Showing 60001 words to 63000 words out of 153675 words

Chapter 21 - Kyawuna Jarabta Ta Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

15 Dec 2024

619

tayi shigan dayayi yamata kyau saiyay kaman wani dan gayu, juyowa yayi dawani irin sauri tadauke kanta kirjinta na dukan uku uku, daukan mug din yayi yazo cikin falon kujeran dake facing nata yazauna akai tareda mika hannu yadauki remote yakunna TV yasaka a tashan ball sanan yayi sanan ya ijiye remote din yay crossing legs dinshi yakai mug din bakinshi yayi sipping coffee ahankali yana kallon TV.


Kasa cigaba da abinda takeyi tayi, gabaki daya jitayi she's so uncomfortable, sai gyara nan da nan da nan take na kayan jikinta, daidai nan Aneesah tasauko kasa ganin Ya Asad yasa ta ware idanunta tace "laaaa Ya Asad daman bakaje office ba" ko kallonta baiyiba haka yasa tawuce kusada Du'a zata zauna yace "make me some omelet ki kawomin part dina" dasauri takalleshi cikin wani irin jin dadi jin yakulata tace "tom Ya Asad" sanan tawuce kitchen, tashi shima yayi rikeda mug din yawuce yafita daga falon, wani irin ijiyan zuciya tasauke tacigaba da aikin har lokacin takasa dainajin kamshin dayakeyi.


Kusan 10min Aneesa tadauka a kitchen tana hadamai lafiyayyen Omelet sanan tafito rikeda hadadden tray data daura plate din Omelet din akai, daidai lokacin aka bude kofan falo wata hadaddiyan faran mata tashigo tana sanyeda Abaya tanama Aneesa murmushi, wani irin tsalle da ihu Aneesa keso tayi tunawa da abincin waye ke hannunta yasa ta ijiye kan hannun kujera dasauri sanan tawani kwasa da gudu tafada jikin matan saikuma kuka. "Oyoyooo Mum, bakincemin gobe zakizo ba" kankameta matan tayi tace "I wanted to suprise my birthday girl" tai maganan tana kallon Du'a dake kallonsu tana murmushi dan taga kamanninsu da matan hakan yasa tagane itace Maman Aneesa, sakin Maman nata tayi tajuyo takalli Du'a tace "Mum kinga best friend dina sunanta Du'a" wani irin kallo Turai tabi Du'a dashi, ahankali Du'a tace "ina yini" lafiya ta amsa sanan takama hannun Aneesa tace "muje sama" juyowa Aneesa tayi takalli Du'a tace "Du'a please tayani kaima Ya Asad Omelet dinshi yanzu karyamin fata, kina fita flat dinsu ne a gefen namu kinji please, baiyi breakfast ba" gyadamata kai Du'a tayi ahankali tana kallon yanda sukebinstairs Mum dinta namata magana, harsunkai karshen stairs Aneesa takara juyowa tace "Du'a hurry karya huce bazaici ba" tashi tayi jikinta har bar bar yake tadauki tray data ijiye kan kujera sanan tawuce tafita hakan yasa Aneesa sukai ciki, flat din datagani kusada nasu tayi, ahankali ta tsaya gaban kofan tama rasa mezatayi she's so nervous hakanan, door bell datagani ta danna ahankali, daga taciki taji ance come in.




💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫


✍️ M SHAKUR

EPISODE 3️⃣7️⃣
Takai kusan 1min tsaye takasa tura kofan tashiga dakin kuma ba'a kara cewa komiba daga ciki ba, kaman ta ijiye abincin anan gaban dakin takeji amman kuma bai daceba dan Aneesa bamata rufe plate na Omelet dinba, daurewa tayi ta mugun daure sanan ta tura kofan ahankali tasakanta ciki, wani irin sanyi da kamshi ne yamata sallama danya Kure AC dakin yana zaune kan kujera ga mug din coffee dinshi agefe saikuma MacBook kan jikinshi yana danne danne, ganin ko dago kanshi baiyiba balle ya kalli kofan yasa tashigo cikin dakin gabaki daya tamaida kofan tarufe takaraso ciki kafanta na harhardewa kaman zata fadi gawani kalan kunya datakeji sabida yanda babu dogon riga ko hijab ajikinta, dan karamin table din dake gabanshi da mug din tea kekai ta kalla dan dagakai tayi takalleshi batare data kara so wajen ba, lips dinta tadan lasa jin yawani irin bushe kafin ahankali cikin yar muryan nan nata tace "unnnn, Aneesa tace nakawo maka unnn....wanan" tadaga tray tana nunamai kaman yana kallonta, dan table din gabanshi yanuna mata batare daya kalleta ba yana aiki akan system dinshi, dan ajiyan zuciya tasauke sanan tashiga takawo ahankali takaraso gabanshi ahankali tadaura tray akan table din ta tashi dasauri zata wuce batare daya kalleta ba kawai yasamata kafa jikake tipppp tai wani irin mugun faduwa danma Allah yataimaketa akan rug ne inda a tiles ne da halan saita karye amman dudda haka ta bugu barinma kirjinta dan akife tafadi, wani irin malalacin kara tasaki na wahala. "wayyooo Allah na Mamiii na mutu" sai kuka ahankali tasakeshi tana kokarin tashi, ahankali yadauke system dinshi daga kan jikinshi ya ijiye agefe sanan yajuyo da kanshi ya kalleta daidai ta tashi zaune da kyar tana goge hawayen kan fuskanta hulan kanta shima yacire yay chan gaba, hada ido sukayi wani mugun kallo yamata yace "that's for not greeting me, duk randa kika kara ganina kina bina da wayanan idanun naki batare dakin gashiniba saina miki wanda yafi wanan" gyadamai kai tayi ahankali tana goge hawayen dasuka kasa daina zubomata, da kyar saida ta dafa kujera sanan ta iya samu ta mike tsaye hakan yasa kalban kanta suka wani zubo har waist dinta, hawaye tasake sharewa sanan ta tsugunna tadauki hulanta sakawa tayi tagoge fuskanta tass sanan tawuce tai kofa harta bude kaman daga sama taji yace "feel free kigayama Ammi ko Hajiya, zakiga abinda zan miki stupid girl" dasauri tafita daga dakin tamaida kofan tarufe, anan bakin kofansu ta tsugunna saida tasha kuka sanan ta share fuskanta tass tarasa maisa ya tsaneta haka, all she ever did was trying to tell him thank you kan abinda yamata, saida tagama tass sanan ta tashi ahankali tasauko tana tafiya akasa, hango pampon wajen flowers din gidan datayi yasa taje wajen, ahankali ta tsugunna tabude pampon ta tara ruwa ahannunta tana wanke fuskanta sanan tazare hulanta tasa akan kafanta ta tattare gashinta ta tufke dan batason sakin gashi sanan tamaida hulan tamike tsaye tajuyo, hada ido sukayi dashi yafito yana tsaye gaban dakinsu rikeda waya a kunne yanayi dawani irin sauri tadauke kanta kaman tada dodo sanan tawuce main flat.


Bude kofa tayi ahankali da sallama tashiga Aneesa tagani tana saukowa tace "yauwa Du'a thank u, kinsan Mum dina akwai masifa, tafi kowa masifa aduka family mu saisa kowa tsoronta yake dan bata wasada yara, inda ban bita ciki ba dana shiga uku da masifanta" tai maganan tana karasowa gaban Du'a ganin idanunta yasa tace "maiya sameki kuka kikayi?" girgizama takai tayida sauri tace "a'a wanke fuska nayi a tap din danagani awajen flowers idanuna sunyi jane" hannunta Aneesa takama tace "eh sunyi ja maybe kinsa ruwa acikin idanun ne zomuje mucigaba da aiki" zama duk sukayi suka cigaba da aikin dasukeyi saikuma chan tadago kanta tace "akwai abinda ke damuna Du'a bantaba gayama kowaba harsu Rahima, dudda nasan bakida any saurayi but I want to tell you sabida nauyin abin azuciyata yaragu the burden is too much for me" yanda tai maganan kadai yasa Du'a ta lura dakoma menene abin na mugun damunta, hakan yasa takama hannunta tarike kaman yanda taga Grandma namata idan tana kuka tace "menene Aneesah" kallon Du'a din tayi for some secs sanan murya chan kasa kaman mai whispering tace "is Ya Asad, wanan dayasani nasoyamai kwai dinan, Mai kamfanin dakike ma zane" gyadamata kai Du'a tayi tace "yacika mugunta ko" dariya sosai Aneesa tayi tace "mugunta ai tambarin Ya Asad ne kowa yasani but wlh yamafi Ya Sharif kirki Allah kuwan" gyadamata kai kawai Du'a tayi batare datace komiba, ajiyan zuciya Aneesa tasauke tace "Du'a wlh ina bala'in sonshi, mahaukacin so nakemai sosai, kinga cousin dina ne, Mum dina dinan dakika gani tazo kanwar Baban shine, ni bantabason wani namiji kaman yanda nakeson shi ba amman kallo ma ban isheshi ba wlh, bansan Yaya zanyi ba, I don't know, ai kinga irin giran damuke yi a group nasha nasa kayan bacci nasa shimi harda towel ma naje wajenshi tambayan wani abu amman ko kallo ban isheshi ba baima nuna yana ganina ba balle inma sa rai, nakasa kula kowa, shikuma baimasan ina existing ba, Yaya zanyi eh Du'a, please ki gayamin mezanyi" dan zaro ido Du'a tayi tana kallonta ita bama tasan mezata mataba, duka yan kalaman bakinta dasuka rage tatattaro tace "kigaya mishi to" zaro idanu Aneesa tayi tace "ke Du'a sokike ya kasheni, wlh ko kare ya cijen bazan iyaba, ko zaki tayani fadamai" dawani irin gudu Du'a tasaki hannunta takoma baya, dariya Aneesah tayi tace "ke dalla chan I was just joking nasan bazaki iyaba but I will need ur help, inama wayanki" tajuya dasauri tana neman wayan Du'a, daukan wayan tayi dagakan saman kujera tabude dayake ba key tana danne danne, matsowa kusada ita Du'a tayi tace "me kikeyi dawanaya" bata amsa Du'a ba saida tagama danne dannenta sanan tadago kanta tana murmushi tace "done" dasauri Du'a tace "me kikayi" wani irin murmushi tayi tace "text naturamai" faduwa gabanta yashigayi tace "text kuma Aneesah dawayana" "eh aini yanada number na kekuma baidashi, yanzu dai kowani kalan reply kikagani kituromin banson kiga text din danamai dannai deleting kina ganin reply kituromin" kaman zatai kuka Du'a tace "kinga karki sani a matsala wlh ni tsoron shi nakeji" dariya Aneesa tayi tace "dalla babu abinda zai miki keda bamakisan maina turamai ba, now let's continue munkusan gamawa ma" cigaba da hada kayan sukayi saida suka gama tatas sanan suka shiga jera kayan a store na kasa, suna gamawa tace "zantafi kawomin hijabina" Ammi dake saukowa ne daga sama tace "ai baki isaba keda komawa sai dare" akunyace ta sunnar da kanta, Ammi takaraso tace "oya kuzo kutayani aiki a kitchen" dariya Aneesa tayi tace "yauwa Ammi daman banso ta tafi" Ammi tace nima haka, sosai Ammi tashiga ko yamusu girki barinma Du'a datafi maida attention akanta, itadai Turai ko fuska batasakin ma Du'a din ballame tamata magana, da kyar Du'a tasamu da magrib Ammi ta barta ta tafi danda su Rahima duk hada baki sukayi sukace saita kwana dan gobe tun safe zasu fara prep, tafiya tayi bayan tamusu alkawari da sassafe zatazo.



💫KYAWUNA JARABTA TA 💫


✍️ M SHAKUR

EPISODE 3️⃣8️⃣
Ko breakfast din kirki Aneesah batayiba ta tashi daga dinning, Dad yace "ina zaki" murmushi tayi tace "zanje nakira Du'a ne Dad mufara prep we have alot of work ko Ya Rahima" gyadamata kai Rahima tayi, Turai dake zaune itama tana breakfast tace "nifa banson tarin kawayen nan naki Aneesa and u know that" dasauri Sharif dayake shirye yaariga yasa kayan zuwa office ash color suit yace "Mum jikan Hajiya ce fa yarinyar batada matsala ga hankali" kallon Turai Ammi tayi da murmushi kan fuskanta tace "karkiji wani abu Anty Turai all friends dinsu nasansu so ba matsala" yatsine fuska tayi tace "shikenan" dasauri tace "intafi" kallonta Dad yayi yace "tunda Ammin ku ta aminta da ita yes go and call ur friend" wani irin tsalle tayi tawuce tafita, juyoda fuska Turai tayi takalli Ammi tace "yanzu sabida danki baida tarbiya tun jiya nazo gidan nan amman baisan dayazo yagaidani ba, kowa yazo yagaisheni banda shi" kafin Ammi tai magana Dad yace "kinga karki takurama Asad yaron nan is very busy u know that, probably aiki yake saisa baki ganshi but I am sure zaizo yaduba ki ni kaina tun jiya banganshi ba" kwafa tayi bata kara cewa komiba, tashi Sharif yayi yana goge bakinshi da tissue yace "natafi" murmushi Ammi tamai tace "adawo lpy Allah yabada sa'a Son" Ameen yace yawuce yafita yay hanyar kofa, bude kofa yayi yafita yana tafiya zuwa wajen parking space aka bude gate din, Aneesah ce tashigo tareda Du'a dake sanye dawani black dogon hijabi mai hula da kan hijabin yadan mata yawa hakan ya bayyana gashinta dayake looking so black and silky, ganinsu yasa ya tsaya a wajen tareda folding hannunshi a kirji yana kallon Du'a, dan murmushi tayi ganinshi tadauke kai zata wuce yace "wlh kizo nan inba hakaba nida ke ne" juyowa tayi takalleshi saikuma ta makemai kafada alamun bazata zoba, dawani irin sauri yazo wajen gabanta yasha tareda kama waist dinshi yakalli Aneesa dake kallonshi tana murmushi yadaure fuska yace "Ke wuce daganan" makemai kafada tayi tace "Ya Sharif bafa wajenka tazo ba wajena tazo" hararanta yayi yajuya yakalli Du'a, ahankali tace "good morning" murya chan kasa yace "yaushe zaki dawo office" dan kallonshi tayi saikuma ta turo baki tace "Grandma tace ranan Monday" yana kallonta still ko kyafta idanu bayayi yace "kin bude bank din" gyadamai kai tayi tace "jiya Grandma ta kaini wani wuri akamin national I'd card aka bani awurin shine mukaje bank tasa aka budemin account" dan ajiyan zuciya yasauke yace "good" da juyawa yayi ganin still Aneesah na wajen tana kallonsu yasa yace "lemme go to the office don't let this girl stress u kinji" gyadamai kai tayi ahankali batare data kalleshi ba dan batason kallon dayake mata this days, ahankali yana kallonta still yace "bazaki min bye ba" kallonshi tayi saikuma tadaga hannunta tamai waving alamun bye, juyawa yayi yawuce wajen mota sanan itama tacigaba da tafiya tareda Aneesah, hada ido tayida Asad daya fito daga flat dinshi sanye da singlet da 3quater yanadan lankwasa wuya alamun yagaji, dasauri Aneesa tace "good morning Ya Asad" gyadamata kai yayi yana saukowa daga staircase din gaban dakinsu, ahankali tabude kofan falonsu dasauri Turai ne kawai zaune afalon dan kowa yatafi sama shiryawa, murya chan kasa Du'a tace "ina kwana" batare data kalleta ba tace "lpy" murmushi Aneesah tayi takama hannun Du'a tace "muje dakinmu" taja hannunta ganin yanda fuskanta ba Rahama dakinsu tabude mata suka shiga su Rahima na arranging kayayyakin dazai amfani dasu anjima.



Saukowa Dad yayi kasa yana sanyeda manyan kaya Ammi biyeda shi, kanwar tashi yakalla yace "bari naje office Turai, yau inada meeting daban daban saikun ganni" murmushi tamai tace "a dawo lpy" juyawa yayi yakalli Ammi dake biyedashi murmushi yamata yace "bye sweetheart" ahankali tace "Allah yabada sa'a" gyadamata kai yayi yawuce yafita daga falon, instead of yay wajen motanshi wani gini dayake gefe daban agidan ginin nada fadi sosai, bude kofan yayi ahankali yanajin karan sauti dake tashi, babban gym ne sosai wajen ga all kinds of machines awajen, Asad dake gudu a treadmill ne yana zufa sosai yajuyo jin anbude fuska, ganin Babanshi ne yasa yadauke kai yacigaba da abinda yake, ahankali Dad yamaida kofan yarufe sanan yashigo ciki home theater dake bada duma ya kashe dakin yay tait sai karan machine din da Asad ke gudu a kaine kadai yarage, karasowa yayi yatsaya gefen Asad din yana kallonshi ahankali yace "Morning Son" dan kallonshi Asad yayi yadauke kai ahankali yace "good morning Dad" cikin wani kalan yanayi na damuwa Dad yace "Asad wai ya kakeso nayi da raina ne eh? Nayi nadaman komi, I've asked Ammin ka for forgiveness ko ita ta yafemin, ina gida bana fita inba fitan office ba but still kana ignoring dina bamaka shigowa side dinmu, haba Asad eh, me kakeso" hannunshi yasa ya kashe machine din sanan yakalli mahaifin nashi yace "I was busy working indoors saisa banshigo side dinku ba bawai sabida kai ba" wani irin murmushi Dad yayi cikedajin dadin respond dinshi yace "to maisa bakazo ka gaida Turai ba" yatsine fuska yayi yace "Dad I don't like her tacika fada da surutu" yay maganan yana wani batarai, dan dariya Dad yayi saikuma yanamamakin sarauta da iskanci iri na danshi cikeda lallashi yace "kowa yasan Turai sai ahankali, but baidace ba yanda bakaje ka gaidata ba tun jiya kana gidan nan kuma, kagama kai wanka saika shiga ka gaidata kaji" yatsine fuska yayi, zai kunna machine din yacigaba Dad yace "wait" kallon Dad din yayi da sauri, dasauri Dad dake kallonshi yace "duko kaga kasan kafini tsowo akwai abu akanka ne zancire maka" ahankali yadan duko batare dayay tunanin komiba, peck Dad yasakinmai agoshi ahankali yace "I love u alot Asad, bari naje" yajuya binshi da kallo Asad yayi saikuma yay dan murmushi yakunna machine din yacigaba da exercise dinshi.


Wuraren Eleven suka gama arranging duka kayan, Rahima takalli Du'a tace "Du'a tashi kifara wanka mu bari mukai kayan kasa sai muje wasu dakuna muyi wanka sabida muje shagon hudayya mu amso kayanmu" gyadamusu kai tayi tace "kayana na gida" hararanta Mariya tayi duk suka tsaya suna kallonta Aneesah tace "mu bamuda kayane halan jekiyi wankan karmuyi latti" gyadamusu kai tayi sukuma suka kwashi kayan suka fice itakuma tawuce tashiga bayinsu.

Sauka kasa sukayi suna ijiye kayayyakin a guest room inda nan aka jera all kayan amfani birthday din aciki, fitowa sukayi zasu koma sama daidai lokacin aka bude kofa aka shigo, Asad ne yana sanye da wani 3quater na sojoji green da white riga, sai uban kamshi yake zubawa kana ganinshi kasan yay wanka, ganinshi yasa duk suka gaidashi. "Ya Asad good morning" "morning" ya amsa su atakaice yana shigowa cikin falon, sanan ya kallesu yace "the 3 of you should go to my flat and clean everthing now, kuyi mopping" gyadamai kai sukayi dasauri babu gardama duk suka wuce dudda sunada abinyi, ahankali yahau stairs din yana tafiya ahankali yashigo falon sama yanason yaje yagaida Ammi yabata hakuri finally su shirya dan yagaji da yanda ta share shi ko nemanshi batayi, muryan Turai yaji tana magana awaya zata bude kofan dakin datake ciki tafito hakan yasa yatura kofan dakinsu Rahima yashiga da sauri daidai tana bude nata kofan tana fitowa yana rufe kofan batare daya bari yay making any sound ba, dawani irin sauri takira sunanshi tace "Asad" dakin yashigo dasauri yana kalle kalle ya tsani matar nan baimason hanya tahadashi da ita ko kadan, ganin wardrobe dinsu yasa yawani irin bude yashiga dasauri ya labe ciki dan yasan dole tashigo tanemai daidai lokacin Du'a tabude kofan bathroom tafito daure da pink towel din datagani abayin akirji tana kalle kalle to wani kaya zata saka yanzu, gaban wardrobe dinsu tayi ta tsaya sanan takai hannunta ta bude wardrobe din ido da ido sukayi da Asad daya ware idanunshi dan yazaci Turai ce, daidai lokacin yaji muryan Turai tana kokarin murza handle din kofa tace "ba takadirin yaron nan nagani yanzun nan yashigo dakin nan ba" hannu yasa yawani irin fizgo Du'a tashigo cikin wardrobe din zuwa jikinshi sanan yasa hannu yajanyo kofan wardrobe din yarufesu daidai Turai ta shigo dakin, wani irin matse Du'a yayi ajikinshi yana daura yatsunshi akan bakinshi murya chan ciki yace mata shiiii alamun kartai ihu ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login