Showing 27001 words to 30000 words out of 153675 words

Chapter 10 - Kyawuna Jarabta Ta Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

15 Dec 2024

601

✍️ M SHAKUR

EPISODE 1️⃣6️⃣
Koda Ammi ta shiga gidan Sharif kawai tagani zaune a dinning yanacin spaghetti da Rahima tadafa, yana ganinta yace "Ammi ina kikaje" zama tayi akan dinning tace "daga wajen Hajiya nake" takalli Rahima data fito daga kitchen tace "iyye yammata na angirma harkinyi girki" murmushi tayi tazauna kusada Ammi ashagwabe tace "Ammi please sai next Monday zamu resuming school this week muhuta muyi shopping kinji Ammi" Sharif dakecin abinci ne yaharareta yace "why mesa yaran this generation basason school saison kula samari" murmushi Ammi tayi takalleta tace "bazakuyi lectures bane" ahankali tace "first week lectures baya serious sosai Ammi fa"gyadamata kai Ammi tayi cikeda gamsuwa tace "okay I will think about it inasu Aneesa da Mariya"? tabe baki tayi tanajan plate tace "sunyi bacci" kallon Sharif dayagama cin abinci Ammi tayi tace "ina Asad" ajiye cup din dayake shan ruwan dashi yayi yace "dazun nan yafita, bansan inda yajeba" "Ammi wai yaushe Daddy zai dawo" Rahima dake kusada Ammi tamata tambayan, murmushi Ammi ta kakalo tace "this week ko next week, bari kiga naje na kwanta" ta tashi tawuce sama Sharif yabita da kallo.



Wani dankareren building wanda nan a offices din senators na Nigeria suke ya dumfara cikin mad ride dinshi na Benz, tsayarda shi sojojin dake guiding building din sukayi, ahankali yasaukar da glass din motar, ganin wanda keciki yasa suka shiga gaidashi, Jan motar yayi ciki har zuwa inda ake parking yay parking sanan ya kashe motar yafito, wanan karan yana sanye cikin wani classic 3quater wanda dakadan yawuce gwuiwanshi dark blue color, sai wata white t shirt mai V neck dayasaka data kara fitar da kyawunshi kana iya hango kwantaccen gashin kirjinshi ta wuyan rigan sabida shape din dayake dashi na V, kafanshi Sanye cikin flat slippers na Gucci, kanshi ya sanya p cap na Gucci, lips dinan nashi yay pink yir looking damn moist and fluffy, sai black eye glasses na Gucci a idanunshi, hannunshi ya daura agogo da bracelet na Rolex akai sai zuba uban kamshi yake, kana ganin shi kaga irin yaran masu kudin nan yan gayu looking casual sabida yau Sunday, maida kofan motan yayi yarufe sanan yafara tafiya ahankali yashiga cikin premises din babu kowa ciki sai security personnel dake gadin wajen wanda dazaran sunganshi gaidashi suke dan sunsan koshi waye, elevator ya shiga zuwa 5 floor, wanda yasadashi dawani mahaukacin building dazaki dauka ataurai ne, ga kujeru na ma'aikata amman sabida yau Sunday babu kowa, cigaba yayi da tafiya zuwa gaban wani hadadden kofa wanda da finger print ake bude kofan, baiyi yatsanshi yasa abin yayi magana Authorize Mr Asad, kama handle din kofan yayi yatura kofan yashiga tashi daya, wani irin zabura mutumin yayi yasauka dagakan yarinyar dayakekai dataji uban attachment ja akai yanajan boxer dinshi dayadan sauke kasa kadan dama dagudu yana rufe abin datai wani automatic kwanciya jikinshi na mugun bari yakalli yarinyar da babu kaya ajikinta yana mata ihu. "leave this office, I said leave" Ahankali yaja kafanshi baya kadan bazaka taba iya tantance wani yanayi yakeba sabida glasses din dake kan idanunshi, dasauri mutumin daya rude yace "Asad look is not what u are think......" awani irin zuciya Asad yajuya fuuuuu, dagudu mutumin yashiga laluban kayanshi yana sakawa batare dayabi takan karuwanshi dake sa kayanta arude ba yasa riganshi baima tsaya saka malum malum ba yazura slippers din office yafice dagudu, sauka kasa yayi gudun da yakeyi yasa yacimmai shan gabanshi yayi yace "Asad listen to me listen to me son please" tsayawa yayi chak yana kallon mahaifin nashi dat so much disgust him now, ahankali yakai hannunshi yacire glasses din dake kan idanun nashi yace "wanan ne US din dakaje ko Dad? Almost 2month babu wanda yasaka a ido kana garin nan Dad" juyawa mutumin yayi yana kalle kalle ganin babu mutane inda suke yasa cikin muryan lallashi yace "listen to me Asad wlh naje US ba karya nayi ba kawaidai dana dawo banje gida bane" wani irin kallon mahaifin nashi yake kallon bakin ciki da tsantsan tsana, Dan murmushi mahaifin nashi yayi irin na marasa gaskiya, cikeda lallashi yace "how are you my boy? Your Mum told me kadawo kaima kaje kano gaida Dadda ka, sanan zakai hosting show ma Youth a TV station, I am so proud of you Asad dina, you are really my son" sosai idanunshi sukai ja ruwa yacika a idanunshi fall ahankali yace "why are you doing this to Ammi? After all the sacrifice da Ammi tamaka why are you treating her this way, why are you maltreating my Mum Dad eh"? kana ganin yanda yayi maganan kasan zuciyanshi namai zafi da daci, ganin yanayinshi yasa Baban yadan sosakai yace "listen Asad, inamaka kallon yaro but I think u are not more a little boy anymore, I love you morethan anything in this world, in fact ma darajan kane ma yasa nai deciding I will leave tareda mamanka har karshen rayuwa but banason mamanka Asad, ko kadan bani sonta, auren hadi akamana nida ita, ur Mum was never my choice, choice din Daddan kane, yar maigadin shine dayarasu dagashi har matanshi lokacin sunje gida kauye suna dawowa suka sami hatsari suka rasu, shine sabida how the gateman was good to Daddan ka yasa yadauki maman ka shida Mamana Allah yajikanta suka raini mamanka aka sata a makaranta aka hadani aure da ita dudda na nuna banso..." yanda idanun Asad sukaija zaka dauka zai makance ne, cikin wata irin murya datai rauni bama ta fita sosai tsabagen bakin ciki da kunci yace "is that the reason why kakebin all kind of useless matan banzan Abuja nan Dad" Dasauri yace "banason aure aure, da mata daya zan iya rayuwa since uwarka ce d lucky one saisa I am stuck with her, look son I don't wanna go into details with you now, nan gaba u will understand after all kai d'ana ne, my blood runs through ur veins, you are just like me" cikin wani irin huge voice yace "I will never be like you, bazan taba zama mutum irin ka ba, I despise you Dad, u are nothing but a shame to my name, wlh da ana chanza uba dana chanza ka cus u don't deserve a son like me much less a good wife kaman Ammi na" yana maganan yawuce yabude motan shi yashiga yana kokarin tadawa Dad yazo wajen. "Asad, Asad, come here son calm down nasan ranka abace yake, but yakakeson nayi eh ur Mum is such an old school babu abinda ta iya sai kunya, Asad" wani irin jan motanshi Asad yayi yabar wajen ubanshi na kwalamai kira. "Asad, Asad" tsaki yaja yadafa kanshi yace "yaro sai bakin zuciya, nima maiya kaini zuwa office yau" tsaki yayi shi kadai yace "to nasan zaizone yaron da fushi yake dani kona kirashi baya dauka" tsaki yasakeyi dukya bala'in damu yace "daka tsaya kajira Zinariyan ka daganan ma kona sami contact din kyakkyawan yarinyar nan dayafimin, yanzu look what I cause yanzu, shiit yanzu sai nakoma wajen wanan matar nan da nonuwan kirjinta sunfi silifas tsawo abu har cinya, dan Allah dai jibi nonon wanan cinyare dinan atsaye, na Zinariya ma haka, amman ace yaro yakasa ganewa uwarshi ba gaba ba baya gatanan ne gabaki dayanta zero ce" yaja tsaki yawuce yana tafiya zuwa ciki ranshi fall da damuwa.



Allah da ikonsa ne kawai yakawoshi gida lafiya, ko parking din kirki bai iya yayi ba yafito daga motan dawani irin gudu security su yace "subhanallah" ganin motan na tafiya yashiga yay parking da kyau shikuma Asad yay wucewan shi batare dayama juyoba, ko katon Sharif dake zaune a garden dake kusada flat dinsu baiyiba yawani irin buga kofa yashiga ciki, binshi da kallo Sharif yayi saikuma ahankali yasauke ijiyan zuciya yacigaba da aikin dayake yi akan system, karan zubarda abu dayaji yasa yatashi da sauri ya ijiye system dinshi awajen, bude kofa yayi yashiga falonsu sanan yamaida kofan yarufe yay kitchen dinsu da sauri tsayawa yayi awajen kofa yana kallon yanda Asad ke zubarda komi na kitchen din yana rotsasu akasa kaman wanda yazare, cikeda damuwa Sharif yace "what's wrong with u Asad"? Wani irin daga kafa Asad yayi yadaki fridge din kitchen din cikin zafin harshe yace "it's none of your business leave me alone Sharif" shiru Sharif yayi yana kallonshi yanda yake haukanshi shi kadai wanda is not new to him, kowa yasan Asad da zafin zuciya haka Ammi ta haifoshi da halin nan.




💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫


✍️ M SHAKUR
Freepage
EPISODE 1️⃣7️⃣
Yagama barinshi duk basu isheshi ba ganin yafara punching kofa da hannunshi yasa dasauri Sharif yashiga kitchen din wani irin kamashi Sharif yayi yasashi ajikinshi ya rungume tsam yace "calm down Asad ba Ammi tace idan ranka yabaci kadinga salati ba, calm down please" kokarin fizge kanshi yake yana ihu. "I said leave me alone Sharif, stay out of this" kankameshi sosai Sharif yayi with all the power he got yace "Ya isa Asad I am here for u, I am here, we gonna be brothers forever okay, ina kaje? what happen? Giran da kayi dazu ina kaje?" shiru yayi yakasa magana ahankali Sharif yace "you went to see Dad ko"?Murya chan kasa yace "I guess kaima kasan babu wani US din dayaje" shiru Sharif yayi sai chan yace "before muje kano lokacin kana UK I saw how worried Ammi is yasa naje office naduba shi, I saw him though shi baiganni ba baisan naganshi ba" shiru Asad yayi saikuma gently yatashi daga jikin Sharif zama yayi akasa ahankali yajingina da cabinet din kitchen din idanunshi sunyi jajir, zama shima Sharif yayi kusadashi yana kallon kasan wajen, ahankali Asad yace "I don't know why Dad choose this life he's 60 but jin kanshi yake kaman dan 20, that Oldman is lost Sharif completely, can u believe niyake gayawa I am just like him eh Sharif" yay dan shiru idanunshi sunyi ja yace "I can never be like that man, bazan taba neman matan banza ba, wlh bazan tababa cus I hate them kyama ma suke bani, I hate that I am his son, wlh da ana chanza uba da na chanza nawa, I hate that man Sharif" kallonshi Sharif yake bakaramin tausayi yabashi ba matsawa yayi kusada shi ya jingina da cabinet shima yace "bazaka taba zama kaman shiba that I am sure of Asad but we gonna do something right now" yay maganan ahankali yace "inaso ka share batun Dad for now dan is affecting u physically and mentally bayan kasan u need to be at ur best gobe zaka fara TV show dinka eh Asad, this whole mess will affect ur productivity as well as ur performance, I cannot be managing everything for u eh, u need to be at ur best mugama this TV program in the next 7days sabida kasamu muyi concentrating a office we need to release new collection eh Asad, banda ma haka kanason Ammi taganka ahaka ne kaga how I am better than u kenan, tunkafin mutafi kano nasan Dad na garin nan amman koda wasa ban nunama Ammi ba sabida I need her happy, kaiko look at u now bayan kasan mu Ammi ke gani taji dadi common be a man for Ammi, let's keep pretending we don't know what Dad has been up to koma yana gari" Ahankali yasaki dan murmushi saiya kalli Sharif din yace "kasami wanan illustrator din?" girgizamai kai yayi yace "no he's on his summer break wai, kaima I don't get u Asad why don't u wanna give Nigerians dinmu a chance" "cus they can't give me what I want" hararanshi Sharif yayi yace "shikenan haka zan zuba idanu inta kallonka wlh idan ka shiga tight corner kaida kanka zaka dinga neman su" tashi yayi ahankali yace "don't worry I will get one" fita yayi daga kitchen din Sharif yabishi da kallo cikeda so dakuma tausayin dan uwan nashi yasan wani zubin Allah kan jarabci yara da iyayensu and that's Asad da dukansu ma a family nan biggest test, Dad gashinan ne kawai living one kind of useless life kaman yaro, imagine Babba dashi he is willing yayi karya yabar gidanshi da sunan yatafi UK just dan yatafi wajen matan banzan shi, tsohon mahaifinshi baida lpy he don't care yaje yaduba shi saidai yayta tura kudin magungunan shi, ayanzu kuma shi kadai ne dandan Dadda namiji, dan dama Dad ne Babba sai mahaifinsu daya rasu, sai Anty Turai mahaifiyar Aneesa, Mahaifinsu daya rasu ne kawai ya haifi yara dayawa a family Shine first born sai Rahima sai Mariya, itakuma Aneesa ita kadaice yar Mamanta Turai, da mijinta yasakota tadaukota suka dawo gidan Dadda dazama kafin tabama Ammi ita aka zo da ita Abuja tafara school gudun kar mijin ya kwace ta dan Anty Turai yar rigima ce fitinanniya saisa ma takasa zaman gidan miji.
Banda haka Ammi is just the best woman aduniyan nan, sosai take tarbiyan yaran batare data nuna gazawanta ko gajiyanta ba, hasalima bala'in son yaran take suma haka suke sonta dan wajen Ammi yafi musu ko'ina.



Mikewa Sharif yayi ahankali yanabin kitchen din da kallo, kwashe abubuwan dabasu wani baci sosai ba yayi sanan yawuce yafita, sama yayi ahankali yabude kofar dakin Asad din, akan gadonshi ya ganshi yana bacci, ajiyan zuciya yasauke sanan yaja kofan yarufe yasauko kasa, masu gyaran gidansu yakira yasasu gyara kitchen din sanan yakoma falon sama yazauna tunawa ma yayi da system dinshi awaje dasauri yatashi yawuce waje.



Dayake tanada yammata hakan yasa Ammi bata dauki yan aiki ba, su take sawa girki, duk tana kitchen taredasu suna aiki takalli Aneesa dake wanke rice tace "namuku kawa fa" dasauri duka yaran suka tsaya suna kallonta, Aneesa ce tace "Ammi a ina"? murmushi Ammi tayi tana maida marfin tukunyan data bude tana rufewa tace "jikan Hajiya ce, sunanta Du'a, she will be ur mate Aneesa keda Mariya" tanuna Mariya da itama ta tsayar da peeling Irish din datake tana kallon Ammi, tafi Aneesa tayi da Mariya tace "yi sauri Mari mugama girki muje gidan Hajiya" murmushi Ammi tayi takalli Rahima data cigaba da aikinta tace "Anty Rahima kinyi shiru" wani irin murmushi tayi tace "Ammi bakina Ya Asad maganan wayoyin muba" dasauri sauran sukace eh Ammi, hararansu tayi tace "wai mesa kuke tsoron yayan ku haka, aiko babu wanda zai kara aikena wajenshi cikinku kuje kusameshi dakanku kokuma kuma Sharif magana yasaimuku" dasauri Mariya ashagwabe tace "Ammi wlh Ya Sharif mugune yace wai babu wanda zaici kudinshi cikinmu wai tara kudin aure yake, duk wanan wahalan inda Dad na nan muna gayamai zai sai mana wlh" shiru Ammi tayi tace "kugama girki kuje ku sami Asad to baruwana kudena sani a lamarin ku" nariga nahada muku komi ku karasa kuyi setting dinning up tai maganan tana fita daga dakin.


Wuraren 5 suka gama girkin tass sukai setting dinning dakinsu sukayi kowa yay wanka, Aneesa data gama shiryawa cikin wata yar rigan zaman gida half gown mai spaghetti hand ya tsaya mata a knee ta kallesu tace "kumuje wajen Ya Asad" kwalalo ido daga Mari har Rahima sukayi atare sukace "kidawo lpy nidai bazani ba" hararan su tayi tace "wlh naje nawa kadai zan fadamai" tawuce fuuu tafice tana tafiya ahankali gabanta nafaduwa, tsayawa tayi takalli kanta a madubin dake bangon falonsu tayi kyau sosai ga kitson kanta yamata kyau abunku da faran yarinya dan gidan Asad ne kawai black cikin yaran, bude kofa tayi tai flat dinsu Asad, tsayawa tayi abakin kofan tai knocking, jin ba'a amsaba yasa ta danna door bell har sau biyu, sake knocking tayi cikin wata irin isasshiyar murya akace. "waye"? faduwa gabanta yayi muryanta har rawa yake tace "Ya Asad is me, Aneesa" shiru aka sakeyi takai kusan 3min atsaye awurin sanan akace "come in" dasauri tabude kofan ta shiga yana zaune a falo dagashi sai towel daya daura a waist dinshi ya zaunar akan kujera ya mikarda kafa yadaura kan enter table yadaura MacBook akan cinyanshi yana aiki ruwan coily gashinshi nabin fuskanshi.

Kallo daya tamai tasaukar da kanta kasa dasauri, tunda take bata taba ganinshi ba rigaba sai yau, wani irin hadiye miyau tayi gabanta na dukan uku uku, tashiga wasa da yatsunta takasa magana, batare daya kalleta ba hankalinshi nakan aikin dayake yi akan system yace "why are you here"? Yanda kirjinta ke dukan uku uku yasa muryanta yama fara rawa tace "Y.....a As...ad, dama....dama...." saita karayin shiru tadan dagokai ta kalleshi aikinshi yakeyi comfortably a MacBook dinshi kaman baimasan tana wajenba, kirjinshi tabida kallo jitayi jikinta yadau rawa da sauri ta maida kanta kasa tadage tace "Ya Asad I want a new phone Ammi tace zata gayama shine yanzu wai muje musameka da kanmu, ahhmm kuma da shopping da resuming school, I want new school bags, pairs of shoes sai Abaya dakuma and kuma pads dinmu yakare duka" saida takai nan tai shiru kirjinta na bugawa fat fat fat bata taba sanin zata iyama Asad magana ba saiyau, juyoda kanshi yayi yakalleta for the first time tunda tashigo dakin, ahankali kaman baison yay maganan yace "what happen to your phone" dagokanta tayi ta kalleshi yanda yake kallonta yasa takasa mai karya langabar da murya tayi tace "babu abinda yasame shi I just wanted a new one" still kallonta yake babu alamun wasa kowani yanayi akan fuskanshi yace "and the other things nawa zai isheki kisaya" wani irin murmushi tamai cikeda jin dadi tace "150k zai isheni Ya Asad" Su Rahima da tuntuni suke gaban dakin suna jiran suji yanda zata kaya jin yana tambayanta nawa yasa suka turo kofan suka shigo suna sallama, duk atare suka gaidashi muryansu narawa. "Ya Asad good evening" dasauri Aneesa tace "Ya Asad kaga saida nace musu fa suzo muje tare sukaki wai tsoro sukeji sai yanzu dasukaji zaka bani kuma wlh ni bazan raba kudina daku na nawa kadai nafadi" dasauri Rahima tadan kyafta mata ido takalli Asad din tace "Ya Asad sorry" Mari ma ahankali tace "Ya Asad sorry ni wlh tsoro ya hanani ma biyota" duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login