Showing 24001 words to 27000 words out of 75226 words
jeans light blue da t-shirt fara sannan ya fice dakin
Kai tsaye dakin Moussa ya wuce babu ko sallama ya shigo dakin kai tsaye ya wuce toilet
Shi kuma Moussa sai kwana ya ke da ga shi sai short ko shigowar Zayd bai ji ba , sai da ya fara jin saukar ruwa sannan ya bude idanun a hankali ya na motsi
Kallon kofar toilet din ya yi ya ga dakwai dan haske
Murmushi kadan ya saki kafin ya fara karanto adu'ar tashi da ga barci ya mike zaune .............................
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 10 ❤🔥
After some minutes ya fito sanye da kayan da ya dauko da ga bedroom din shi
Kallon shi da kyau Moussa ya yi kafin ya ce " ango ! Me kuma ya kawo ka toilet di na "
Ko kallon shi Zayd bai yi ba ya sa kai ya fice bedroom din
Ya na fita Moussa ya mike ya na dariya ya shiga toilet shi ma
Inaya
Misalin karfe 6 ta farka da ga barcin ta
Ta na bude ido ta fara bin dakin da kallo ,
Sai da ta dan dauki lokaci sannan ta mike zaune ta sauko kafafun ta kassa sannan ta mike tsaye ta fara takawa ta nufi toilet
Bai fi five minutes ba da shigar ta toilet ya shigo dakin ya na sallama a tunanin shi ta farka
Sai ya ga dakin ba kowa ga kuma karar ruwa
Sai ya tako bakin gadon ya zauna ya kai saman drawer ya dauki bakin glass din shi ya sa , ya sunkuyar da kan shi kassa
Bayan wasu mintina
Ya na zaune a haka ta fito da ga cikin toilet din ta na daure da towel a kirjin ta
Ta na ganin shi ta saki murmushi , a hankali ta tako wajen trolley din ta ta bude ta dauki uniform din ta
Har ta juya za ta koma toilet wata zuciyar ta ta ce mata " ina kuma za ki koma mutumin da ba gani ba ya ke "
Daga kafadun ta ta yi ta na turo baki nan na ta gaba ta koma ta ajiye kayan na ta saman trolley
Sannan ta kai hannu zame towel din jikin ta, ta koma naked
Hum kamar an ce mishi Zayd dago kai haka ya dago kai dai'dai lokacin da ta saki trolley din ya fadi kassa ta duka ta dauki pant din ta
Da sauri ya rumtse idanun shi ya kauda kai gefe cikin ranshi ya ce " na shiga uku ni Nawfel ba ta ga da mutun ne cikin dakin ko ita ma ta koma makafniya "
Tsab ta shirya war ta cikin uniform din ta, ita ta ma manta da mutun a cikin dakin
Sai da ta gama shiryawa sannan ta dauki towel din da ta yadda kassa ta meda shi toilet sannan ta fice dakin
Duk takun ta ya na jin ta amma ya ki bude idanu ya na tsoron ya sake bude su ya yi arba da ilahirin surrar jikin ta
Sai da ya ji ta bude kofa ta fita sannan ya bude idanun shi slowly ya kali saitin kofar ya sauke ajiyar zuciya mai karfi
Inaya kuma bayan ta fita kitchen ta wuce ta shirya musu breakfast
Sai wajen karfe 7 cib sannan ta baro kitchen din ta shirya musu komai saman dining table sannan ta koma bedroom din ta
Ya na nan zaune inda ta bar shi ko motsi bai yi ba
Bakin ta dauke da sallama ta shigo dakin
Cen cikin zuciyar shi ya amsa mata
A hankali ta tako gaban shi ta tsaya sannan ta Zube saman guyiwowin ta ta ce " ina kwana yaya Zayd "
Jinjina mata kai kawai ya yi bai ce mata komai ba
Murmushi ta yi kafin ta mike ta nufi trolley din ta, ta dauki hijabin ta ta saka ta dauki school bag din ta sannan ta dawo gaban shi dan nesa kadan ta ce " yaya Zayd zan biya wajen Nesrine sai mu ta fi tare "
Jinjina mata kai ya yi kafin ya sa sannu shi cikin aljihun wandon shi ya ciro gudi yan dubu dubu sun kai goma sannan ya mika mata
Dan zaro idanu ta yi ta na kallon kudin ta na tunanin ina ya sami wadanan kudade duka
Ganin har yanzu ba ta karba ba ya sa shi dago kai a hankali ya kale ta
Da sauri ya rumtse idanun shi dan ya tino kallon da ya yi mata ta na naked
Ita kuma ba ta lura ba da ya datse idanun shi ba dan ya na sanye da glass bakake
Ajiyar zuciya ta sauke ta yi murmushi kafin ta ce " yaya Zayd ka barshi kawai "
Girgiza mata kai ya yi ya mike tsaye ya tako a hankali gaban ta ya kara mika mata kudin
Wannan karan ba yadda za ta yi sai da ta karba ta na yi mishi godiya sannan ta saka su cikin bag din ta
Sai da ya ga ta sa kudin cikin jakar ta sannan ya juya ya fice
Da sauri ta bi bayan shi ita ma ta fito dakin
A nan falo su ka isko Moussa ya na zaune saman sofa ya na latsa wayar shi
Ya na dago kai ya gan su ya saki dan murmushi ya ce " baby na har kin fito ? "
Sunkuyar da kai kassa ta yi ta na fadin " ina kwana yaya Moussa "
" lafya lau baby na , sa fatan wannan jarabbaben bai takura miki ba " ya kai karshen ya na medo da kallon shi kan Zayd da ya zauna saman sofa da ke fuskantar tashi
Girgiza mishi kai tayi kafin ta ce " yaya Moussa na shirya muku breakfast din ku , ko ku na bukatar wani abu ne ? "
Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce " no baby hakan ma ya isa , sai kin dawo Allah kiyaye hanya "
Da amine ta amsa mishi sannan ta fara takawa ta fita falon
Ya na jin ta fita ya sa hannu ya janye glass din shi ya ajiye su geffen shi ya zubawa Moussa wadanan hazel eyes din shi
Sarai Moussa ya lura da shi amma ya yi banza da shi ya tashi ya nufi dining room ya fara breakfast
Inaya
Bayan ta fita gidan ta fara tafiyar ta cikin minti biyar ta iso gidan su
Da sallama ta shigo cikin gidan
Mama na zaune bakin kofar dakin ta , dai'dai lokacin da Nesrine ke fitowa da ga dakin su ta na sanye da uniform ita ma
Ta na ganin Inaya ta saki wani kyawatencen murmushi da gudu ta je ta rungume ta ta na fadin " na yi kewar ki sosai "
Rungume ta ita ma Inaya ta yi ta na murmushi
Cen su ka tsinci Muryar mama ta na fadin " toh malama kin sake ta, ta zo ta gaishe ni ko ? "
A tare su ka yi dariya su na raba jikin su da na juna sannan Nesrine ta riko hannun ta su ka nufi mama
Ta na isa mama ta bude mata hanayan ta akan ta zo
Ba musu ta fada jikin ta ta na murmushi ta ce " ina kwana mama ? "
" lafya lau autar mama ya ki ke komai dai'dai ko " ta fada ta raba jikin ta da na Inaya
Kallon ta da kyau mama ta yi cike da mamaki ta ce " ban gane ba school za ki koma tun wuri haka "
Murmushi Inaya ta yi kafin ta ce " eh mama yaya Zayd da kan shi ya sayo min uniform ki na gani ? " ta kai karshen ta na juyawa
" shikenan sai kun dawo " mama ta fada ta na murmushi
Hannu Nesrine ta kamo su ka juya ta ce " mu tafi "
Jinjina mata kai Nesrine ta yi kafin ta juya su fara takawa su ka bar gidan
A tare su ke tafiyar su cikin konciyar hankali su na tafe su na hira gwanin ban sha'awa
Sai da su ka kawo bakin kofar college din , Inaya ta ga masu sayarda kayan marmari
Da sauri ta saki hannun Nesrine ta nufi guda da ga cikin su
Karasowa wajen Nesrine ta yi ta kai hannu ta daura a kafadar ta ta na fadin " to sarkin ciye² me kuma za ki saya "
Kallon ta Inaya ta yi sannan ta ce " Apple mana , ina marmarin Apple sosai wlh "
Ta kai karshen ta na meda kallon ta kan mai sayarwar ta ce da shi ya saka mata Apple shida ta na kai hannu cikin jakar ta, ta ciro kudin da Zayd ya bata
Zaro idanu Nesrine ta yi ta na kallon kudin cike da mamaki ta ce " ke Inaya ina ki ka samu uban kudi haka ? "
Ba tare da ta kaleta ba ta na kokarin ciro dubu biyu ta bawa mai sayarwa ta ce " yaya Zayd ne ya bani " ta kai karshen ta na karbar ledar Apple din ta juyo ta kali Nesrine ta ce " mu tafi ? "
Ba musu su ka juya su ka shiga cikin college din su na tafe su na hira har sai da su ka kai bakin kofar class din su sannan su ka rabu
After some hours
Zaune su ke saman chair din cafeteria , Inaya sai faman cin Apple ta ke ,Nesrine kuma na kallon ta ta na murmushi
Sai da ta kusa kamalawa ta dago kai ta kali Nesrine , murmushi kadan ta yi kafin ta mika mata Apple din hannun ta ta ce " za ki ci ne ? "
Girgiza mata kai Nesrine ta yi ta na murmushi ta ce " a'a ci kayan ki babyn Zayd "
Daga kafadun ta Inaya ta yi ta ci gaba da cin Apple din ta hankali konce
Sai da Nesrine ta ga ta Kamala sannan ta ce " Inaya zan so na tambaye ki wani abu "
Jinjina mata kai Inaya ta yi ta na fadin " wane abu kuma ? "
Ajiyar zuciya Nesrine ta sauke sannan ta ce " da gaske ki na son yaya Zayd , a yadda ya ke hakan ba ya magana kuma ba ya gani ? "
Murmushi kadan Inaya ta yi kafin ta jinjina mata kai allamun e
" why Inaya ? Ki duba duk mazan da ke cikin duniya , ki rasa wanda za ki so sai kurma kuma makaho "
" wai Nesrine wa ya fada miki yaya Zayd kurma ne , ko kuma shi ya fada miki shi makaho ne " Inaya ta fada cikin bacin rai
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 11 ❤🔥
Dan zaro idanu Nesrine ta yi ta na kallon ta cike da tantama ta ce " wai Inaya me ya ke damun ki ne , inda ya na magana duk shekaru hudun nan da mu ka yi tare da shi me ya sa ko kalma daya ban ji ta fito da ga bakin shi ba , kennan a haka ku ke rayuwa cikin gidan na shi , kennan rayuwa da kurma na yi miki dadi ? "
Mikewa tsaye Inaya ta yi ta dauki jakar ta ta na fadin " kin ga Nesrine ban san me ya sa ba ki son yaya Zayd ba, ni fa ina son shi a haka kuma duk abun da za ki fada bazai sa na daina son shi ba , ku duka kallon kurma da makaho ku ke yi mishi amma ai ni ina gane abun da ya ke fada kuma da makaftar tashi ya ke aiki , kin ga ya fi karfin a ce mishi makaho kin ga idan ba za ki fadi abun al'heri a kan yaya Zayd ba ki daina yi min magana "
Ta kai karshen ta na juyawa za ta bar wajen kawai sai ta ji ta bugi mutun
Dan bayan kadan ta ja ta dago kai ta kaleshi ta ce " sorry "
Murmushi kadan Moctar ya yi kafin ya ce " ba komai "
Da sauri ta raba ta geffen shi za ta wuce
Da sauri ya riko hannun ta ya ce " haba ina kuma za ki je , ni fa wajen ki na zo "
Cikin bacin rai Inaya ta kwace hannun ta ta juya ta fara takawa za ta bar wajen
Da sauri ya sha gaban ta ya ce " ba da ke na ke ba , za ki wuce ki kyale ni ? "
Cikin bacin rai Inaya ta ce " ka ga malam ka ba ni hanya na wuce ni matar aure ce "
Dariya ya yi har da dafe ciki
Sai da ya tsagaita dariyar shi sannan ya ce " oh sannu madam to , shi ne za a yi biki ba'a gayace mu ba ? " ya kai karshen ya na kashe mata ido guda
Dan tsaki Inaya ta ja kafin ta raba ta geffen shi ta wucewar ta
Da kallo ya bi har sai da ta kurewa ganin shi sannan ya juyo ya kali inda Nesrine ke zaune
Sai dai kuma me ?
Babu ita babu mai kama da ita, tun lokacin da ya bata baya ta tatare kayan ta a hankali ta tsere dan ta sani tabass Moctar ya na tare da Hafiz , idan kuma Hafiz ya zo wajen ta san tabass ba zai kyale ta ba shi ya sa ta tsere
Abun da ba ta sani ba Moctar shi kadai ya ke tafe , Hafiz bai san da cewa college din zai zo kawai ya ce mishi zai fita ne
Tsaki kadan ya ja kafin ya fara takawa ya fice cafeteria din
Inaya
Ta na barin wajen ta koma kai tsaye class din su ta koma dai'dai lokacin da prof din su zai shiga class din
After some hours
Bayan sun sauka da ga school ko wace ta wuce gida , Inaya kuma ta wuce gidan mijin ta kai tsaye ta wuce dan yau fa Nesrine da Moctar sun tado mata na bacin ran
Zayd
Su na zaune cikin falo shi da Moussa ko wane sai faman latsa wayar shi ya ke
Su na zaune a haka Inaya ta shigo falon ta na sallama kassa kassa
Dago kan shi Moussa ya yi ya na amsa mata sallamar ta da murmushi
Ya na shirin yi mata magana ya ga ta wuce corridor kai tsaye ko gaida su ba ta yi ba
Da kallo ya rakata har sai da ta shiga bedroom din Zayd sannan ya dawo da kallon shi kan Zayd ya ce " Amir ina ga yau wani ya tabo ran baby na "
Slowly Zayd ya dago kan shi ya zubawa Moussa wadanan hazel eyes din shi ta cikin glass kafin ya ce " wai wanene babyn ka cikin gidan nan ? "
Hararrar wassa Moussa ya yi mishi sannan ya ce " bayan wadda ka ke kira da matar ka wa ke cikin gidan nan, ita ce baby na mana, ka ga na ma tafi na rarrashi abu na " ya kai karshen ya na mikewa tsaye zai shiga corridor
Da sauri Zayd ya riko hannun shi ya ce " kai Diya ban san rainin sens matar tawa ka ke kira da baby ? "
Kwace hannun shi Moussa ya yi kafin ya ce " tun da kai ba ka so ni ina so wlh , ni wlh ka ci gaba da kyale ta ma , hakan ya yi min dadi , ko na samu son da ta ke yi maka ya dawo kai na , i really love her, i don't know how ko yaushe hakan ta faru i'm falling in love for her , ni da za ka min Alfarma ka sake ta na je na roki malam ya aura min ita tun da kai ba ka son ta "
" Diya wai ka na jin abun da ka ke fada ne "
" ka ga malam ni don Allah kyale ni , wai ba ka ga yadda baby na ta dawo ne gidan ko gaisuwar arziki ba ta yi min ba , ka ga ni na tafi rarrashin ta " ya kai karshen ya na juyawa ya shiga corridor ya nufi bedroom din Zayd
Sumar zaune Zayd ya yi ya na jin abun da Moussa ya ke fada mishi nan take ya ji wani uban kishi ya taso mishi yanzu shi Moussa zai yanka a baya ya zagayo ya ce matar shi ya ke so kuma
Da sauri ya