Showing 3001 words to 6000 words out of 153675 words
murna koba komi yau zataga wayanda bayan gidansu ba, hijabinta tadauka tasaka sanan tabi bayansu Nana dasukai gaba batareda sun cemata komiba suka fito Abba na tsaye kan stairs yana jiransu su fito yagansu, hada ido yayi da Du’a dake nonnoke kai, ahankali yace “ke banda ke koma daki ki zauna” wani irin murmushi Hawwa tayi ranta fess jin ankorata, Gyadama Abba kai tayi ahankali cikeda mugun sanyin jiki tajuya ahankali tashiga daki tareda maida kofan tarufo daidai lokacin Hamad yafito daga dakin Mum dinshi, hada ido Abba yayi dashi yace “let’s go tunda kafito” shida Abba suka jera yaran kuma abayanshi har zuwa kasa.
Abokanen aikinshi ne su uku da matayensu da yaransu kanana suna ganinshi Babban cikinsu yace “what a nice family kakedashi HOD” dan murmushi Abba yayi yakaraso wajen yabasu hannu sukuma yaran suka shiga gaida kowa, Mami da Mum da Uwani suka shiga kawo abinci da kayan kwalama, ahankali Mami kebin kowa na falon da kallo saikuma tasauke ijiyan zuciya ahankali, daya daga cikinsu yace “wayan nanne kadai yaranka HOD”? Gyadamai kai yayi yace “eh” ahankali Mami dake kokarin bama matar abokinshi plate na snack tadan saci kallonshi saikuma tai murmushi tacigaba da serving while Abba yacigaba da magana yanuna Hamad yace “wanan shine first son dina Hamad he’s 30, yakaranta engineering” dasauri bakin sukace “like father like son” danshima engineering yayi yanzu shine HOD engineering department a BUK, murmushi yayi yace “yayi joining NDA yanzuma wani program yakeyi anan kano saisa yakenan, sai Aisha” yanuna Nana yace “muna kiranta da Nana dan tanada sunan Mamana, ankusa bikinta nan da bayan salla, sai Hawwa sai Du….” Shiru yayi dasauri saiya nuna Amal yace “sai Amal, Aneela, Asiya da Muhammad da Mudasir, yarana takwas” “wow masha Allah, nice family wlh, Allah ya rayamaka su kaga aurensu” murmushi Abba yayi yace “Bismillan ku mufaracin abinci” nan aka shiga cin abinci akai shiru, ahankali Hamad yatashi yay excusing kanshi yay sama binshi da kallo mahaifiyarshi tayi babu daman kiranshi sabida bakin dake wajen.
Dakinsu Du’a yabude yashiga tareda maida kofan yarufe sanan yajuyo ya kalli gadonta, a kwance yaganta tarufa da hijabinta, ajiyan zuciya yasauke aboye sanan yashigo dakin yace “Hey Duudo look what i got for you” shiru tayi kaman tana bacci taki motsi, ahankali yasa hannunshi yakama kafafunta yadagasu sama sanan yazauna abakin gadon sanan yasaukar da kafafunta kasan gadon tareda saka hannu yaja hijabin data rufe fuskanta dashi, dasauri ta yunkura zata juya fuskanta kawai yadagota yace “come here Du’a” sata yayi ajikinshi kaman jira take ta kankameshi sosai sai kuka, ko kadan baiyi attempting hanata kukan ba, duk kanninshi babu wanda yakejin tausayinta yake kuma so kaman Du’a sabida tafi kowa rauni, he don’t care about kalaman da family su suke fadi akanta ana cewa itaba yar Abba bace, mayya ce, yar aljanu ce bla bla bla, all he knows is Mami da Abba suka haifeta and she’s his little sister kuma yanason kanwarshi sama da tunanin kowama.
Cikin kuka tace “Ya Hamad ni wlh inaso namutu” dasauri yacirota daga jikinshi yace “ke are you crazy? Karki kara fadin haka” bayan hannunta takai tana share fuskanta tace “Abba bayasona, Mami bata sona, Mum ma batasona, Kaka ma batasona, kaga ni kadai Abba ya tsana ayaranshi, yakorani nakoma daki dazu, kuma kaga yace yaranshi 8 yacireni daga cikin yaranshi, kullum ina kulle adakin nan kaman mayya, dama Kaka tace ni mayya ce ni aljana ce, sabida ni kadai aka haifa daban bana kama daku does that means am a witch ko aljana eh Ya Hamad? Ya Hamad bakacemin kananan ranan da aka haifeni ba kuma kace Mami ta haifeni maisa su Aneela dasu Muhammad da Mudasir kadai takeso eh? Ya Hamad babu asibitin dake chanza kalan fatan mutum ka kaini naje nakoma kalan yan gidan mu sabida Mami na da Abba su soni nima eh Ya……..” hannunshi yadaura akan lips dinta yace “ya isa haka listen to me all abubuwan nan dakikaga Abba da Mami nayi bawaidan basa sonki bane sunayine to protect you, Du’a tun kina primary school ansha ayi attempting ayi raping naki nasan lokacin kina yarinya ba lallai kituna ba, but kin tuna lokacin dakike JSS 2 abinda teacher ki da Abba ya kulle yamiki ko” runtse idanunta tayi dakarfi alamun ta tuna, hakan yasa ahankali yakai hannunshi yakama hannuwanta guda biyu yace “listen to me, Abba is only trying to protect you, Abba bai tsaneki ba” ahankali cikeda raunin murya tace “amman yana kunyan ya nunani amatsayin Babana” tai maganan tana kallon Ya Hamad kurii da manyan idanuwanta dayasa yakasama mata karya dan to some extend all abinda take fadi gaskiyane, ahankali kawai yajawota jikinshi ya rungumeta yakai hannunshi yashafa gashinta murya chan kasa ta yanda dagashi sai ita sukeji yace “kin tuna abinda nake yawan fadamiki” gyadamai kai tayi ahankali ajikinshi hakan yasa yace “fada inji” murya chan kasa hawaye nabin kuncinta tace “Du’a kome kikaga yana faruwa arayuwanki Allah yasan dake, jarabawanki ne, karki kaucema Allah karki butulcemai, bake kikai kanki ba Allah ya yoki, love yourself, kiyi imani da Allah kikuma dage da addu’a watarana sai labari my beautiful little Duuudo” suka karashe maganan atare hakan yasa takara kankameshi, murmushi yayi sanan yacirota daga jikinshi, handkerchief yaciro daga aljihunshi yace “now let’s wipe those tears no more kuka okay” gyadamai kai tayi tareda murmushi yan kananun white teeth dinta suka bayyana, sharemata fuskan yayi tass sanan shima yamata murmushi yace “idan bakin nan suka tafi zan dauko miki sababbin novels din dana sayomiki kinji” gyadamai kai tasakeyi, kumatunta yaja yace “idan kika sake kuka saimun bata” dasauri tace “bazan sakeba” “kinci abincin dare?” Girgizamal kai tayi, tashi yayi yace “bari naje nakawo miki saiki bani labarin wayan nan novel din” gyadamai kai tayi yawuce yafita yana murmushi, Allah yamata brain, english novels yake sayomata dasukakai 1000+ pages cikin 2days tagama kuma tsaf zata bashi labarin novel din, abinda yataimaka mata da english ma kenan.
Bai wani dadeba yadawo dakin da bowl na hadadden pepper soup da cow head, kafinma ya iso ta tashi tsaye dasauri tace “Ya Hanad kaman pepper soup ko” bata plate din yayi yace “mayyan nama kawai” dan tana balain son nama tun tana yarinya, murmushi tayi takarba dasauri tazauna tashiga ci ya tsaya shikuma yana kallonta, she looks so happy hakan made him so happy, dan yarinya ce da dawuya kaga she’s happy saisa anytime she looks happy happiness dinta is infectious sai kawai kaji kaima ka kamu da farin ciki. Juyowa tayi takallai tana tana naman kaman wata yar baby looking so adorable ganin ita yake kallo yasa tamikamai last piece na meat din tace “zakaci” hararanta yayi yace “marowaciya sai yanzu zaki bani to banci” dan dariya tayi tace “yakuri bari naci wanan gobe saimuci tare, Ya wai yaya ake dafa nama ne”? “Har yanzu ba’a barinki ki shiga kitchen?” Gyadamai kai tayi tace “ba Kaka tahana ba” gudun karta tunakomi dan yanzun nan kuma tahau kuka tasa yace “zan sayo nama saina koyamiki a kitchen din side dina” sosai tashiga jin dadi tana tauna namanta bude kofa akayi dasauri dukansu suka waiga, Mum ce fuskarta amurtuke, wani mugun kallo tama Hamad tace “mena gayamaka? Zokabar dakin nan” tai maganan tareda nunamai kofa, tashi yayi ahankali batare dayamata gaddama ba yazo yabita gefenta yafice, shigowa dakin tayi tazo har gaban gadon Du’a data sauke kanta kasa tana rikeda bowl din pepper soup din data cinye tace “ke bazakiji da bakin jinin ki kinemi yanda zakiyi ubanki yama yarda cewa ke yarshi ce ko yadinga lissafawa dake cikin yaranshi kina nan kina nema kisama dana bakin jininki ne, sabida kinga yanda ubanku keji dashi first son dinshi ga ilimi ga kyau shine zaki biyo tanan, to ta Allah batakiba bakar mayya kawai, kijechan kiji da kanki, na tsani uwarki amman naga matsalan da haihuwanki kesata ciki wlh har tausayamata nake, wayama sani ko wani aljaninne yadura mata cikinki dan naji ance tayi aljanu datana gida da kyar namijin dare yamabarta tai aure” ahankali tashare hawayen daya zubomata sharr babu abinda ta tsana irin adinga kiranta da yar aljanu ko mayu, Mum tasake wurgamata mugun kallo tace “wawiya dakikiya kawai babu abinda tasani sai zaman daki, kannenta ma sunfita iya karatu sunfiki iya komi Babanki yamaidake gidahuma yaryar aljanu kawai” wanan karan fashewa da kuka tayi sosai takai hannunta tadaura kan fuskanta tana kuka, murya chan kasa ta yanda Baza ajiba tace “niba yar aljanu bace” da sauri Mum dake tsaye kanta tace “me kikace Du’a? Mayarmin da magana kikayi? Did you just talk back at me eh?”.
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️ M SHAKUR
Don yin magana directly da M Shakur click on this link wa.me/+2347012181461
M Shakur nada group din Matan Aure wanda idan kinason kishiga is just 1k.
hakama idan kinason advert shima M Shakur duk tanayi.
free page
EPISODE 3️⃣
Girgizamatakai tayi ahankali gwaninban tausayi alamun bada ita takeba, cikeda mugun tsana tace "haka zaki kare rayuwanki awanan dakin, agabanki yayyinki da kannenki duk zasuyi aure ke kina nan adakinnan har tsufa bazakiyi aureba saidai ko indaga dangin ubanki aljanune wasu zasuzo kuyi wup dake, mai bakin jini kawai mara kunya" tana maganan tawuce tafice daga dakin, sosai tafashe da kuka, har bakin suka tafi su Nana suka dawo dakin nan kuka take bata denaba, dayake sun saba bawai sabon abubane kukantaba saisaima babuma wanda yabita kanta saima shirin kwanciya dasuka shigayi suka gama Hawwa takashe wutan dakin, haka taci kukan nan har batasan sanda bacci yay awon gaba da itaba.
Yau Monday sabida taci kuka batai bacci dawuri ba sai wuraren 8 ta farka, koda ta tashi babu kowa adakin saidai sababbin novels datagani manya guda uku agefenta dasauri ta tashi zaune ta dauka tana dubawa, sunan Novel din farkon The Noisy Naigbour, na biyun sunanshi the killer tree, saina ukun Disastrous Love, wani kalan murmushi tayi sanan ahankali tace "thank you Ya Hamad" ajiyesu tayi tawuce bayi alwala tadauro sanan tafito tai sallan asuba tabude Al Qur'ani tana koya Haddan da Abba yabata, saida ta tabbatar ta haddace shafi daya darabi sanan ta tashi, dakinsu ta shiga gyara musu wanda yanzu zata iyacewa a rayuwa that's the only thing data iya gyaran daki shima da karfi da yaji takoyama kanta, ta gyaramusu gado sanan tawuce bayi tayi brush tayo wanka tafito ta shafamai sanan tasaka wani riga da skirt na atampa daya mata kyau tai parking gashinta da kyar sanan tadauki novel kaman barauniya tabude kofan dakinsu ahankali sanan tasakai taleko kadan ganin babu kowa yasa tafito duka, sanan tashiga sadadawa tafara tafiya ahankali zatai stairs. "Ina zaki"? kaman daga sama taji muryan Mami dasauri tajuyo, hada ido sukai da Mami data fito daga dakinta tana kallonta, saukar da kanta kasa tayi tana kara kankame novel dinta ahankali tace "Mami good morning" batare data bata amsaba tace "wuce kikoma dakinku ga Uwani nan zansa takawomiki break" gyadama Mami kai tayi ahankali sanan tajuya zata koma dakinsu bintada kallo Mami tayi harta shige sanan tasauke ijiyan zuciya ahankali tawuce tasauka kasa, hada mata breakfast tayi kunun gyada da kosai, samin kanta tayi da daukan wani karamin plate tajuyemata ragowan naman da Abban su yarage sanan ta kwalama Uwani dake wanke wanke kira dasauri Uwanin tazo tray tabata tace "kaima Du'a abinci adakinsu" karba tayi tawuce sama bude kofa tayi tashiga tana kallon Du'a data bude novel tana karantawa, har gaban Du'a tazo sanan ta tsugunna ta ijiye tray din still kallon Du'a take, ahankali Du'a ta janye novel din datake karantawa daga kan fuskanta jin kaman ana kallonta hada ido sukayida Uwani, almost 2yrs Uwani na aiki a gidansu but she thinks yaune 3rd time datake ganin Uwanin hakan yasa cikin yar muryan nan nata tace "kece uhmm yama sunanki U....uuuuu...." takasa tuna sunan dasauri Uwani tawashe baki tace "Uwani sunana mai aikin gidan nan" gyadamata kai Du'a tayi sanan tasake maida fuskanta kan novel din tacigaba da karatun dan ko kadan batada surutu kusan cikin duka yaran tafi gado halin mahaifinta indai rashin surutu ne.
Sosai Uwani takasa motsi daga wajen sai wani irin kallon Du'a take dabamatasan tanayiba, bude kofa Mami tayi ahankali ganin yanda Uwani ke kallon Du'a dabamatasan tanayiba dan ita karatun novel dinta take bilhakki yasa ta dakamata tsawa. "Uwani" firgigit ta farka daga dogon tunanin datake haka itama Du'a tadan firgita jin muryan Mami hakan yasa duk suka kallo Mami, cikeda bacin rai Mami tace "kin manta kinbar aiki a kitchen ne zoki wuce kifita" dasauri ta tashi ta taho tace "yakuri Hajiya" fita tayi Mami kuma ta watsa watsama Du'a data zubama mahaifiyar nata manyan fararen idanunta harara sanan tajuya tafice, tai kasa danso take tadaura girki, kitchen ta shiga tana duba naman data saka a wuta itakuma Uwani tacigaba da wanke wanke tana tunani sai chan tajuyo ta kalli Mami da hankalin ta kekan juya naman datake dake wuta tace "Hajiya" "ya akayi Uwani"? Mami tamata tambayan batare data kalletaba, tsayarda komi Uwani tayi tace "Hajiya kunada y'a haka maisa kuke boyeta wanan yarinya taki haka aiko shugaban kasa tafi karfinshi, maisa kuke kulle ta adaki haka" tunda tafara maganan Mami takasa cigaba da juya naman datake ta tsaya chak harta gama maganan datake sanan tace "ki tsaya a huruminki Uwani inba kinaso mu sallameki mu nemo watabane" dasauri tace "yakuri Hajiya tuba nake, kawai daman abin ya tsayamin araine" juyawa Mami tayi tacigaba da aikinta bata karabi takanta ba.
*******************
Yau Friday
Sunada wata al'ada agidan ranan jumma'a kowama gidan nacin gayun Jumma'a. Su Nana tun 11 suka dawo yau sabida lectures daya kawai sukeda shi, tun safe batai wanka ba sabida Novel din Disastrous Love datake karantawa daya daukemata hankali gabaki daya, su Nana ko harsun sake wanka sunci gayu abinsu sunfice daga dakin zuwa dakin Mum dinsu. Bude kofa akayi Mami tashigo daga bakin kofan ta tsaya binta tayida kallo sanan tace "yau bazakiyi wankan bane"? Dasauri ta ijiye novel din ta kalli Mamin ta dataci gayu cikin wata hadaddiyar bubu na shadda, tashi tayi dasauri tasauka daga kan gadon daga ita sai rigan baccin data saka iya guiwa, ahankali tasaukar da kanta kasa tana wasada yatsunta tace "yanzu zanyi Mami" tana maganan dasauri tajuya zuwa bathroom dinsu tabude kofa tashiga Mami tabita da kallo harzata bude kofa tafice saikuma ta dawo cikin dakin, gaban wardrobe din dakinsu taje budewa tayi ta tsaya tana kallon side din kayan Du'a, bangaren bras dinta ta kalla danta lura kwanan nan bata saka bra at all, daukan bra din tayi ta kalla sai lokacin tagane duk su mata kadanne saisa bata sawa kuma bazata iya fadan mataba, kwasosu tayi gabaki daya tadauki wani leda tazubasu aciki sanan tawuce tafita daga dakin, dakinta tashiga ta ijiyesu agefe sanan ta kwaso mata wasu new manyan bra masu kyau guda uku sanan tafito tadawo dakin, wardrobe din taje ta ijiye bra din sanan tazakulo mata wani lace mai bala'in kyau pink and white flowers dan tasan Du'a da hauka babu abinda ta iya kowani kalan kaya tasamu saka wa take, taciro tahada mata da sabon bra da pant tadauko ta ijiye mata kan gado, sanan tamaida wardrobe din tarufe takoma dakinta, kwalli tadauko mata sabo dawani sabon turare tadawo ta ijiye mata kan gadonta daidai lokacin tafito daga wankan daureda towel a kirji, juyowa Mami tayi takalleta daga sama har kasa, sunnar da kanta tayi kasa cikeda kunyan Mami tana gyara towel din dan bai rufe mata cinya da kyau ba kuma batasan zata sami Mami adakinba data maida rigan baccin ta, juyawa Mami tayi tafice abinta, dasauri tazo kan gadonta ta zauna, kwallin da Mami ta ijiye tafara dauka tace "laaaaa yama sunanshi irin nasu Ya Nana dasuke sawa a ido" wani irin murmushi tayi ta ijiye tadau kwalin turaren tana budewa tace "laaaa nima inada turare yanzu sunanshi Zara" budewa tayi ta ijiye cikeda farin ciki, agurguje tashare jikinta sanan tashiga shafa mai sabon bra tadauka tasaka aiko yamata cip cip lace din tasaka yamugun mugun mata kyau turaren ta tadauka ta feffesa yafi feshe goma sai murmushi take sanan tadau dan kwalinta da kwallin ta tafi gaban madubi, zama tayi tadauki comb taje gashin tayi sanan tai parking gashin da kyar sanan tadau dan kwalin duk yanda taso tadaura takasa daga karshe daurin yan kauye kawai tayi dan bata iyaba amman dudda haka tai kyau sanan ta bude kwallin taciro zata saka takai idanunta looking so excited kafin tasaka tawani tsirama idanunta ihu tayi sosai tawani zarooo hakan yasa tama tundaga idanun har zuwa gefen idanun har kunnenta bakin zanen layi, sosai ta kankame idanunta tana ihu ga radadi sai kuka batasan lokacin data mikeba tana tangadi tana ihu. "wayyo idanuna wayyo idonta" Mami da haurowanta sama kenan taji ihun ta dasauri tai hanyar dakin bude kofa tayi daidai yana shirin kuma kanta da bango tana ihu dawani irin sauri Mami ta tarota tana kokarin tallabo fuskanta tace "maiya sami idon"? Rirrike Mamin tayi cikin kuka tace "Mami idona zafi kwallin nanne ya tsiremin kwayan idanun" Mami na rikeda ita ajikinta tai bathroom dinsu da ita bude tap tayi ta tare hannunta ta debo ruwa wanke mata fuskan tayi tass sanan takashe tap din tana rikeda fuskan nata tace "bude idanun naga" ahankali tabude idanun kadan, aiko idon yayi jajir, kallon Mami tayi tanadan kyafkyafta idon tace "yadena zafi Mami" Mami na rikeda ita tafito da ita daga bayin zuwa gaban madubi zaunarda ita tayi sanan tadauki wipes din Nana data gani awajen tabude taciro kwara daya sanan takama fuskanta tagoge kwallin dayamata layi har kunnenta tagoge tass, sanan ta gyara kwallin dabama tasa a ido ba saidai kasan idanun sanan tadauki kwallin, habanta takama tace "bude idanun nagani" budewa tayi sanan Mami ta zizara mata kwallin aduka idanun rirrike Mamin tayi tawani tura fuskanta kan cikin Mami tace "Mami idona wani iri daman haka yakeyi wayyooo" chak Mami ta tsaya tamanta the last time da hannunta yama taba jikin yarta saiyau, firgigit kaman wacce ta tuna wani abu sai kawai ta hankadeta daga jikinta batare data kalleta ba tace "dau dankwalinki ki