Showing 51001 words to 54000 words out of 75226 words
murmushi ya kai hannu ya dan bubugi kumatun ta
Shiru ko motsawa ba ta yi ba , sake bubuga ta ya yi nan ma shiru ba ta motsa ba
Da sauri ya kai hannun shi wajen hudar hancin ta , nan ya ji ko nunfashi ba ta yi
A razane ya mike tsaye ya na kallon ta ya na zaro idanu ya na fadin " no no no ba dai mutuwa ta yi ba "
Bai kai ga rufe bakin shi ba ya ji kara a na kokarin bude kofar falon za a shigo
Da sauri ya juyo ya na kallon kofar zuciyar shi na duka uku uku , dai'dai lokacin da Hafiz ya shigo gidan kai a sunkuye ya na sallama
Dum Moctar ya ji gaban shi ya fadi ya kassa ko wani motsin kirki
Hafiz kuma ya na dago kai idanun shi su ka sauka kan Nesrine da ke konce naked saman sofa cikin jini
Slowly ya dago kai ya kali Moctar da ya yi sumar tsaye ya na kallon Moctar
A hankali Hafiz ya fara takowa ya nufi Moctar ya na kallon shi cikin ido
Wasu yawu Moctar ya hadiye kafin ya bude baki murya na kerma ya ce " bro me ka k......"
Bai kai ga karasa maganar shi ba Hafiz ya kai mishi wani wawan bugu a ciki har sai da ya zube saman guyiwowin shi ya na daura hannayan shi saman ciki
Cikin bacin rai Hafiz ya kai hannu ya damko kwalar rigar Moctar ya mikar da shi tsaye ya daka mishi tsawa ya na fadin " why za ka min haka Moctar , why ? ka fi kowa sanin irin son da na ke yi ma Nesi , kafi kowa sanin auren ta na ke son yi har Daddy ya san da maganar, shi ne za ka yi mata haka , me ta yi maka , me ya sa za ka karbi abun da ya ke nawa "
Ya kai karshen ya na sakin shi ya sake zubewa saman guyiwowin ta , shi kuma Hafiz ya nufi Nesrine , ya zauna bakin sofar ya kai hannu ya dan bubuga ta ya na fadin " baby please tashi , i'm sorry kin ji zan yi maganin shi , tashi don Allah "
Shiru ko motsi ba ta yi ba , sa sauri ya kontar da kan shi saman kirjin ta ya na son ya ji bugun zuciyar ta , sai dai kuma shiru zuciyar ta ba ta bugawa
Da sauri ya mike tsaye ya na girgiza kan shi ya dunkule hannu ya bugi table din tsakiyar falon har sai da ta watse glass din ya fassa mishi hannu
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 22 ❤🔥
Da sauri ya mike tsaye ya na girgiza kan shi , ya dunkule hannun shi ya bugi table din tsakiyar falon har sai da ta watse glass din ya fassa mishi hannu , sai zubar da jini ya ke , duk ya bi ya birkice idanun shi sun yi jazir don bacin rai
Cikin fitar hayaci da kai ma Moctar bugu a fuska har sai da bakin shi ya fashe , ya na fadin " na tsane ka Moctar , ka na matsayin kane na amma za ka ci zarafin matar da zan aura , duk irin iskancin da mu ke yi ka fi kowa sanin ko so guda ban taba kallon mace da sunnan so sai a kan ta , shi ne za ka kashe min ita , me ta yi maka Moctar , me na yi maka ? " ya kai karshen kamar zai yi kuka
Cikin kuka Moctar ya dago kai ya kale shi ya ce " i'm sorry bro , wlh ban si yin hakan ba zuciya ya ce kawai ta debe n......."
Bai karasa maganar shi ba Hafiz ya sa hannayan shi duka biyu ya tura shi ya fadi kassa ya ce mishi " ka je cen kaida zuciyar ka , ka kashe ta , ka huta ko ?"
Ya na gama fadar haka ya juya cikin bacin rai ya Haye stair ya bar Moctar nan konce
Jim kadan ya sauko rike da jallabiya dark blue , bai tsaya bin ta kan Moctar da ke konce kassa ba , ya nufi Nesrine ya saka mata jallabiyar sannan ya dauke ta cak kamar baby ya fice da ita , ya nufi motar shi ya kontar da ita gidan baya
Sannan ya juya ya koma cikin gidan inda ya bar Moctar nan ya tardo shi , ya na zaune saman guyiwowin shi ya sunkuyar da kai
A hankali ya tako ya tsaya gaban shi ya ce " duk abun da ka yi bazan iya cire ka ba a matsayin dan uwa na ba , amma wannan abun da ka yi bazan iya yafe maka shi ba , Moctar ni ka yi wa ba ita ba , ka sani wannan abun da kayi bazan kyale ka ba a haka , ka jira kiran yan sanda " ya na gama fadar haka ya juya ya bar wajen
Kai tsaye motar shi ya nufa ya shiga ya bar wajen da uban gudu
Dai'dai lokacin da Moctar ya fito da ga falon ya na kiran sunan Hafiz amma ina ya tafi
Da sauri ya koma cikin falon ya dauki wayar shi da ta fadi kassa ya shiga kiran layin babban shi
Cikin fitar hayaci ya kira Abban shi kira na farko ya daga kiran , babu ko sallama ya ce " Daddy please help me , big bro kara ta zai kai police station "
Da sauri ya katse shi da cewa " calm down my son , kontar da hankalin ka ka fada min abun da ke faruwa "
Wasu yawu ya hadiye kafin ya fara ba shi labarin duk abun da ya faru tun haduwar su da Inaya har zuwa yanzu maganar da Hafiz ya yi mishi
Cikin ko in kula ya ce " kontar da hankalin ba abun da zai faru da kai , yanzu ka yi zaman ka a nan gidan gonar zan ji da Hafiz "
Da to ya amsa mishi kafin ya sauko da wayar ya kashe kiran ya koma bakin sofa ya zauna ya rike kan shi da hannayan shi duka biyu
NESRINE
da mugun gudu ya bar gidan gonar cikin abun da bai kai one hour ba ya isa cikin gari
Kai tsaye police station ya wuce da ita ya shiga da wani matsanincin gudu , dai'dai lokacin da su Zayd su ka bar police station din su ka koma gida
Ya na shiga ya yi parking , maimakon ya fito sai ya tsaya ya kontar da kan shi saman steering din motar
Sai da ya dauki lokaci a hakan kafin ya dago kan shi slowly ya bude kofar motar ya fito , sannan ya bude kofar bayan ya dauko Nesrine da ke konce kamar gawa
Ya shiga police station din, dai'dai lokacin da DPO ya bada umarnin a tafi neman Nesrine
Ya na sallama ya shigo police station din , duk officer din da ke wajen sai da su ka sara mishi dan sun san wanene Hafiz
Jinjina musu kai ya yi kafin ya nufi wani banci sa ya hango cen gefe ya kontar da Nesrine ,
Sannan ya dago kai ya kali dayan officer cikin sanyin murya ya ce " ina son ganin DPO "
Da sauri dayan officer ya juya ya nufi office din D.P.O
Ko minti daya bai yi ba su ka fito shi da D.P.O
Ya na sauke idanun kan Nesrine ya nufe ta da sauri ya na kare mata kallo , cike da rudu ya dago kai ya kali Hafiz ya ce " Hafiz ina ka samo yarinyar nan ? Yanzun nan mu ke shirin fita neman ta " da ya ke ya san Hafiz ya na yawwan zuwa gidan su amma shi sam bai san halin Hafiz ba
Cikin wata sanyayar murya ya ce " uncle ku yi hakuri bazan iya fada muku inda na dauko ta ba, amma please ku taimaka ku fara kai ta Hospital da sauri kafin ku kira ahalin ta bazan so su gan ta cikin wannan halin ba "
Ya kai karshen ya na sa hannun shi cikin aljihu ya ciro bandir fin kudi dan dari biyar biyar ya mikawa D.P.O ya ce " ga wannan ku kai ta asibiti amma don Allah duk abin da likitan zai fada muku ya tsaya a iya tsakanin ka da shi please " ya kai karshen ya na marairaice fuska sannan ya juya ya fice police station din
Ya na barin wajen wayar D.P.O da ke cikin aljihun shi ta fara ringing
Da sauri ya sa hannu cikin aljihu ya ciro wayar ya na tunanin ko Zayd ne ya sake kiran shi
Amma sai ya ga governor ne da kan shi ya ke kira, sa sauri ya daga kiran ya kai kunne ya na sallama
Bai tsaya bin ta kan sallamar shi ba ya ce " D.P.O ina son case din yarinyar da Hafiz ya kawo ya mutu ba na son maganar nan ta fita waje "
Da sauri D.P.O ya katse shi da cewa " bai fadi komai a kan ta ba cewa kawai ya yi a kai ta Hospital da ga haka ba wani abu da ya fada , amma familyn ta sun zo sun yi report a kan batar ta "
" that's good , ba ni son a bude wani file a kan ta kawai ka kaita Hospital ba na son kowa ya san abun da ya faru da ita maganar da tsaya da ga ni sai kai , ba shawara na ke baka ba , umarni ne da ga na sama da kai " ya na gama fadar haka bai jira amsar D.P.O ba ya katse kiran
Kallon wayar D.P.O ya yi cikin ranshi ya na tunanin wai me ya samu yarinyar nan ne da governor da kan shi zai ce a kashe case din ta
Ya dan jima a haka kafin ya kali dayan officer ya ce ya tada mishi mota zai kai ta asibiti shi kadai
Bai kai ga rufe bakin shi ba officer din ya fita da gudu , shi kuma D.P.O ya duka ya dauki Nesrine ya fice da ita ya nufi motar da officer ya kawo mishi bakin kofar
Da sauri ya bude kofar baya ya kontar da Nesrine sannan ya shiga mazaunin driver ya tada motar ya fice
Cikin abin da bai fi 20 minutes ba ya isa babban Hospital na garin kano
Kai tsaye parking space ya nufa ya yi parking sannan ya fito ya bude kofar baya ya dauko Nesrine ya shiga likitar da ita
Ya na shiga ko nurse ta tafo ta na ture da gadon jinya ta ce ya kontar da Nesrine sannan ya tafi reception ya cika duk wasu files da kuma kudin duba ta
Ba musu ya kontar da ita sannan ya juya ya tafi reception , kudin da Hafiz ya ba shi ya ciro ya biya , sannan ya koma saman chair din reception ya zauna ya na jiran doctor ya fito
After one hour
Bayan awa daya doctor ya fito da ga A&E room ya nufi D.P.O
Tun da D.P.O ya gan shi ya mike ya tunkare shi ya na tambayar shi me ya same ta
" mu je office di na mu yi magana " doctor ya fada ya na juyawa ya nufi office din shi
Da sauri D.P.O ya bi bayan shi su ka isa office din shi ya ce mishi ya zauna
Ba musu D.P.O ya zauna ya na fuskantar doctor ya ce " please doctor me ya same ta ? "
" calm down D.P.O , zan fada maka komai amma zan so in san minene alakar ka da ita ? " doctor ya fada ya na tsare shi da ido
" ban san ta ba, kawai an kawo karar cigiyar ta ne , saurayin sa ya kawo ta ne ya ce na fara kai ta likita kafin na kira familyn ta "
Jinjina kan shi doctor ya yi kafin ya ce " ya yi tunani mai kyau dan na san idan su ka gan ta cikin wannan halin ba za su yi dadi ba "
Da sauri D.P.O ya katse shi da cewa " don Allah doctor fada min me ya ke damun ta ne "
Cikin sanyi doctor ya ce " calm down , zan fada maka , gaskia sai dai ku yi hakuri raping din ta a ka yi , ga Dukan allamu kuma ba sau daya ba har dinki sai da mu ka yi mata , sannan ta zubar da jini dayawa hakan ya jefar da ita cikin doguwar suma , ta yiyu ta tashi ko kuma akasin haka , i'm sorry "
" Ina'lillahi wa'ina illaihi raji'un " shi ne kadai abun da ya ke fitowa da ga bakin D.P.O
Cikin ranshi ya na fadin " kenan shi ya sa governor ya kira ya ce a kashe case din dan ya san dan shi ne ya yi aikin "
Shi a tunanin shi Hafiz ne ya yi hakan saboda shi ne ya kawota sam bai kawo Moctar a rai ba
Ya na a haka ya tsinci Muryar doctor ya na fadin " ya kama ta ku kira familyn ta ku fada musu mun riga da mun yi na mu aikin , yanzu haka ku na iya zuwa ki gan ta an sauya mata daki "
Godiya D.P.O ya yi wa doctor kafin ya mike ya fice office din ya tafi dakin da a ka kontar da Nesrine
Bai fi ten minutes ba ya fito ya kira Moussa ya sanar da shi inda su ke
❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤
(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥
( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )
STORY & WRITTEN BY : ANISH
Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 22 ❤🔥
STORY 🔥
A hankali Zayd ya juyo ya na kallon D.P.O ya na shirin magana Moussa ya rika shi cewa " D.P.O ka ba ni amsa mana , kun kamo wanda ya yi mata hakan "
" ku yi hakuri bazan iya kama shi ba , umarni a ka ba ni daga sama a kan na rufe case din nan , ko da na san wanda ya yi hakan bazan iya kama shi ba , kuyi hakuri " D.P.O ya fada cikin rarrashi
Da karfi Moussa ya ce " what ? Kun san wanda ya yi mata hakan, ina ruwa na da umarni da ga sama ya yi laifi dole a kama shi ....."
Da sauri Zayd ya dafa kafadar shi ya katse shi da cewa " Diya yi hakuri , abun da ya faru ya riga da ya faru , ko da an kama shi bazai goge abun da ya yi mata ba " ya fada cikin nitsuwa
Katse shi Moussa ya yi da cewa " Amir me ka ke fada haka kennan yanzu ya yi mata hakan ya ci bilis kennan ba za mu dauki wani mataki a kai ba "
Girgiza mishi kai Zayd ya yi kafin ya ce " a'a bai ci bilis ba , ya je shi da Allah , nasan dole ka ji zafin abun da ya faru saboda son da ka ke mata , amma ka san ba laifin ta ba ne abun da ya faru , nasan da wuya yanzu a ce ka ci gaba da son ta bayan abun da ya faru , ina mai baka hakuri a madadin ta "
Ya na kai karshen ya juya ya fara takawa zai bar dakin
Har ya riko handle din kofar ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya ce " zan yi magana da doctor , za mu tafi da ita Abuja yanzun nan , za a ci gaba da kula da ita a cen , idan har yanzu ka na da sha'awar auren ta ka min magana zan nema maka auren ta wajen uncle "
Ya na gama fadar haka ya yi ficewar shi ya bar D.P.O da Moussa nan tsaye
Sai da ya tafi sannan D.P.O ya ce da Moussa " ni zan tafi , don Allah ina mai kara ba ku hakuri akan abun da ya faru " sannan shi ma ya ficewar shi
D.P.O na fita Moussa ya zauna saman chair din bakin gadon ya zubawa Nesrine ido
Bangaran Zayd kuma ya na fita ya nufi office din doctor ya sanar dasshi zai kai yar uwar shi Abuja za a ci gaba da kula da ita a cen
Ba musu doctor ya yarda ya sa a ka shirya musu ambulance din da za ta dauke ta
Da ga haka kuma ya baro likitar baki daya ya yi tafiyar shi
After some minutes ya iso gidan malam
Kai tsaye gidan ya shiga ya na sallama , ban ya isko duk mutanan gidan su na zaune harabar