Showing 18001 words to 21000 words out of 153675 words
yaje mucirota wai bazaiyiba gashi ba maza sai tulin uban mata kaman gidan biki duk suna kuka, shine nace musu mujeni nacirota dan nasan that's the only thing dazai fitoda Asad daga cikin motan nan danni kadai nasan irin mugun halinshi, aiko ina shiga saigashi yataho ashedai yana sona yasan ban iya ruwaba fear of my death yasa yazo bawaidan he meant to save the girl ba, shine yashiga fa yacirota, Ammi kinsan menene" yay maganan yanajan kujera da sauri yana zama sanan yakalli Ammi dake kallonshi yace "Ammi nifa dasuketa yarinya I thought small girl ce fa tafada rijiyan saigashi Asad yafito da zankadediyan budurwa innalillahi Ammi kinga kyanta kuwa" Ammi dake sauraronshi tace "haba" dasauri yakalli Asad dake cin abincin anatse yana danna waya yace "Asad isn't the girl beautiful" batare daya kallesu ba yace "I don't know bankalleta ba" wani mugun tsaki yaja yace "Ammi wlh Asad dan rainin wayau ne" dan dariya Ammi tayi ganin yanda Sharif ya tunzura sosai tace "don't mind him kaji cigaba da bani labarin" murmushi yama Ammi yace "wlh Ammi tunda nake Allah Ammi harna gama yawona across the globe ni bantaba ganin kyakkyawa irin yarinyar nanba Ammi she don't even look Nigerian, hala half cast ce, Ammi she's so pretty gashinta har waist, she's so pretty I wish I can even see her again" ture plate din abincin dayagama ci Asad yayi yamike Ammi dasauri ta kalleshi tace "harka koshi? Baka cinye ba ai" gyadamata kai yayi yace "ya isheni, natafi wajen Dadda" dasauri Sharif yatashi yace "wait for me Asad" ko kallonshi baiyiba yawuce Ammi tabisu da kallo tana murmushi, Sharif is such a gentle man with a very very forgiven spirit, shikuma Asad is opposite na hakan, churarren mutum ne baka gane gabanshi da bayanshi ko itama sabida ita tahaifeshi ne saisa take iya fahimtan halinshi tass,.
Wani flat suka shiga kayataccen falo ne da kujera ke ciki sai lallausan carpet da aka rufe ko ina na kasan dakin dashi sabida sanyi sai wani tsohon dattijo da akalla zaikai shekara 90 ko fin haka ke zaune kan wata kujera mai ultra taushi wacce kanagani kasan musamman sabida shi akayita yana zaune gashinan tsaf tsaf sai wani bakin glasses a idanunshi hannunshi rikeda ayaba yanaci da aka yayyankamai awani clean bowl, tunda yashigo gidan this is the first time yayi kayataccen murmushi yace "Dadda" da sauri tsohon dake tauna ayaba abaki ya tsaya chak saikuma da sauri yasake gyara zaman glass dinshi a idanunshi yakalli kofa sabida haske kofa yasa baiganesu ba cikin muryanshi ta tsufa da still kuma take fitada kyau yace "amaida kofan arufe" dasauri Sharif dake hadiye dariyan shi yamaida kofan yarufe hakan yabashi daman ganinsu ahankali yanuna Asad da yatsa yace "Sharif Asad nake gani" dawani irin sauri Asad yaje bowl din jikinshi yacire ya ijiye agefe sanan yawani rungume kakanshi tsam tsam yace "Dadda kai kadai nayi missing wlh, kaga Sharif tunda na shigo garin nan yake batamin rai Dadda" washe bakinshi da hakora sun fiffita yayi yace "to wlh su kiyayeni aina gayamusu duk wanda yataba Asad toni yataba kona mutu bazan yafemai ba" dariya sukayi duka Sharif yazo yace "Dadda kai bazakamai fadaba mugun halinshi yay yawa" hannu yamika ya kamo hannun Sharif yace "banace ku hada kanku ba kome yayi kamai hakuri, shi hali zanen dutse ne ko mutum zai rabu dashi saidai da kadan kadan, halin mahaifinshi Abdullahi yagado sak" kankameshi sosai Asad yayi yace "i love you Dadda na"
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️ M SHAKUR
wa.me/+2347012181461
Free page
EPISODE 1️⃣1️⃣
Da taimakon Matan dake compound din aka kwasheta akai falonsu da ita jikinta na mugun barin sanyi daidai lokacin motarsu Abba tai parking akofar gida wani irin azababben gudu sukayi dayake Hamad shiya tukasu da Mami da Abba ne kadai sauran duk sun barsu awajen Kaka achan Ikara, dawani irin gudu Mami tashigo gidan idanunta sunyi jajir, this is the first time data iya cire koma meke sata yima yarta wani kala tanuna tsantsan damuwa da so akan yartata tadubi matan tace "ancirota ancirota daga rijiyan? jama'a kufadamin ina y'ata Du'a, ina take"? Tai maganan tana kama kirjinta dataji yana wani irin bugawa tsabagen fargaba, daki matan gidan suka nunamata sukace "tana daki, yanzun nan aka shiga da ita ciki" dawani irin gudu Mami tai flat dinsu Abba ma dayashigo yabita dasauri Hamad shima dagudu yabisu da shine last na shigowa sabida parking mota dayake, tana shiga falo taga some few mata akan Du'a dahar lokacin take ajike akasa tana wani irin rawan sanyi hakoranta na karkar kar kaman ana hada kacha ana gwarasu, wani irin ihu Mami tayi. "Du'a! Du'a" yanda Mami tayi baya kaman zata sume yasa dasauri Abba yatareta yace "calm down" juyawa Matan dakin sukayi suka fice ganin maigida, daidai Uwani tasauko kasa dawasu kaya da bargo daban daban a hannunta, tashi tayi daga jikin Abba dasauri takarasa wajen Uwani, karban kayan hannunta tayi sanan takoma inda take, dagota tayi dasauri takalli Hamad tace "Hamad bani wuka" dagudu yay kitchen wuka yadauko yafito yaga rigan jikinta Mami tayi Abba da Hamad duk suka juyar dakai chanza mata kayan Mami tayi agurguje sanan tawani irin rungume yarinyar dasauri tarufeta da bargo tana kuka. "I am sorry Du'a sorry" matsowa wajen Abba yayi hannunshi yakai yadaura kan wuyanta jin sanyi yasa yakalli Uwani yace "jeki hado garwashi" sanan yaciro hannun Du'a daya yana murza tafi hannun dasauri Hamad shima yazo yakama dayan hannunta yana murzawa duk tana jikin Mami data kankameta sosai, ba'a wani dauki lokaci ba saiga Uwani da uban rushi a kasko dan makota taje tasamo, ajiye wa sukai agabanta still suna murza hannunta ahaka suka samu kadan kadan tarage rawan sanyin hartazo tada ina gabaki daya kallon fuskanta tayi yanda idanunta ke a lumshe shafa fuskanta Mami tayi ahankali takira sunanta.
"Du'a" bude idanunta kadan tayi saikuma tabudesu gabaki daya tana kallon fuskan Mami, dasauri Hamad yataso kansu yana kallonta yace "Du'a taya kika fada rijiya"?zubamishi idanu tayi shima tana kallonshi saikuma ahankali tamaida idanun kan Mami tana kallonta asanyaye, Mami hakanan taji jikinta yay sanyi sabida yanda yarinyar ke kallonta, hawaye taga sun zulalo ta gefen idanunta kafin ahankali tabude bakinta cikin muryanta dabata fita sosai tace "maisa aka cironi daga rijiyan eh? Mami inaso namutu kowa yahuta saisa kodana fada saidai nadinga lumawa cikin ruwan ko tsoro daya banji ba saima kwanciyan hankali danaji domin ajalina yazo, Mami naso namutu sabida kihuta hankalinki ya kwanta kince tundaga randa kika haifeni baki karasamin kwanciyan hankali ba, yau dana fada rijiya all I could thought of was yanzu zaki fara samin kwanciyan hankali, bazan kara jawo matsala agidan nanba, bazan kara saki ko Abba a matsalan Kaka ba, Ya Nana zata auri Muhsin dinta, bazan kara zamema kowa matsala ba, Abba bazai kara wahalan boyeni ba dan nariga namutu" yanda take maganan tana kuka mara sauti sai hawaye kobakada imani sai zuciyanka ta sosu, ahankali tace "Mami akwai wata tambaya dana dade inaso namuku keda Abba" taidan shiru saikuma ahankali tace "bayan kun haifeni maisa tun a asibiti dakuka ganni daban bakusan yanda kukai dani ba maybe ko kuce baku sona a kaini gidan marayu kokuma kuce a chanza muku yarinya bani kuka haifa ba, maisa kuka daukeni still kuka raineni maisa kukamin haka, wanan kalan rayuwan dakukasa inayi kullum zaban mutuwa nakeyi akanta dan tafimin alkhairi I just want to die nahuta, dan Allah kubarni na mutu" tafashe da kuka sosai dayasa daga Abba Mami da Hamad were damn speechless itako Uwani dake gefe kuka tadingayi, tadade tana kuka ajikin Mami babu wanda yay attempting hanata ahaka bacci yay awon gaba da ita, ahankali suka kwantar da ita akan kujera suka lullubeta sanan Mami tazauna gaban kujeran tana kallon fuskanta, Tashi Hamad yayi yakalli Abba da Mami yace "Abba I want to see you both" yay sama tashi Mami tayo takalli Uwani da jajayen idanunta tace "ki zauna da ita" gyadamata kai Uwani tayi Mami tawuce sama itama, Abba yadade tsaye awajen sanan yawuce yay sama, dakinshi Hamad yabude ya shiga Mami tashigo Abba dashine na karshe shima yashigo yasami waje yazauna, kallon Abba Hamad yayi yace "Abba what are you going to do? Yaya zakayi da maganan Kaka?" kallon Hamad yayi yama kasa magana saikuma chan yace "all I know is bazan taba iya koran y'ata daga gidan nan ba" dasauri Hamad yace "Abba yazakayi da bakin Kaka, tace inhar yarinyar nan batabar gidan nan ba bata yafemaka ba, itaba mahaifiyarka bace kaza kaza kaza, Abba Kaka ta tsufa and we all know yanda tsofaffi sukai believing akan all this superstition, Du'a tazaman ma gidan nan da family mu gabaki daya matsala, jibi duka su Baffa dazu sunce duk akoreta ni I think inhar hakane zan dauki Du'a natafi da ita chan Jaji tai zamanta a apartment dina" dasauri Mami tace "Hamad duk randa mahaifiyar ka tasan kaika tafi da Du’a abin bazai muku kyau ba, kuma Du'a mace ce bazaiyi kyau tayi rayuwa dakai kai kadaiba dama kanada mata ne, ni kaina ayanzu all I want is peace, tunda Du'a ce matsalan afitarda ita daga gidan saisa na yanke shawaran kaita wajen Mama na achan Abuja" kallon Abba tayi ahankali tace "Dadyn Hamad" kallonta yayi yay shiru batare dayace komiba, ahankali tazo kusadashi zama tayi sanan takama hannunshi tarike tace "I know tunanin dakake da abinda ke ranka, mu dinan bamuke kula da Du'a ba wlh Allah ne, so it's high time we free this girl mu mikama Allah komi and I assure u idan tana hannun Mama she's safe nasan Mama na, I don't want u to be stubborn, u are a family man, ba Du'a ce kadai yarka ba, sauran ma dole ka kalli yanda rayuwan su zata cigaba da gudana, sabida Du'a kar peace da family ka ya wargaje just look at what Nana is going through now itama ai yarka ce, the way u look out for Du'a itama haka kake looking out for her, kayakuri kaduba lamarin kaji" tunda take maganan yake kallonta harta gama, ajiyan zuciya yasauke sanan yace "I will think about it, kubani waje yanzu" gyadamai kai kawai Mami tayi ta tashi tawuce tafice, yakalli Hamad yace "ka kira Dr na yazo yadubata tashi katafi" tashi yayi ahankali yafice shikuma Abba ya kishin gida da kujera ya lumshe idanu Allah kadai yasan meke going azuciyanshi.
Wuraren magrib likita abokin Abba wanda shine likitanta tun tana yar karama yazo yadubata allura yamata sanan yabata magunguna Abba ya sallameshi yatafi.
"she's alive! she's alive I can feel her pulse" sama sama takejin maganganun nan kaman a eco saikuma chan tabude idanunta sukai clocking da nashi......tarrrr tabude idanunta daga baccin datake tanabin inda take da ko'ina na dakin da kallo, ganin tana dakinsu kan gadonta ne an lullubeta da bargo, mafarki take kenan, mutumin data bude ido tagani dazu yacirota daga cikin rijiya tagani yanzun nan amafarki, ahankali ta yunkura ta tashi zaune ta jingina da bango tana kallon ko'ina ganin gari yama soma wayewa, saukowa tayi daga gado sai alokacin taga wani jibgegiyan akwati da batasan daga ina yazo ba baka kwara daya atsaye gaban wardrobe dinsu, bathroom dinsu tawuce tashiga wanka tayi da ruwan zafi sosai tana karajin karfi ajikinta sanan tafito daga wankan daidai lokacin Mami nabude kofan dakinsu tana shigowa hada ido sukayi da Mami ahankali ta sunnarda kanta kasa tana tuna all maganganun data gayama Mami jiya suna dawomata fresh a memory dinta kasa motsi tayi itama Mami tadauke kai tawuce wardrobe wasu kaya taciro mata tajuyo ta ijiyesu kan gado tace "ki shirya kiyi salla bari naje nakawo miki breakfast".
Fita Mami tayi daga dakin itakuma tashiga shiryawa agurguje sanan tahau kan dadduma tai salollin dake kanta saida tai azkar sanan ta tashi ta cire hijabin tazauna akan gado, bude kofa Mami tayi tashigo dauke da tray na abinci sanan takaraso cikin dakin ajiye abincin tayi kan side drawer gadonsu sanan tadawo tazauna ahankali kan gadon kusada Du'a da kanta ke kasa har lokacin dan wani irin kunyan Mami taji tanaji, murya chan kasa tace "Mami ina kwana" shiru Mami tayi tana kallonta batare data amsa ba saikuma gently takai hannunta kan fuskarta ta tallabo habarta hakan yasa tadago idanunta ahankali takalli Mami, murya chan kasa Mami tace "Du'a" ahankali tace "Mami I'm sorry Kinji" murmushi Mami tayi tace "shiiii I want you to listen to me" gyadama Mami kai tayi, Mami tadan numfasa tace "all abubuwan dakikaga nida mahaifinki namiki badan mun tsaneki bane saidan we are all trying to protect you Du'a, Du'a nasan kinsan wanan abin dan nasan kinsha jin yan uwan Abban ku nafadi, dana haifoki babu kalan maganan da ba'a fadiba akanki, ance ke ba yar Abba bace, naje na nemi ubanki nahadaki dashi, ke mayya ce ke yar ruwace" shiru Mami tayi tana sauke ijiyan zuciya sanan tace "Du'a akwai many things which u don't know kuma banmason kisani, I fought mahaifinki, we fought hard muka samu yan uwanshi da Maman shi suka barki kika zauna agidan nan left to them koranki sukaso ayi" Mami tasakeyin shiru sanan ahankali takai hannunta tadaura kan kumatun Du'a dake kallonta ahankali tace "Du'a you are special! tun ranan damuka haifeki mukasan hakan, you are special saisa kikaga muna boyeki, Du'a ke dabance! muna boyeki ne cus munyi tunani ta hakan zamu iya kareki and protect you, but u got it all wrong kin zaci mun tsaneki ne amman bamu tsaneki ba, kintuna abinda yafaru dake a JSS2 dayasa Abba yahanaki fita at all kinaso yakara faruwa dakene" girgixa ma Mami kai tayi dasauri hawaye nacika mata idanu. Ahankali Mami tasauke ijiyan zuciya tace "nakira Mama, Grandma dinki tariga tasan komi dama, yanzu da safen nan Hamad zai kaiki chan wurin ta a Abuja harsai komi nagidan nan ya daidaita, I think kema is best for u, your childhood has been terrible, kin taso cikin kyaran kowa is high time kije inda nasan u will receive d best care batare da an kyareki ko an ware ki ba, kinason kije wajen Mama na ko" ahankali ta gyadama Mami kai hawaye na zubomata, hannu Mami takai tashare mata hawayen tace "nasan namiki laifi, I've wronged you in so many ways just to please yan gidan nan but bazan karaba, nina daukeki na raineki for 9 months I can never hate you, abinda nakeso dake is take very good care of yourself, kizama yarinya mai wayau da basira, know when u are in danger and when u are not, kidage da addu'a, ki rike Allah danshi kadai ya isarmiki, I want you to be a good girl, karki sake kima grandma dinki ko any of your uncles rashin kunya kinji Du'a, I know u are in a good hands this is the first time dazaakije wani wuri da hankalina ya mugun natsu, now eat your food saiki fito ki gaida Abban ki kuyi sallama bari nakai jakan I waje" gyadama Mami kai tayi Mami ta tashi jakan taja tawuce tafita daga dakin, shiru Du'a tayi Allah ma yasan har cikin ranta tana farin ciki zatabar gidan nan sabida tasan yanda Maman Mami kesonta lokacin tana yarinya idan sukaje gidan kaman zata cinyeta, koba komi bazata kara ganin Muhsin ba, mugun mutum, koba komi idan baiganta ba zai hakura ya auri ya Nana, Hawwa zata huta da hararanta kullum Mum ma tahuta babu wanda zai kara kiranta yar aljanu, and at the same time yau saitaji wanan bakin cikin da kunci na haushin Mami dayakeji dukya fita daga zuciyanta sabida fir the first time Mami ta zaunar da ita tamata bayanin abinda bata taba mataba kenan. hannu tamika tadauki tray abincin ta abincin taci bama tawani ci sosai ba ta ture ta ijiye, shigowa dakin Mami tayi takalleta tace "tasoto muje kiyi sallama da mahaifinki" gyadama Mami kai tayi gabanta nafaduwa hijabinta tasaka sanan tabi bayan Mami suka fito, Abba na zaune akasa yana karanta jarida hangita yasa ya tsayar da karatun yana kallonta harta karaso, dan nesada shi ta tsugunna ahankali tace "ina kwana Abba" "ya jikinki akwai abinda ke miki ciwo"? Abba yamata tambayan bayabo ba fallasa wanda idan tasabo tasaba dan Abba naturally he's not that kind of a friendly father dake wasa da yaranshi, gyadamai kai tayi ahankali tace "babu ko'ina Abba" gyadakai yayi cikeda gamsuwa yana kallonta, batare data dagokai ba tace "Abba kayakuri bazan kara abinda nayiba" ahankali yace "l know" dagokai tayi ta kalleshi, hannu yasa a aljihu yaciro bandir nayan 200 20k yace "zo" tashi tayi ahankali takarasa gabanshi karba tayi ahankali tace "nagode Abba" "Allah kiyaye hanya, jeki Hamad na jiranki a mota ta" hakanan batasan mesaba kawai taji kuka yazo mata dasauri tajuya tana daura hijabinta kan fuska Abba kuma yabita da kallo, fita tayi daga falon, Mami ta biyota abaya rikeda hadadden kula na abinci.
Hamad na tsaye gaban motan sienna Abba yaga fitowanta yana kuka, murmushi yayi yabude mata gaban motan tana karasowa tashiga ta zauna, karasowa itama Mami tayi tana murmushi tace "bazakama kanwarka magana tarage kuka ba tadauka yarinya ce ita" murmushi yama Mami baice komiba, Mami ta ijiye mata kulan akan cinyanta tace "ga abinci inkinji yunwa kici naga baki waniyi break da kyau ba and stop crying" gyadama Mami kai tayi, tashi tayi takalli Hamad tace "kutafi Allah kiyaye hanya" rufe kofan yayi sanan yazagaya yashiga yatada motan yaja Mami namusu bye bye suka fice daga Gate din. ajiyan zuciya Mami tasauke ahankali tace "Allah ya azurtaki da farin cikin rayuwa Du'a, I love you so much y'ata, zan dinga miki addu'a kinji Du'a"
💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫
✍️M SHAKUR
Free page
EPISODE 1️⃣ 2️⃣
Sosai Hamad ke zuba gudu akan titi, har cikin ranshi he is happy for Du'a na barin gidansu datayi, bini bini yake kallonta yanda saibin hanya da komi take da kallo kana gani kasan bata saba fitowa ba, dan juyowa yayi yakalleta ganin yanda take kalle kalle yasa yay dan murmushi yace "iyye basaban ba