Showing 153001 words to 153675 words out of 153675 words

Chapter 52 - Kyawuna Jarabta Ta Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

15 Dec 2024

616

zamanta kewan aure, ilimin dazai amfaneki wajen haukata Oga akan gado, ki iya different styles, da abubuwa da dama na gyara jikinki, dakuma yanda zaki gyara jikin mijinki ta yanda zakiji dadin shi.

Inayin classes din Saturday and Sunday of kowani sati ne.

Idan kinason ki shiga group din registration is 1k kacha.

Zaki turo ta 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turomin evidence of payment sainai adding naki a group din

Duk yanda Asad yakai da tarin zuciya saida zuciyanshi ya tsinke dayaga yanayin Dad, kankameshi Dad yayi yana kuka sosai yace "Asad dan Allah kayafemin, Asad kacireni daga hospital dinan ku kaini outside banson na mutu basusan mesukeyi ba basu iya aiki ba, Dr yace wai organs dina are failing, Asad don't let me die kaji yarona, Asad I love you so much kayakuri abinda namaka kayafemin dan Allah" ganin yanda bandejin da aka samai aciki ke jikewa da jini yasa Asad really understood dat his organs are failing din, dan jininshi yadena clothing kawai zuba yake yariga yatsinke, daurewa yayi yadake sanan ahankali yakalleshi murya chan kasa yace "nayafe maka Dad, but stop talking bari nakira maka Ammi, karoki kowa ya yafe maka" gyadama Asad kai yayi daga inda yake Asad ya kwalama Ammi kira, dasauri tashigo idanunta sunyija sauran duk suka biyota ciki, hannun Dad itama tarike tana kuka sosai ahankali yace "kiyafemin Zainab yarana dukanku kuyafemin, Du'a kiyafemin, Turai kiyafemin sanan kifadama Dadda yayafemih, Hajiya kiyafemin, My Sharif kiyafemin kaima" babu wanda ya iya magana sai kuka, wani kalan mikewa yafara idanunshi nafitowa waje sosai kaman za'a cisgesu, ahankali Asad dake rikedashi yace "Dad kace Lailaha illallah Muhammadu Rasulullah" duka dakin dauka sukayi suna bashi Amman yakasa karba yafadi ahaka rai yay halinshi. Kaico Allah yasa mucika da imani.


Asad ya tsaya akai komi aka kaishi makwancin daga baya yaji labarin komi daga bakin security da Munari dasuka kulle agidan yace suje su saketa baida wanan lokacin na sata akotu taje chan da halinta duk wanda yay mai kyau zaiga mai kyau, su Mami da Abba da duka family su Du'a harda Kaka saida sukazo ma Ammi taaziya, Du'a taji dadin ganin yan gidansu, saida akai bakwai sanan suka tafi, kowa yakoma aiki Ammi ma is holding up fine sama da yanda Asad yadauka ita ke llallashin su Rahima ma kafin kaceme kowa yakoma normal life dinshi, Asad yadauki matarshi suka koma gidansu suka cigaba da soyewa daga inda suke tsaya.


Bayan shekara daya, yau ake bikin Sharif dasu Rahima, da Mariya da Aneesah data sami wani lecturer su a Nile ta aura, adaddafe take komi sabida mugun laulayin datakeyi, tun bayan barin datayi sai yanzu tasami wani cikin, tai wani irin kyau na ban mamaki, babu wanda yake family dabaisan kalan son da Asad kema yarinyar nan ba, killaceta yake na bala'in dan he's a very jealous husband yahanata karatu amman yabata employment a company shi as illustrator dinsu tana aiki daga gida tana musu zanen takalma kuma duk wata yana biyanta banda uban kudaden dayake bata.


Su Nana da Hawwa ma tuni sukai aurensu, Nana wani abokin Ya Hamad tasamu ta aura soja ne shima, itakuma Hawwa wani dan anguwansu ta aura, Mom tuni tai hankali taroki Mami da Du'a gafara dan tariga taga nagaba yay gabane kawai, kazan da Allah yanufa da chara saitayi fa against all odd dan tuni Du'a tabama Babanta gida da school data gina mishi Abba yay mamaki kuma yakara reliasing shima yay kuskure arayuwan nan.


Bayan wata tara Du'a ta haifo yarta mace mai kama da ita sak a kyau dakomi, Asad kaman zai xauce da murna, ranan suna yarinya taci suna Noora suna kiranta da Noor ko Noori dan haka Grandma da Ammi ke kiran lovely girl din.

Ahaka rayuwa takasance ma Du'a, bata taba nadaman auren Asad ba dan tasan babu wanda zai taba sota kaman yanda yasota and tanason mijinta da yarta Noora sama da komi da kowa. Karshe!!!!!



Alhamdulillah anan nakawo karshen littafin nan mai suna KYAWUNA JARABTA TA.

Kuskuren danayi ciki Allah ya yafemin.


AKARSHE DUK WACCE TAKARANTA LITTAFIN NAN BATARE DATA BIYABA BAN YAFE MATA BA HAR LAHIRA.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login