Showing 57001 words to 60000 words out of 75226 words
sofar ya daga kai sama ya lumshe idanun shi
Dago kai ta yi ta kaleshi, duk sai ta ji zuciyar ta ba dadi
Nan take idanun ta su ka kawo ruwa , ba ta san lokacin da kuka ya kubce mata ba
Da sauri ya bude idanun shi ya dago ya na kallon ta
Cike da rudu ya ce " me ya faru ki ke kuka ? "
Ko kallon shi ba ta yi ba ta ci gaba da kukan ta , hawaye wasu na bin wani
Duk ya bi ya rude sai tambayar ta ya ke me ya faru amma ina ko kallon shi ba ta yi
Da ya ga abun na ta ba mai karewa ba ne sai ya kai hannu ya rungumo ta a jikin shi ya na dan bubuga bayan ta ya ce " stop crying please , me ya faru ki ke wannan kuka haka ? "
Cikin disashashiyar murya ta ce " ba kai ne ba yaya Zayd , kullum sai na tambaye ka abun da ke damun ka amma kullum sai ka ce ba komai "
Da sauri ya katse ta da cewa " i'm sorry, yi hakuri ki daina kukan nan wlh ba na so "
Dagowa ta yi daga jikin shi ta na goge hawayen ta, ta ce " shikenan yaya Zayd na bar kukan amma don Allah ka fada min abun da ke damun ka ! "
Mikewa tsaye ya yi sannan ya mika mata hannu a kan ta tasso
Ba musu ta daura hannun ta saman nashi sannan ta mike tsaye ta na kallon shi cikin ido
Ta na mikewa tsaye ya fara takawa ya yi gaba ita kuma ta bi bayan shi
A haka su ka Haye stair a tare ya na rike da hannun ta
A tunanin ta bedroom din da ta ke barci nan za su koma sai ta ga ya wuce ta
A haka har su ka wuce duk bedroom din da ke sama , su ka nufi bedroom na karshe
Tun da ta shigo gidan ba ta taba shigo shi , kuma ba ta taba ganin wani ya bude shi ba ya shiga
A hankali ya kai hannu ya murda handle din kofar ya tura ta ya shiga
Nan ta ga wani falon daban , dauke da wasu sofas biyu white colour guda three seaters dayar one seater sai wasu biyu two seaters sky blue , da ga tsakiyar su kuma wata table ce ta glass saman wani carpet fari mai ratsin blue , geffen doguwar sofa akwai wasu kananan tables na glass , sannan ta na fuskantar wata makekiyar Tv plasma makale a bango
Ba ta ida shan mamaki ba, sai da su ka shiga bedroom din
Kyawon bedroom din wannan book din ya yi kadan ya fade shi , girman shi ya fi falon part din , komai na cikin dakin white colour ne ,
Da ga shigo dakin sai saman wani makeken royal bed fari kal shinfida da bedsheet fara , ya na fuskantar wata makekiyar Tv plasma girman ta daya da ta falon da su ka baro
A geffen gadon kuma na hagu wani dressing mirror ne dauke da perfume da lotion kala kala
Dressing mirror din na tsakiyar wasu door , guda toilet guda dressing room
( a nawa tunanin 🤷♀️ )
A geffen dama na Tv din wata door ce ta glass wadda za ta sada ka da balcony din dakin
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 23 ❤🔥
Da kallo ta ke bin shi cikin zuciyar ta ta na tambayar kan ta wanene Zayd
Ta yi nisa cikin tunanin ta ta cintsi murya shi ya na fadin " konta ki yi barci ina zuwa "
Da to ta amsa mishi sannan ta saki hannun shi ta zauna bakin gadon
Shi kuma ya ci gaba da takawa ya nufi daya daga cikin kofofin geffen dressing mirror
Ya na shiga ta ida Hayewa gadon ta konta
Bayan wasu mintina ya fito daga toilet sanye da bathrobe , bai tsaya shafa lotion ba ya wuce dayan door ya shiga dressing room
Jim kadan ya fito sanye da kayan barcin shi ash colour ma su kyau
Gadon ya nufa ya Haye geffen guda ya konta ya na fuskantar ceiling
Cen ya juyo da kan shi ya na kallon ta , ta juya mishi baya har ta yi barci
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya lumshe idanun shi ya sake bude su slowly a kan ta
Cikin sanyin murya ya ce " ko na fada miki ba za ki gane ba , akasi ma ni da kai na ban san abun da ke damu na ba , amma na san duk lokacin da na ke tare da ke ina jin sauki a cikin zuciya ta , ina ji a jiki wani mumunar abu na shirin faruwa da ni kamar zan rasa wani abu mai mahimanci a rayuwa ta , duk da san ba tabas abun da na ke ji ya faru ba , amma ba ni fatan na rasa ki cikin rayuwa ta , dan a yanzu ke kadai ce family na , na so na yi miki irin son da ki ke yi min amma zuciya ta ta kassa ban san dalili ba "
Ya kai karshen ya na juyo da kan shi ya fuskanci ceiling ya lumshe idanun shi
Kamar da ga sama ya tsinci wannan zazzakar Muryar ta ta, ta na fadin " na sani yaya Zayd ba laifin ka ba ne dan ba ka so na , laifi na ne da na fada soyayyar ka da karancin shekaru na , na yi maka alkawari zan yi kokarin na cire shi da ga cikin zuciya ta "
Cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " ni ban ce ki cire shi da ga cikin zuciyar ki ba "
Slowly ta juyo ta kaleshi, sannan ta ce " me ya sa to baza ka iya so na ba , ba ni da kyau ne ? "
" pleaseeee ni ba wannan ba , kin fi kowa sanin ki na da kyau Masha Allah "
" to minene matsalar yaya Zayd ? " ta fada kamar za ta yi kuka
Juyo da kan shi ya yi ya kale ta cikin idanun ta da su ka kawo ruwa ya ce " i have never been in love , na hadu da mata dayawa a duniya , masu kyau , masu dukiya da mulki amma ko kallon kirki ban taba yi musu ba , ni a tsarin rayuwa ta ban shirya zama da mace ba , amma ke kin shigo lokaci guda kuma har ga Allah ba ni fatan ni fita da ga cikin rayuwa ta "
Ya kai karshen ya na mika matta hannu a kan ta zo
Ba musu ta karaso ta fada jikin ta boye fuskar ta a kirjin shi
Rungume ta ya yi a jikin shi , ya lumshe idanun shi a haka har barcin da ya jima bai yi ba ya dauke shi
Washe gari
Misalin karfe 10 na safe
Duk mutanan gidan su na a zaune a falo na kassa Banda Nesrine da ke cen konce a word room
Sai hirar su su ke cikin konciyar hankali banda Zayd da ya kurawa Inaya ido cikin bakin glass din shi , ita kuma ta kurawa TV ido kamar ita ta ke kallo
Su na tsaka da hirar su su ka ga an turo kofar shigowa falon
A tare kowa ya kai duban shi kan kofar Banda Inaya da Zayd
Kowa ya zubawa kofar ido ya na jiran ya ga wanda zai shigo
Nan su ka ga nurse din da Zayd ya dauko ta kula da Nesrine ta shigo falon ta na sallama ta na rike da Nesrine sanye da wata riga blue ta na jan kafa
A dubu dari mutanan falon su ka mike su ka yi kan ta
Mama har da sakin kuka ta rungume ta , ta na fadin " Nesrine di ta ke ce , Allah na gode maka, sannu kin ji "
Ita ma rungume mama ta yi da kyau ta na sakin kuka mai cin rai
Duk abun da ke faruwa Zayd ko janye idanun shi bai yi ba da ga saman Inaya
Ita ma ta kurawa Tv ido babu ko kiftawa
Ya na tsaka da kallon ta ya ga ta ja wani dogon nunfashi ta saki wata razananiyar kara da karfi ta ce " kar ku zo ku kyale ni , ku kyale ni ahhhhhhhhhhh " ta kai karshen ta na sake sakin kara
Dan lumshe idanun shi Zayd ya yi dan dama abun da ya ke tunani kenan dan ya na tune ta taba yin hakan
Da sauri mutanan gidan su ka jiyo su ka kale ta , ta sa hannayan ta duka biyu ta toshe kunnuwan ta sai kara ta ke
Da gudu malam ya juyo ya yi kan ta ya na fadin " auta lafya ? Me ya faru ?"
Cikin fitar hayaci ta ce " Abba sun san muna nan , sun sani , sun sani " ta kai karshen ta na sakin kuka
Da sauri Zayd ya mike ya yi kan ta , sai dai kafin ya iso ta dauke lokaci guda ta sume a wajen
Ya na isa bai tsaya yi wa malam magana ba kawai ya dauke ta da hannayan shi biyu kamar baby ya nufi stair da ita
Malam na nan zaune ko wani kwakwaran motsi bai yi ba
Sakin Nesrine mama ta yi ta tako wajen malam ta dafa kafadar shi ta ce " Abban Abdoul me ya same ta kuma "
Ta na taba shi ya dawo cikin hayacin shi , da sauri ya mike tsaye ya nufi stair da gudu
Ya na barin wajen Moussa ya kali Nesrine ya ce " sister ya jikin na ki ? "
Dan karamin murmushi ta yi kafin ta bude baki ta ce " da sauki " sai dai lips din ta ne kawai su ka motsa sautin bai fito ba
Murmushi shi ma ya yi mata ya jinjina mata kai sannan ya juya shi ma ya nufi stair ya Haye
Dakin Inaya malam ya tafi sai dai ya na shiga ya ga bedroom din ba kowa a ciki
Da sauri ya juyo ya fito dakin dai'dai lokacin da Moussa ya hayo wajen
" Moussa ina kuma Zayd ya kai ta ? " malam ya tambaye shi
Kallon kofar dakin Zayd ya yi, ya ga ta na bude kadan kafin ya juyo ya kali malam ya ce " uncle , ina ga bedroom din shi ya wuce da ita ! "
" bedroom din shi kuma ? " malam ya tambaya cike da rudu dan a iya sannin shi kullum a falo ya ke ganin Zayd na barci
Jinjina mishi kai Moussa ya yi sannan ya ce su tafi ya yi gaba
Ba musu malam ya bi bayan shi su ka nufi part din Zayd
Sallama Moussa ya yi sannan ya shigo falon part din , malam na biye da shi a baya
Zayd kuma , ya na zaune saman sofa ya na latsa wayar shi , cen kassan makoshi ya amsa musu sallamar su
Da sauri malam ya nufo shi ya na fadin " Zayd ina auta , ba abun da ya same ta dai ko "
Ba tare da ya dago kan shi ba ya ce " zauna uncle , ina ga yanzu lokaci ya yi da za ka fadamin gaskiyar abun da ke damun ta "
Wasu yawu malam ya hadiye kafin ya zauna geffen shi ya sunkuyar da kai
Sai da ya dauki lokaci kafin ya fara magana kamar haka " ni dai suna na Ibrahim , cikaken bafulatani da ga gari yola , a cen a ka haife ni , a cen na taso , bayan na cika shekara 23 na baro Garin neman aiki na taho jahar kaduna inda mahaifiyar mu ke da wasu yan uwa na sauka a gidan su , sannu sannu na fara fitowa neman aiki har Allah ya hada ni da wasu abokanai na , Issa da Youssef , a tare mu ka tafi neman aikin har Allah ya sa wani mai kanti ya dauke mu a tare , to dai haka mu ka ci gaba da aikin mu tsawan watanni , bayan wani lokaci a ka kawowa Aunty ta wa wata yarinya da ga ilori za ta zauna a wajen ta ta dinga yi mata aiki , kawai sai na ji na kamu da son yarinyar nan , duk yadda zan yi ta kula ni sai da na yi , a haka har mu ka fara soyayya da ita , har mutanan gidan su ka sani , gudun kar shaitan ya shiga tsakanin mu ba su bata lokaci ba a ka daura auren mu , na kama mana gida mu ka koma cen da zama , bayan shekara guda haka Allah ya ba mu yaro wanda ya ci sunnan Abdoul , abun kamar da wassa sati biyu bayan zuwan shi duniya , uban gida na ya ba ni amanar shagon shi saboda wata tafiya da ta tasso mishi , cikin wani ikon Allah da ma na fara kula da shagon, kasuwanci ya habaka , kullum sai mun ninka ribar jiya , abun ba karamin dadi ya yi wa mai shagon ba , hakan ya sa ya buda min wani shagon daban na dinga kula da shi , abun da ban sani ba Youssef ya na bala'in kishi na, musaman da ya ga uban gidan mu ya ba ni shago na dinga kula da shi ....... "
Katse shi Zayd ya yi da cewa " wait uncle ni fa ban gane inda ka dosa ba abun da na tambaye ka daban , why za ku ba ni wannan labarin ? "
Malam na shirin magana Moussa ya riga shi cewa " kai fa Amir matsalata da kai gajen hakuri , ka tsaya ka saurari abun da zai fada ko "
Jinjina mishi kai ya yi kafin ya kali malam ya ce " uncle ci gaba "
Murmushi malam ya yi kafin ya ci gaba da cewa " a haka mu ka ci gaba da rayuwa , ina kula da shagon nan har bayan wasu shekaru Allah ya ba mu kyakyawar yarinya wadda na sakawa sunnan Nesrine , bangaran Youssef kuma kishin nan nashi ya na nan har ya kai wani lokaci ya daina zuwa zaman da mu ke yi bayan sallar isha a cen gida na , hakan bai dame ni ba dan a tunani na aiki ne ya yi mishi yawwa saboda shi ma ya na da nassa ahalin kuma ga shi ya shiga harkar siyassa , bayan shekara uku , Allah ya sake ba mu haifuwar kyakyawar baby kamanin ta sak da na Nesrine , na saka mata sunnan mahaifiya ta wato Inaya , ranar da a ka yi zanan sunan ta , mu na zaune bakin kofar gida ni da Issa da Youssef mu na hira , mu na a haka ingozomar da ta karbi haihuwar matata tun ta Abdoul ta fito za ta tafi , cikin murna na tare ta ina yi mata godiya har na bata dubu biyar na hanya , har ta tafi na dawo , ina zauna tare da su issa kawai sai ganin ta na yi ta dawo , na tambaye ta ko ta yi mantuwa ne na shiga na dauko mata sai ta ce min " a'a ban yi mantuwa ba , ya kamata na sanar da kai , wannan yarinyar da Allah ya baka, ba kamar kowace yarinya ta ke ba , na ji a jiki na ta na da kashin arziki kamar mahaifiyar ta , musaman ga mijin da za ta aura , sannan akwai wani boyayen al'amari a tatare da ita , na ji a jiki na ta na da wata baiwar da Allah ya yi mata dan ganin karshe wani zalinci , ka kula da ita kar ka bari ta fada hannun mara gaskia mai niyar cutar wa , kaddarar ta na gaba , na ga wani batacen bakko mai cike da ayar tambaya , tabas kaddara za ta hadasu , haduwa ta har abada " ta na gama fadar hakan ta juya ta yi tafiyar ta , ni duk cikin abun da ta fada kashin arziki kawai na rike , har da ma Youssef , ashe cikin zuciyar shi dakwai abun da ya shirya , sannu sannu lokaci na tafiya har ya kai Inaya ta kai shekara 7 , kassuwanci na sai habaka ya ke yi , yayin da Youssef ya shiga harkar siyassa ta mugayan mutane masu anfani da tsafi wajen ganin sun yi nassara , har ya kai matsayin minister cikin gida , bayan Inaya ta ci ka shekara 8 wani mumunan abu ya faru da ni , shago na ya kone kurumus babu abun da ya yi saura , wasu sun ce barayi ne , wasu kuma su ce ba mu kashe injin shagon ba , mun tabka babbar assara ni da uban gida na , da ya ke mutumin ya na da kirki sai ya ce Allah ne ya rubuta hakan ya hakura ba komai , ganin bazan iya ci gaba da kula da shagon ba sai na ce mishi ya dauki Abdoul ya dinga taimaka mishi , a lokacin ya na shekara 18 ba musu ya yarda, duk lokacin da Abdoul ya sauko da ga school sai ya tafi shagon wajen aiki , ni kuma na bude wata karamar makarantar islamya inda na ke koyar