Showing 30001 words to 33000 words out of 75226 words
zaune cikin falon gidan ta cire hijabin jikin ta , ta ajiye shi gefe ta saki wani dark hair din ta har cikin baya , kun san fulani su ma ba baya ba wajen gashi bare uwa bafulatana uba bafulatani kun ga ba mamaki ta yi gashi
Ta na zaune ta na kallon tashar Arewa 24 a Tv duk hankalin ta ya na wajen Tv din a na shirin mata a yau
Ta na a haka ta jiyo sallamar Moussa
Dan murmushi ta yi kafin ta amsa sallamar shi ta na yi mishi sannu da zuwa
Murmushi ya yi kafin ya tako a hankali ya zauna saman sofar da ke fuskantar ta ta
Ya na zama Zayd ya shigo falon ya na sallama cen kassa kassa yadda shi kadai ya san ya yi abu ne
Abun mamaki kuma sai da Moussa ya amsa sallamar dan ya san abokin shi da wuya ya shigo wuri bai yi sallama ba, ko da kuwa ba wanda ya ji ta
A hankali ya karaso cikin falon ya zauna geffen Moussa
Sannu da zuwa Inaya ta yi mishi ta na murmushi , jinjina mata kai kawai ya yi ya na kallon ta ta cikin bakin glass din shi , kamar bai taba ganin ta ba
Ya na a haka ya tsinci Muryar Moussa ya na fadin " baby me kuma a girka mana ni fa yunwa na ke ji "
Da sauri Zayd ya juyo ya kaleshi ya juya ya kali Inaya sai ganin ya yi ta saki murmushi ta mike tsaye ta dauki hijabin ta ta saka ta ce mishi " yaya Moussa ni fa tun dazu na gama ina jiran ku " ta na gama fadar haka ta shiga dining room
Mikewa Moussa ya yi ya bi bayan ta ya shiga dining room ya ja kujera guda ya zauna sai bin ta ya ke idanu
Shi kuma Zayd sai kallon su ya ke wata zuciyar na ce mishi ya tashi ya shake Moussa ko ya rage zafin kishin da ya ke ji
Ya na kallon su har Inaya ta yi serving din shi ta mika mishi plate din ta na murmushi sannan ta janyo kujerar da ke fuskantar tashi ta zauna ta yi serving din kan ta , sannan ta fara ci
Da allamun ta manta da mijin na ta baki daya sai abincin ta ta ke ci su na hira ita da Moussa har da dariya
Zayd kuma ganin abun na su na neman ya yi mishi katutu ya sa ya mike a hankali ya nufi corridor ya shiga bedroom din shi kai tsaye ya Haye saman bed din shi ya yi rub da ciki
Moussa da Inaya kuma sun ma manta da shi sai hirar su su ke , sai da su ka Kamala cin abincin su sannan su ka tatare dishes su ka kai kitchen su ka wanke a tare sannan su ka dawo falo su ka zauna, Moussa ya saka musu wani horror film su ka fara kallo
Su na a haka Zayd ya fito da ga cikin corridor sanye da wando three cuter baki da t-shirt purple yanzu ma ya na sanye da bakin glass din shi
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 13 ❤🔥
A hankali ya takowa cikin falon cike da izza kai a sunkuye
Har sai da ya karaso sofar da Moussa ke zaune ya zauna shi ma ya na kallon Tv din
Jim kadan da zaman shi Moussa ya mike ya ce ma Inaya sai da safe shi zai shiga barci da to ta amsa mishi sannan ya juya ya shiga corridor ya wuce bedroom din shi ya bar ta nan ita Zayd
A haka su ka ci gaba da kallon film din a tare har sai da a ka zo wajen wata scene mai ban tsoro
Da karfi Inaya ta saki kara ta tashi da gudu ta fada jikin Zayd ta kankame shi ta na sakin kara ,
( KO NI SAI DA NA NEMI NA FADA MISHI A JIKI WANNAN SCENE DIN BA KARAMIN TSORO YA BA NI BA , SHI MA MOUSSA DA GANGAN YA KE YA ZAI SAKA MA YARINYA KARAMA IRIN WANNAN FILM 😠😠😠 )
Da gudu Moussa ya fito da ga cikin bedroom din shi ya na sanye da jallabiya fara ya karaso wajen ya na tambayar lafya
Cak ya tsaya ya zuba musu idanu ya na sakin wani kyawatencen murmushi, da gudu ya koma bedroom din shi ya dauko wayar shi ya dawo ya dauke su hoto sannan ya komawar shi daki
Inaya kuma ita ko fitowar Moussa ba ta ji ba ta na zaune saman cinyar Zayd ta boye fuskar ta a kirjin shi ta datse idanun ta da karfi ta kankame shi da kyau kamar na ce zan kwace mata shi
Shi kuma bawan Allah Zayd duk ya bi ya yi sumar zaune dan babu wata macen da ta taba zama saman cinyoyin shi har ta rungume shi haka kawai sai jin shi ya yi cikin wani bakon yanayi ya tsaya ya zuba mata ido ta cikin glass din shi
Dan lumshe idanun shi ya yi ya daga kan shi saman ya sauke nanauyar ajiyar zuciya har sai da Inaya ta bude idanun ta jin ya sauke ajiyar zuciya
Ba shiri ta ji ya mike tsaye da ita a jikin shi ya sa hannayan shi ya dauke ta kamar baby ya juya ya fara takawa ya nufi corridor ya wuce kai tsaye bedroom din shi ta ita
Bai dire ta ko ina ba sai saman bed din shi ya kontar da ita sannan ya mike ya juya zai bar dakin
Taku daya ya yi ya ji ta riko hannun shi ta saki kuka ta ce " don Allah yaya Zayd kar ka tafi wlh tsoro na ke ji bazan iya kwana ni ka dai ba " ta fada cikin kukan nata
Dan lumshe idanun shi ya yi cikin zuciyar shi ya ce " kai Diya , ina hankalin ka da za ka saka mata horror film yanzu ga shi kan janyo min " ya kai karshen ya na dan karamin tsaki ya bude idanun shi
Ba dan ya so ba ya koma ya zauna saman gadon ya jingina bayan shi a bayan gadon ya lumshe idanun shi
Inaya kuma ta na ganin ya dawo ya zauna ta saki murmushi ta konta ta zuba mishi ido sai kallon shi ta ke
Sannu sannu har ya dauke ta ta na kallon shi
Ya na jin ta fara sauke nunfashi a hankali a hankali ya sa ya juyo ya na kallon ta
" wannan yar karamun abun wai ita ce matata ? Ni ban ma san dalilin da ya sa na yarda da auren nan gashi yanzu a neman a janyo min matsala , kai da sake wlh " ya fada a cikin zuciyar shi ya na sakin dan karamin tsaki ya kauda kai gefe
Ya dan jima a haka kafin ya sauko fararen kafafuwan shi kassa sannan ya mike tsaye ya fara takawa ya fice dakin
Dakin Moussa ya shiga, nan ya tardo shi ya na konce ya yi rub da ciki saman gadon shi da ga shi sai short da singlet
Takowa ya ci gaba da yi ya karaso bakin gadon ya zauna, ya cire bakin glass din shi ya ajiye saman bedside drawer sannan ya karasa Hayewa gadon ya konta
Ya na kontawa Moussa ya farka a tsorace ya na fadin " waye ne ? "
Ya na gama fadar haka idanun shi su ka sauka a kan Zayd da ke konce geffen shi ya daura hannu daya saman forehead din shi dayan kuma saman cikin shi ya lumshe idanu
Tsaki Moussa ya ja kafin ya mike zaune ya na hararrar Zayd ya ce " kai malama me kuma ka ke min a cikin daki ka ga don Allah tashi fitar min da ga daki " ya fada ya na nuna mishi kofar dakin
Ko bude ido Zayd bai yi ba bare ya amsa mishi
Ganin ya na shirin ya bata mishi rai ya sa Moussa juyawa ya sauke kafafun shi kassa ya ce " shikenan konta a nan, ni zan je na kwana tare da baby na , sai da safe " ya kai karshen ya na mikewa tsaye ya nufi hanyar fita dakin
Har ya kai bakin kofar dakin ya ji an shako shi ta baya da karfi a ka tila shi gefe ya fadi kassa
A dubu dari ya dago kai ya na kallon Zayd da ke tsaye gaban shi
Ya na shirin magana ya ga ya juya ya koma wajen bed ya Haye ya konta kamar da farko ya bar Moussa nan Zube a kassa
Tabe baki Moussa ya yi ya na kokarin mike wa tsaye ya na fadin " amma Allah Amir ka cika dan rainin hankali, yanzu dan na ce zan je na kwana da baby na shi ne za ka min haka, ina ruwan ka to ? " ya kai karshen ya na karasowa bakin gadon ya zauna ya bawa Zayd baya , ya daura hannun shi daya saman bayan wuyan shi ya na shafawa a hankali dan ba karya Zayd ya damko shi da karfi
Ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce " Diya wai me ya sa ka ke yawwan takura min ne haka ? "
Ba tare da ya juyo ba ya ce " ni ban takura maka ba kai ne ka takura min ina cikin barci na mai dadi ina mafarkin malam ya ba ni auren baby na shi ne za ka zo ta tashe ni , na ga kai ma ka na da dakin na ka me ya sa ba ka je ka kwana a cen ba , shikenan tun da baza ka iya kwana a cen ba ni zan koma cen dan ni bazan kwana da kato ba "
Bude idanun shi Zayd ya yi ya kali Moussa kafin ya ce " amma fa ka san a kan matata ka ke wannan maganar ? "
Juyowa Moussa ya yi ya kale shi cikin ido ya ce " eh na sani a kan matar da ba ka so na ke magana, kuma gobe sai na je na fadawa malam ba son ta ka ke ba ya matsa maka ka sake ta na aure ta "
Ya na gama fadar haka ya ida Hayewa gadon ya konta ya juyawa Zayd baya
Zayd kuma ya na kallon shi har sai da ya konta sannan ya ce " Diya in har ka na son ta me ya sa tun farko ba ka nemi auren ta ba sai da ka bari lokaci ya kure "
Juyowa Moussa ya yi su na fuskantar juna ya ce " ai yanzu ma lokacin bai kure ba na ga ai matar ka matata ce ka ga ai lokaci bai kure ba "
" ka yi fa karatun kur'ani " Zayd ya fada ya na kallon shi
" na ga kai ma ka yi karatun kur'ani, kassan sarai mi a ke nufi da aure, ka kuma san hankin da yarinyar nan ta ke da a kan ka , ba na ciyar da ita da tufatar da ita kadai ba , ta na bukatar ka a kusa da ita , you know she is too young, duk a shekaru baza ta wuce 15 years ba a ka aura maka ita, har yanzu fa da kuruciya a tatare da ita amma ba ka gani , Zayd yanzu wajen two weeks da ta dawo gidan nan da zama amma ko so daya ba ka bude baki ka yi mata kalma daya da za ta sa ta ji dadi cikin gidan nan , shin ka san wani abu dazu da na tambaye ta dalilin mi ta ke son ka haka har ta yarda da auren ka da karancin shekarun ta baza ta tsaya ta more rayuwar ta ba , ce min ta yi ta fi son ta more rayuwar ta cikin gidan mijin ta , ko da ba ka iya ganin ta, ko da in ta yi maka magana baza ka amsa mata ba , ta na jin dadin zama da kai a hakan , ta ce min tun kafin ta san minene assalin so ta ke fama da soyayyar ka a cikin zuciyar ta , ta tambayi kan ta so adadi dalilin mi ta ke son ka amma ko wane lokaci zuciyar ta amsa guda ta ke bata shin kassan micece wannan amsar ? " ya kai karshen ya na daga mishi gera guda
Girgiza mishi kai Zayd ya yi allamun a'a
Murmushi kadan Moussa ya yi kafin ya ce " Kaddara , kaddarar ta ce kamuwa da soyayyar wanda ko ganin ta bazai iya yi bare har ya kamu da son ta saboda kyawonta , a haka kuma ta amshi kaddarar ta hannu bibiyu , na tambaye ka lokacin da ka ke Amir Nawfel , mata nawa ne a basu tunkare ka ba da kalmar so , da d'iyan sarakuna har na cikin gari, mace nawa a bata kawo maka kanta ba da sunnan ka yi konciya da ita ma kawai, saboda dukiya da tarin mulkin da Allah ya yi maka , amma yanzu duba ka gani inda rayuwa ta kawo ka tun shigowar mu Nigeria ban ga macen da ta zo ta bude baki ta ce ta na son ka , sai wannan yarinyar da ko wuta ka ce mata ta fada sai ta fada saboda irin son da ta ke maka , duk da ba ta san ko kai waye ba ba ta san assalin ka ba, karewar zancen kallon kurma da makaho ta ke yi maka amma a hakan ta ke son ka , ba ka tunanin kai ma ta ka kaddarar ce ta hada ka da ita, ba ka tunanin kashe ka da a ka yi kokarin yi cikin masarauta har ka tsero nan Nigeria ba dan ku hadu ba ne kai da ita , wlh Amir na yi rantsuwa babu ko kaffara duk ranar da yarinyar nan za ta daina son ka wlh wlh baza ka taba samun Macen da za ta so ka tsakanin ta Allah da zuciya daya kamar wannan "
Ya na gama fadar wannan ya juya ya bawa Zayd baya ya lumshe idanun shi
Zayd kuma da ya zuba mishi ido tun da ya fara magana ya na kallon shi har sai da ya ida ya juya ya bashi baya
Duk jikin shi ya bi ya mutu jin abin da Moussa ya fada mishi sai juya kalaman shi ya ke cikin kai
Sannu sannu har barci ya dauke shi ya na wannan tunanin
Washe gari
Inaya
Misalin karfe 6 na safe ta farka da ga barcin ta , ta yi duk wasu ayikan gidan ta shirya musu breakfast ta ci , sannan ta koma bedroom din Zayd ta yi wanka ta shirya cikin uniform din ta, misalin karfe 7 ta bar gidan ba tare da ta nemi kowa ba bare ta gaishe da su
Bayan ta baro gidan kai tsaye college ta wuce ko gidan su ba ta biya ba wajen Nesrine dan har yanzu ta na fushi da ita
A haka ta isa school ita kadai ta wuce class din su , ko lokacin break ba ta fito ba ta na cikin class har sai da su ka Kamala lokacin saukar su ya yi sannan ta fito nan ma ba ta nemi Nesrine ba ta kama hanyar gida
A hankali ta ke tafiyar ta saman titi ita kadai, ta sunkuyar da kai
Ta na a haka ta jiyo Muryar Nesrine ta na kiran sunan ta , sarai ta ji ta amma ta ki tsayawa ta ci gaba da tafiyar ta
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 14 ❤🔥
Da gudu Nesrine ta tunkaro ta ta na kwalla mata kira amma Inaya ta ki tsayawa
Har sai da ta karaso wajen ta ta na fadin " ke Inaya ki na ji na za ki kyale ni "
A hankali Inaya ta dago kan ta, ta kali Nesrine da ke ta faman haki saboda gudun da ta yi ta ce " lafya ki ke nema na haka ko yanzu ma kin zo ki ci zarafin yaya Zayd ne ? "
Hararrar Nesrine ta yi kafin ta ce " Inaya wlh ba ki da kirki yanzu kennan duk son da ki ke ma yaya Zayd dan kin san gaskiyar shi ba makaho ba ne , ba kuma kurma ne ba amma ki ka shanye ki ka ki fada min "
Tsaki Inaya ta ja kafin ta juya ta fara takawa ta na fadin " ni ban san maganar me ki ke ba kin fi kowa sanin yaya Zayd kurma shi ne za ki zo min da wata magana cen daban kin ga ni don