Showing 72001 words to 75000 words out of 153675 words

Chapter 25 - Kyawuna Jarabta Ta Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

15 Dec 2024

610

am unjust towards you, and kinsan wani abu u are right Du'a" Yaydan shiru sanan yace "koma yaya kike u are my daughter and hakkinki ne nakira sunanta cikin yarana so" yadan sakin mata murmushi for the first time tunda yashigo gidan yace "I hope this time around I am just dan namiki abinda kikeso, kince kinason aure kuma amatsayina na mahaifinki na aura miki wanda kikeso wanda Kakarki tayaba da tarbiyanshi bama ita kadai ba ko a masallacin anguwan yanzun nan mutane dayawa sun yaba halin Asad din hakan yakara samin natsuwa hankalina ya kwanta danhaka" yay maganan yana zare hannunshi daya daga rikon dayama hannayenta yatura hannun a aljihu yaciro wrap na sababbin 1k guda daya yadaura akan hannunta yace "ga sadakin kinan Du'a naira dubu dari, Allah ubangiji yamiki albarka" batasan mesa na hakanan taji kuka yazo mata kodan sabida wanan ne karo na farko da Abba kemata magana mai tsayi haka oho amman dai jitayi kuka yazo mata, dagakai Abba yayi yakalli Asad yace "come Son" wani irin murmushi Ammi tayi, ahankali Asad kanshi nakasa yataho gaban Abba shima, hannunshi Abba yakama sanan yadauki na Du'a daya rike yasa asaman nashi yace "ga Y'ata Du'a nan nabaka amananta, ka riketa tsakani da Allah karka cutarmin da ita, ka kulada cinta, shanta, suturanta da lafiyanta dan yanzu duka sun tashi daga kaina ko kan Kakanta sun koma kanka Asad, zuciyata ta aminta dakai dan haka nabar muku ita, yanzun Du'a matarka ce halak malak sai yanda kace sai yanda kace ayi za'ayi dan haka, idan kunso kuyi biki ko taro duk ba matsala takace Allah ubangiji yamuku albarka, zan koma gida zan sanarda Kakanki tachan cewa na aurar dake zan sanarda yan uwanki, kibi mijinki kimai biyayya Du'a, Allah yamuku albarka" yay maganan yana zare hannunshi dagakan nasu yanadan murmushi sanan yakalli Mami da idanunta sukai jajir yace "tashi mukama hanyan tafiya" sanan yatashi yakalli Dad dakawai binsu yakeda ido dankomi yafaru akan idanunshi kaman mafarki ne yabashi hannu yace "surukina sai munyi waya, Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa" dasauri Dad yatashi yana kakalo murmushi yabashi hannu da fara'a yace "Ameen Ameen, zamuyi waya muje namaka rakiya" gyadamai kai Abba yayi yakalli Grandma dake zaune awajen ahankali cikeda girmamawa yace "kiyakuri Mama dakomi, zamu tafi" dan murmushi tamai tace "babu komi baban Hamad agaidamini da yara dan Allah barinma mijina Hamad" murmushi yayi shida Abba suka wuce suka fice, dakin yarage saura Mami data kasa tashi da Ammi dakuma Grandma dake kallonta, tashi Ammi tayi tadaga Mami ta rungumeta bakinta tadaura akan kunnen Mami tace "I know what u are thinking right now Zainab karki manta nima uwace, but zanmiki wanan alkawarin inhar inada rai Du'a bazata taba wulakanta na, zan kulada ita Asad ma zai kulada ita amana, namiki alkawarin nan Du'a tariga tai miji bazan miki karya ba she is in a good hands I assure u that" wani irin ajiyan zuciya Mami tasauke dan har kasan ranta taji dadin kalaman Ammi kankameta tayi tace "thank u Anty Zainab" sakinta Ammi tayi tace "yima mahaifiyarki sallama" gyadamata kai tayi sanan takarasa wajen Grandma ahankali ta tsugunna, dauke kai Grandma tayi hakan yasa gently tace "Mama kiyakuri kiyafemin kinji dan Allah" juyowa tayi takalli yarta ta ga mamakinta saitaga tasakin mata murmushi takai hannunta kan fuskanta tace "komi yawuce, Du'a tayi aure tana kuma kusa dani danhaka komi yawuce, tashi kitafi tafiyan ku nada nisa" tashi tayi ahankali Sana tajuya zata fice hartakai kofa tadan waigo tasaci kallon Du'a hada idanu sukayi hakan yasa tai sauri tafice Ammi dake murmushi tabita abaya dasauri, Du'a batasan lokacin data cire hannunta dake cikin na Asad ba tawani irin tashi cikeda murna tai kan Grandma tafada jikinta tana wuntsula kafa Grandma basu tafi dani ba wayyooo Allah na wlh dadi nakeji yayyy, tawani irin kankame Grandma da mamaki yagama kasheta tana murna, tashi Asad yayi ta gefen ido yakalleta sanan yay hanyar kofa batare daya kalli Grandma ba yace "bari naje office Grandma" baima jira respond dinta ba yafita daga falon wani irin makirin murmushi yasaki tareda biting lips dinshi ahankali yace "killing two birds with one stone feels good, ranshi fess kaman fresh madara....



Saida Abba da Mami suka wuce amotansu sanan Dad yajuya yakalli Ammi yace "what have you done dayasa Asad yace yes to this marriage dan nasan Asad ba son yarinyar nan yakeba, mekikayi Zainab" wani irin murmushi Ammi tayi da zuciyanta daya tace "rokonshi nayi, Alhaji Du'a is a very good girl, ga tarbiya gata so calm, bata bude idanu ba, kuma I am sure ko Asad bayasonta now he will grow to love her trust me and zasuyi making a very nice and healthy family, I just made the best decision for him tr........""Malama kimin shiru" Dad yadaka mata tsawa cikeda fushi yace "what kind of nonsense is all this eh? kinzaci aure abin wasane dazaki lallaba yaronki ya auri yarinyar da batama taba burgeshi ba" ahankali Ammi tace "to inda bai aureta da yanzu sun tafi da yarinyar data kara shiga depression haba Alhaji this girl is so innocent da kallonta kadai zaisa mutum yaji bakison anything that will hurt her, Asad save this girl and muna nan dakai zaisota" cikin kunsan rai Dad yace "just stop with this nonsense idan Asad yashigo gidan nan zan tambayeshi dakaina idan bayasonta this night zansa yarubuta saki yabama yarinyar mutane and free her tunkafin wani abu ya shiga tsakanin su" Cikeda lallashi Ammi takama hannunshi tace "listen Alhaji badanniba dan Allah na yarda idan Asad bayasonta yasaketa but ba da zafi zafi hakaba mutanen nan zasuzo su tafi da ita, adan bari all this heat yalafa tukunna, inhar yasaketa yanzu zasuzo sutafi da ita kano ne that is inma basu maidata kauyen da Mamanshi ke zama ba so please kabar komi ya lafa, dansuma am sure yasami Mamartashi da sauran yan uwanshi kan yama yarinyar aure wani sabon bala'i ne zai barke, amman kaga yanzu da auren nan Asad keda iko da ita kome zasuyi suyi bazasu iya taba tafiya da ita ba kaji" shiru Dad yayi yana kallon Ammi yakuma yarda da maganan ta dan yanzu suna tafiya da yarinyar he stand no chance so dole ya yanke decision din dat is in his interest, kallon Ammin yayi yace "naji bazan sashi yasaketa ba just for now sha sai komi yalafa, my poor boy uwarka tasaka a poor kona" dariya daga Ammi harshi sukayi suna shiga gidansu Ammi tace "he will come around", Dad yace "muje nafadima Turai da kaina nakira Dadda shima nafadamai kafin suji agari" dasauri Ammi tace "wlh amman mubari sai anjima idan ana dinner lokacin kowa na nan, yanzu zokatafi office" gyadamata kai yayi baima shiga cikin gidan ba yashiga mota direban shi yajashi sukatafi Ammi tawuce ciki ranta fess one thing is koma yayane bazata taba bari auren nan ya lalace ba saima tafara tunanin hanyoyin da she will make it work, abubuwan dazaisa danta yaso Du'a sosai.



Gidansu yashigo ranshi fess yaja motanshi yatafi office abinshi.

Saida Asad yafita Grandma taji karan bude gate da fitanshi sanan ta daddage ta dakama Du'a dakekan jikinta duka acinya tace "tashi dan gidanku kidubeni nan" tashi zaune tayi ahankali tana turobaki, Grandma tace "ba asama na barki ba da yaushe kika fita danaga kin shigo ta kofa" turo baki tayi tace "ta window" shiru Grandma tayi tana kallonta anyway bama ta tambayan nan takeba wanan ne most important one ahankali tace "Du'a yaushe kika fara son Asad" sosai take kallon Grandma lips dinta harrawa yake tanaso tafadi mata gaskiya but tana tuna uban kashaidin da Asad yamata, tashi tayi takai hannayenta kan fuskanta tace "ni kunya nakeji" tai stairs da sauri tanadan dingishi, tafi Grandma tayi tace "jama'a yau naga yarinya, agaban kowa tagama cewa tanason yaro, yanzu ni dana tasata agaba ina mata tambayan shine take cemin tanajin kunya ai shikenan" tai maganan tana murmushi wlh bazatai karyaba har cikin ranta taji dadi, tun ranan da Hamad yakawo Du'a data daura idanunta akanta aranta taji zataso tahada Asad da Du'a aure, sai gashi Allah yatayata kome zai faru yafaru she will make sure that this marriage work, kwalama Razika da Shemau kira tayi dasauri suka fito, cikeda fara'a Grandma tace "kuzo inaso na aikeku kasuwa direbana na kaiku ku sayomin sweet da goro, an daurama Du'a aure da Asad dan wajen Ammi yanzun nan mahaifinta a masallaci kutayani murna" gani kawai Grandma tayi sunhau tsalle, Razika tace "Ammi ni duk idan yazo gidan nan dama nakanji inama ace Du'a budurwanshi ne wlh naji dadi" dariya Grandma tayi tace "nima haka, ungo kudin nan kuga kuje ku sayomin narabama jama'an Annabi suci su shaida su sama auren jikata albarka insha Allah mutu karaba, wuce kutafi" karban kudin sukayi, Grandma tadau wayanta takira danta tasanar dashi sanan tashiga kiraye kiraye tana sanarda jama'a.



💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫


✍️ M SHAKUR

EPISODE 4️⃣5️⃣
Wuraren Magrib suka shigo gidan, motan Sharif ne agaba na Asad biyedashi, suna parking suka fito agurguje sukai alwala anan pampon tsakar gida sanan suka fita zuwa masallaci salla sukayi suna idarwa Sharif yaga sai musabaha akeyi da Asad ana cemai Allah ya sanya alheri Allah ya sanya albarka, tabe baki yayi yace wanan hala yasayama masallacin wani abune, gaba yayi dan yunwa yakeji, Asad din yabiyoshi daga baya, suka shiga gida Sharif yace "muje muci abinci please I am starving" hararan Sharif din yayi hakan Yasa Sharif yaja hannunshi yace "common d more kana gudunma Anty Turai d more tanamaka iskanci idan ta ganka muje jor" janshi falon yayi kowama zaune a dinning harda Dad ganinsu yasa Dad yace "daman ku muke jira let's eat" karasowa sukayi ahankali yace "evening everyone" sanan yaja kujera yazauna Anty Turai ta ballamai harara amman ko kallonta baiyiba, ahankali sukecin abincin jikake tsit babu mai magana ma Aneesa sai satan kallon Asad din take dataga yamata kyau, saida aka gamacin abincin sanan Dad yadau tissue yashare bakinshi yace "nobody should leave the table akwai abinda zan gayamuku listen up" duk gyara zama sukayi suna kallon Dad din banda Asad da yaciro wayanshi yana daddannawa, gyaran murya Dad yayi yace "I believe dukan ku nan kunsan Du'a, Du'a yarinya ce that has been through a whole lot.........nan yabasu labarin Du'a har zuwa dalilin zuwan ta Abuja everyone was shock barinma Sharif dayaga he's a bit closer to him and bata taba gayamai rayuwanta ba, sanan Dad yacigaba yace "yau mahaifinta da mahaifiyarta sunzo........ nan yabasu labarin komi harzuwa inda Du'a tace Asad takeso har aka daura aure har kawowa yanzu" yanda gaban Sharif ke fadi haka na Aneesa kefadi danasu Rahima dan sunsan yanda Sharif keson Du'a, haka kuma sunsan yanda Aneesa keson Asad dudda bata taba fadamusu da bakinta ba, kasa hakura Sharif yayi yajuya yakalli Asad dake daddanna waya abinshi kamanma baisan mesukeyi ba yace "kai kanason ta ne Asad" girgixa mai kai yayi yana tabe baki, cikin yanayin wulakancin nan da halin basarwa irin nashi yace "Ammi made me do it" dukansu juyawa sukayi suna kallon Ammi, dasauri Ammi tabude baki zatai magana Dad yace "yes Ammi ku tasa yay haka but I am in support of hakan datayi inba hakaba tafiya da ita zasuyi maybe ma amaidata kauye, so for now abar maganan aurensu ahaka harzuwa komi yay sanyi ya lafa, auren is not like irin eh aure aure is just to save the girl ass, dazaran komi yalafa Asad zai iya rubuta mata takarda and free the girl idan tasami miji ta auri duk wanda takeso" ahankali da Anty Turai ranta yake a mugun bace tadan saci kallon yarta dake gabda kuka amman daurewa kawai take jitayi ta harzuka sosai tace "maganan banza maganan wopi, wani irin banzan abu kukasa danku yayi eh? Ina ruwanku dawata Du'a ba dangin iya bare na Kaka haduwan Abuja, yar uwanmu ce ko danginmu ne dazakusa yaro ya aureta just to save her, ba kauyeba ko wuta sukakai yarinyar me ruwan mu ba yarsu bace inma sun kasheta ai su suka haifi kayansu, ni dama tun ranan dana fara ganin yarinyar naji bana sonta, nidai wlh inhar da raina banyi accepting auren nan ba so I as much am concern Asad is still very single in my eyes kuma zamu nemamai mata......" tsareta Dad yayi yace "to menene abin tada jijiyoyin wuya anan Turai eh? Kedai wlh baki raina abin fada, shi yaron kinga yanaso ne"? Cikin fushi tace "wani irin tambaya Yaya kakemin haka? Asad fa namiji ne eh? Inhar yarinya nada nono da duwawu mezai hana kar Asad yasota nan gaba? Anfa riga an daura aure yarinya tazama tashi halak malak, namiji anbashi mumnunan yarinya dabayaso amatsayin mata yadurama yarinya ciki balle kuma anbama Asad mai kama da mayun nan dako yan uwan ta tsoronta suke, ai wlh Asad ya shiga kenan, ni wlh ku masifan batamin rai and nagayamuku I will never ever accept that girl, Yaya sabida rashin mutunci da rashin ganin amfani na ma ace ina gidan nan fa babu inda naje, ni kadaice kanwarka yar uwarka aduniyan nan amman kuje kuyi abu dagakai sai munafukar matarka baku sanar dani ba san......" Tashi Sharif yayi fuuuu yawuce yafita, Turai tabishi da kallo, ahankali Asad dake daddanna wayanshi yatashi yabishi yafice shima, tashi Aneesa tai dagudu tai sama su Rahima da Mariya suka bita sama itakuma Anty Turai tashiga surfafama Dad da Ammi bala'in ta inda take shiga batanan take fitaba Abba yay shiru kaman ruwa yacinyeshi dan he's even confused, ba'a taba trusting namiji da mace shi karan kanshi bazai iya kirga mata munana da bayasonsu yan office dinsu dayaci ba, baya sonsu ko kadan amman saida yacisu balle kuma mai kyau, what if Asad sleep with this girl, what if yama yarinyar nan ciki ga yarinyar da shegen kyau ya zaiyi kenan?.....



Fadawa kan gado Aneesa tayi tafashe dawani irin mugun kuka, shigowa su Rahima sukayi suna maida kofan suka rufe, ahankali Rahima takaraso gaban gadon ta zauna tana shafa kan Aneesah tashi tayi dagudu ta rungume Rahima sosai tana wani irin kuka, ahankali Rahima tace "kiyakuri Aneesah ba" dasauri Mariya tace "kiyakuri Aneesah ni banmaga abin kuka ba kema ai kinsan Asad bayasonta kumama ai temporary aure ne" wani irin hararanta Rahima tayi tace "angayamiji akwai wani abu waishi temporary aure ne aduniyan nan, ni wlh Sharif ma yafi bani tausayi, ita Aneesah babu wanda yasan kina naki ai komu baki fadamana ba, shiko Sharif ya nunama kowa yanason Du'a, kwata kwata Ammi batai planning abin da kyau ba but nasan harda sabida Asad ne agida Sharif bayanan da am sure Ammi Sharif zatasa ya aureta dan yafi kirki dan Ya Asad dakeda bakin halin nan ai gana mata azaba zaiyi" dagakai Aneesah tayi cikin kuka sosai tace "da yardan Allah sai Ya Asad yagana mata azaban da saitai dana sanin cewa tana sonshi, wlh wlh Du'a mayaudariya ce kuma makira ce algunguma maicin amanan friendship, ita kadai nafadama inason Ya Asad" dasauri su Rahima har suna hada baki sukace "dagaske" gyadamusu kai tayi tace "ana gobe birthday dina ranan Thursday wlh saida na gayamata har tana cemin tona gayamishi ai gashi ita tagayamai, wlh Du'a makirace Allah ya isa tsakanina da ita wlh bazan taba yafemata ba duniya walahira wlh wlh ko" tsabagen bakin ciki tama kasa magana sai kuka, ta bala'in bama su Rahima tausayi.




Ahankali yatura kofa yashiga dakinsu tsaye yaga Sharif yakafa goran ruwan sanyi abaki yanasha kaman wanda yaje yaki, dan tabe baki yayi yawuce stairs abinshi, binshida kallo Sharif yayi kawai yacire goran ruwan daga bakinshi ya jefar ruwan yazuba atsakar dakinsu wani irin kifa kanshi yayi a fridge din yana kokarin daidaita heartbeat dinshi yace "Ammi why? Why? Eh" ahankali yazauna a kasan bango yakifa kanshi yana magana shi kadai ahankali. "nasan ni kika fara nema rashin ganina yasa kikai reaching out to Asad for the help, Ammi maisa baki kirani awaya ba? Don't u know that Asad is bad choice ma Du'a haaa? He will maltreat the poor gurl and make her suffer, Asad baya sonta" wani hawaye mai zafi ne suka zubomai dasauri yashare ahankali yace "but Dad yace ita dakanta tace tanason Asad, Du'a how could u love Asad mutumin da all abinda zaiyi shine ya wulakanta ki and make u cry all the time" ajiyan zuciya yasauke yace "I've been so good to you starting from the first day dana fara ganinki aduniya, ta dalilina kike araye yau, I forced Asad to save u a rijiya, I've been very generous good and romantic towards u but all this baki ganiba kikaje kinason wanda bai damu dakeba daidai da zarra daya, maisa mata sunfison mazan that makes them cry always mazan dake wahalar dasu eh"? Wani irin fashewa da kuka yayi mara sauti awajen yana taushe bakinshi he is deeply hurt, like deeply, part din da Du'a ne tai proposing komi shiyafi cimai zuciya, ko kadan baya ganin laifin Asad dan yasan tursasashi akayi.

Asanyaye Asad yamaida kofan dakinshi yarufe tareda jingina da kofan yana lumshe ido dan he could hear sautin kukan Sharif dan dakin komi akashe yake ba'a kunna AC ko TV so so zakaji sound na komi very well, ahankali yazauna akasa gaban kofan still idanunshi a lumshe, he really care about his brother yanason Sharif sosai he hates seeing him hurt, ahankali yace "I am so sorry Sharif, I am sorry".




💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫



✍️M SHAKUR

EPISODE 4️⃣6️⃣
Wani irin lafiyayyen bacci tayi da kyar ta tashi shima sabida Grandma data tadata ne tawuce tafice ahankali ta tashi zaune da kyar tana hamma, sanan tasauko da kafafunta tamike tsaye daga gado jin tsamin da kafafun nata sukayi jiya duksun bace yasa taji wani dadi tawuce ta tafi bayi, brush tashigayi saikuma tadago kanta ahankali ta kalli kanta ta cikin madubi tace "ke matan aure ne yanzu fa Du'a" wani irin kawarda maganan tayida sauri dan daga ita sai Asad sukasan komi tasan wanan ba aure bane besides ma ita ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login