Showing 33001 words to 36000 words out of 153675 words

Chapter 12 - Kyawuna Jarabta Ta Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

15 Dec 2024

607

aiki aciki wuce kitafi" kallon Hajiya tayi idanunta sukai zuru zuru kaman zatai kuka tace "Grandma mezance" dariyan da Grandmaa keji ta hadiye tace "just go this is beginning of new phase, anriga an baki aikin so amsan da zuwanki idan kikaje akwai receptionist awajen ki gayamata sunanki she will tell u what to do, come here" Hajiya tama goshinta peck tace "Allah bada sa'a don't forget abubuwan dana fadamiki" gyadamata kai tayi gabanta nafaduwa sanan tabude kofan ta fita, direban grandma yajata suka wuce suka tafi suka barta tsaye awajen, haduwan ginin kadai yasa taji she's having change of mind ita daketa murna zatai aiki ita ko kadan batai picturing something like this ba irin wanan big organization dinne Ammi zata saman mata aiki ba, takai kusan 5min tsaye awajen sanan ta dage tafara tafiya towards the entrance door da kofan yay kala da kofan bank, taga yanda mutanen dake wucewa ke shiga hakan yasa itama taje, security dake wajen ne dake bada hand sanitizer ne yabita da kallo sanan yace "ur hand Miss" muka hannunta tayi aka zuba mata ta shafa yace "u can go in" shiga kofan tayi nan kawai taga glass yarufe ta ihu tayi tashiga buga glass din. "wayyooo Allah na innailaihi Grandm......" bata karasa kiranta ba taga kofan ya budu ga mutane dayawa awajen kowa na harkan gabanshi bama a lurada ita ba yasa tashare hawayen daya zubomata da sauri tashiga tana kalle kalle still ganin desk da counter da aka rubuta reception yasa tai wajen, wata hadaddiyar chic ce awajen kafinma Du'a ta isa wajen yarinyar ke kallon Du'a kaman zata hadiyeta tace "how can I help u Miss" ahankali Du'a tace "my name is Du'a Muhammad" dasauri receptionist din tace "the new illustrator, please come with me Miss Du'a" Receptionist din ta tashi tai hanyar elevator Du'a biyeda ita suka shiga, 4th floor ta danna da elevator yafara tafiya runtse ido tayi danji tayi hanjinta na neman fitowa, wani complete new section tagansu aciki saiga wata secretary dake zaune gaban system ga kujeru zaman mutane awajen, nunama Du'a kujera tayi tace "have a sir Miss Du'a" sanan takalli secretary dake kallon Du'a tace "she's the new illustrator, u take it from here" gyadamata kai tayi tawuce itakuma Du'a ta zauna tana kallon office din dake gabanta dakenan arufe jikin kofan anrubuta M.D Mr Sharif Alameen Kitse, takai kusan 1hr azaune awajen sanan aka bude kofan wasu manyan baki dake sanye da suit turawa suka fito tareda Sharif dake sanye da suit yayi wani irin kyau, binta yayi da kallo sai baice komiba yawuce yataka bakin har zuwa wajen elevator sanan suka shiga yadawo ya tsaya gaban secretary din cikeda fushi yace "tun yaushe Miss Du'a ke zaune anan Miss Amal"? dasauri matan tace "about an hour ago" "and u couldn't take her to her office" yafadi ranshi abace, tashi Miss Amal tayi tace "sorry sir I thought zaka fara ganinta ne tukunna saisa na bartaka sallami baki tukunna" cikeda takai takaici yawuce gaban Du'a yace "I apologize for that Miss Du'a, shall we" tashi tayi tana gyadamai kai yabude office dinshi yashiga tana biyeda shi sai kallon office din take yanda office din yahadu kujera yanuna mata ta zauna sanan shima yawuce ya zauna yakalleta da murmushi a fuskanshi yace "you want coffee kona kaiki cafeteria kici abinci"? Gizgizamai kai tayi ahankali cikin muryan nan nata mai bala'in dadi tace "I had breakfast thank you" cikeda gamsuwa yana kallonta yace "it's fine, anyway welcome to EPIC & COs LTD, company ne that is into creating and inventing all kind of shoes dakika sani da different materials, starting from animal skins har zuwa leather shoes, munada lots of investors da abubuwa da yawa which I believe since kina nan yanzu u will understand everything, Today is all about introduction babu abinda zakiyi gobe ne zaki fara aiki officially, that aside. My name is Sharif Al Ameen Kitse, nine MD wato managing director of this company, sorry bazaki sami daman ganin CEO dinmu ba dan he's officially on leave sai next week zai dawo, I will give u a tour around the company har zuwa warehouse dinmu dake kasa inda ake hada takalman da ire irenki ke zana mana, zan kaiki HR department zaki miki small abu za'a dauki hotonshi da some biometric dan za'a miki ID card na aiki, we have mosque we have church, rest room cafeteria duk acikin nan, and if u are having any difficulty with anything feel free to give me a call okay I'm ur brother banda haka Hajiya tace nakulan mata da jikan ta inba hakaba saitaci kaniyana" yay maganan cikeda wasa yana kallonta dan murmushi tayi itama dan sosai yanada kirki, ahankali yace "are you ready for ur tour ko kina bukatan wani abu, water juice ko cingum ko sweet kinsan mata da kwadayi remember I have sister nasanku, nabaki sweet"? yay maganan yana jawo wata yar locker shi yanuna mata, uban sweet ne na chocolate da sauransu aciki yana kallonta, kasa cemishi a'a tayi ahankali yasa ahankali tace "eh" ciko chocolate da sweet yayi a hannunshi yamika mata hannu tasa takarba ahankali tace "thank you" jakanta tabude ta zuba sanan tadauki daya tabude tasa abaki, murmushi yamata yace "let's go" gyadamai kai tayi tabishi suka fito tana biyedashi suka shiga elevator, ya danna 5th floor yace "let's start with 5th floor nanne floor na Oganmu duka, CEO anan kuma office din illustrator company yake dan haka anan office dinki yake" jin shiru yasa yajuyo yakalleta gani yayi ta kankame idanunta lips dinta na motsi, dan murmushi yayi yace "scared of elevator"? Gyadamai kai tayi ahankali daidai kofan nabudewa yafice ahankali tafito itama idanunta har sunyi ja sabida tsoro, tazaci 4th floor nada kyau dasukazo fifth floor dinnan saitaga wane 4th, ga mutane sai aikinsu suke sai gaida Sharif ake ana bin Du'a da kallo dashi kanshi Sharif saida ya lura, gaban wani office yaje dake kusada CEO dan tazaran ba yawa taga an rubuta illustration, bude kofan yay ya shiga yajuyo ya kalleta yace "come in" shigowa tayi tana bin office din dakallo table ne hadadden gaske da laptop ke kai ga kujera dake juyawa, ga dogon couch, sai frames a bango na zanen takalma masu kyau, sa shelf dawasu irin hadadden drawing book dabata taba ganinsu arayuwanta ba suke ganin su take kallo yasa, Sharif yadauko daya yace "anan zaki dinga zanen it's digital drawing book, kome kike zanawa is connection to this MacBook" yanuna mata laptop din dake kan kujeranta, yace "we can't wait for xanenki, you can keep ur bag dan nanne official office dinki" gyadamai kai tayi ahankali ta ijiye jakanta kan table sanan yakalleta yace "mucigaba kokin gaji" murmushi tamai ahankali tace "mucigaba" fita yayi tabishi wanan karan saitaga baibida ita elevator ba sun dauki stairs hakan bakaramin dadi yamata ba harsaida ya lura dansai murmushi takemai, suka tafi kowani floor yana nuna mata komi, sukaje Cafeteria company babban gaske all employees dinsu are entitle to lunch kaje za'a baka free lunch, dasafe kuma kowa is entitle to either coffee ko lip tea saisa kowa nan yake fara tsayawa dasafe ya karbi tea sanan kowa yawuce office, yakaita mosque incase tanaso tazo tai salla, yakaita warehouse, yakaita HR yana tsaye akai taking biometrics dinta aka mata passports saida tagama komi sanan suka taho abin har mamaki yadinga basu wanan tour din dayake bata ba aikinshi bane, sake komar da ita Cafeteria yayi yakalleta yace "tea or coffee"? murmushi tayi kaman mai tsoro tace "tea" sawa yayi aka hada tea a coffee aka kawo musu a disposable cup mai marfi yabata nata yana rikeda nah I yace "muje" sakebin bene yayi da ita suka tafi har 5th floor, office dinta yakaita yace "now sit round relax do anything dakikeso, if u want anything just dial my number awanan landline Din" yanuna mata telephone din wajen yace "dial 444 zaiyi connecting naki to me" gyadamai kai tayi, waving mata hannu yayi yace "bye" ahankali tace "bye" harya wuce saikuma yaleko yace "drink our tea kiji da dadi kafin yahuce" gyadamai kai tasake yi tana murmushi, wucewa yayi yatafi abinshi, zama tayi kan kujeran ta da tuntuni yake shigan mata idanu tahau wasa akai tana juye juye saikuma tamika hannu tadauki cup din tashiga shan tea aiko dadi hakan yasa tacigaba dasha tana murmushi ita kadai.

wa.me/+2347012181461




💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫



✍️ M SHAKUR


free page
EPISODE 2️⃣1️⃣

Sosai takebin office din da kallo kaman wacce bata taba ganin office ba arayuwanta, ga katoton TV dake makale a bangon office din, gawani camera Ata sama amakalle shima dabata san koname ba, ahaka tana zaune ita kadai har lokacin azahar tayi, knocking office dinta akayi saikuma aka budo kofan, Sharif ne murmushi lullube kan fuskanshi yana kallonta batare daya shigo cikin office dinba, dan murmushi tasakinmai itama dan wani irin kunyanshi takeji ganin yanada kirki sosai, ahankali yace "is time for zuhur u wanna join me?" Gyadamai kai tayi da sauri dan tuntuni takejin fitsari dama amman kunyan tafita ita kadai takeji taje, tashi tayi ahankali tafito duk yana kallon ta sanan taja kofan office din suka wuce tare har mosque yanuna mata side din mata ta tafi, wucewa tayi bayinsu sai kallonta matan dake wajen suke itadai babu wanda take cema uppan besides ma kanta akasa dan kunyan yanda suke kallonta takeji, fitsari tayi tayo alwala sanan tashigo masallacin ganin cupboard dake cike da hijabai yasa tadauki hijabi tasaka tai salla abinta, tana idarwa ta zauna tana kokarin rolling gyalenta babu yanda batayiba takasa hakan yasa takama gyalen ta wajen wuyanta gamgam tamike tafito, jigine da bango masallacin taga Sharif yay folding hannunshi akirji da alamu ita yake jira, ganinta yasa ya yunkura yataho inda take yana kallonta yace "maiya sami gyalen"? Ahankali tace "ban iya yanda Grandma tamini ba" Dan murmushi yayi yace "then u have to learn dagayau, let's go have lunch" yay maganan yana hawa stairs yay hanyar canteen dinsu tana biyeda shi, shiga sukayi ga few employees dinsu dake wajen suna cin abinci cikeda girmamawa suka shiga gaidashi amsasu yayi batare daya kallesu ba sanan yaja kujera yanuna mata alamun ta zauna zama tayi ahankali tana kallonshi ganin yanda yake wani kulada ita kaman yar kanwarshi, shima zama yayi yakalli yarinyar datazo cikeda girmamawa tace "mezan kawo muku sir" batare daya kalleta ba yace "I want pasta da salad, mezakici Du'a" yay maganan ahankali yana kallonta, kallon yarinyar tayi sanan tace "jallof rice" juyawa yarinyar tayi ta tafi itakuma tasauke kanta kasa tana wasa da yatsunta Sharif sai kallonta yake kaman yamata magana saikuma yay shiru shima ahaka har aka kawo musu abincin, cin abincin shi yafara hakan yasa yace "bazaki ci ba" Dan dagokai tayi ta kalleshi ahankali tadau spoon tafara cin abincin, bini bini yake satan kallonta, ta bala'in yima kyau, komi nata daban ne, harya gamacin abincin shi batai rabin nata ba hakan yasa yacigaba da jiranta, kadan takara akai ta ture hakan yasa yace "u okay" gyadamai kai tayi tasha ruwa sanan ta tashi alamun su tafi tafiya sukayi har office yasake rakata sanan yawuce nashi office din, wuraren 4 tana zaune a office dinta telephone din wajen yahau kara dasauri ta dauka, muryan wani security taji.


"Miss Du'a your driver is here to pick u up" dawani irin sauri ta tashi tana hada yan tarkacenta ajaka ta kosa ta ganta agida sanan tafito tana tafiya ahankali tasauka kasa zatai hanyar kofa taji magana a bayanta. "so you're living without saying goodbye" dawani irin sauri tajuyo ganin Sharif ne yana rikeda waya a kunnenshi da alamun ma waya yake but still saida yamata magana yasa adan kunyace tamai waving hannunta tace "bye" gyadamata kai yayi yacigaba da magana. "yes I can hear u Asad" waje tafita ta shiga motan Grandma dinta driver yatafi da ita, Allah Allah take takai gida, suna kaiwa gida tafito daga motan dasauri harda dan gudun ta tai falonsu tana budewa taga su Rahima Mariya da Aneesa duk sunci gayu sosai suna zaune afalon Hajiya atare sukace. "surprise" suka tashi suna rungumeta, wani irin murmushi tayi ta kallesu tace "yaushe kukazo sorry" dasauri Aneesa tace "bakomi Hajiya da Ammi daman sun gayamana kinji aiki, jekiyi wanka kizo kici abinci mutafi" gyadama musu kai tayi takalli Grandma dinta dake zaune tana kallonsu tana murmushi, wajenta taje ahankali tace "Grandma ina yini" fuskanta tashafa tace "Du'a dina sannu da zuwa, yi sauri kije ki shirya kunga tuntuni su Aneesa ke jiranki" wucewa sama tayi da saurinta dakinta ta shiga, wanka tayo tafito, tunawa da abinda Grandma tafadi mata yasa tasake dauko wata gown wanan is simple dan ba designers bane irin na dazu data sakaba milk color, saka shi tayi sanan tadauki mayafinshi ta feffesa turare tafito kasa, duk juyowa sukayi suna kallonta Aneesa tace "mena rike dankwali a hannu kiyafa mana" karasowa falon tayi tace "ban iya bane grandma zatamin" tabama grandma dan kwalin, dasauri Mari tace "Hajiya bari mu mata sabida ta iya" tana maganan ta karbi veil din daga hannun Hajiya sanan ta wani irin yafama Du'a akai gaban kanta daya cika da kwantaccen gashi yawani fito, Rahima tace "wow wlh kinyi kyau Du'a mutafi to, Aneesa ina kudinta da Ya Sharif yace mubata" dasauri Aneesa tashiga bude handbag dinta wani kudi taciro a envelope sanan tamikama Du'a din tace "ga kudinki, tundazu dasafe kafin yatafi office yabamu mubaki" dasauri Du'a takalli Hajiya danharga Allah batasan mezatayi ba, murmushi Hajiya tayi tace "karba Allah ne ya ciyar dake kafin aci kudin Sharif saidai idan Allah ya tsaga da rabonki ne" kwashewa da dariya yaran dukansu sukayi sukace "wlh kuwa Hajiya Ya Sharif kare bayacin kashinshi, karba muje" Ahankali tasa hannu takarba tace "thank u" sanan tasa ajaka, sallama sukama Hajiya sukai tafi direba ya kwashe su, sosai sukema Du'a hira a mota ita abin mamaki yake bata yanda suke sonta daga ganinta jiya dan har labarin samarin su suke bata, Aneesa data zauna agaban mota ne tajuyo ta leko takalli Du'a tace "ke baki bamu labarin saurayinki ba" Dan zaro idanu tayi tanuna kanta tace "ni"? dasauri Mariya dake gefenta tadan bugi kafadanta tace "common on don't be shy, tell us about the lucky guy" dan murmushi tayi saikuma tadauke kai dan tambayan tabata kunya ahankali tace "ni banda saurayi ko daya wlh" wani irin bude baki sukayi suna kallonta sabida mamaki, Rahima dake gefen Mariya tace "Du'a wasa kike ko" girgixa kai tayi tace "wlh ba wasa nake ba" shiru duk sukayi yanda yarinyar nan keda kyau ace bata da saurayi basu wani karyata ta sosai ba sabida sunga ko wayama batada shi, share maganan sukayi suka shiga wata hiran har sukakai mango dazasu, nan Du'a taga yanda ake shopping ita bama tasan mezata dauka ba hakan yasa kome suka dauka itama saisun daukan mata anata cart din, tundaga kan Bra da tuni suka gwadata suka shiga zakulo mata sizes dinta zuwa pants, pads kayan makeup, duk suna tura cart dinsu kowa na diban abinda akeso TV super market din dake makale asama na aiki Channels television news inda ake program REINVENTING THE NIGERIAN YOUTH....



Suna tsaye bangaren English wears Rahima ta amshi tape tana kokarin ana waist din Du'a dan asan size din jeans dinta itama ta dauka kaman daga sama wani kyakkyawan eloquent voice yadaki dodon kunnuwan Du'a da hakanan taji kaman tasan muryan, dawani irin sauri tadaga kanta sama takalli TV, chak ta tsaya ko motsi kirki tasaka, idanunta ne suka sauka kan fuskan da kusan kullum saitaga fuskan, wanda yacetota daga rijiya, yana sanye cikin wasu classic suit dark blue, ga necktie awuyanshi, yana zaune kan wata hadaddiyar kujera yayi crossing legs dinshi in a stylish way, yadaura hannunshi biyu kan cinyanshi wrist dinshi na daure da agogon Rolex, idanunshi fari kalll wanan karan babu bakin glasses akan su, lips dinshi sunyi wani masifaffen pink kaman ya shafa janbaki pin akai, gashin kanshi dake da yawa sunyi wani kalan extraordinary coils, yana magana da english da accent dinshi na bristish, kaman acikin mafarki taji ana Du'a, Du'a, Du'a, tabatan da akayi yasa tai firgigit tafarka ta kallesu da sauri dan sai alokacin ma tasan ashe tayi nizan tunani ne, neck dinta Rahima takai hannunta ta taba tace "baki da lafiya ne? Tunanin me kike haka kin tsare TV da ido eh harmun gama siyan kaya" binsu tayida kallo ganin yanda suke kallonta kaman sun damu yasa takakalo murmushi tace "tunanin abubuwan dazan saya fa nake" murmushi dukansu suka mata, Rahima tace "mungama da wanan shop din next stop is abaya store, mutafi mubiya mufice yamma nayi" gyadamusu kai tayi tabisu zuwa wajen cashier tana kara waigowa tana satan kallon TV da Asad har lokacin ke magana, kowa kudinshi yabiya sanan aka musu parking kayan a leda sanan suka wuce suka fita still saida takara waigowa takalli TV, sanan suka fice, ranan basu suka dawo gida ba sai 8 nadare kasa bude kayan tayi salla ta lallaba tayi sai bacci tashinta grandma tayi saida ta tasa ta agaba taci abinci sanan tabarta takara komawa bacci da tagaji bata saba fita ko wahala hakaba, all abinda tasani is wanka kwanciya da cin abinci shikenan saisa tai bacci awahale.


DAN MAGANA DANI M SHAKUR CHAT ME UP BY CLICKING ON THIS LINK wa.me/+2347012181461




💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫


✍️ M SHAKUR

EPISODE 2️⃣2️⃣
Kaman an tsikareta wuraren 4 na asuba tafarka da kanta batare da an tadataba, TV dake bangon dakinta ta tsaya chak tana kallo kaman mai tunanin wani abu, dasauri ta yaye bargon data lulluba dashi tasauka daga kan gadon, kunna switch din bangon tayi nan TV da decoder na DSTV duk suka kunna komawa tayi tazauna kan gadon tana sosa idanunta dake cikeda bacci, tadauki remote tashiga neman channels television news, da kyar ta iya ganoshi ta saka da sauri tana gyara zama kaman akwai abinda take shiri ta kalla, ganin ba abinda take nema sukeyi ba yasa tashiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login