Showing 45001 words to 48000 words out of 153675 words

Chapter 16 - Kyawuna Jarabta Ta Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

15 Dec 2024

609

kwance, karasawa tayi gaban gadon zama tayi tashafa fuskanta ahankali tace "yammatana atashi daga bacci, Du'a Du'a" da kyar Du'a tabude idanunta takalli Grandma cikeda bacci a ido batare datai magana ba, kumatunta Grandma taja tace "da ace yanda kikeson bacci haka kikeson cin abinci danaji dadi saisa kullum cikinki kaman ana diba ayi biyan bashi dashi tsabagen yanda yake ashafe kaman cikin jinjiri" dan murmushi tayi saikuma ta jinkirto tadaura kanta akan cinyan ta takama hannun Grandma dake kan fuskanta ta rungume ajikinta sosai ahankali tace "Grandma agidan ki kadai nasami farin ciki haka tunda aka haifeni, Grandma please karki bari Abba yakomar dani gidanshi I am so happy anan da I don't wanna leave, da kullum sainai kuka Ya Hamad kadai ke lallaahina da Aneela" fadada murmushin dake kan fuskanta Grandma tayi tana kallonta tace "bazaki komaba ai nagayamiki sai inda karfina yakare babu wanda zai kara wahalar min dake, yanzu addu'a na shine Allah yakawo miki miji nagari" murmushi tayi sosai saikuma ta tashi tazauna takalli Grandma tace "Grandma nina isa aure ne? Ya Nana da Ya Hawwa fa duk basuyi aure ba, kumama ai sai mutum ya iya girki akemai aure ko nikuma ban gama iyawaba tayaya zanyi aure to"? sosai Grandma ke kallonta yanda take maganan saida tagama maganan sanan taja hancinta tace "har wayauma baki gamayiba dan Aneela zata iya sayarda ke agaban idanunki baki saniba, tashi kiyi salla ki shirya yau akwai office" gyadama Grandma kai tayi tana tashi ta sauka daga kan gadontai hanyar bayi kananun kalaban da aka mata sun zubo har waist dinta suna lilo kaman wata balarabiya tabude kofa tashiga bayi, ajiyan zuciya Grandma databita da kallo ta sauke sanan ta tashi ahankali tafice daga dakin.


Saida tashiga bayinma taga batada salla daman tun jiya takejin ciwo ciwon ciki, brush kawai tayi tai wanka da ruwan zafi sosai tafito daure da towel tanada feeling ciwon ciki kadan kadan dayake ita batada wanan serious ciwon aran nan saidan dan ciwon ciki kadan hakanan, wani black mickey riga tasaka, t-shirt ne amman irin na baccin nan babban gaske daya saukan mata har guiwa, batabi takan kama gashinta ba tasake shi ahaka yana lilo abinshi, komai ma bata shafa fa tasaka slippers dinta tabude kofan dakinta tafito ahankali, dakin Grandma tayi ganin bata ciki yasa tamaida kofan tarufe tai hanyar stairs tana sauka kasa, ganin Grandma zaune kan kujeran dakin rikeda Al Qur'ani tasaka glass a idanunta tana karantawa yasa takarasa wajenta zama kusada ita tayi ahankali batare datai magana ba tana sauraron yanda Grandma ke karatun anatse Akuma hankali Aya ta dire sanan takalli Du'a din alamun ya akayi, ashagwabe tana wani turo baki kaman yar baby tace "Grandma good morning cikina naciwo kadan kadan, MP ne, kinada magani"? girgiza mata kai Grandma tayi tace "bari zansa akawo miki, yanzu tashi kidebo ruwan lipton a flask kije daki kisha saikidan kwanta kafin lokacin zuwa office yayi" gyadamata kai tayi ta tashi dinning tayi cup tadauka tadauki flask ta tsiyaya ruwan shayi dayasha kayan kamshi sanan tadauki spoon tasa a cup din tawuce tai stairs tana tafiyan nan nata ahankali tana kallon shayin da kamshin shi sai ratsa mata hanci yakeyi, tsayawa tayi chak jin wani irin sanyi ya ratsa kafafunta dakenan abude zuwa jikinta gabaki daya, wani dan kara tafitar daga bakinta ashhhh sanan taduka kaman wacce zatai ruku'u tana duba kafafunta tana daga kafanta sama tana duba tafin kafan kota taka kankara ne ganin babu abinda ta taka yasa ta dago tacigaba da tafiya ahankali tana hawa stairs din zuwa karshe tashiga falon sama daidai Asad shima yafito daga corridor hanyar dakinshi yashigo cikin karamin falon yana lazy tafiyan nan irin na wayanda suka sha bacci, wani irin hada idanu sukayi dagashi har ita, chak ta tsaya tana kallonshi da duka idanunta awaje kaman zata hadiyeshi da ido, yana sanye da kayan jiya dataganshi dasu a hotel dinnan bambamcin kawai shine babu jacket din suit din da neck tie da alamu yaciresu ne, farin long sleeve t-shirt din ciki ne kawai ajikinshi daya bubbude boturan gaban rigan har zuwa kasan kirjinshi kana iya gashin kirjinshi dasuka kwanta lubbb idanunshi sundan tashi da fuskanshi lips dinshi sunyi pink yirrrr alamun yasha bacci sosai looking a bit scattered kaman ba shiba, yanda take kallonshi haka shima yake kallonta da wanan expression nashi dinan dabaka taba gane takamaimen wani yanayi yake ciki.


Wani irin rawa hannun data rike mug din shayin ta dashi ne yashiga wani irin rawa tana kallonshi jikinta na bar bar da batasan mesaba takasa koda motsi, tundaga kafa yakalleta zuwa kai saikuma ya basar kaman bai ganta ba yacigaba da tafiyanshi normal normal yazo tagefenta zai wuce kamshin da jikinshi keyi yawani yi splashing akan fuskanta wani irin salubewa mug din hannunta yayi ruwan shayin ya bare some of it yazuba akan kafanta kofin yay wani kara yahau tsalle yana tsaltsalleke stairs kafin daga bisani ya tarwatse, wani irin runtse idanunta tayi gam jin yanda kirjinta ke bugawa dum dum kaman zai fita jinta kusada shi kaman jikinshi zai gogi nata yattsun kafanta namata radadin zafi amman takasa ihu sabida yanda tashiga wani yanayi, wani irin beating kirjinta yakeyi tanajin sahun tafiyanshi yanabi ta gefenta yawuce yay stairs abinshi mayen kamshin turarenshi yagama wanke mata numfashi yasauka daga stairs din yay falo abinshi.



Sai alokacin tabude idanunta wani irin zama tayi a kasan wajen dagudu takama kafarta tadaura akan cinyanta tana hura yatsunta dake mata radaddin azaban zafi sosai tana kuka sosai amman mara sauti tana hura kafan.......


Zama yayi kusada Grandma dake karatu abinta har lokacin, murya chan kasa irin nawanda yasha bacci sosai yakoshi dinan yace "good morning Grandma" saida takai Aya sanan tai addu'a tarufe Al Qur'ani takalleshi tace "wanan bacci dakasha haka kaga yanda kai subu subu kuwa kaman wanda yay kwana uku yana bacci" dan murmushi yamata tareda lumshe ido yabude baice komiba, tashi tayi tace "bari kaga nakawo maka shayi mai zafi kasha zaisa kadan saki ko" gyadamata kai yayi yana kwanciya kan kujeran data tashi kaman wani dan yaro, itakuma tai hanyar dinning harzata wuce saikuma idanunta suna sauka kan mug daya gangaro zuwa nan stairs na kusa to the last dasauri takalli sama ganin Du'a zaune tana hura kafa tana share hawaye yasa tace "subhanallahi Du'a meya sameki kike kuka haka? Ince badai kin koma kafarki ba shine baki kirani ba" tai maganan tana hawa sama, tana kaiwa wajen takarbi kafan tana kallo aiko gashi nan yatsun sunyi jajir alamun sunsha ruwan zafi, hannunta takai takama kafadar Grandma tana kuka sosai mara sauti tace "Grandma zafi wlh" dasauri Hajiya tashiga kwalama Razika kira. "Razika Razika" Razika dake daki fitowa dagudu tari jin Hajiya na kwalamata kira, turus ta tsaya afalon tana kallon Asad dake kwance abinshi idanunshi bude kaman yasan ta inda zata fito kenan kallonta yayi shima, fitowa Shemau tayi ganin Asad yasa dasauri tadan rusunna tace "ina kwana" gyadamata kai kawai yayi batare data amsaba hakan yasa Razika itama tace "ina kwana" ko kallonta baiyiba yadaura idanunshi kan TV dasauri duk sukai stairs, Grandma tace "kawomin zuma Razika Du'a tazuba shayi akafa" dawani irin sauri tajuya tace " to" zuman dake dinning tadauko tadawo sama, karba Grandma tayi tashafamata sanan takalleta idanunta sunyi jajir tace "sannu dena kukan to" gyadama Grandma kai tayi tana share fuskanta takalli Razika tace "kaita dakinta ke Shemau biyoni ki debi wani shayin ki kaimata saiki gyara wajen nan" duk amsawa sukayi da to sanan tawuce kasa, Ganin Asad na nan inda tabarshi yasa tace "wai jikata ce shayi ya bare ayatsun kafarta take kuka shegen raki irin na Du'a bawani konewan kirki bane bafa, itace jikata datazo daga kano yar wajen Zainab, bari kaga nabaka shayin ka".



💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫


✍️ M SHAKUR

This book is 500 nakusan gama free pages, you can join the group by paying 500 into 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment ta watsapp number na wa.me/+2347012181461 sainai adding naki to the group.


free page
EPISODE 2️⃣8️⃣

Zubomai shayin tayi a mug dakanta sanan tadawo kusada shi kafanshi tadauka tace "sit up my friend" dan murmushi yamata yatashi yazauna tareda mika hannu yakarbi shayin yace "thanks Grandma, you are the best you know that right" murmushi tamai tace "nasanar da Ammin ka kana nan, ya TV show dakayi angama lpy"? yatsine fuska yayi yakurbi shayin kadan yacire daga baki yace "it was stressful but Alhamdulillah nagama" dan dariya tayi tace "kai Asad, yanzu dai mezan dafamaka yau kaci ka koshi" ahankali yace "rice and beans nakeso Grandma" "kaida shinkafa da wake Asad shikenan zan dafamaka" murmushi yamata yace "Grandma bakiyi fushi dani ba tunda nadawo banzo ba" hararanshi tayi tace "ja'iri ashe kasan kayi laifi" dariya kadan yayi yana kurban tea, tace "ai nayi fushi dakai but Sharif nata gayamin how busy u were saisa andena fushin, yanzu daka gama bagaka kazo ba, ai ba'a raba jika da kakanshi" hira suka cigaba day haryana bata labarin aikinshi sosai taji dadi yanda yasake dudda batamai maganan abinda yasameshi jiya ba, saida yagama tass sanan ya ijiye cup din yace "Grandma bari naje na shirya natafi office, I have huge work awajen ma" tashi tayi tace "tafi Asad, Allah yataimaka kaji, nidai kadingayi kana neman mata inaso naga jikana kafin namutu" yatsine fuska yayi irin ewww dinan bayamason maganan sanan yawuce yafita daga falon yatafi itakuma Grandma takoma tai zamanta dan akwai shirin dazata kalla.
**


Zaunar daita Razika tayi akan gado sanan takoma tarufo kofa dagudu tanadan zaro idanu tace "naga mutumin jiya a falo Du'a biyomu yayi ne" cikin tsoro muryanta dabai gama washewaba sabida yanda tai kuka tace "nima shina gani bansan lokacin da kofi yafadi daga hannuna ba yanzu idan yafadi ma Grandma Yaya zanyi? Wai waye shi? Ya akayi yasan Grandma sosai har yafito daga lungun flawas din falon saman nan eh" hannu Razika tabude itama alamun oho cikeda damuwa tace "oho amman kaman Shemau tasanshi naga ta gaidashi da sauri tana ganinshi kinsan ita tadade tana aiki agidan nan ni ba'a dade da kawoni ba" shiru Du'a tayi har lokacin gabanta faduwa yake, zama kusada ita Razika tayi murmushi tayi takalli Du'a tace "sonshi kike ko Du'a"? wani irin kwalalo idanu waje tayi tace "so kuma" gyadamata kai Razika tayi tace "eh naga yanda kike ta kallonshi jiya ana koranki kinki tafiya kinata cemai thank you for saving my life keda bakima sanshi ba, sonshi kike ko? Yanada kyau sosai wlh gashi dan gayu gashi mai kudi har ana nunashi a TV, sonshi kike"? Girgixamata kai Du'a tayi tace "a'a kawai nasanshi ne tun a kano, shine yataba cironi daga rijiya saisa dana ganshi nace sainaje namai godiya" gyadakai Razika tayi da gamsuwa tace "to Allah sa shiyace yana sonki wlh danaji dadi" dan daure fuska tayi tace "ni banson maganan nan" yatsun kafarta dahar jan dasukayi yasoma washewa takalla tace "bazakije office ba? naga yatsun harsun washe kinga yau Monday fashi ranan Monday is a serious offense" Yatsun itama takalla tace "yadena zafi, tayani zabomin kaya kinga banda lafiya saina shirya natafi" hannu Razika tasa ta dungure mata goshi tace "kewai mai wayau ko" tai maganan tana zuwa gaban wardrobe dinta wani ja da bakin abaya taciro mata sabo fill tana kallonshi tace "wowwww abayan nan yay bala'in kyau, Hajiya tasai miki"? murmushi tayi tana girgixa kai tace "Aneesa tazaban min ranan damukaje shopping yay kyau" warware rigan Razika tayi tace "wlh kam yayi kyau kai yayi bala'in kyau ma, oya tashi kizo ki shirya" tashi tayi tana kallon yatsun nata jin sundena mata zafi, wucewa Razika tayi tafice daga dakin tace "saikin fito" tom Du'a ta amsata tana kokarin cire rigan dake jikinta sanan ta ijiye ta shirya cikin rigan kafin tazo gaban madubi tatsaya tana kallon kanta for the first time yau taga kyanta da ake fadi ja da bakin color ya bala'in mata kyau, zama tayi tana daukan ribbon parking kitsonta tayi a tsakiyan kan yay kaman acucu gashin goshinta sun wani irin bala'in kwanta, sanan tai rolling gyalen abayan, man baki talakata ta shafa a lips dinta dayay wani pink sanan ta tashi tana hada jakanta tadau pad tasaka dakomi da Grandma takoyamata sanan tazura wani flat takalmi mai budadden sama daya bayyana fararen cute kumbunan kafanta, ahankali tasa hannu tabude kofarta tana lekawa gabanta nafaduwa ganin babu kowa yasa takarasa karasawa wajen bene tashiga tafiya ahankali, Grandma kadai tagani zaune tana fere apple dawani karamin wuka, dago kanta tayi jin sahun tafiyanta, kasa daurewa tayi sabida yanda tai kyau tace "Masha Allah tubarkalla Du'a kinyi kyau sosai har kafan ya warke ne"? murmushi tayi tana zama kusada ita tana gyadamata kai, Hajiya tace "to dama banda shegen shagwaba naki ruwan lipton wani konewan kirki ne, kedai kawai rakin ki yay yawa, tashi ki tafi aiki yau Monday aka ciki taran latti baruwana wanan da Ogan ku yadawo ai kunbani" dan zaro idanunta tayi sai yanzu ma ta tuna Sharif yacemata this Monday Ogan su zaiyi resuming office, zumbur tamike tace "bye Grandma" murmushi Grandma tayi tabita da kallo sabida yanda yarinyar tai kyau tace "ayi addu'an fita daga gida Allah tsare" tsalle tayi kaman yar yarinya tace "tom" "kidena tsalle" Grandma tafadi tana murmushi ganin yarintarta.


Motan Grandma tashiga zama tayi driver yajata sai alokacin ma ta tuna batai breakfast ba, har campanin yakaita, yau kawai taji tana having wani irin wired feeling kaman tace sujuya su koma gida kartazo aikin.




💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫


✍️ M SHAKUR
free page
EPISODE 2️⃣ 9️⃣
Parking driver yayi awajen parking motoci yana kallonta ta glass haryau yakasa daina mamakin inda Hajiya tasamo kyakkyawan yarinya haka a jika, yasan Zainab(Mami) baka ce to kodai mijinta irin fararen yan shuwa arab dinnan ne, bude kofa tayi ahankali tafito sanan tajuya tadauki wayanta da jakanta screen din wayan dayay haske ta kalla ganin 15mins after 9 nasafe yasa taji jikinta nadan rawa dan bata taba latti ba kuma batasan ko boss din nada kirki ba karya mata fada, maida kofan tayi ahankali tarufe tace "thank you Uncle" dan haka take kiranshi sanan tajuya tafara tafiya zuwa entrance sanan tashiga ciki, Sharif tagani tsaye gaban kantan reception yana sanye cikin cooperate kaya ba suit ba amman wando da riga yay tucking ga belt dayasa mai kyau yana duba Rolex din dake daure a wrist dinshi kaman akwai abinda yake jira, kaman yaji ajikinshi kallonshi ake yasa yadago kanshi yakalli entrance hada idanu sukayi ajiyan zuciya yasauki sanan yasakin mata wani irin cute smile yana dumfaro ta, saida yakai gabanta ya tsaya ahankali yace "you look ahhhhh mema zance"? Yay dan shiru yana kallon sama yadaura yatsanshi daya kan kumatunshi kaman mai tunani saikuma yakalleta ganin yanda take kallonshi irin ta kosa taji mezaice dinan yasa cikeda tsokana da wasa yace "you look like indon kauye" gabaki dayan murmushin datakeyi bacewa yayi tai raurau da idanu kaman zata fashemai da kuka hakan yasa yay dan dariya yace "just teasing you" saikuma ya tsareta da idanunshi da for the first time tunda tasanshi suke shiri sosai tana kallonshi kaman yayanta taji wani iri hakan yasa tadauke kanta, murya chan kasa yace "you look damn cute Du'a kaman in saceki in gudu" murmushi tadanyi kanta akasa dan tasanshi da wasa still tana wasada yatsunta, for a moment yamanta inda suke tsaye all yake gani wasa her tsaye agabanshi, ahankali yadan waiga yabi wajen da kallo sanan yajuyo yakalleta yace "I've been calling you baki dauka maisa" dago kanta tayi takalleshi ita bamatasan tayaya yasami number taba, saikuma tanunamai wayannata dake hannunta tace "anan ka kirani"? Wayan ya kalla yace "yes, I gave u about 3 to 4 calls I think" wayan tajujjuya takalla dan ko kadan bataji ringing ba ahankali tace "banji ringing ba" hannunshi yamika mata yace "let's see maybe kintaba wani waje ne" bashi wayan tayi yakarba yabude ganin ba key saikuma ya kalleta yace "bari zan miki setting nashi anjima wayan nason update, yanzu dai our Boss yazo he's in his office, maisa kikai latti, our Boss is such a wired dude fa" yay maganan kaman mai whispering din gulma da hakan ma yasa tai murmushi, tsayawa yayi yana kallonta yace "instead of kifara tsoro kinyi latti murmushi kike ko zaiyi deducting a salary ki sanan yau saikin biya bashi time din dakikaci by adding extra hours kan lokacin tashinki, oya let's get going" yay maganan yana tafiya tana biyedashi abaya yace "zai miki tambaya, so yanzu idan kinje as normal yanda any boss zaiyi he will ask u few questions ma sababbin staff nashi, yadan miki tambaya karkiji tsoro be very bold and answer him kinji" gyadamaikai tayi suna hawa stairs, yace "and idan yace maisa kikai latti me zakice? Uhmmm kuma banaso nakoya miki karya"? yay maganan yana tunani yadaura yatsanshi akai yana tafiya, dasauri tana kallonshi itama tana tafiya tace "zance mai nakone akafa" kwalalo idanu yayi ya tsaya yana kallonta, gyadamai kai tayi kaman wata yar yarinya tace "wlh dazu nadebo ruwan tea shine yazube akafana yay zafi sosai saisa nai latti" tunda take maganan yake kallonta saida tagama ahankali calmly yace "kinyi kuka"? Gyadamai kai tayi da zuciya daya tana raurau da idanu tana tafiya, chak yatsaya heart dinshi nawani irin racing he feels kaman yajawota ya rungumeta ya lallasheta, jin shiru yasa tawaigo ganinshi abayanta yasa tadan zaro ido tace "menene, ka manta dawani abu ne" dan murmushi yayi yataho da saurinshi yace "no, how's the leg now? Yadena zafi?" gyadamai kai tayi tace " yadena" daidai nan sukakai 5th floor, tsayawa yayi daganan yace "our Boss is a bit harsh but don't get scared okay" gyadamai kai tayi tanadan zaro manyan idanunta, dan yatsine fuska yayi yace "naaaay! I don't like that face, now smile and go you got this" 👍 yamata thumbs up da hannu dayasa tai murmushi sanan tawuce tafara tafiya mutanen dake wajen sai kallonta suke, gaban office dinshi da aka rubuta CEO taje ta tsaya,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login