Showing 117001 words to 120000 words out of 153675 words
ke mata batare datai magana har lokacin ba, dan murmushi tayi cikeda hikima tace "kidena kuka everywoman must go through this phase, saisa ai nasa Mamin ki tazo dan nasan u will need her now stop crying" makema Grandma kafada tayi kaman tana gabanta cikin kuka sosai da muryanta dabaya fita sosai tace "ni wlh kizo ki daukeni Grandma gidanki zan dawo baran kara kwana anan ba wlh mutuwa zanyi, Grandma please kizo kitafi dani wlh Ya Asad mugune Grandma" baki Grandma ta rufe tana murmushi sosai ranta fess ko banza su Mom da Grandma zasuga Du'a natsassiyar yarinya ce, kuma yanzu tariga tafi karfinsu nagaba yay gaba nakasa sai tsintan hula, Allah yama Asad albarka, anatse Grandma tace "listen to me Du'a dena kukan" rage kukan tayi Grandma tace "Asad bai miki mugunta ba it's a normal thing da ma'aurata keyi, shi ake kira da auren shine auren, Asad nada iko akanki yanzu sama da ni da mahaifanki, duk randa ya nemiki a shimfida bakijeba mala'iku zasuyita tsinemiki ne, and whatever Asad did is a sign cewa mijinki na sonki Du'a and akwai lot of affection, tausayi and so tsakaninku, nariga nabama Maminki magani tabaki, ballema keda jikinki keda saurin warkewada ciwo, nan da gobe kinji sauki garau kaman ba'a yiba, and komene yafaru tsakaninki da mijinki is between u and him, kizama mai dauriyan kinji koyaya mijinki yake kizama mai dauriya kinji" gyadamata kai tayi kaman tana gabanta ()Grandma tace "good Girl, Tom stop crying kwanta kiyi bacci abinki"
6️⃣8️⃣
Katse wayan Grandma tayi ahankali ta ijiye wayan tana share kwallanta, Mami tadade agaban dakin idanunta sunyi jajir she really made a mistake arayuwanta yau yarta ne abu kedamu gata kusada ita amman takasa mata magana saidai takira kakarta awaya, hawayen daya zubomata ta share dagudu tagoge fuskanta tass sanan ahankali ta tura kofan tashiga dakin, abincin ta kalla tace "oya tashi nacigaba da baki abincin" girgixa ma Mami kai tayi tace "Mami nakoshi naci dayawa amai zanyi" zama ahankali Mami tayi kusada ita sanan ahankali ta kwanto da ita tadaurata kan cinyanta, ajiyan ahankali Du'a tasauke tai lamo da kanta ajikin Mami, Mami na shafa mata kanta tana kallon fuskanta ahaka bacci yay awon gabada ita mai nauyin gaske tana sauke ijiyan zuciya ahankali, harga Allah tanason yarta sama dakomi na duniya kawai Du'a y'ace wacce tunda ta haifeta tadinga shiga matsala kala kala tundaga kan yan uwan mijinta zuwa mutanen datasani kawayenta da sauransu ana mata kallo kaman maza takebi, bawai ta tsani yarta bane but matsaaloli da wahalan data fuskanta kan Du'a kawai yasa ta tattare yarinyar ta ijiye agefe dan kawai tasami peace na mind not knowing that was the biggest mistake na rayuwanta badadan Grandma ba da halan yanzu Du'a tamutu da depression, hawayen datake rikewa ne yaduga akan fuskan Du'a din dasauri tasa hannu tashare hawayen cikin wani kalan muryan kuka tace "I'm sorry baby, I am so sorry for all I've done to you, Du'a u are very special, you are gifted, dudda baki makaranta ba but you've archived so much in this life da wayanda ma sukeje makaranta basu samu na, and I love u so much kinji" hawayen kan fuskanta ta share ahankali tana shafa fuskanta har lokacin, wayan Asad dayay kara yasa Mami takalli wayan, dudda taga sunan bata daukaba dan tasan shine, tana kallon wayan ya katse yasake kiranta akaro nabiyu amman bata daukaba, akaro na uku ne Mami ta kwantar da ita ahankali kan gadon sanan tadauki wayan dake ringing tafito tasauko falo takwalama Aneela kira dake dinning sunacin abinci, dasauri tazo, wayan Mami tabata tace "dauka kice Ya Du'a na bacci" dasauri duk su Mom da Kaka dake falon sunacin abincin rama da aka kawo suka kalleta, daukan wayan Aneela tayi tace "Hello Ya Du'a is sleeping" saikuma tai shiru kaman magana ake mata sanan ta katse wayan takalli Mami tace "Mami Uncle say I should come with someone to come and carry something for Ya Du'a" kafin ma Mami tai magana Hawwa ta tashi dasauri tace "muje Aneela" suka wuce suka fita, Kaka ta kalli Mami tace "mijin ne yasake kira? dayake yasan yay aika aika meyace"? Ahankali Mami tace "yace yana waje wai Aneela tazo dawani Babba" tabe baki Kaka tayi tace "yaji dashi daga baya kenan bayan yabar mana aikin bannar dayayi".
Dagudu Aneela ke zuwa wajen Asad dake wajen parking motocin gidan akarkashin tent yafito ya jingina da mota yay folding hannunshi akirji idanunshi sanye da glass yay wani irin bala'in kyau irin na angwayen nan Hawwa takasa daina kallonshi, karasawa sukai wajen Aneela takama hannunshi tana murmushi tace "Uncle gani" ahankali Hawwa tace "ina yini" dan gyadamata kai yayi kaman ansashi dole, jitayi guiwanta yay sanyi, yana rikeda hannun Aneela yabude bayan motan wani katoton jaka dake cike da manya manyan robobin ice cream na coldstone different flavor yaciro batare daya kalli Hawwa ba yamika mata ahankali takarba hannunta narawa dan wani irin kwarjini da cika idanu Asad kedashi, sanan yasa hannu yasake ciro wasu manya manyan paper bags guda biyu yamika mata, saikuma yaciro wani karamin jaka yabama Aneela itama tarike sanan yamaida kofan motan yarufe yadan kalli Hawwan, yatsine fuska yayi kaman ansashi dole yay magana da ita yace "it's for wife, kibata" gyadamai kai Hawwa tayi tana kallonshi kaman zata hadiyeshi yajuya yashiga mota yatada Aneela takalli Hawwa tace "Ya Hawwa muje" juyawa tayi tabi Aneela suka tafi tana kara yaba ajin Ya Asad da gayun shi, jibi yanda yake wani ciccinkunu yana daure fuska kaman bashine yay aika aika ba, lallai Du'a is just a lucky girl data sami miji irinshi inama itace.
Suna shiga falo kafin kowa yay magana Kaka tace "wanan uban kayanfa" kafinma Hawwa tai magana Aneela tace "Uncle yace mukaima Ya Du'a" wani irin murmushi Kaka tayi uwar kwadayi tace "oh ni Asma'u yau naga yaro dan duniya, baimajin kunyan mu shine yasayoma matar tashi kayan dadi yakawo mata agaban mu, ai shikenan kawosu nan kiga" kai komi gabanta yaran sukayi sanan takalli Mami tace "zo ki diban ma Du'a nata dan wanan hardamu ya siyo ta ina zata cinye abubuwan nan, kawo mata plate Hawwa" dasauri Hawwa tawuce kitchen. Kaka tashiga bude sauran paper bags wani lafiyayyen yankakken gasasshen ragone mai bala'in kamshi daya cika dakin, ji Kaka tayi yawun bakinta ya katse batasan sanda tace "Allahhu Akbar bantaba sanin haka yarinyar nan keda kashin arziki ba, deba kiga Kikai mata mu cinye sauran" karban dauko plate din da Hawwa takawo tayi sanan tadebama Du'a tadauki ice-cream guda biyu su tasamata a fridge naman ma a warmer tasa takaimata dakin.
Grandma kuma ta kakkasa naman tabama kowa ice cream Mom tabama nata tace "ga naki" batare da Mum takalleta ba tace "banci" Nana tabamawa tace jeki samin a fridge Du'a takara da nata idan ta tashi, naman dazata bawa Mom tajuye akan nata< batare datama nawa Mom dinba tashiga ci, su Hawwa ma ci suke abinsu sunashan ice cream wa
6️⃣9️⃣
Komawa gida yayi parking motanshi yayi sanan yafito yashiga flat dinsu, ahankali ya kwanta kan kujera kana ganinshi kaga wanda ke cikin damuwa, wayan Ammi dake aljihun gaban riganshi yaciro yana jujjuyawa a hannu yana kallo, tafiyan dayaji yasa ahankali yadago kanshi Sharif ne yasa manyan kaya yana kallonshi yana murmushi yana saukowa yace "ango kaga wani kyan daka karayi" daure fuska yayi yaharareshi yace "ina zaka all dressed up like this" "glass Sharif yasa yace " zanje wajen friends dinmu namusu godiya ne, kasan daman ninai inviting nasu all" gyadamai kai kawai yayi Sharif yafice abinshi,
Gajiya yayi dazama yasake tashi he's just so restless fitowa yayi daga flat din yayi nasu, bude kofa yayi ganin babu baki yasa yaji dadi sosai ciki yashiga, Ammi yagani tafito daga kitchen rikeda wasu kuloli ganin Asad yasa tay wani kalan murmushi ijiye kulolin tayi tazo inda yake tace "Son ya kagama da wayan nawa ne" girgixa mata kai yayi yace "no, Ammi naje dakinki na kwanta" kafin ma Ammi tabashi amsa Anty Turai data fito daga kitchen din itama rikeda wasu kuloli tace "jeka kwanta Asad uban amarci dakasha jiya da daddare dayar mutane ba dole kanemi wajen bacci ba" wani irin kallon Anty Turai yayi, hararanshi tayi ta ijiye kulolin tace "dukana zakayi? Allah yaso Aneesah y'ata tahakura dakai da yanzu ita kakusan kashewa" taidan dariya sanan ahankali tace "like father like so....." Turai! Ammi takirata rai abace, tunda take bata taba maidawa Turai martani ko magana ba sai yau, ahankali tace "please ki kama girmanki" sanan tajuya ta kalli Asad tace "go to flat dinku son ganinan zuwa" gyadamata kai kawai yayi yajuya yafita, Ammi tajuyo takalli Anty Turai datai mutuwa tsaye cikeda mamaki tana kallon Ammi, ahankali Ammi tace "haba Anty Turai, kefa matsayin uba kike awajen Asad, you are his Dad sister maisa koda yaushe kyaran yaron nan kikeyi kin matsamai, so kike yamiki rashin kunya? Wani kalan magana ne haka kikemai da girmanki? Mekike nufi da like father lik....." shiru tayi jin anbude kofa dasauri tajuyo Dad ne yashigo yana sanye da malum malum fuskarshi looking so paled, Turai na ganinshi cikeda masifa tace "Yaya wlh wlh zokama matar nan maka magana ni take kallon tsabar idanuna tanama rashin kunya, yarinyar danice nan na raineta" kallon Turai yayi yace "waike maisa kincika bakar masifa ne ana biki ma bakibar masifan ba idan baki suka shigo fa haba" baki tabude zatai magana yadaga mata hannu alamun tamai shiru sanan yakalli Ammi yace "what happen?" daga shigowan Asad har zuwa abinda Turai tafadi tagayamai, ga mamakin ta gani tayi Dad yakalli Anty Turai dasauri yace "kewane yagaya miki yama yarinyar wani abu" cikeda wani irin mugun mamaki Ammi ke kallon Dad, Anty Turai tace "dazu kawayena suka kirani sukace zasuje su duba gidan Amarya shine namusu kwatancen gidan, suka kirani suna fadimini sunje ance bacci takeyi, amman sai sukaga wata mata atsakar gida na tabbatar kishiyan Maman Du'a ce dan bazatai karya ba tace ai ango yama Amarya kacha kacha ne yarinya ba lafiya" ahankali Dad da jikinshi yay wani irin sanyi yace "shi yanzu Asad bai sarara mata ba daga kaita jiya jiyan nan" wani kalan kallo Ammi tama Dad ganin yanda yabiyewa Anty Turai suna maganan banza kan rayuwan dansu Allah yasama ba yaran dukansu agidan sun fita yasa kawai tawuce tai sama, dariya sosai Anty Turai tayi tana kallon Dad tace "bana gayamaka namiji koyaya mace take inhar akwai nono da duwawu ba'a yarda dashi ba, wai Asad da da kyar ya auri yarinyar nan yana kukkumbure kumbure uwarshi na lallabashi yana cijewa shine adaren farko harya afkama yarinya kaman jira yake" kallon Anty Turai kawai Dad yakeyi yasan duk kishi da bakin cikin bai auri yarta ne ba yasa duk take haukan nan, shi batasan takanshi yakeba nashi nacinshi, wcikeda kulewa tace "shegen yaro miskilan jarababbe kawai mai bakin hali" tajuya zata sama Dad yace "Turai" ahankali tajuyo takalleshi, "zonan" yakirata babu alamun wasa, tahowa gabanshi tayi tace "gani Yaya" ba kunya yace "wai yaushe zaki tafi ne naga bamaki maganan" kallon Dad take cikeda mamaki tace "Yaya ni kake kora daga gidanka" cikin masifan da Dad kawai yaji yazomai tsabagen kishin labarin dayaji na Asad haryay sex da Du'a tace "dakika kirani cewa kikayi birthday Aneesah zakizo, daga zuwa kinzo kin tare, as it is nariga nacika ma matata aiki danma Allah yasa tanada hakuri, yaran marigayi kanina, da yarki, kema kinzo instead of kiyi shiru azauna lafiya amman ki ishi matata mai hakuri, kin takura nata, kin tasa d'ana agaba da fitina, shegen fitinanki dayasa kika bari gidan mijinki babu namijin daya iya zama dake, ki shirya yinaki yinaki ki tattara kibarmin gidana gobe inkinga dama bakin kano yan uwan su Du'a zakibi ki bisu duk kuhadu ku koma kano tare, anbar Dadda shi kadai da Nurse dinshi da Dr dayawa ki koma kicigaba da kula dashi inba hakaba zanyi mummunan saba miki, wlh duk kudin danake baki wata wata saina yanke nadeba baki, jarababbiyan fitinanniyar mata kawai" Dad yawuce fuuuu yay sama Anty Turai da kaman an kafeta awajen tabishi da kallo danyau taga masifa kai tamaga abinda yafi karfinta, mutumin datake bama labari yana responding sosai all of a sudden ya birkice mata yana surfafa mata bala'i kaman junnu sai shafeshi, abin ya masifan bata mamaki batasan kishi ke neman kashe Dad ba.
Jin Anxiety na neman kasheshi gashi sai kiranta yake bata dagawa yasa yatashi kawai wuraren 5 yafice security su yabama wayar Ammi yakai mata dan bazai ma shiga gidan ba yaga matar nan sanan yashige motar shi yawuce abinshi, awani eatery ya tsaya babu abinda bai siyamata ba sanan yashiga motanshi yaja, su Mom da Kaka dukansu na falo an karasa gyara gidan fess fess, anyi mopping ansaka turaren wuta, Mami na sama tana bama Du'a data tashi tamata wanka takara gasata abinci sukaci an bude gate, dawani irin sauri Kaka ta mike tadanja labulen windown datake kusadashi gefe tace "jama'a badai mijin bane yakara dawowa ba ni Shatu kwas kwas, wanan wani kalan so yakema yarinyar nanne haka, Du'a Allah yabaki jarabatu, kai ku tashi mu tattara yinamu yinamu mutafi" tai maganan tana mikewa tsaye tana daukan mayafinta sanan takwalama Mami kira, "Zainab sakko mutafi mijin yarinyar nan yadawo" sanan takalli sauran yaran daduk suka mike tsaye harda Mom tace "kumutafi kafin shida kanshi yacire kunya yazo yakoramu" dukansu waje sukayi, Mami data gama magana da Du'a asama tacire kunya tabata shawarwari yanda zata kulada kanta sanan tamata sallama ta sanarda ita gobe zasu koma kano sanan tamata addu'a sosai, kuka kawai Du'a tafara hakanan Mami ta juya tatafi, tana saukowa kasa su Kaka nafita daga falo.
Kaman jira Asad yake ganin sun fito yasa ahankali yafito daga motan, Kaka dake kallonshi tace "to mudai zamu tafi, saduwan alheri gobe war haka mun tsufa a kano, ga yarmu nan Asad amana, daga ganinka nasan yaran kirki ne karka yarda ka chanza inba hakaba nima zan chanza maka" dan murmushi yayi yana kallon Aneela da dasauri tazo takama hannunshi tace "Uncle idan mukai hutu nadinga zuwa" gyadamata kai yayi ahankali yana murmushi sanan yasa hannunshi a aljihu yaciro wrapper kudi yan 1k sababbi guda biyar zai sama Aneela a hannu dawani irin sauri Kaka tasa hannunta ta fizge tace "gani Babba zaka bama yar karaman yarinya kudi" dan karamin murmushi yayi yace "wanan na yarane, ga naki nan zan baki" wani irin washe baki Kaka tayi tace "auuuho to ungo Aneela jebama Ya Nana kowa yadauki bandir dai dai banda cuce" dasauri Aneela tawuce wajensu Nana, sanan yasa hannu yadauko dollars sababbi yan 100 100 yabama Kaka guda goma, karba tayi dagudu tana kallon kudin tana kara goge idanu, sanan yabama Aisha kanwar su Abba dasauri takarba tace "Allah amfana" sanan yabata guda goma again yace "gashi kibata" dudda bai kalli Mum ba tasan Mom yake nufi tace "Allah ampana" gama kallon kudin tass tayi sanan tamikama Asad tace "ni ka chanza min bansan kallan kudin nan ba" dariya duka yaran sukahau yi banda Mom da idanunta sukai jajir wato ita Asad yama maida banza, 50k yadauko yakara mata akai, godiya tahau mai sanan tace "kumuje mu shiga mota" wucewa duk sukayi sanan ahankali Asad yajuya yakalli Mami dake tsaye abayansu tanadan murmushi, akunyace yakarasa gabanta sanan ahankali yadan duka ya amshi handbag dinta, murya chan kasa cikeda ladabi yace "Allah ya kiyaye hanya Mom" cikeda so dakuma kunya Mami tace Ameen har gaban motan yarakata, dakanshi yasa hannu yabude mata gaban motan duk Mum na kallo, murmushi Mami tayi tashiga sanan yadauki jakanta yabata amsa tayi yamaida kofar yarufe yace "Allah ya kiyaye hanya Mom" direbansu yajasu, Kaka tace "wato harda budema Mamar matanshi kofa ni bai budemin ba, lallai wanan yaron, naga yana tura abu ajakanki meyasa miki" dasauri Mami tabude jakanta, envelope yasamata mai kyau aciki that is sealed, dasauri Kaka tace "mugani" karba tayi ta tattaba tace " wlh kudi ne, yaron nan takadiri ne, wato yafifitaki sama damu ko ai shikenan ungo kayanki" karba Mami tayi tamaida jaka batare data budeba, Sheshekan kukan da duk sukaji yasa kowa ya waigo Mom suka gani tana kuka tasa bakin gyalenta akan idanunta dasauri Nana tace "Mom menene bakida lafiyane" hannun Nana ta ture tabarke da kuka sosai dan takasa rikewa tace "wlh wlh Allah ya isa bazan taba yafewa ba, an cutar dani an cutar da y'ata, anrabata da mijinta dan gidan arziki ita kuma tag do tazo tai auren kudi anan, wlh bamu yafeba, musamman nazo bikin nanne dannaga waya kwashi yarinyar nan nai dariya nai shewa amman ni za'a gumama bakin ciki wlh Zainab dagake har yarki van yafemuku cutata dakukayi ba" kaman jira Kaka take tace " wlh tir da halinki, kin shiga uku da bakin ciki, gayamin tunda kike kintaba zuwa bikin dakika dawo gida da uban kudi, kinsan yanzu nawa muka samu akan Du'a kuwa bari namiki lissafi, ranan dasuka zo gaidamu shida suka bada miliyan biyar, ranan sa lalli suka manna miliyan kusan shadaya shida abokan shi, budan baki aka bada miliyoyi da kannenshi suka barma su Nana yaranki sabida su yan gidan arziki ne basu damu ma dakudi ba, yanzu kalli kyautan daya mana, ko kudin nan muka hada muka bawa mijinki saiya bude babban kampani, nidai Allah yawa Du'a albarka gashinan naga arziki sabida ita, babu irin zigani dabaki kan yarinyar nan ba, kika cemin mayya ce, tana zuwan miki da daddare, aljanna ce, mecece yanzu ba gashinan ba itace tai aure har mijinta ya bare ta ba, inda aljana ce ko mayya da saidai muzo muga hawan mijin takashe shi amman gashinan shine yamana wanan kyautan, bazan kara biyemiki ba, Du'a jikata ce, yar Muhammadu ce da Zainaba kiyi ki mutu shegiya mai bakin hali matsalan yaran talakawa irinki kenan yar wahala kawai" Kaka tadinga kwapkeapa mata mari Mami uppan batace musu ba sai murmushi kawai
7️⃣0️⃣
Saida yaga fitansu sanan yajuya ahankali yakoma wajen motarshi yabude abubuwan daya sassayo mata ya kwaso sanan yamaida motan yarufe sanan yawuce