Showing 75001 words to 75226 words out of 75226 words
waye wadanan ? "
" Akhie ? " Abdoul ya maimaita kalmar da ya ke shi ya na jin larabci
" Abbi , Ammie , Amira , wadanan nan ma family di na ne so ku kontar da hankalin ku " ya fada da larabci shi ma
Kallon shi Abdoul ya yi baki sake kafin ya ce " Zayd , wadanan Familyn ka ne " ya fada da larabci
Zayd na shirin magana Moussa ya riga shi cewa " Amir ina ga yanzu lokaci ya yi da za ka fadawa kowa gaskiya a kan ka "
Hararrar shi Zayd ya yi kafin ya sa hannu ya raba jikin shi da na Inaya ya zaunar da ita bakin gadon sannan ya kali sauran mutanan dakin ya ce " ku samu waje ku zauna , kun yi tsatsaye sama na " ya kai karshen ya na zama geffen Inaya da duk ta bi ta rikice
Ba musu duka sauran mutanan su ka nufi sofas din dakin su ka zazauna
Amira kuma ta zauna daya geffen Zayd
TO YA KAMATA MU LEKO TARIHIN RAYUWAR ZAYD YANZU
ALHAMDOULILAH ALHAMDOULILAH !
YAU DAI NA KAMALA BOOK 1 DI NA , NA EXILED PRINCE
SAI MUN HADU DA KU A CIKIN BOOK 2 DAN JIN WANENE AINAHIN ZAYD
THANKS A LOT ❤❤