Showing 12001 words to 15000 words out of 75226 words
kadan kafin ya komawar shi gida
Bayan ya koma gida bai tsaya bin ta kan Moussa ba kai tsaye ya wuce bedroom din shi
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 5 ❤🔥
Washe gari
Yau ta kama week-end ce Inaya da Nesrine ba su tafi college ba, sai misalin karfe 9 na safe Nesrine ta farka da ga barci
Inaya kuma sai wajen karfe 10 ta farka , ko da ta farka ta ji kan ta na yi mata dan ciwo amma sai ta jure
Ta mike ta fito dakin ta shiga toilet ta yi wanka sannan ta fito ta shirya cikin wando jeans baki da doguwar riga zuwa guyiwa pink colour ta saka dan karamin hijab zuwa kirji sai tashin kamshi ta ke
Kai tsaye kitchen ta nufa dan ta taya mama girki tun da yau week-end
A tare su ka yi dafuwar su cikin konciyar hankali har misalin karfe 12 na safe sannan su ka Kamala
Bayan sun ida Inaya na shirin shiga dakin ta ta tsinci Muryar malam ya na fadin " Auta dan Allah dauki abincin Zayd ki kai mishi " ya fada ya na ida shigowa cikin gidan
Dan murmushi ta yi sannan ta ce mishi to ta juya ta koma kitchen
Dama mama ta fida mishi na shi cikin wani kwano ta ajiye gefe dama sun saba fida mishi abincin rana kullum wani yaro da ke sangayar malam ke zowa ya kai mishi wannan karan ne na farko da za ta kai mishi da kan ta
Jim kadan ta fito rike da wani dan basket a hannun ta, ta fita gidan, a lokacin har malam ya shiga dakin shi
A hankali ta ke tafiya saman hanya ta na kallon kassa kamar mai tunanin wani abu
Sai da ta karaso kofar gidan sannan ta dago kai, ta kai hannu ta tura kofar ta shiga ta na sallama
Wannan karan farko da ta shigo gidan shi ,
Ta sha ruwan mamaki ganin yanayin gidan, har da wata mota fara ta tambayi kanta ta ina motar ta shigo , in ta shigo ai fitar ba za ta yi wuya ba kuma ita kofa daya ta gani kuma karama ce
A hankali ta ci gaba da takawa har ta isa terrace din gaban ta
Ta kai hannu ta bubuga kofar, sau daya
Shiru ba a bude ba sai ta sake bugawa karo na biyu
Wannan karan bai fi one minute ba ta ga kofar ta bude
Sai ga Moussa ya na tsaye rike da kofar ya na sanye da wando three cuter da t-shirt ya na shan iska
Sallama ta yi mishi ta gaishe da shi cikin fara'a sannan ta mika mishi basket din hannun ta ta ce ga abincin su in ji malam
Dan murmushi yayi kafin ya dan ja gefe kadan ya ce " bismillah shigo mana dama yunwa na ke ji idan mun ida sai ki koma da basket din ko "
Jinjina mishi kai ta yi ta na murmushi kafin ta sa kafa ta shiga falon ta na sallama
Ya na zaune saman sofa da ke fuskantar kofar shigowa, ya na sanye da jallabiya fara mai kananan hannu, ya na sanye da wadanan glass din na shi baki, ya jinjina a bayan sofar ya daga kai sama ya lumshe idanu duk da su na cikin glass
Ya ji sallamar ta amma ko motsi bai yi bare ya amsa mata
A hankali ta karaso cikin falon ta na bin shi da kallo gaskia ya yi mata kyau
Ta na cikin dube duben ta ta tsinci Muryar moussa ya na fadin " ko kin dawo nan da zama "
Girgiza mishi kai ta yi ta na murmushi sannan ta karasa ta ajiye basket din hannun ta saman table ta ce " ina wuni yaya Zayd "
Shiru bai amsa mata ba ko motsi bai yi ba
Da sauri Moussa ya ce " barci ya ke " dan ya kare dan uwan shi
Murmushi ta yi sannan ta koma bakin sofar da ke wajen kofar shigowa ta zauna kassa saman carpet
Karasowa Moussa ya yi ya zauna saman sofar da Zayd ke zaune, ya kai hannu ya janyo table din gaban shi ya kai hannu ya ciro kwanonin da ke ciki da plate guda ya fara serving din kan shi ya fara ci ya na yi mata hira ta na amsa mishi a kai a kai
Duk abun da su ke Zayd na sauraron su dan ba barci ya ke ba kawai dai ya lumshe idanun shi
Sai da ya Kamala cin abincin tass ya cinye komai sannan ya meda kayan cikin basket ya tashi ya je dining room ya bude fridge ya dauko gorar ruwa guda sannan ya dawo inda ya tashi ya zauna ya bude ya sha ruwan
Sai da ya ida sannan ya koma ya jingina a bayan sofar ya lumshe idanun ya bude a hankali ya kali Inaya ya ce " Gaskia abincin nan ya yi dadi "
Shiru ta yi ta kurewa waje guda ido babu ko kiftawa
" Inaya tunanin mi ki ke " ya tambayeta ya na kallon ta
Nan ma shiru ba ta motsa ba
Tasowa ya yi da ga jikin sofar ya kai hannu ya dan bubuga cinyar Zayd
A hankali ya ware idanun shi ya taso da jikin sofar shi ma ya kali Moussa
" duba ka ga, ko tunani me ta ke ? " Moussa ya fada ya na nuna mishi Inaya
A hankali ya juyo kan shi ya kale ta
Ta yi zugum waje guda kamar wadda ta suma
Mikewa tsaye ya yi ya koma saman sofar da ke bayan ta ya zauna ya kai hannun shi ya dafa kafadar ta
A razane ta dawo cikin hayacin ta , ta na sakin kara ta kai hannayan ta ta toshe kunnuwan ta ta na fadin " Ku kyale ni , ku kyale , kar ku tabani , wayo Abba na, aaaaaaaaaaaa "
A rude ya sauko kassa ya riko ta da hannayan shi biyu, shi ma Moussa da sauri ya tasso ya koma gaban ta ya tsuguna ya na fadin " Inaya lafya me ya faru "
Ina sam ba ta jin shi ta toshe kunnuwan ta
Da karfi Zayd ya sa hannayan shi duka biyu ya riko nata ya yanye su da karfi ya sauke su kassa ya kali Moussa
Jinjina kan shi Moussa ya yi sannan ya karanto ayatul kursi'u dan a tunanin shi aljanu ne gare ta
Kamar da gaske ya na fara karanta, ta fara nitsuwa ta na kallon shi ta na sauke ajiyar zuciya a hankali ta lumshe idanun ta ta fada jikin Zayd
Sai da ya karanta ajatul kursi sau biyar sannan ya bari ya kali Zayd ya ce " Amir ba dai aljanu ne da ita ba ? "
Girgiza mishi kai Zayd ya yi ba tare da ya ce komai ba ya na rungume da ita
Ya na jin ta sauke ajiyar zuciya ta ke a jere idanu a lumshe
Sai da ta ji ta nitsu sannan ta bude idanun ta, ta mike da ga jikin Zayd ta na kallon Moussa
Dan murmushi ta saki kafin ta mike tsaye ta ce " yaya Moussa zan koma gida "
" shikenan muje na raka ki " ya fada ya na mikewa tsaye ya dauki basket din saman table ya riko hannun ta ya ce mu tafi
Ba musu ta bi bayan shi su ka bar falon
Shi ma Zayd mike wa ya yi ya bi bayan su a hankali dan nesa kadan da su
Sai da su ka iso bakin kofar gidan sannan ya saki hannun ta ya mika mata basket din ta ya ce ta shiga
Karbar basket din ta yi sannan ta ce mishi sai an jima ta shige gidan su
Har ya juya zai bar wajen
Cak ya tsaya ya na kallon Zayd da ke tsaye bayan shi cike da mamaki " yaushe ya biyo mu kuma ? " ya tambayi kanshi
Ya na shirin magana ya riga shi cewa " shiga ka yi min magana da uncle "
Ba musu ya juya ya shiga gidan ya na sallama shi kuma ya tsaya nan ya na jiran su
Jim kadan Moussa ya fito , malam na bayan shi
Sallama malam ya yi mishi sannan ya bashi su ka yi musbaha
Sai da su ka gaisa sannan Zayd ya ce " Uncle ina son muyi wata magana "
" ina sauraron ka, mi ka ke son muyi magana a kai ? " Malam ya fada ya na tsare shi da ido
Ajiyar zuciya Zayd ya yi kafin ya ce " uncle ina son in san dalilin da ka aura min yarinyar nan "
Nan take yanayin face din malam ta sauya ya rasa amsar da zai ba shi
Ga kuma Zayd ya tsare shi da ido
Wasu yawu malam ya hadiye kafin ya ce " Zayd ba zan iya fada maka ba a yanzu ka gane lokacin in ya yi za ka gane komai "
" shikenan next week zan zo na dauki matata zan gano abun da ake boye min da kai na " ya na gama fadar haka ya juya ya bar wajen ya na taku cike da izza
(TO FA NA MULKIN SUN FARA TASHI 🤣🥀 )
Ba karamin kwarjini ya yi ma malam ba kawai ya tsaya ya na kallon shi ya rasa me zai ce
Kallon shi Moussa ya yi sannan ya ce mishi " malam zan tafi " sannan ya juya ya fara takawa
Jinjina kan shi malam ya yi sannan ya fara takawa dama ya fito zai je mosque ya ji sallamar Moussa
Bayan sallar isha
Inaya
A hankali ta ke fitowa da ke fitowa da ga cikin dakin su
Ta na sanye da gown pink colour mara nauyi da hijab pink shi ma zuwa guyiwa
A hankali ta ke takowa cike da nitsuwa ta ke takowa ta nufi kitchen
Har ta kai kofar kitchen ta jiyo mama na magana sama sama
A hankali ta juyo ta nufi kofar dakin mama dan a tunanin ta ita ka dai ce ko da ita ta ke magana ba ta ji da kyau ba
Har kai kofar dakin ta bude baki za ta yi sallama ta ji Muryar malam ya na fadin " abun da ki ka ji Amina, auta dai na aurar da ita tun shekara biyu da su ka wuce kuma yanzu mijin ta ya ce ya na son ta koma gidan shi "
Dumm ta ji gaban ya buga da karfi nan take idanun ta su ka kawo ruwa da gudu ta juya ta bar wajen
Maimakon ta koma bedroom din su , sai ta bar gidan baki daya
Gudu ta ke da iya karfin ido a rufe
Da karfi ta bangaje kofar gidan shi ta shiga ta nufi wajen motar da ke cikin gidan ta buya a baya ta Zube saman guyiwowin ta ta aza kuka da karfi
Ba ta fi ten minutes da shigowar ta wajen Moussa da Zayd su ka fito da ga cikin falon
Su na sanye da jeans baki da t-shirt amma ta Zayd fara ce ta Moussa kuma blue
Su na tsaka da tafiyar su su ka jiyo kukan mutun
Cak su ka tsaya a tare su na kallon juna su na zaro idanu
A hankali su ka fara bin wajen da kallo ba su ga kowa ba
Cen Moussa ya ce " ko dai aljanu ne ke wannan kukan ? "
Girgiza mishi kai Zayd ya yi kafin ya fara takawa a hankali ya nufi motar shi
( WATA SABUA MAKAHO DA TUKA MOTA 🤣✌)
ya na kara nufo motar sautin kukan na karuwa
A hankali ya fara zagayen motar har ya iso inda ta ke
Ta na zaune ta cusa kan ta tsakanin cinyoyin ta sai kuka ta ke kamar ba gobe
A hankali ya tako ya zo geffen ta ya zauna shi ma sannan ya kai hannu ya dafa kafadar ta , Moussa kuma ya na tsaye gaban su
A hankali ta dago kan ta cikin kukan nata fuskar ta duk ta yi jaga'jaga da hawaye
Ta na daura ido saman shi ta ji wani kukan ya zo mata
Da hannu ya mata allamun " minene ki na kuka ? "
TO A NAN ZAN DASSA AYA SAI MUN HADU GOBE✌✌✌✌
KAR KU MANTA KU NA TARE DA ALKALAMIN ANISH ❤
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 6 ❤🔥
Da hannu ya mata allamun " minene ki na kuka haka ? "
Cikin wata disashashiyar murya ta ce " yaya Zayd wai Abba ya yi min aure "
Da sauri Moussa ya ce " to mine matsalar ba ki na son wadan a ka aura miki ba "
Medo da kallon ta ta yi kan Moussa cikin kukan ta ce " yaya Moussa ni fa ina da wanda na ke so , kuma ni ban ma san wanda Abba ya aura min , ni ko ma wanene ba na son shi , dan Allah yaya Moussa ka je ka same shi ka ce ya raba auren nan wlh ba ni son shi " ta kai karshen ta na meda kan tsakanin cinyoyin ta
Dan satar kallon Zayd ya yi kafin ya ce " shikenan babyn malam , yanzu fada min wa ne wannan wanda ki ke so "
Da sauri ta dago kai ta ce " yaya z........." kut maganar ta yanke ta zaro idanu ta na kallon Moussa
Shi dai Zayd ya na zaune ya zuba mata ido ya na jiran ya ji sauran maganar in da gaske akwai wanda su ke soyayya to ya dauki niyar zai sake ta ya aura mata wanda ta ke so
Ganin ta yi shiru ta tsaya sai kallon Moussa ta ke sai ya kai dan yatsun shi saitin face din ta ya kyasta mata
Sai da ta dan razane sannan ta medo da kallon ta kan shi
Tambayar ta ya yi minene
Girgiza mishi kawai sannan ta meda shi tsakanin cinyoyin ta amma ba kuka ta ke ba wannan karan
Kallon Moussa ya yi sannan ya daga mishi gera guda
Jinjina mishi kai Moussa ya yi sannan ya sunkuyo gaban ta ya ce " shikenan yanzu tashi mu koma gida ko "
Ba tare da ta dago kai ba ta ce " ni wlh ba inda zan je "
Ya na shirin magana Zayd ya daga mishi hannu ya na girgiza mishi kai
Mikewa tsaye moussa ya yi ya dan ja baya kadan
Shi ma Zayd mike wa tsaye ya yi sannan ya fara takawa ya bar gidan
Ta na jin ya fara takawa ta dago kai a hankali ta na kallon shi ta wutsiyar ido
Sai da ta ga ya fita gidan sannan ta sake sakin wani sabon kukan
Juyawa Moussa ya yi zai bar wajen sai ya dawo ya ce mata " tashi ki shiga cikin gidan tun da baza ki koma gida ba "
Ya na gama fadar haka ya sa kai ya fice shi ma
Cen ya hango Zayd har ya yi nisa da tafiyar shi
Da sauri ya fara takawa har ya kamo shi dai'dai ya karaso kofar gidan su Inaya
Su na karasowa wajen Abdoul da malam su ka fito da sauri kamar sun ga wani abun gudu
Da sauri Moussa ya ce " Abdoul ina za ku je haka da sauri wani abu ya faru "
Abdoul na shirin magana malam ya riga shi cewa " Inaya ce ba ta cikin gidan nan ban San inda ta yi ba "
Dan murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " ku kontar da hankalin ku , yanzu nan mu ka baro ta gidan mu, kar ku damu ba abun da ya same ta "
Ajiyar zuciya malam da Abdoul su ka sauke a tare
" uncle kun san da yarinyar nan ta na da wanda ta ke so " su ka tsinci Muryar Zayd ya na fada
Kallon juna Abdoul da malam su ka yi kafin su kali Zayd har su na hada baki wajen cewa " ita da kanta ta fada maka hakan ? "
Jinjina musu kai ya yi bai ce komai ba
Dan murmushi malam ya yi sannan ya ce " yo ai wannan ba matsala ba ce dan..... "
Da sauri Zayd ya katse shi da