Showing 45001 words to 48000 words out of 75226 words
" ka yi hakuri ka sada mu da shi maganar ta na da mahimanci sosai "
Fir officer din ya ki ya ce " na fada muku duk karar da za ku shigar ni za ku fada ma DPO ba shi da lokacin kananan case "
Cikin bacin rai Zayd ya ce " an fada maka karamin case ne ya kawo mu , kanwa ta fa ta bata, ina son magana da DPO now ! " ya kai karshen ya na buga desk din da karfi
Da sauri sauran officer din su ka karaso wajen su na fadin " kai malam nan fa ba gidan ku ba ne , ka yi a hankali ko kuma na sa ka cell "
Tsaki Zayd ya ja ya kauda kan shi gefe kafin ya juya a hankali ya fice da ga cikin police station din
Ya na barin wajen malam ya matso ya ce da officer din " yi hakuri yaro zuciya ce ta debe shi , mun zo shigar da kara a kan batar yarinya ta, tun jiya da safe a ka aike ta har yanzu ba ta dawo ba "
Cikin ko in kula ya ce " ya wuce ta bi saurayin ta sun tafi yawon cin duniyar su ku na nan kun damu a kan ta , ta na cen ta cin dadin ta " ya kai karshen ya na dariya
Su ma sauran officer din su ka bushe da dariya
KAI JAMA'A YANZU KO GIRMAN MALAM BAI GANI BA DA YA FADI HAKAN 😔😔
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 20 ❤🔥
Maganar ba karamin bata musu rai ta yi ba , da Zayd na wuri ya yi maganar da tuni zuciya ta debe shi ya musu dukan mutuwa , shi fa Zayd irin mutanan nan ne da ba su son raini duk girma kan idan ka ce za ka raina shi to wlh sai dai a dauki gawar ka , dalilin da ya sa ba ya sakewa Inaya fuska dan kar ta ga ranar shi raini ya shiga tsakanin su
Su na tsaka da dariyar su DPO ya fito da ga cikin office din shi ya na sanye da kakin su na soja , ba laifi ya dan lattijantaka , ya na da kyasumba amma ba sosai ba ya na sanye da hular su irin ta sojawa ba a iya ganin gashin kan shi , fuskar shi babu yabo babu falassa
Su na ganin shi kowa ya shiga tai'tayin shi , duk su ka sara mishi su na fadin " sir! "
Bai bi ta kan gaisuwar su ba ya ce " dariyar me ku ke yi haka ? "
Da sauri daya da ga cikin su ya ce " ba komai sir " ya fada cikin girmamawa
Jinjina kan shi ya yi kafin ya kali daya da ga cikin officer din da ke tsaye bakin kofar office din shi ya ce " PDG din Shell Petrolium ya na waje , je ka mishi iso zuwa office di na "
Ya na gama fadar haka ya juya zai koma office din shi , officer din kuma ya mike zai fita
Har ya yi nisa ya jiyo DPO ya na fadin " ya na sanye da jeans black da t-shirt white " sa ga haka ya shige office din shi officer din ya fice
Ya na fita Moussa ya dafe forehead din shi ya ce " Amirrrr ! Ba dai kiran DPO kai tsaye ka yi ba ? "
Da sauri malam ya kaleshi ya ce " me ka ke nufi Moussa "
Cike da rudu Moussa ya kali malam ya na zaro idanu shi ya ma manta da su na tare da malam
Officer din kuma bayan ya fito harabar police station Ya duba dama ya duba hagu bai ga kowa ba
Har ya juya zai koma ya hango wani mutun cen nesa tsaye ya bashi baya ya na sanye da jeans baki da t-shirt fara kamar yadda DPO ya fada mishi ya sunkuyar da kai ya na latsa wayar shi
A hankali officer din ya tako gare shi ta bayan shi ya tsaya ya sara mishi ya ce " Good morning sir "
Ko juyowa Zayd bai yi ba bare ya amsa mishi ya ci gaba da latsa wayar shi
Ganin bai amsa mishi ba ya sa officer din cewa " sir DPO n........" kut maganar ta yanke sakamakon juyowa da Zayd ya yi ya fara takawa ya bar wajen
Officer din sumar tsaye ya yi kennan shi ne PDG din Shell petrolium, tun dazu ya ce ya na son magana da DPO amma su ka raina mishi hankali , yanzu zai iya kai kararshi gaban DPO ma kuma ta zauna shikenan an koreshi ?
Da sauri ya juya ya bi bayan Zayd da har ya kusa shiga police station din
Kafin ya shiga ya tarbo shi ya mara mishi baya
Babu ko sallama Zayd ya shigo police station din kai tsaye ya na sanye da bakin glass din shi , ya rike hannayan shi a baya , ya nufi office din DPO
Officer din nan na farko na ganin shi ya matse fuska ya ce " kai gidan ku ne nan da za ka shigo babu ko sallama "
Da sauri officer din da ke bayan Zayd ya girgiza mishi allamun ya yi shiru
Malam da Abdoul na ganin irin shigowar da ya yi duk su ka bi su ka rude sun ka ce anya wannan Zayd ne , dan fa nan kwarjinin shi ya karu fiye da farko taku ya ke cike da izza da isa kamar shi ne president din Nigeria baki daya
Su na isa bakin kofar office din , DPO ya fito ya na murmushi ya mikawa Zayd hannu ya ce " welcome sir ! "
Kallon hannun DPO ya yi kafin ya dago kai ya kali Moussa , ya juya ya shiga office din DPO ya bar shi nan tsaye
Da sauri Moussa ya karaso wajen ya riko hannun DPO su ka yi musbaha ya na murmushi ya ce " Sorry DPO bai cika gaisawa da mutane ba ne "
Murmushi DPO ya yi kafin ya " ai ba komai na san labarin sir Latif , mutumin da ba kowa ya taba ganin shi ba ai ban yi mamakin haka ba , bismillah mu shiga da ga ciki "
Murmushi Moussa ya yi kafin ya jinjina kan shi ya shiga office din , DPO ya bi bayan shi
Su na shiga Abdoul ya kali malam baki sake ya ce " Abba wai wanene wannan ba dai Zayd din da muka sani wajen shekara biyar , shi ne mamalakin babbar company ta sayar da bakin oil a Nigeria baki daya ba "
Malam na shirin magana daya da ga cikin officer ya riga shi cewa " yanzu ku na nufin ba ku san shi ne PDG din Shell petrolium "
Officer din da ya tarbe su da farko ne ya amsa mishi da cewa " kai dan Allah matsa , kai yanzu duk Nigeria ka taba jin wanda ya fito ya ce maka ya taba ganin shi , ko kuma DG din shi , duk wani taro da za ayi ba su zuwa duk wata magana da za su yi da yan jarida ta voice call su ke yin ta , ko kwangila ka kai musu iya kar ka da ga manager din su , shi zai kai musu file din kwangilar ka in sun yarda manager din nan sai zai fada maka , mutane nawa su ka yi aiki da shi amma ba wanda zai fito ya ce maka ga kamanun shi , kai karewar zancen ko his excellency da ya nemi zama da shi manager din shi ya je a madadin shi , wannan mutumin ya tara uban kudade dole ganin shi ya zama kamar kallon rana "
HMMM A HAKAN MA BA KU SAN AINAHIN ASSALIN SHI BA AMMA MU JE ZUWA 😌😌
Kallon malam Abdoul ya yi baki sake ya na shirin magana su ka ga Zayd ya fito da ga cikin office din DPO
Su na ganin shi duk officer din wajen su ka mike su na sara mishi
Ko kallon su bai yi ba ya ficewar shi
Da kallo malam da Abdoul su ka raka shi har ya fita sannan su ka kali junan su
Ya na fita Moussa ya fito shi ma DPO na biye da bayan shi
Sai da su ka ida maganar su sannan Moussa ya karaso wajen su malam ya ce " uncle mu tafi " ya na fadar haka ya yi gaba
Da sauri malam da Abdoul su ka bi bayan shi su ka bar police station din baki daya
Su na barin wajen DPO ya kali officer din wajen ya ce da su " zan turo ma kowanan ku hoton wata yarinya, nan da two hours ina son in gan ta cikin office di na, ku nemo ta duk inda ta ke "
Sara mishi su ka yi baki daya su na fadin " okay sir ! "
Bai tsaya basu amsa ba ya juya ya koma office din shi
Tafiya su ke saman hanya su na a jere malam, Moussa da Abdoul , Zayd kuma ya na cen gaban su ya na rike da hannayan shi a baya ya na taku cike da nitsuwa
Sai da su ka yi tafiya mai dan nisa kafin malam ya kali Moussa ya ce " Moussa , in shi ne assalin sunan ka , wanene Zayd ko in ce Latif dan yanzu na fara tantama a kan ku "
Murmushi Moussa ya yi kafin ya daga kai ya kali Zayd su na ci gaba da tafiyar su ya ce " gaskia ne uncle Moussa ba shi ne cikaken suna na ba , sai dai ku yi hakuri bazan iya fada muku komai ba a kan mu , amma zan fada maka , Zayd da Latif duk ba su ba ne cikaken sunan shi ba , ya yi anfani da sunnan latif lokacin da muka bude company din mu , Zayd kuma dan in ya ce sunan shi latif mutane za su dinga dangan tashi da PDG din Shell petrolium shi ya sa ya ke sauya sunaye a waje daban daban , kuma personallity din shi ke sauyawa tare da sunnan , amma da za ku san wanene ainahin Zayd ko daga kai baza ku yi ku kaleshi ba , duk cikin kassashen duniya babu wadda ta fi karfin Zayd ya je cen ya yi rayuwar shi yadda ya ga dama amma kaddarar shi ta kawo shi Nigeria , kaddarar shi ta haduwa da yarinyar ku , har aure ya shiga tsakanin su , ku godewa Allah da ya hada Zayd da yarinyar ku uncle dan ba kowace mace a duniya za ta samu irin wannan damar ba "
Ya na gama fadar haka ya yi sauri ya yi gaba dan ya kamo Zayd
Kallon Abdoul malam ya yi kafin ya ce " Abdoul ni fa yanzu na fara tambayar kai na a kan assalin Zayd "
" Abba ba ku kadai ba, ni ma ina tambayar kai na , amma babu mai ba mu amsa " ya kai karshen ya na dawo da kallon shi kan Zayd
Dai'dai lokacin da Moussa ya kamo shi
Ya na isowa geffen Zayd , Moussa ya kaleshi ya ce " Amir me ya sa za ka kira DPO kai tsaye , yanzu uncle sai da ya tambaye ni a kan ka "
A hankali Zayd ya juya kai ba tare da ya tsaya da ga tafiyar shi ba ya kali malam kafin ya juyo ya kali gaban shi ya ce " zan fada mishi amma ba yanzu ba , ka kira manager ka ce ya tura a gyara gidan mu na Abuja cen za mu koma da zama har da su malam "
Cak Moussa ya tsaya da tafiya ya na kallon Zayd ya na maimaita abun da ya fada cikin kwakwolwar shi
Sai da ya dan jima kafin ya ci gaba da tafiyar shi a haka har su ka karaso gidan malam
Nan Moussa ya tsaya ya juya ya ce da malam duk abun da DPO ya sanar da su za su kira shi su fada mishi
Da to malam ya amsa mishi kafin ya shiga cikin gidan, su ka yi sallama shi da Abdoul
Sannan ya juya ya kama hanyar gidan su , cen ya hango Zayd har ya isa bakin kofar gidan ya tura kofa ya shiga
Gyada kan shi Moussa ya yi kafin ya ci gaba da takawa ya iso gidan shi ma shiga
Bakin shi dauke da sallama ya shigo falon gidan
Cen kassan makoshi Zayd ya amsa mishi sallamar shi ya na zaune saman sofa ya zubawa Inaya idanu ta cikin glass
Geffen shi Moussa ya karaso ya zauna ya kaleshi sannan ya kali Inaya ya ce " lafya ka kura mata ido haka "
Ba tare da ya juyo ya kaleshi ba ya ce " nothing " ya fada a takaice
Dan murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " wai har yanzu ba ka shirya daukar ta a matsayin matar ka ba ? "
" never, bari ma wannan zancen , yarinyar nan fa ko period ba ta fara ba "
Salati Moussa ya yi ya na kama habar shi ya ce " Amir yanzu yarinyar nan ido ka saka mata har ka san ba ta fara period ba "
" ni ban saka mata ido ba , kawai abun da na gani ne na fada maka "
" okay kennan in ta fara period za ka dauke ta a matsayin matar ka "
Sai da ya dan dauki lokaci kafin ya ce " i don't know "
Hararrar Moussa ya yi kafin ya ce " you'll know very soon , Idan mun koma masarauta a ka matsa maka sai ka auri diyar sarkin Rouma za ka gane kuran ka " ya kai karshen ya na dariya
Juyo da kan shi ya yi ya kali Moussa ya ce " wai wa ya fada maka zan koma "
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 21 ❤🔥
Da sauri Moussa ya tsagaita dariyar shi ya ce " ban gane , Amir wai ka na nufin baza ka koma gida ba, me ya sa abun da ya faru ya riga da ya wuce "
Katse shi Zayd ya yi da cewa " Diya na sani , kuma har ga Allah ina kewar Ammie da mamie da kuma Tesnim amma zuciya ta bata yarda na koma ba , ina ji idan na koma wani mugun abu zai faru wanda ya fi na farko , ina jin tsoron komawa ta ga ahali na ya janyo musu assarar sa bazan maye gurbin ta ba , Diya ka fi kowa sanin Mai martaba a ka so a kashe ba ni ba , akasi ne kawai aka samu ranar ni na kwana a part din shi , da yanzu na san shi zai mutu a madadi na , dalilin da ya sa su ka kyale shi yanzu dan sun san ba shi da wanda zai gaje shi , ko ba su kashe shi ba in lokacin shi ya yi dole zai tafi su zauna saman karagar mulkin "
Dafa kafadar shi Moussa ya yi kafin ya ce " na sani Amir , amma dole ka koma ka karbi kujerar ka , yanzu ka na ji ka na gani wani zai zauna saman gadon ka , Amir kai kade ne fa magajin Daular saudiya tsawan shekaru sama da dari biyu duk sarkin da ya hau karagar muliki ba zai taba haifuwar da namiji ba , cikin wani ikon uban giji mai martaba ya same ka , ba ka ji sunan ka ba Nawfel , kyauta mai daraja , ba a banza a ka saka maka wannan sunnan ba "
Jingina bayan shi Zayd ya yi a jikin sofar ya lumshe idanun shi ya ce " Diya na san wannan duka, amma ba yadda zan yi kassan ba zan iya tafiya na bar yarinyar nan ba ko "
Ya kai karshen ya na bude idanun shi ya kali Inaya da ta sharar barcin ta kamar babu ita a wajen
" shikenan yanzu ina son ka fada min za ka koma masarauta ko kuma ba za ka koma ba " Moussa ya tambaye shi
Dawo da kallon shi ya yi kan Moussa kafin ya ce " za mu koma Diya, za mu koma amma ba za mu zauna ba , tafiyar tsaye za mu yi "
Ya na gama fadar haka Inaya ta fara motsi ta na son tashi
A tare shi da Moussa su ka dawo da kallon su saman ta
A hankali ta ware idanun ta , ta fara karanto adu'ar tashi da ga barci , ta fara bin wajen da kallo
Idanun ta na sauka kan Zayd ta