Showing 66001 words to 69000 words out of 75226 words

Chapter 23 - Exiled Princess Book 1 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

301

lips din ta na kassa
Ba tare da ya kale ta ba ya ce " shikenan , next week za ki fara zuwa kema "

Washe baki ta yi, ta na murmushi , ta ma rasa abun da za ta ce mishi, kawai sai ta yi shiru ta , ta medo da kallon ta saman hanya

Sun dauki wajen good ten minutes su na tafiya kafin su karaso unguwar su ,

Su na yin kwanar da za ta kai su gidan su , wata dankareriar mota baka kirin ta sha musu gaba har sai da Zayd da Inaya su ka buge kawunan su a jikin motar

Da sauri Zayd ya dago ya daura hannun shi saman shoulder din ta ya na fadin " ba ki ji ciwo ba "

Girgiza kai ta yi, ta na kai hannu ta dafe wajen da ta bugu

Su na a haka wani katon basamude baki kirin ya fito da ga cikin motar, fuskar shi a daure tamau kamar kashi

Duk da Zayd na da murdadan jiki wannan ya ce mishi ba ka san komai ba , kallon shi kadai ya isa hantar ragon namiji ta kada

Takowa ya ke cike da kwarjini ya karaso geffen Inaya ya ja murfin kofar da karfi har sai da ta bale

Hannu ya kai ya damko hannun Inaya , kafin ta yi wani yunkuri ya duka ya saba ta a kafada ya juya ya nufi motar shi

Sai kara Inaya ta ke ta na kai mishi bugu a baya ta na ka sauke ni ka sauke ni , amma ina ko jin ta ba ya yi

Da sauri Zayd ya fito da ga cikin motar ya nufi wannan katon ya na fadin " ina za ka je da ita maza sauke ta "
Ko kallon shi katon nan bai yi ba ya ci gaba da takawar shi

Da sauri Zayd ya sha gaban shi ya matse fuska , ya sa hannu ya cire bakaken glass din shi ya ce " sauke ta na ce "

Hannu katon nan ya daga zai kai mishi bugu
Cak Zayd ya riko hannun na shi ya na kallon shi cikin ido babu ko kiftawa ya daka mishi tsawa ya na fadin " ka sauke ta na ce "

Bai kai ga rufe bakin shi ba ya ji saukar wani mugun bugu a bayan keyar shi , ban take wajen ya fashe ya fara kawo jini

Baiwar Allah Inaya ba ta ma san abun da a le ba dan tun ta gaba karar ta da ta yi ta sume a kafadar wannan katon

Slowly Zayd ya fara sakin hannun katon nan ya zube saman guyiwowin shi ,
Sai ga wani katon shi ma tsaye a bayan shi ya na rike da wata bat irin ta baseball

Ya na ganin Zayd ya zube saman guyiwowin shi, ya kara kai mishi wani bugun a kai , har sai da ya furzo da jini ya fadi kassa a wajen kamar gawa

Ya na ganin ya fadi ya kali katon da ke dauke da Inaya , cikin wata irin murya mara dadin ji ya ce " mu tafi "

Ba musu ya daga kafa ya tsalake Zayd ya bude gidan baya ya kontar Inaya sannan ya zagayo ya shiga geffen driver ya tada motar su ka bar wajen da mugun gudu , kun san dama irin unguwan nin nan na ma su kudi , ba bu kowa a saman hanyar sai Zayd da ke konce a kassa ya na zubar da jini kamar gawa

( TO JAMA'A SU WA NE SU KA DAUKE INAYA ? KAR A JE ZAYD MUTUWA YA YI 😭😭😭😭 )


❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥


( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )



STORY & WRITTEN BY : ANISH


Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 27 ❤🔥

Ya kai wajen good ten minutes a wajen ba ya ko motsi , ya na a haka motar Moussa ta shayo kwana

Wani irin wawan burki ne Mahaman Moussa ya yi , lokacin da idanun shi su ke me arba da Zayd konce, har sai da Abdoul ya kale shi ya na tambayar shi lafya ya danna birki haka

Bai tsaya amsa mishi tambayar shi ba ya bude kofa ya sauka da wani irin gudu ya nufi ya na kwalla mishi kira

Da sauri Abdoul ya bude kofar shi ya sauko shi ma ya nufi Zayd da gudu

Ya na karasowa wajen Moussa ya zube saman guyiwowin shi ya talabo fuskar Zayd ya na fadin " Amir ! Ka bude idon ka Amir ! "
Sai jijiga shi ya ke amma ina ko motsi Zayd ba ya yi , karewar zancen zuciyar shi ba ki daya ta daina bugawa amma Moussa bai lura da hakan ba duk ya bi ya rude

Dafa kafadar shi Abdoul ya yi ya na fadin " mu kai shi asibiti da sauri tun......."

Bai karasa maganar shi ba ya ga Moussa ya mike ya dauki Zayd ya saba a kafada ya koma wajen motar shi da gudu , ya bude gidan baya ya kontar da Zayd sannan ya shiga mazaunin driver ya tada motar ya bar wajen da gudu ko jiran Abdoul bai yi ba


Shi kuma Abdoul bai kawo komai a ran shi ba sai ma motar Zayd da ya shiga , ya tada ya bi bayan Moussa da gudu shi ma

Cikin kankanen lokaci su ka iso wani tanpasheshen private Hospital
Da gudu Moussa ya nufi parking space ya yi parking
Da ya ke yanayin Hospital din na kwararu ne , su na ganin gudun da ya shigo cikin Hospital din da shi wasu nurse su ka fito da gadon da a ke kontar da majinya ta su ka nufi motar Moussa


Su na isowa ko ya sauko da ga gidan driver ya bude baya ya sauko da Zayd ya kontar da shi saman gadon sannan su ka tura su ka yi cikin Hospital din tare da nurse ko kofofin motar shi bai like ba


Su na barin parking space Abdoul ya shigo da gudu da motar Zayd ya yi parking shi ma ya fito da gudu ya shiga Hospital din


Ya na shiga ya ga Moussa tsaye bakin A&E Room ya na kai kawo

Da sauri Abdoul ya karaso wajen ya na fadin " Moussa ya ? Ina Zayd ya ke "

Wani dogon nunfashi Moussa ya ja kafin ya nufi chair din bakin kofar dakin ya zauna ya dafe kan shi da hanayan shi biyu ya ce " Abdoul , wlh in wani abu ya samu Amir Malik ba zai kyale ni ba , na shiga uku ni Diya "

Chair din geffen shi Abdoul ya zauna ya kai hannu ya dafa kafadar shi , ya na fadin " calm down, ba abun da zai same shi in sha Allah ka kontar da hankalin "


Ya na gama fadar haka wayar shi ta fara ringing
Janye hannun shi ya yi da ga saman kafadar Moussa kafin ya kai hannun shi cikin Aljihu ya ciro wayar ya na kallon screen din * my mama * shi ne abun da ya bayana


Mikewa tsaye ya yi ya juya wa Moussa baya kafin ya dauki kiran ya kai waya a kunne ya na sallama

A daya bangaran kuma , Nesrine ce rike da wayar cikin kuka ta ce " yaya Abdoul wasu mutane sun zo sun dauke Abba har su ka jiwa mama rauni yanzu haka ga ta nan konce ta suma " ta kai karshen ta na sakin kuka

Abun da ba ta sani ba tun lokacin da ta ce an dauke Abba ya saki wayar ta fadi kassa ya fice Hospital din da gudu

Moussa ya na kallon shi amma bai tsaya tambayar shi lafya, shi da kan shi cikin mugun hali ya ke a yanzu

Bangaran Abdoul kuma ya na fitowa ya nufi parking space da gudu ya shiga motar Zayd dama key din na hannun shi , ya tada motar ya fice Hospital din a 360 kamar zai tashi sama


Cikin abun da bai fi five ba ya iso gidan , tun kafin ya iso bakin kofar ya ke danna uban horn

Da gudu gateman ya taso ya bude mishi kofar gidan
Da gudu ya danna hancin motar cikin gidan , ko parking space bai nufa ba, ya tseda motar ya sauko ko kashe ta bai yi ba ya nufi falon da gudu


Babu ko sallama ya fado cikin falon
Sai da zuciyar shi ta buga
Falon duk a birkice ya ke kamar an yi dambe a cikin , ga mama nan konce tsakiyar falon , Nesrine na zaune geffen ta sai kuka ta ke

Da gudu ya nufi Nesrine ya Zube saman guyiwowin shi geffen mama ya na fadin " Nesrine wai me ya faru ne haka "

Cikin kukan ta ce " yaya Abdoul wasu mutane ne su ka zo su tafi da Abba , da ya kiya shi ne su ka dake shi su ka tafi da shi da karfi , mama ta yi kokarin tseda su , guda cikin su ya tura ta , ta bugu da bango da ga nan ta fadi ta suma "

" kin gane ko su wanene " ya tambayeta cikin rudu

" yaya Abdoul, wlh ban san su ba , kuma duka sun rufe fuskokin su "

" shikenan kukan ya isa haka dauko min gorar ruwa guda "

Bai kai ga rufe bakin shi ba ta tashi da gudu ta nufi dining room , ta shiga kitchen
Jim kadan ta fito rike da gorar ruwa mai sanyi
Da sauri ya karba ya bude ya zubo kadan a hannun shi ya shafawa mama a fuska

Dogon nunfashi ta ja ta na sauke ajiyar zuciya kafin ta bude idanun ta a hankali ta na kallon ceiling

Ajiyar zuciya Abdoul ya sauke, Nesrine kuma ta fada mata a jiki ta rungume ta

" Nesrine ina Abban ku " mama ta jefo mata tambaya

Mikewa da ga jikin ta Nesrine ta yi sannan ta taimaka ma ta , ta mike zaune

" mama kontar da hankalin ki duk ina Abba ya ke zan kawo miki shi " Abdoul ya ba ta amsa

Ajiyar zuciya ta sauke ta shiga karanto aduo'in tsari cikin zuciyar ta , dan mama irin matanan nan ne ma su ta'amali da Allah, ta san ko kukan ta tsaya yi ba abun da zai anfana gwara ta dinga yi mishi adu'a

Ta na a haka ta ga Abdoul ya mike ya na shirin barin wajen
Da sauri ta tseda shi da cewa " Abdoul ina kuma za ka je "

" mama wlh Zayd ne ya yi accident , yanzu haka ya na cen Hospital "

Kalmar shahada mama da Nesrine su ka yi a tare su na mikewa tsaye
Cikin murya kamar ta mai kuka mama ta ce " ya Allah me ya ke shirin faruwa da mu ne haka "

Da sauri Abdoul ya katse ta da cewa " in sha Allah mama ba abun da zai faru ki kontar da hankalin, bari na koma likita ni "

" a'a tare za mu tafi " mama ta fada ta na yin gaba

Da sauri Nesrine ita ma ta bi bayan ta su ka fice falon
Girgiza kan shi kawai Abdoul ya yi kafin ya bi bayan su ,
Motar Zayd su ka shiga su ka bar gidan a tare

Wannan karan bai yi gudu ba sosai dan ya san mama ba ta son gudu a mota

Sun kai wajen good 10 minutes kafin su iso Hospital din, Abdoul ya yi parking su ka fito su ka shigo cikin

Tun da su ka shigo su ka hango Moussa ya na nan zaune ya dafe kai da hannayan shi biyu

Ya na jin sallamar Abdoul ya dago kai a hankali ya kale shi
Bai amsa mishi sallamar shi ba ya ce " Abdoul lafya na ga ka tafi da gudu "

" wasu mutane ne su ka je gida su ka dauke Abba , yanzu haka Police station zan je na kai kara, su ma dan kar wani abu ya same su ne na taho da su nan " Abdoul ya fada mishi

Ya na shirin magana ya jiyo Muryar Nesrine ta na fadin " yaya Moussa ina Inaya "

Dum ya ji zuciyar shi ta buga a dubu dari ya mike tsaye ya na zaro idanu shi da Abdoul, su sai yanzu su ka lura babu Inaya a wajen da su ka dauko Zayd

Ganin ya yi shiru sai muzurai ya ke da idanu ya sa mama cewa " Moussa ina Inaya ta ke ne , ko ita ma ta ji ciwo ? "

Cike da rudu Moussa ke kallon Abdoul ya ce " Abdoul ni fa ban ga Inaya a wajen da mu ka dauko Zayd, ko dai ta na cikin motar shi "

Girgiza mishi kai Abdoul ya yi kafin ya ce " ni da kai na Zayd ne kawai na gani a wajen , sam tunani na bai kawo Inaya ba ta wajen "

" kai dan Allah ku min bayani yanda zan gane, ina Inaya ta ke " mama ta fada ta na daga murya kadan

A tare Moussa da Abdoul su ka kale ta su ka ce " mama, an sace Inaya "

Sannan Moussa ya daura da cewa " tabass sace ta a ka yi , nassan wajen ceton ta ne Zayd ya ji ciwo "

Bai gama rufe bakin shi ba, Nesrine ta saki wata irin razananiyar kara ta na kiran sunan Inaya , mama kuma sumar tsaye ta yi dama abun da malam ke gudu kenan yau ya tabata

Da sauri Moussa ya nufi Nesrine ya rungume ta dan ya lura ta na neman ta fita cikin hayacin ta , haka ya shiga rarrashin ta har sai da doctor ya fito

Da sauri Abdoul ya nufe shi ya na tambayar shi ya jikin Zayd

" adu'ar ku ya fi bukata a yanzu , mu mun yi na mu aikin " ya na gama fadar haka ya yi gaba zai bar wajen

Sakin Nesrine Moussa ya yi ya taro doctor ya ce " doctor ban gane abun da ka ke fada ba "

" sorry , ya shiga doguwar suma saboda jinin da ya zubar , ga shi ya samu mumunan bugu a kai , mun yi mishi karin jini da duk wani abu da zai bukata amma ba na tunanin zai iya tashi , da wuya ya wuce yau ko gobe , adu'a kawai za ku yi mishi " ya na kai karshen ya bar wajen


Sumar tsaye Moussa ya yi ya shiga girgiza kan shi ya fara juyawa waje guda kamar zarare ya na fadin " na shiga uku , wlh Malik kashe ni zai yi , yanzu shikenan Amir mutuwa zai yi , Kaiii, don Allah in mafarki na ke ku tashe ni " ya kai karshen kamar zai yi kuka


Dafa kafadar shi Abdoul ya yi ya na fadin " ka kontar da hankalin Moussa da izinin Allah zai tashi adu'a kawai za mu yi mishi "

" kai Abdoul akwai matsala in Amir bai tashi ba , wlh akwai matsala , cire min kai kawai Malik zai sa a yi "

Shi dai Abdoul sam bai gane sambatun Moussa ba sai rarrashin shi ya ke , ya na kontar mishi da hankali

Mama da Nesrine kuma ba su da bakin magana dan su ma cikin irin halin Moussa su ke , ba malam ba Inaya to su na ina ? Tashin hankali ba a sa maka date

Ga Zayd konce tsakanin rai da mutuwa , an sace malam da Inaya a rana guda duka wane tashin hankali da me ya yi kama



❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥


( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )



STORY & WRITTEN BY : ANISH


Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

PAGE 28 ❤🔥


After some hours

Inaya

Konce ta ke cikin wani daki baki kirin babu haske ko kadan ciki ko Windows babu

A hankali ta fara motsi ta na karanto kalmar shahada , sannan ta ware idanun ta slowly amma ba ta ganin komai

Mikewa zaune ta yi ta dan jujuyawa ta na fadin " yaya Zayd ka na ina "

Kamar da ga sama ta jiyo Muryar malam ya na fadin " Auta ke ce "

Dum ta ji gaban ta ya fadi nan take kuka ya kubce mata ta na fadin " Abba , Abba , ina ka ke Abba "

" kontar da hankalin ki Auta , kar ki motsa " ya fada mata ya na tashi ya fara laluban ta cikin wannan uban duhu

Cikin sa'a ko ya gano ta da sauri ya Zube saman guyiwowin shi ya na fadin " auta, me ya kawo ki nan "

Ta na jin ya tabo ta ta fada jikin shi ta na kara sautin kukan ta ta ce " Abba , ni ma ban sani ba, mu na tafe ne ni da yaya Zayd, wata mota ta tsaya a gaban mu wani katon mutun ya fito ya dauke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login