Showing 9001 words to 12000 words out of 153675 words

Chapter 4 - Kyawuna Jarabta Ta Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

15 Dec 2024

600

yadade tsaye akanta sanan yawuce yafita daga dakin.




💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫



✍️M SHAKUR


Free page
EPISODE 5️⃣
Dakinshi yawuce, bude kofa yayi yashiga dakin Mum na zaune kan kujera itakuma Nana tana zaune akasa tana share hawaye danhar lokacin kuka take ganin Abba yashigo yasa gabanta yacigaba da faduwa dan gabaki dayansu suna tsoron mahaifinsu danko kadan baida wasa sanan yanada zafi.


Maida kofan yayi yarufe sanan yashigo ciki har lokacin kanta nakasa sanan yawuce yazauna kan kujeranshi yana facing bata, cikin kakkausan murya yace "maiya hadaki da kanwarki Du'a Nana"?Hawayenta tashare cikin sheshekan kuka tace "Abba dazu Muhsin yazo na shimfida mai dadduma a garden shine nakoma nadauko zobo ina zuwa naganshi tareda Du'a....." yanketa Mum tayi tace "fadama Babanku komi kina bobboyemai kikaga dai Du'a ajikinshi" wani irin kallo yama Mum sanan yace "kika kara magana batare danabaki izinin kiyiba wlh saikinyi mamakin abinda zan miki" yajuya yakalli Nana yace "ina jinki" sake share hawaye tayi tace "Abba tarena ganshi da Du'a babuma dan kwali akanta yarikemata hannu yana kokarin tabamata gashi, shine Du'a na ganina tahau kuka wainace yasaken mata hannu, sakinta yayi ta tafi shine yacemin waishi bazai aureni ba wai Du'a yakeso ita zai aura yanzu bayasona waizaije yagayama babanshi" shiru tayi takai bayan hannunta ta goge wasu sababbin hawayen dasuka zubomata.
Gyara zama Abba yayi ranshi amugun bace yana kallonta yace "dago fuskanki ki kalleni nan" girgixa mai kai tayi takasa, hakan yasa yadaka mata tsawa yace "I said look at me" dasauri tadago kanta takalleshi jikinta har bari yake tsabagen tsoro da shakkan Abban ta yace "so sabida namiji ne kike neman kashe blood sister ki, da Allah bai kawoni gidan nanba dayau kinyi kisan kai eh!" yasake dakamata tsawa kana ganin yanda yake maganan kasan ranshi abace yake, yace "to the extend kina ciremata riga exposing your fellow sister body kannenku su ganta, Nana is that how I train you eh answer me" fashewa tayi da kuka sosai tace "Abba kayakuri bazan karaba" girgixa mata kai yayi yace "kece y'ata mace tafarko yau idan namutu I believe kece zaki kula dasauran kannenki u will be their mother but look at what you did today, sabida namiji eh? sabida yace bazai aureki ba and so what zaki kashe yar uwarki ur blood sabida wani eh? Saina hukuntaki sosai Nana, stand up jeki kawomin wayanki, your laptop ki kawomin ATM card dina danabaki" fashewa tayi dakuka sosai dan babu abinda yafi tadamata da hankali irin wayan dawani wayazata kira Muhsin su shirya, ita karan kanta Mum saida ta girgixa amman takasa magana dan taga ranshi inyay dubu yabaci. cikin kuka Nana tace "Abba dan Allah kayakuri nayi kuskure amman namaka alkawari bazan karaba" wani kallo yamata yace "you know my principle bana dukan yara, but kika bari natashi daga wajen nan batare dakinje kin kawo what I asked for ba sainamiki jina jina" wani kallo Mum tamata na alamun taje takawo hakan yasata tashi tafita bata bata lokaci ba tadawo takawo komai kujera yanuna mata yace "keep them there and leave this room, sanan dagayau!" yajuya yakalli Mum yace"ki sallami Uwani duk wani aikin Uwani ita zata dingayi bazatabar gidan nanba saita gama kodako zatai lattin lectures get out" dasauri tajuya tafita tarufo musu kofan.




Wani kallo yabi Mum dashi yace "I am so disappointed in you Hajara, halinki nabani mamaki and ki sauraren kiji bazan zauna inaji ina gani ki rabamin kan yarana ba, wlh duk randa kika kara attempting abinda kikayi yau kinasa anacirema yarana mata kaya kina kiran yara suyi ihu wlh wlh saina rabu dake take this as a warning" cikin kwantar da murya tace "kayakuri Alhaji na yarda nasan nai kuskure I know I took everything far, but raina abace ne maganan da Kaka keyawan fadi duk yadawomin kai, wlh Alhaji da gaske Du'a yar aljanu ce to inba hakaba ya za'ayi Muhsin dake tareda Nana kusan sjekaru biyu kenan yau kawai daga ganin Du'a yace ita yakeso yafasa auren wacce yasani for years, dududu bikinsu saura wata daya, tuntuni Kaka tace ka tattara yarinyar nan ke korata chan duniya inba hakaba bala'i da masifu iri iri sundinga samunta gidan nan kenan, yanzu maganan Muhsin baiwani dadani da kasaba amman what if dagaske yake eh? da gasken gaske yake shi yafasa auren Nana Du'a yakeso bahakan ya tabbatar mana itadin yar Aljanu bace ba kenan, wlh indai aka fasa auren nan saina kira Kaka na sanar da ita komi gwara tun yanzu nagaya maka sabida kar bayan kaji nayi kaga kaman na yaudareka ne" "tashi kifita daga dakin nan" Abba yay maganan cikeda fada, tashi tayi tace "narasa me kakeyi da yarinyar dakai karan kanka kasan bataka bace agidan nanba saisama baka ambato sunanta cikin y'ayan ka, hakanan wlh koma mezai faru saidai yafaru I am a mother bazan zauna inada zankada zankadanyanmata ba sukasa aure ba sabida yar aljanun da aka haifa maka agidan nan, gaskiya nake fadi I can go to any limit dannai protecting yarana, grounding nata adaki doesn't solve anything dan gashinan fita take causing trouble, the best thing is tabar family mu takoma chan family su na aljanu" tai maganan tana bude kofa tafice abinta, gabaki daya duka abinda tafadi yajisu.



Ajiyan zuciya yasauke ahankali tareda fuzarda iska daga bakinshi yadade ahaka zaune sanan yatashi kaman an tsikareshi, bude kofa yayi yafice, hanyar dakin Mami yayi, ahankali yasa hannu yabude dakinta wani kamshi ne yamai sallama, shiga ciki yayi tareda maida kofan yarufe, tashi tayi tsaye daga kan gadon datake zaune idanunta sunyi jajir takakalo murmushi tace "sorry Dadyn Hamad bankawo maka abincinka ba" tazo da sauri zatabi ta gefenshi tawuce hannunta yakamo sanan yajawota jikinshi fuskanta ya tallabe yace "you've been crying ko jibi yanda idanunki suka kukkumbura" girgizamai kai tayi zatai magana saiga wani kukan kuma hakan yasa dasauri yasata ajikinshi yana bubbuga bayanta batare dayayi magana ba, tadade ahaka sanan tadago ta kalleshi tace "Abban Hamad kafin muyi aure ai kokai saida aka tabbatar maka dana warke ko naji sauki, babu any form of jinn ajikina, bana wasa da azkar safe rana da dare, yau shekara nawa muna tare ba kara having any form of attack ko mafarki ba, but yau nafara tunanin kodai sune baban Du'a di......." hannu yadaura mata akan baki yace "shiiiiii banson maganan nan, kintaba ganin jinn sun haifi mutum? nine mahaifin Du'a, kawai Allah yabamu y'ace daban damu nothing more nothing less" girgizamai kai tayi tace "what if Muhsin da gasken yafasa auren Nana Yaya zamuyi? how are we going to explain this to the family Yaya zamuyi" saiga wasu sababbin hawayen, yatsanshi yakai yasharemata hawayen daya zubomata yace "when we get to the bridge we will know ta yanda zamu tsallaka shi karki damu kanki kinji" gyadamaikai tayi ahankali wasu hawayen na zubo mata tace "Dadyn Hamad Du'a batajin magana, we've grounded her for years now tundaga JSS3 har zuwa yau, amman kwanan nan tasoma sneaking tana fitowa, hakanan inaji araina something is about to happen, what if tasake samin attem........." hannunshi yadaura kan lips dinta yace "stop talking, and stop thinking negative, idan tafarka nida ita we will have some serious talk, yanzu all abinda nake bukata is natsuwa dan banda ita ko kadan, ina bukatan natsuwa sanan nasamu nayi tunani, bari nasami natsuwa dake" yana maganan yadauketa zuwa gado bashi yafito daga dakinba sai wuraren 5 ya chanza kaya zuwa jallabiya fuskanshi tayi wani annuri alamun akwai full natsuwa taredashi yasauka zuwa falo, Mum na zaune a falo tadauke kai kaman bata ganshi ba.



Saukowa Mami tayi taci sabon kwalliya Mum tabita da harara tace "kidaiyi kigama gobe zan karbi girkin" serving Abba tayi sanan tazauna gefenshi tana bashi duk wani abu dayake bukata.




💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫



✍️M SHAKUR

Free page
EPISODE 6️⃣

Bayan sallan isha'i Abba baima dade da dawowa daga masallaci ba shida Hamad dasu Muhammad ba mai gadi yayi sallama izini Hamad yabashi yashigo, shigowa yayi har gaban Abba yace "barka da hutawa Alhaji, kanada baki, sunce wai Alhaji Ibrahim mai tabarau ne" kallon Abba Hamad yayi yace "Baban su Muhsin ne Abba" tashi Mum dake zaune afalon tayi ta kalli su Muhammad tace "yara kuwuce mutafi sama Abban ku yay baki" binta yaran sukayi sukai sama, kallon mai gadi Abba yayi yace "kamusu iso" Maigadi yawuce yatafi, Hamad yakalli Abba dayaganshi anatse yace "Abba yaya zamuyi idan dagaske Muhsin yake"? Murmushi Abba yayi bai bashi amsaba yace "just stay here and learn, duk randa bani kaine zakai making decision akan kannenka mata" gyadama Abba kai yayi daidai lokacin mai gadi yay sallama yabude kofa yashigo dasu hakan yasa Abba da Hamad suka tashi don agaisa, wasu Manya manyan attajirai ne su uku sai Muhsin dake taredasu kana ganinsu you don't even need an explanation kasan masu hannu da shuni ne, hannu Abba yamika musu cikeda girmamawa suka gaida dan mahaifin Muhsin ne Alhaji Ibrahim maitabarau sai kannenshi guda biyu Alhaji Isyaka Maitabarau sai Alhaji Mubarak Maitabarau, sosai Abba yagaisa dasu cikin mutuntawa yasa suka zazzzauna Muhsin shima ya gaida Abba cikeda girmamawa ya amsa, Hamad ma yagaidasu suka zauna cikeda girmamawa, shigowa Uwani tayi takawo drinks da ruwa sanan tawuce falon yay shiru.



Gyaran murya Mahaifin Muhsin yayi yace "To bari mufara da kalamai mafi kyawu wato da Sunan Allah Mai Rahama Maikuma Jinkai, Alhaji kaganmu agidanka da dare haka kuma unannounced ko, bawani yakawomu nan ba sai wanan yaron" yanuna Muhsin dake gefenshi da kanshi ke kasa, sanan yakara sauke ijiyan zuciya yace "wlh Alhaji idan nace namasan ta yanda zanmaka bayanin nan kafahimta tonamaka karya amman bari nafara da tantance gaskiyan lamarin kafin nakoro bayani" yay dan shiru kafin yanisa yakalli Abba kaman yanda shima yake kallonsu yace "Alhaji wai dan Allah kanada y'a mai sunan Du'a ne? Danni wayanda muka sani shine wanan Baban dan naka wato Hamad, Aisha, Hawwa, Amal, Aneela, Asiya da Muhammad da Mudasir, dan Allah katabbatar min da gaskiyan lamarin nan kanada y'a mai sunan Du'a ne wacce duk bamusanta ba"? Shiru Abba yayi yana kallonsu kaman bazaice komiba danhar dagakai Hamad yayi yana kallonshi sanan yadan nisa yace "eh inada y'a mai sunan Du'a" ahankali Baban Muhsin yace "to Alhamdulillah, nasan banida wanan hurumin dazan tambayeka maisa baka taba ambato mana itaba ko wani abuba dan nasan kanada dalilinka nayin hakan, daman tabbatarwan kawai ita nake bukata tunda yanzu ka tabbatarmana kanada y'a mai sunan Du'a toga dalilin da yakawomu wurin ka da daddaren nan" ya sakeyin shiru sanan ya numfasa yace "shi so hallitan ubangiji ne, danhaka so gaskiya ce hakama ki, Alhaji d'ana yazo gidanka jiya sai cikin iko irin na Ubangiji yaci karoda yarka Du'a kuma Allah ya jarabceshi da sonta ainun aranshi danyau haukace mana kawai ne baiyiba ga kannina nan katambayesu kaji, yace shiyabarma Nana duka abubuwan dayamata amman yafasa aurenta dan baya sonta Allah yahadashi da Du'a ita yakeso itakuma yakeson Ya aura inhar ka yarda zaka bamu" tunda suke maganan Abba yake kallonsu babu ko kyafta ido, yakai kusan minti biyar ahaka baice komiba dakin tsit kakeji sanan yay gyaran murya yace "to Alhamdulillah naji dadi yanda kukazo kukasamen, shi gaskiya dayace koda batada dadin ji, naji dadin yanda kuka sanardani gaskiya batare da kwana kwana ba ko kuma boyeboye ba danhaka nima zan sanardaku gaskiya Alhaji" yay maganan cikin mugun hikima da ilimi sanan yace "it's very okay idan danku Muhsin yaji bayason y'ata bazai aureta ba shi aure daman yagaji haka ko anyi ana rabuwa, amman gaskiya itace bazan iya bama Muhsin wacce yaji yakeso dinba wato Du'a" dasauri Muhsin yadago kanshi yakalli Abba idanunshi sunyi jaaa sosai.



Abba yacigaba. "Alhaji kai mahaifine haka nima mahaifine, yanzu wani yazo yana tareda yarka har a kusa bikinsu sai yaga kanwarta yace yafasa aurenta kanwar yakeso zaka yarda kabashi"? Abba yamai tambayan shiru Baban Muhsin yayi yakasa amsa tambayan, Abba yace "duk wani abinda zai raba kan y'ay'ana ko family na bazan taba yinshiba, gwara afasa auren gabadaya da inbaka wata, dan haka I am sorry idan maganata ko amsata bata kuma dadi ba amman bazan iya baku auren Du'a ba, as for kayayyakin dakuka kawo duka in sha Allah zamu aiko muku dashi, Allah yasa hakan ne yafi alkhairi"


Kafinma Baban Muhsin yayi magana Muhsin ya rarrafa da gudu zuwa gaban Abba, kneeling yayi yahade hannayenshi biyu muryanshi narawa kaman wanda zai fasheda kuka yace "Abba Abba wlh wlh wlh na rantse da Allah bawai dan cin mutunci ko toxarci kodan inci zarafin Nana nai hakaba, wlh kawai Abba azuciyata naji bana sonta wlh tunda nasa Du'a a idanuna nake so ko kulkewa nayi saina ganta, Abba kataimakamin dan Girman Ubangiji" tunda yake maganan daga Abba har Hamad kallonshi sukeji, ahankali Abba yasa hannayenshi yakama hannun Muhsin dayake rokonsu dashi yace "Son kayakuri kotayaya zaka roken I don't think I can risk my family for this, I can't stand naga kan family na ya rabu sabida one bad decision dazanyi ba, bazan iya baka Du'a ba, it's final" to Abba biggest suprise kawai yaga Muhsin yafashe da kuka sosai, daura kanshi yayi kan cinyan Abba cikin kuka yace "Abba wlh idan baka bani Du'a ba zan iya mutuwa dan Allah kayakuri, I am sorry if I hurt you sabida nace banson Nana...."



Iyayenshi kasa koda motsi sukayi, sunsan Abba made the right decision dankosu basuso sunzo ba mugun so da gatan dasukema Muhsin dinne yasa sukazo su gwada luck dinsu.


Ganin yanda Muhsin ke kuka yasa zuciyan Babanshi yafara breaking shifa baida wanda yakeso kaman Muhsin aduniyan nan, kallon Abba yayi yace "Alhaji name anything dakakeso wlh zan maka indai zaka bama dana Du'a dinan dayakeso, kaga wlh zan iyasa acireka daga matsayin HOD dinan abaka Deen na BUK gabaki daya, idan bakaso zan baka aiki akasan waje, wanan gidan na chanza maka nabaka lafiyayyen gida anan GRA kano, mota kudi koma mekakeso just name it zan baka inda zaka hakura kabama yarona wacce yakeso kaganshi nan shikadai gareni kataimakamin please" sake tashi Muhsin yayi daga jikin Abba fuskarnan nashi hawaye ya wankeshi yahade hannayenshi yana kallon Abba, dan murmushin manya Abba yayi yace "I am happy da position da dukiyan da Allah yamin a rayuwa bana bukatan kari, nariga nayi maganata idan babu matsala zan haura sama inada y'a mara lafiya naduba, Hamad you can see them off okay" gyadamai kai Hamad yayi Abba yatashi, sosai Muhsin yafashe da kuka, kanin Baban Muhsin Alhaji Mubarak yatashi yay wajen Muhsin yace "Kato dakai kana kuka, ga matanan agari kaman ledan pure water kodaga kasan waje kakeso kayi aure Babanka zai auromaka tashi mutafi" kintashi yayi saifada sukayi da gaske suna dagashi sanan suka fitardashi daga falon Hamad yatashi yarufe kofa jikinshi a sanyaye.



koda Abba yatafi sama dakinsu Nana yabude yashiga, bin kowa nadakin yayi da kallo Nana na kwance kaman mara lafiya idanunta a lumshe sai Hawwa ce idanunta biyu, tana ganin Abba tace "sannu da zuwa Abba" gyadamata kai kawai yayi yakalli Du'a dake barci har lokacin sanan yajuya yafice yakoma dakinshi, ko zama baiyiba Mum tabude kofa tashigo dakinshi, juyowa yayi yakalleta sanan yazauna akan kujera yana ganin idanunta kadai yasan taji duka maganganunsu a falo dan idanunta sunyi ja kaman ma hardan kukan bakin ciki tayi. zama yayi kan kujera yana kallonta, daurewa tayi tahadiye abinda ya tsayamata arai tace "yakukayi dasu Alhaji" jaridan shi dakekan table yadauka ya gyara zamanta akan hannunshi sanan ya kalleta yace "idan Allah yakaimu gobe duk wani abu na gidansu Muhsin ki tattarasu tass zansa azo adauka amayar musu" wani irin faduwa da rawa gabanta keyi dan babu kalan burin dabata dashi akan auren Nanan ta da Muhsin, finally yarta zatai rayuwa gidan masu kudi shine tashi daya kaman aradu zancen aure yamutu, daurewa tayi tace "does that mean babu zancen aure? Ba za'ayi auren Nana da Muhsin ba kenan?" bude jaridanshi yayi zaifara karantawa yace "eh babu zancen aure, Allah yabata wani mijin nagari" yay maganan tareda gyara zama kan kujera yana karatun littafin shi dakyau sosai take kallonshi jitake kaman tarufeshi da duka tsabagen bakin ciki, wai ace anfasa auren yarsu 26yrs finally year student din yarsu, yarinyar dayasan tanason Muhsin dinta yau all of a sudden amman this guy is still acting kaman it's nothing, jitayi idanunta sunjuya sama wutan bala'i nacimata zuciya tajuya fuuu tafice ko tsayawa kulle mai kofa batayiba tana fita tacikaro da Hamad daya hauro sama zaizo yaduba Du'a, idanunta kadai yagani yasan ba lafiya hakan yasa yajuya dasauri zai koma dasauri cikin mugun ihu tace "dan ubanka wlh katafi saina tsinemaka albarka agabanka aka fasa auren yarka bakai komi dan taimakon lamarin ba dawonan" juyowa yayi ahankali sanan ta shiga kwalama yaranta kira. "Amal Asiya" dasauri suka fito daga dakin su harda Aneela yar Mami, jin ihun Mum tasa Mami itama tafito, kama hannun yaran tayi tawani irin tura kofan dakin yaran, yanda kofan yay mahaukacin kara yasa Du'a ta firgita sosai ma tabude idanunta, shigowa Mum tayida Hamad da Amal da Asiya, sanan ta kalli Nana da Hawwa daduk ita suke kallo tace "Nana saurareni kiji anfasa aurenki, Muhsin har kuka yake yakama kafan ubanki yana roka abashi wanan yar Aljanun" tanuna Du'a, dasauri Hamad yace "Mum please stop all this bahaka ake handling situation like this ba sokike zuciyan Nana yabugu eh"? Cikin bakin masifa Mum tace "buguwa na nawa kuma" tasake juyawa takalli Nana da kallonsu kawai take kaman gunki tace "Nana Muhsin yace bazai aureki ba yanzu haka ubanki yace ahada komi nasu harda akwatin dasuka kawo naki amaidamusu abinsu gobe dasafe" kokarin yunkurowa take tatashi tasauko daga gado kawai jiri yadebeta ta yanke jiki zata fadi dawani irin sauri Hamad yatareta yace "Nana Nana" juyowa Mum tayi takalli Mami data tsaya daga bakin kofan tana kallonsu kawai saitaikan Mami shakumo Mami tayi tace "wlh saina kasheki duk abin nan dake faruwa dadi kikeji yarki ta kacema y'ata miji har celebration kike kikaji Babansu daki kina cinshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login