Showing 15001 words to 18000 words out of 75226 words

Chapter 6 - Exiled Princess Book 1 Hausa Novel Complete

Meerah   

13 Dec 2024

295

cewa " no uncle tun da ta na da wanda ta ke ni zan nemo shi in aura mata shi da kai na , baza ta ji dadin zama da mutuman da ba ta so , a karancin shekarun nan na ta bai kama ta ta shiga cikin kunci ba , dama ni ta yi min karama sosai " bai jira amsar malam ba ya juya ya bar wajen


Sai da ya bar wajen sannan malam ya kali Moussa ya ce " wai maganar me ya ke yi ne haka ? "

Dan murmushi Moussa ya yi kafin ya ce " wai zai saki babyn malam tun da ta ce ta na da wanda ta ke so , ku kyale shi yayi ta neman kan shi , zan koma gida sai da safe " ya juya ya bar wajen

Da sauri Abdoul ya yi shirin bin bayan shi, amma malam ya riko hannun shi ya ce " nassan auta ce za ka je daukowa kyale ta, sa safe sai mu je a tare "

Jinjina mishi kai Abdoul ya yi sannan ya juya ya koma cikin gidan malam ya bi bayan shi

Da sallama su ka shigo cikin gidan

Da sauri Nesrine da ke konce ta tada kai da cinyar mama ta na kuka, ta tasso ta tarbo malam cikin kukan ta ke cewa " Abba ina Inaya ta yi ne "

Dan murmushi yayi kafin ya ce " kontar da hankalin ki, ta na gidan mijin ta "

Dan zaro idanu ta yi ta na maimaita kalmar miji cikin ranta

Ta geffen ta malam ya raba ya wuce ya karaso inda mama ke zaune shi ma ya zauna

Shi kuma Abdoul ya wuce bedroom din shi

Ya na zama Nesrine ta juyo da sauri ta nufo malam ta zo gaban shi ta tsaya ta ce " Abba wane mijin kuma, Abba Inaya fa shekarun ta 15 ina ta kai aure ko period ba ta fara ba " duk cikin kukan ta ke mishi wannan maganar ta ma manta da mahaifin ta ta ke magana


Malam na shirin magana mama ta riga shi cewa " yanzu dan Allah malam ina Inaya ta isa aure me ma ta sani a kai , ka hada ta da wanda ba mu san shi ba , wanda ba son shi ta ke ba yanzu in ya je ya cutar mana da ita da wane za muji malam bibiyar da ake mana ko wannan " ta kai karshen ta na sakin kuka

Da sauri Nesrine ta karaso wajen ta ta Zube saman guyiwowin ta ta rungume mama ita ma ta na sakin kuka


" yanzu Amina ya ki ke son na yi kin fi son na saka ido wancen yaron ya gano inda muke ya zo ya dauke mana ita, kuma na fada miki auren ya yi wajen shekara biyu yanzu , kuma ta na son mijin na ta dan ni da kai na na tambaye ta in ta na son shi , ku yanzu a tunanin ku in Sudais ya gano inda muke ba sai ta fi shiga cikin matsa la ba dan Allah ku kontar da hankalin ba abun da zai faru da ita " ya kai karshen ya na kai hannun shi saman kafadar mama


A hankali mama ta dago da ga jikin Nesrine ta kali malam ta ce " shikenan na ji abun ka fada amma ba ka fada min wanene wanda ka aura mata "

Jinjina kan shi ya yi kadan sannan ya ce " ba kowa ba ne face Zayd "

A dubu dari Nesrine ta mike tsaye ta na fadin " Zayd ???? " da karfi ta na zaro idanu, yanzu mutumin da ko hanya ba ta fatan ta hada su wai shi ne mijin kanwar ta, mutumin da ko gani ba ya yi kamm akwai ta


" e Zayd , wanda ke zowa gidan nan wanda ku ke ma kallon makaho da kurma shi din dai " malam ya fada ya na kallon ta

Cikin bacin rai mama ta ce " haba malam, wannan makaho ta ya zai iya kare mana yarinyar mu , ko shi ta kan shi ya ke , ya zai kula da ita, inda ma abokin shi Moussa ne da sauki amma Zayd ? "


Mikewa tsaye malam ya yi cikin bacin rai ya ce " bara ku ji aure dai an riga da an aura ku ba bazai sake ta ba in kun ga dama ku karbe shi in kun ki ku ta matsewa "
Ya na gama fadar haka ya kama hanyar dakin shi ya shige ya bar su nan tsaye


Juya wa ita ma Nesrine ta yi ta koma dakin ta da gudu ta na sakin sabon kuka

Ita ma mama ta juya ta koma dakin ta zuciya ba dadi

Duk abun da su ke Abdoul na jin su amma ya yi banza da su ya yi konciyar shi


Zayd


Bayan ya koma gida kai tsaye bedroom din shi ya wuce, ga Dukan allamu ya manta da Inaya da ke cikin gidan


Shi ma Moussa ya na shigo wa ya wuce kai tsaye cikin falo

A tunanin shi ta na nan amma da ya shigo ya ga ba kowa a cikin falon

Da sauri ya juya ya fita falon ya koma wajen da su ka baro ta

Ta na nan kamar yadda ya baro ta , amma ta daina kuka sai ajiyar zuciya ta ke saukewa a hankali allamun ta yi barci


Dan murmushi yayi kafin ya juya ya koma cikin gidan

Kai tsaye bedroom din Zayd ya wuce

Sai da ya yi mishi knocking sannan ya shiga dakin ya na sallama

Ya na zaune saman gadon shi ya jingina a bayan gadon ga computer a gaban shi , ya cire wadanan glass din na shi na gado


Karasowa wajen shi Moussa ya yi ya tsaya gaban shi ya ce " Amir don Allah je ka dauko babyn malam ta yi barci a wajen motar "

Ba tare da ya dago kai ba ya ce " kai me ya hana ka dauko ta ? "

Hararrar shi Moussa ya yi kafin ya ce " Amir ban San rainin sens ka fi kowa sani ba muharama ta ba ce bazan iya dauko ta ba , dan haka malam tashi ka je ka dauko matar ka "

Dago kai Zayd ya yi ya wurga ma Moussa wani mugun kallo

Shi Moussa dariya ma abun ya bashi dama da gangan ya ki dauko ta , ya zo ya tada shi ya je ya dauko ta


Wani file da ke geffen shi Zayd ya doko ya tila wa Moussa

Da sauri Moussa ya kwace gefe ya na dariya ya ce " to malam da ga taimako na ga dai matar ka ce ba tawa ba in ka ga dama ka bar ta a cen mutu "
Ya na gama fadar haka ya juya ya fice dakin ya shiga bedroom din shi


Dan kauda kai gefe Zayd ya yi ya na jan tsaki a fili ya ce " wlh sai na yi maganin ka, jarabbabe kawai "

Ya na gama fadar haka ya ajiye computer din geffen shi sannan ya sauko da ga saman gadon ya fito dakin

Kai tsaye parking space ya nufa inda su ka baro ta

Ya na zuwa bai tsaya wani dogon tunani ba ya sa hannayan shi biyu ya dauke ta cak kamar baby ya koma cikin gidan da ita


Maimakon ya wuce bedroom din shi da ita sai ya kontar da ita saman doguwar sofa sannan ya juya ya koma bedroom din shi ya ci gaba da aikin shi


Washe gari


Inaya


Washe gari ba ta farka da ga barcin wahalar ta ba sai wajen karfe 10 na safe, ko da ta farka ta ga ba motsin kowa a cikin gidan allamun sun fita


Jin hakan ya sa ta mikewa ta fara takawa ta bar falon ta fito harabar gidan
Abun mamaki babu motar nan a cikin gidan, to ta ina ta fita ?

Ganin ba ta da me ba ta amsa kawai sai ta sa kai ta bar gidan baki daya ta koma gidan su

A hankali ta ke tafiya kamar wadda a ka zarewa lakar jiki har ta karaso gidan su

Bakin ta dauke da sallama ta shigo gidan

A hankali mama ta dago kan ta, ta amsa mata sallamar ta

Ganin ita ce ya sa mama sakin wani dan murmushi ta ce " Auta zo nan ina son magana da ke "

Ba musu ta tako a hankali ta zo geffen mama ta zauna ta na sunkuyar da kai ta na gaishe ta


Sai da mama ta amsa mata sallamar ta sannan ta ce " Auta a ina ki ka kwana ? "

Ba tare da ta dago kai ba ta ce " gidan su yaya Moussa " ta fada a takaice

Jinjina kan ta mama ta yi kafin ta ce " Auta fada min gaskia ki na son Zayd a yadda ya ke hakan ? "

Sai da ta dan doki lokacin kafin ta dago kan ta slowly ta ce " shin mama ko ina son shi ai yanzu lokaci ya kure, Abba ya aura min wani cen daban wanda ban sani ba " ta kai karshen kuka na kubce mata
Ta tashi da gudu ta shige dakin su


Mama sai kiran ta take amma ina sam ba ta jin ta

Dama tambayar da ta yi mata dan ta tabbatar da abun da malam ya ce na ta na son mijin ta, gashi ta tabbatar amma ta lura ita Inaya ba ta san waye mijin na ta ba , ta so ta fada mata ta ki tsaya wa


Jinjina kanta kawai mama ta yi ta ci gaba da yanke kayan lambun sa ke gaban ta


❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥


( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )



STORY & WRITTEN BY : ANISH


Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡


PAGE 7 ❤🔥


Bayan ta shiga bedroom din su , kai tsaye saman gadon ta Haye ta yi rub da ciki ta na sakin sabon kukan


Ta na shiga bedroom din su Nesrine ta shigo gidan ta na sallama hannun ta rike wasu ledodi allamun mama ta aike ta cepane , amma duk yanayin face din ta babu alamun fara'a a cikin


Inda mama ke zaune ta karaso ta zauna ta na ajiye ledodin gaban ta sannan ta ce " mamwawai har yanzu Inaya ba ta dawo ba ? "

Murmushi mama ta yi kafin ta ce " hmmmm ta dawo ta na cikin dakin ku "

Da sauri Nesrine ta mike ta nufi dakin su da gudu

Kallon ta mama ta yi ta saki wani dan karamin murmushi ta ce " ke ma Allah ya ka miki mijin auren in rabu da wannan shirman naki "


Nesrine kuma ta shiga dakin su ba budurwa ko sallama ta hango Inaya konce saman gado ta yi rub da ciki sai kuka ta ke


A hankali ta tako ta karaso bakin gadon ta zauna ta kai hannu ta, ta dan bubugi kafar Inaya


Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juya a hankali ta mike zaune ta kai hannu ta dauki pillow din ta , ta rungume shi a kirjin ta ta na kallon Nesrine

Dan murmushi Nesrine ta yi kafin ta kai hannu kan face din ta , ta goge mata hawayen ta sannan ta ce " haba sister di na, na miye kuka kuma ? "

Hadiyar zuciya Inaya ta yi kafin ta ce " Nesi wai fa ki na ji Abba aure ya yi min , ni fa wlh ina da wanda na ke so ba ni son wadan aka aura min " ta kai karshen ta na boye face din ta cikin pillow


" sannu malama yanzu har kin San minene so ? " Nesrine ta fada cikin sigar zolaya

Dago kan ta ta yi ta wurga mata hararra

Yar dariya Nesrine ta yi kafin ta ce " shikenan yi hakuri ai ni dama sai da na fada miki , ba wadda za ta iya son wacen makaho ga shi kuma kurma am........."

Ba ta ida maganar ta ba Inaya ta katse ta da cewa " wai dan Allah me ya yi miki a duniya da ki ka tsane shi haka, na ga bai taba shiga harkar ki ba , ko gaisuwa ba ta taba shiga tsakanin ku ba amma kin dauki tsanar duniyar nan kin daura mishi, in ke baki son shi toh wlh akwaye ma su son shi dayawa a duniya ciki har da ni "
Ta na gama fadar haka ta tila pillow din hannun ta gefe sannan ta diro da ga saman gadon ta fice dakin


Ta na fita Nesrine ta rike habar ta ta ce " yanzu fa ta ce ba ta son shi amma wai shi har da kare shi yanzu ko a tunanin ta ita kadai ke iya cewa ta na son shi ko ba ta son shi "
Dan tsaki ta ja sannan ta mike ta fito dakin

Ta dawo inda mama ke zaune ta zauna ta na tsuke fuska ta ce " wai wannan yarinyar minene matsalar ta , yanzu fa ta ce ba ta son yaya Zayd, yanzu kuma za ta sake cewa ta na son shi "

Yar dariya mama ta yi kafin ta ce " kyale ta haba ina ga ba ta san da shi ne Abba ya aura mata "

Kauda kai gefe Nesrine ta yi ta na tsaki ta ce " yanzu dan Allah mama haka za mu zuba ido mu na kallo Abba ya bawa wacen makahon auren Inaya, yanzu da wane ido zai kula da ita , da wane bakin zai yi mata magana ni fa gaskia ban yarda da hakan ba "

" toh Nesrine ya za ki yi na ga ba ki da izinin raba auren nan , ko kin ki, ko kin so Inaya matar Zayd ce , ni gwara ZAYD din ma da wancen dan iskan Sudais , ko ba komi ya na da tarbiya da kyawawen halaye kuma nakassar shi bai sa ya zama rago ba, ki na gani tun safe ya ke fita ya tafi aiki duk da baya gani da kan shi ya ke neman abincin shi, to me ya fi wannan ka ci halal din ka , ko wa ya na maka shedar mutumin gwarai, bara ki ji , ni wlh ko da ya fi makaho da kurma, zan aura mishi Inaya dan na san zai kula da ita duk da ba mu San assalin shi ba shekara hudun nan da mu ka yi da shi ya isa ka gane shi wane irin mutun ne "


" hmmmm yanzu kennan mama kin yarda da auren nan, autar ta mu guda za a dauka a bawa kurma, makaho wanda bai ma san da me ta ke kama ba "

Yar dariya mama ta yi kafin ta ce " to ina ruwan Allah da wannan ai zuciyar mutun ya kamata ki duba , sai ki ga mutun kamar shi ya yi kan shi dan kyau amma zuciyar a bushe ta ke kamar kafiran farko, amma sai ki ga wanda bashi da kyau ya na da zuciya mai kyau tsarkakiya, ke yanzu a ganin ki Zayd bai fi Inaya kyau ba kuma a hakan ya yarda ya aure ta , duk da bai gan ta ba kin ga wannan auren na su ya ishe ki ishara Allah ba ya barci , kaddara ce kawai ta hada su , amma ba dan haka ba ni na san inda zayd na da cikakiyar lafya wlh ko inda ya taka ba ki kai ki taka ba "


Nesrine na shirin magana Inaya ta fito da toilet, ta wuce bedroom din su ko kallon inda su mama su ke ba ta yi ba

Dan zaro mama ta yi ta na girgiza kai sannan ta ce ma Nesrine " kin ga tashi ni ki yi min aiki na "

Da to Nesrine ta amsa mata sannan ta tashi ta shiga kitchen

A takaice ranar yau Inaya a cikin bedroom din su ta yi ta, ko harabar gidan ba ta leko ba, abinci ma sai Nesrine ta kai mata daki su ci , abu guda ke fido ta sallat ,
Zayd kuma yau tun safe da su ka bar gidan shi da Moussa har bayan sallar isha ba su dawo ba

Washe gari


Yau ta kama ranar monday, tun karfe 6 Nesrine da Inaya su ka tashi su ka yi duk wani aiki na gidan sannan su ka shirya sai karfe 7:30 su ka bar gidan su ka kama hanyar college

Tun bisa hanya Nesrine ke yi ma Inaya magana amma ta kyale ta ko kallon ta ba ta yi ba
Sai da abun ya bawa Nesrine haushi ta daina mata magana ma
Har sai da su ka iso AMINU KANO COLLEGE OF EDUCATION sannan ko wace ta wuce class din ta

11pm

Zaune ta ke cikin cafeteria din school din , ta na rike da book , ga bottle drinks nan a gaban ta saman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login