Showing 30001 words to 33000 words out of 153675 words

Chapter 11 - Kyawuna Jarabta Ta Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

15 Dec 2024

605

tsayawa yayi yana kallonsu yanda duk suke trembling, ahankali yasaki dan murmushi, wani kalan dadi ne yakashe su dasauri Rahima tace "Ya Asad nima I want new phone" dasauri Mariya tace "Ya Asad nima" ganin suna neman samai ciwon kai yasa yakalli Aneesa yace "go to my room, check the left sidebed drawer bring all the money that is there" wani irin dadi taji tace "tom Ya Asad" dasauri tawuce stairs tai sama dakinshi tabude ta shiga wani kamshi ne yamata sallama, drawer taje ta kwaso duka kudin wrappers na yan dubu dubu ne guda 10, kwaso su tayi tasauko, Su Rahima na ganinta suka shiga murmushi, gabanshi tazo zata bashi kudin gefenshi ya nuna mata hakan yasa ta ijiye kudaden awajen, hannu yasa yadauki rapa biyu yabata dasauri takarba tawani washemai baki tama kasa godiya, "Rahima" "na'am Ya Asad" dasauri tazo dauka biyu yayi yabata dagudu Mari tazo itama yabata biyu dukansu yabasu 200k each, ahankali yace "u will get the phones tommorow" wani irin ihu sukayi sukahau tsalle awurin suna rungume juna. "Ya Asad thank u, yaaayyyy, Ya Asad u are the best wallahi" ihunsu yatada Sharif dake bacci hakan yasa yasauko ganin kudi a hannunshi suna rawa suna nunamai yasa cikeda wasa yace "yanzu sabida ku yan bakin ciki ne Asad na rabon kudi shine bazaku tasoni nazo na amshi nawaba " dasauri Rahima tace "bayan kahanamu damuka maka magana" hararanta yayi yaje gaban Asad dake aikinshi yana kallon ragowan 4 raps na kudin yace "Ya Asad nima abani nawa"? Dan hararanshi Asad yayi saikuma kaman bashiba yakalli su Aneesa yace "abashi" atare sukace "nooo Ya Asad" wani irin biyo su dagudu Sharif yayi aiko suka kwasa dagudu suka fita daga dakin yace "shegu yan bakin cikin yara kawai" murmushi Asad yayi sosai yace "kasai musu waya" juyowa yayi yaharari Asad yace " marasa kunyan yaran nanne zasuci kudina, ashe zasu mutu bawaya, Tara kudin aure nake" tabe baki Asad yayi yace "says wanda baida girlfriend" hararanshi Sharif yayi yace "Malam ya isheka fa kaita daga harkata tunda dai kahanani kudi".
wa.me/+2347012181461







💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫



✍️ M SHAKUR

EPISODE 1️⃣8️⃣
Tashi Asad yayi ya rufe system din ya ijiye sanan ya kwashe ragowan kudinshi yawuce wanshi sama, baiwani dade ba yasauko cikin jallabiya sabida sallan magrib da aka kira sai baza kamshi yake bayin falo shima Sharif ya shiga ya dauro alwala sanan yafito suka fice tare zuwa masallaci.

Ana Magrib suka shigo gidan, dinning direct sukayi, zama sukayi Ammi na fitowa, Sharif yace "Ammi ina yaran nan wai nisukema dariya" dan hararanshi Ammi tayi tace "toba dole suyimaka ba nan nan yaran nan suka rokeka kudi kahanasu, anyway suntafi wajen Hajiya, kasan jikan Hajiya tazo shine ita sukaje gani nace musu nai musu kawa age mate dinsu ce wai zasu cemata ta shirya suje shopping tareda ita gobe" tsaki Sharif yayi yace "Ammi bani abinci na naci nima naje naga jikan Hajiyan muga ko za'ayi ta gida ne, Ammi tanada kyau"? Hararanshi Ammi tayi tace "inkaje ka gano da idanunka" tai maganan tana bashi plate na biryani rice, karba yayi yafara ci sanan ta zubama Asad dake daddanna wayanshi kaman bashi awurin. Biryani ta zubamai sanan ta turamai gabanshi tace "ina kaje dazu Asad" dagokai yayi yakalleta spoon yadauka zai faracin abincin yace "naje nasha iska ne kawai Ammi" ture abincin Sharif yayi yamike yace "Ammi natafi" wanan karan dariya Ammi tayi tabishi da kallo fita yayi abinshi, tashi itama Ammi tayi tai sama bata wani dade ba tafito rikeda drawing book din Du'a samin shi tayi zaune inda tabarshi yanacin abinci, kujeran kusada shi taja tazauna sanan ta ijiyemai drawing book din agabanshi, Ammi yabi da kallo saikuma ya ijiye spoon din dayakecin abinci dashi yadauki drawing book din yabude yana dubawa, ahankali yakalli Ammi yace "Ammi who drew this"? murmushi Ammi tayi tace "zanen yayi kyau" dasauri yana kallon drawing din yace "this is classic, I mean the hands behind this drawings is a genius, Ammi wow, idan yanzu nabada wayan nan zanen akai bringing this shoe to life my company zai zama number show brand company in the whole Africa" murmushi sosai Ammi tayi tace "zaka bama mai zanen aiki kenan"? sai alokacin ya kalli Ammi yace "who drew it Ammi" ahankali Ammi tace "zan gayamaka, but my zanen is very dear to me nai alkawari zaka bama mai zanen aiki dudda batai makaranta ba" dasauri yace "Ammi u mean mace ce tai zanen!" gyadamai kai tayi tace "yes mace ce, but batai school ba sabida some matsaloli irin na rayuwa, but she's talented, inason kabata aiki sanan kabiyata tsakani ga Allah yanda kake biyan illustrators dinka" yatsine fuska yayi yace "Ammi kinsan qualifications din illustrators dina kuwa, how can I pay wacce bada da credentials haka is not possible ma" fizge drawing book din Ammi tayi tace "then forget it" dasauri yace "okay naji Ammi kawo" ya karbi drawing book din yana kara dubawa, Ammi tace "yanzu yaushe zata fara aiki" ahankali yace "gobe Monday, for now Sharif will handle everything dan sai next week zan koma"

wa.me/+2347012181461




💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫



✍️M SHAKUR

Free page
EPISODE 1️⃣ 9️⃣
Gyadamai kai Ammi tayi cikeda jin dadi tace "Allah maka albarka Asad dina" murmushi yayi yace "Ameen Ammi, but who is the girl"? kaman bazata fadamai ba tace "jikan Hajiya ce, she's 21" yatsine fuska yayi yace "Ammi ni all those children banson raini fa" hararanshi Ammi tayi tace "to Uncle Asad, ya za'ayi ma tamaka raini, jikan Hajiya ai she's just like ur sister su Mariya idan tayi badaidai ba ka gyaramata, kuma batada raini ko kadan that I know" yatsine fuska yayi irin baimasan maganan nan ahankali yace "Ammi I want coffee" tashi Ammi tayi tace "bari nahado ma tunda yaran nan duka sun gudu gidan Hajiya sun barni nikadai" kitchen tawuce tashiga....



Yau idan kaga bakin Du'a har kunne, har Rahima dake feeling tagirme su bazata iya zama friend din Du'a ba jitayi tanason Du'a sabida yarinyar akwai kyau dudda sun lura duk sun fita wayewa basu wani damuba kafin kice me cika falon Hajiya sukayi da hayaniya, suka tasa Hajiya agaba sai tabama Du'a itama kudin shopping gobe duk suka tafi tare, itama 200k tadauko tabata daman tanason takai yarinyar shopping but bata sami lokaci ba waya ma tace "gobe idan zata dawo zata taho mata da waya" duk suna cikin uban hanayinan Sharif yay sallama, dasauri Rahima tace "kinga Du'a we have two brothers, wicked and harsh, yanzu zakiga weekend one din shike mana murmushi da wasa amman shine ba'acin kwandalan shi" Hajiya dake kallonsu tace "Au haka kikace Sharif shigo kaji yanda kannenka kebata maka suna" turo kofan yayi yashigo hakan yasa Du'a itama tadaga kanta dantaga wanda ake batawa, wani kyakkyawan gayene dogo mai tsayi gashinan fari fat kaman su Rahima, tana ganinshi taga kamanninshi da Rahima da Mariya, baida kiba ko kadan, sai uban kyau ga sajenshi baki sidik dasuke nan akwance, gashin baida tarin gashi irin na Asad amman akwai gashi kadan da lowcut yakeyi ko kadan bata ganeshi ba hakan yasa kawai ta tsaya tana kallonshi daga inda take zaune kusada Hajiya dasu Rahima.


Dauke kai yayi daga kallon Du'a ganin kannenshi da kowa na wajen yace "Hajiya yanzu har gidanki suka tattaro sukazo suna gulmana yaran nan, aiko wlh zan baku kashi" yay maganan yana dunfaro su, ihu sukayi duk suka tashi suka kankame Hajiya Du'a ko sai dariya dasauri Hajiya tace "jama'a na shiga uku, wani yamikomin wayata yaga wlh Ammin ku zan kira tazo ta kwashi yaranta kutafi gida tunda neman kasheni kuke kai kuma wlh bazaka taba yaran nan agidan nan na ko kazo kazauna kokuma kawice katafi idan mugunta kazo yi nagayamaka kukuma ku dagani" Da sauri suka dagata shikuma yazo gefenta yazauna kusa da ita yay folding hannu yace "Hajiya jikanki batada kunya ita batasan yayanta yazo tagaidani ba wlh idan tace zata biyema marasa kunyan yaran nan nida ita bazamu shirya ba" yay maganan yana hararan Du'a, sosai Du'a ke murmushi ganin yanda Sharif keda ban dariya, ahankali cikin yar muryanta tace "Ya Sharif ina yini" hararanta yayi yace "lpy lau" Mariya dake gefenta tace "Ya Sharif kaga harda ita zamuje shopping din gobe tunda Ya Asad yabamu namu kai kabata nata ai itama kanwarka ne yanzu" dasauri Hajiya tace "ohh ni yasu Mari ke Mariya yaushe kika dawo scammer eh, Sharif yaran nan damfaran ka zasuyi ba yanzun nan nabama Du'a nata 200k dinba" dan sosakai Sharif yayi yace "Hajiya ni bansan ko yaran nan basuso nai aure bane, kudin aure fa nake tarawa" saikuma ya kalli Du'a yace "nasan sun riga sunce miki banda kirki I will prove them wrong, kinga ban shigo da kudi ba, but zanbama Mari gobe tabaki okay" gyadamai kai tayi tana kallonshi irin kaman bata yarda ba dinan dan ita Grandma tariga tabata kudin ta, kaman Hajiya ta lurada hakan ne yasa tace "baki cema Yayanki kingode ba" murmushi tayi ahankali tace "nagode Ya Sharif" nan fa dakin ya kachame da hira, shi Sharif baida girman kai yana shiga kannenshi yayi hira dasu sosai iyayensu dasuka rasu yasa yafara haka dan he is all dasuke dashi couple with the fact Asad baida wasa, saisa yake hira dasu yasasu dariya yasasu bakin ciki komi ba, daga karshema zamewa Du'a tayi tai bacci shoulder ta nakan jikin Rahima, sai wuraren 11 Sharif ya tarkatasu sukama Hajiya sallama suka tafi kaman karsu tafi, itakuma ta tada Du'a tawuce taje ta kwanta.



Flat dinsu ya shiga yana maida kofa yarufe sanan yashigo ciki Asad yagani zaune afalo yana kallon wani horror movie a smart TV dake falonsu, tsaki Sharif yayi danya tsani horror movie zama yayi yace "kafara kallon film din aljannun nan naka ko" dagamai gira daya Asad yayi sanan yadauki drawing book din da Ammi tabashi ya jefama Sharif din, dasauri ya chapke yace "what is this" yay maganan yana budewa, ganin wasu hadaddun zanen takalma yasa yamike tsaye yacigaba da kallon su one by one. "woooooo Asad who drew this??? Wow Wow, waye yay zanen nan eh, we need this talent a company mu wlh, who drew this Asad" dan batarai yayi yace "Ammi takawomin wai I should hire wacce tai zanen a company mu" dasauri Sharif yace "of course Asad you should hire this talent karfi all those competing companies su gano mai zanen su rigaka hiring nashi, but waye mai zanen a ina Ammi tasamo maka" tabe baki yayi yace "tace wai jikan Ammi ce mai zanen, she's a small girl 21, kuma karatun ta a JSS2 ta tsaya due to some reasons best known to them, how can someone dabaida qualification zaimin aiki eh" dasauri Sharif yace "in this case don't look at qualification look at the talent, Asad ko bature illustrator dinka baitaba zana takalma masu kalan kyau dinan ba, this is masterpiece wlh, mukai takalman nan trust me all celebrities across the globe will be rocking ur brand, yarinyar nan tun wuri without second thought kadauketa" yatsine fuska yayi yace "Ammi tariga tasa nadauketa gobe zata fara aiki" dasauri Sharif yace "gobe" dan yasan gobe zasuje shopping, gyadamai kai Asad yayi yace "yes, inaso you should handle everything, interview her kasata a office na illustrator din let her get to work, guide her, before nagama this TV program in yaso once am back sai afara work on production" gyadamai kai Sharif yayi yace "okay Asad, bari naje na kwanta, kaine night owl" yay maganan yana stairs yana murmushi da gangan yaki fadamai wacece jikan Ammi yanaso yaga reaction dinshi ranan dazaiga wacce yace to daga rijiya ce jikan Hajiya ita yabama aiki.




Wuraren 5:30 Hajiya tashigo dakinta, tadata tayi ahankali tabude idanunta tashi tayi ahankali tazauna Hajiya dake kallonta tace "guess what" bude idanunta tayi tarr tana kallon Hajiya, murmushi Hajiya tayi tace "kinsami aikin" wani irin murmushi tayi tawashe fararen hakoranta, Hajiya tace "amma ance yau zaki fara aiki, danhaka tashi kiyi salla kiyi wanka ki shirya yarinya na is now a working class young lady, my lucky jika" murmushi sosai tayi ahankali cikin muryan baccinta tace "Grandma shopping dinmu dasu Rahima fa" murmushi tayi tashafa gefen fuskanta tace "don't worry about that karfe 4 zaki tashi daga office idan kindawo sai kuje, yanzu tashi kije kiyi salla" gyadamata kai tayi ta tashi dasauri tai bayi alwala tayi tafito tai salla saida tai karatun Al Qur'ani tai addu'a Allah ya sanyama aikinta albarka sannan takoma bayi tayo wanka tafito mata shafa ta shirya cikin riga da skirt na atampa sanan tafito falo, tunda take saukowa Hajiya ke kallonta ganin yanda mahaukacin shape dinta yafito akayan yasa taji bata natsu ba, ko aikin ma data bari tayi sabida tasan Ammi da yaranta ne tasan yanda sukeda natsuwa kuma tasan zasu sa ido akan Du'a, saisa ta natsu da bata bartaba, sanan kuma tanason yarinyar takara girma tai wayau tasan ya rayuwa take outside home, kujeran dinning Hajiya taja mata hakan yasa ta zauna tace "grandma cikina namin wani iri idan natuna zani aiki" dan dariya Hajiya tayi tana zuba mata tea da Irish tace "kina feeling butterflies a ciki, it's normal, yanzu ci abinci karki latti fa, 8 ake zuwa aiki" dasauri tashiga cin bata wani ci sosai ba dan bata iyacin abinci sanan ta tashi, Hajiya tace "anya bazan sayo miki Vitamin B complex ba kuwa Du'a baki iyacin abinci, oya tashi muje sama kiga" tashi tayi sukai sama, dakinta suka shiga Hajiya tabude wardrobe dinta, wani sabon abaya taciro mata black mai mahaukacin kyau ta ijiye kan gado tace "inaso ki zama very wise girl, kinga kalan jikin da Allah yabaki dan haka bazaki dinga saka atampa haka kina zuwa aiki ba, zan karo miki hadaddun abaya masu kyau su zaki dinga sawa kina zuwa office okay, inaso idan kikaje ki natsu ba ruwanki da gulma ko surutun office respect ur senior idan kikai laifi aka miki fada take ur correction, karkiga sabida kinga Sharif ko Asad sabida kin sansu suna kaman matsayin yarana ne kidinga musu magana anyhow ko rashin kunya no, a office is strictly work and formal communication okay, ki natsu kafin ki zauna akan kujeran aikin ki da za'a baki kiyi addu'a, kullum idan kika shiga office dinki kafin kifara aiki kiyi addu'a hakan zaisa kidinga samin cigaba Allah na Buda miki, ki zama mace mai kamunkai, abinda yasa nama barki kiyi aiki sabida inaso ki sami experience ne kisan menene rayuwa dan bakisan komi kan rayuwa ba Du'a, be very smart okay, karki damu yau zan sau miki wata" gyadama Hajiya kai tayi tace "thank u Grandma" ajiye mata kayan tayi tace "oya shirya nima bari naje na shirya zan shiga office yau saina saukeki a company ku" wucewa tayi tafice, shiryawa tayi cikin doguwan rigan ita kanta saida ta kallo kanta saboda yanda tai wani kalan kyau, parking kalabanta tayi sanan tazauna kan kujeran tadau gyalen abayan tana kokarin rolling bata iyaba aka turo dakin aka shigo, Hajiya ce ta shirya cikin ubansun gown din lace rikeda waya tamikama Du'a tace "ga Mamin Ki" karba tayi takai kunnenta ahankali tace "ina kwana Mami" ajiyan zuciya taji Mamin ta tasauke tace "Du'a ya kike" murya chan kasa tace "lpy lau" murmushi Mami tayi tace "ance kinsami aiki Allah ya sanya alheri ki kulada kanki kinji" murya chan kasa tace "to" "OK bye" bye tace Mami ta katse wayan karban wayan Hajiya tayi tace "bani gyalen kiga namiki rolling" rolling Hajiya tamata tsaf, saita juya tana kallon gaban mirror hannu tasa tadauko wani pink janbaki da kwallin saka mata kwallin tayi sanan ta shafa mata Jan bakin kadan daya saje da lips dinta, kafin tadau turaruka ta fesa mata sanan tadauko wata jaka tace "idan mace zata fita most especially office haka makesure kinada pad kwata daya aciki incase of period yazo miki, sai wipes, sai lip balm, sai dan karamin turare haka dayar hoda ko madubi, pen da dankaramin jotter haka" tai maganan tana daukan komi tana samata ajakan sanan tabata jakan, karba tayi tana murmushi Hajiya tawuce tafita tace "sa takalmi ki sako" takalmi tasaka sanan tajuya takalli kanta a mirror wlh kaganta bazaka iya tantanceta da balarabiyaba tai wani irin kyau akayan, hakanan saitaga tama kanta girma tadawo wata babba kaman yar mai kudi jin Grandma ta kwalama ta kira yasa tajuya da gudu tafice.

don magana dani M Shakur chat me up by clicking on this link wa.me/+2347012181461





💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫



✍️ M SHAKUR


Free page
EPISODE 2️⃣0️⃣
Razika da Shemau tagani a falo tsaye duk suna kallonta suna murmushi sabida tsabagen yanda tai kyau, sake washe musu baki tayi tace "natafi office" kwashe wa sa dariya sukayi sukace "adawo lpy Du'a, Allah yabada sa'a" Ameen ta amsa sanan tawuce tafita waje tana musu bye, tsakar gida tayi tana tafiya ahankali ita kanta Hajiya tsayawa tayi tana kallon Du'a to some extend bata wani cika blaming Kaka ba data dage cewa Du'a ba jikan ta bane dan wlh Du'a bata da banbanci da balarabiya ga kyau ga diri ance mutum tara yake baicika goma ba Du'a tamafi ashirin, fararen kafafunta Hajiya tabi da kallo dake kara haske bakin abayan data saka karasowa wajen tayi tace "muje grandma" murmushi tamata ta rungumo kafadan ta tace "kinyi kyau jikalle, yau kukaje shopping ki zabo takalma masu kyau da hills ba chan chan ba kinji, good shoes takes a woman to good places, takalman Du'a dina should be epic kaman cendarella koba hakaba" "hakane Grandma" tai maganan tana shiga mad jeep din Grandma, Grandma ma tashiga driver ta yajasu, hira Hajiya keta mata ganin she's a bit nervous daurewa kawai take wayaga sabon shiga, cikin wani ubansu glass building taga sun shiga mai tsawo wanda daga gani kasan akwai elevator dan sabida yanayin tsayinshi sunan company EPIC & COs LTD, parking direban Grandma yayi takalleta ganin yanda take kalle kalle tace "this is company dazaki dinga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login