magana Abdoul ya riga ta cewa " Nesrine me ki ka ma Zayd kuma "
Cike da mamaki ta ce " yaya Abdoul ba ka mamakin yadda yaya Zayd ke magana ko dai kunnuwa na ne "
Malam ne ya bata amsa da cewa " ba kunne ki ba ne Zayd ya na gani kuma ya na magana , a sani na bai taba bude baki ya ce miki shi kurma ne ko makaho ni ban san me ki ka mishi ba amma zan tambaye shi , kai Abdoul wuce mu tafi massalaci " ya kai karshen ya na juyawa ya fita gidan
Shi ma Abdoul takawa ya yi ya bi bayan shi su ka bar gidan su ka bar mama da Nesrine nan tsaye sai faman muzurai su ke
Sai yanzu Nesrine ta tuno da kalamun Inaya da ta ke ce mata " wai Nesrine wa ya fada miki yaya Zayd kurma ne , ko kuma shi ya fada miki shi makaho ne " kennan Inaya ta san cewa ba makaho ba ne shi ya sa ta ke son shi ? Ko kuma ya zancen ya ke ?
Nesrine na shirin magana mama ta riga ta cewa " kar ki tambaye ni abun da ki ka ji shi na ji " ta na gama fadar haka ta wuce ta shiga dakin ta
Ita ma Nesrine ta juya ta koma dakin ta zuciyar ta na duka uku uku kamar ta ga abun tsoro
Inaya
Ta na jin ya fara takawa ya bar dakin ta dago kai ta bi bayan shi da kallo har sai da ya fita dakin sannan ta mike tsaye ta gyara komai na cikin dakin sannan ta shiga ta yi wanka ta shirya cikin wandon palazzo pink colour da riga zuwa guyiwa white colour ta saka dan karamin hijab zuwa kirji
Falon gidan ta fito nan ta ga babu kowa duk sun fice , sai ta wuce kai tsaye kitchen dan ta shirya musu abinci
Misalin karfe 5 na yamma ta Kamala girkin ta shirya komai saman dining table sannan ta gyara gidan tsab har da bedroom din Moussa ta wanke toilet din dakin , har da harabar gidan sai da ta fito ta share sannan ta koma ta feshe gidan da turare
Wajen kiyaye²n sallar magriba ta koma dakin ta ta yi wanka ta dauro Alwalla sannan ta sauya kayan jikin ta ta saka gown mara nauyi purple sannan ta saka hijab har kassa shi ma purple sannan ta gabatar da sallar ta , bayan ta gama ta zauna yin karatun kur'ani , ba ta Kamala ba sai da a ka yi kiran sallar isha ta tashi ta gabatar da sallar
Misalin karfe 8 na dare
Ta na