Showing 6001 words to 9000 words out of 153675 words
daura" tawuce tafita daga dakin, bin Mamin tayi da kallo sanan tajuya ta kalli Madubi kwallin sunma idanunta wani irin hadadden kyau, murmushi tayi tadauki dankwalin tasake mai wanan local daurin yan kauyen nan sanan ta tashi hijabi tasaka tai sallan azahar ganin biyu tamayi sanan ta tashi tacire hijabi taje tagaban window dakinsu ta yaye kannenta tagani su Aneela da Amal a compound suna guje guje suna wasa duk sunci gayu suma, hakanan taji inama itace komawa tayi tazauna sanan tadauki novel dinta tabude zata fara karantawa saikuma kannenta datagani a compound suka kara fadomata arai jitayi she's damn tempted to go out, maida novel din tayi tarufe sanan tamike tsaye tana rikeda novel din tabude kofa taleko ganin babu kowa yasa da sauri tafito ta maida kofan ahankali ta rufe sanan tai stairs dagudunta har tana neman faduwa tasauka kasa nanma babu kowa, motsi dataji daga sama anbude kofa taji muryan Mum tanama Nana magana "kinduba zobon dayasa kimai hope yay sanyi"? wani irin kwasa tayi dagudu tashiga kitchen dinsu gabanta nafaduwa, gani tayi anama girki a kitchen din ga hadaddun kula na baki dataga an jera asaman kan fridge tana mamaki baki zasuyi yaune kuma, jin muryan su sun sauko kasa yasa da sauri tabude kofan kitchen dazai sadata da backyard tafita dasauri tamaida kofan tarufo dasauri daidai sun shigo kitchen din sanan tawani irin kwasa da gudu taidan mini garden din da Abban su yamusu awajen yawanci weekend Abba nazuwa garden din yazauna yasha iska, is very small a portable ga flowers sosai na daidai kudi ba irin na masu kudiba, ko kadan bata lurada mutumba sabida tana gudu tana waigan bayane jitayi kawai tai tuntube da mutum taiwani irin tumble tasaman kanshi tatsallako gabanshi zatai baya ta fadi yawani irin rikota gam gam hakan yasa dankwalin kanta yawani irin zamiye yafadi kasa, novel din datake rikeda shi yawani fadi shima, yanda gabanta ke faduwa dan tariga tasarai fadi zatayi yasa ta kankame idanunta gamgam cikeda tsoro tana wani irin nishi da bakinta dake fitowa afili.
Chak ya tsaya batare daya saki hannunta ba yake kallonta tundaga kan tattausan hannunta daya rike zuwa kyakkyawan fuskanta da yanda ta runtse idanunta cikeda tsoro tana nishi zuwa yanda jelan gashinta ke gogan kasan wajen. cikin wani irin murya yace "who are you beautiful lady"? jin muryan mutum wanda batasaniba dan duk azatonta da Abba taci karo danshi ke zama awurin nan danhar tasadakar yautamutu a hannunshi yasa tabude idanunta dasauridasauri sanan tawaresu sosai ta kalleshi hada ido tayi dawani kyakkyawan Matashi wanda akalla zaiyi mate din Ya Hamad dinsu yana sanye cikin wani farin yadi mai laushi sai zuba uban kamshi yake, kara zaro idanu tayi tana kallonshi batare datayi maganaba, murya chan kasa yace "who are you? what's your name Pretty Lady" kokarin fizge hannunta daga nashi tashigayi sanan tace "My name is Du'a" wani irin lumshe ido yayi yabude yana karabinta dawani irin mayen kallo yace "you have a very very, verrryyy beautiful name, keyar gidan nanne ko bakuwace ke" kokarin fizge hannunta take takasa sabida yanda yariketa gam gam tace "ni yar gidan nanne, nika sakenmini hannu intafi" ganin hankalin ta nakan hannunta dayaki saki yasa yace "kinaso in sakenmiki hannu"? gyadamai kai tayi batare data kalleshiba ta kalli gefe daya, yace "to answer my questions saina saken miki hannu" dasauri ta gyadamai kai tana kallon gefe dan batason hada ido dashi sabida kallon dataga yanamata ahankali yana kallonta still yace "ke kanwar su Hamad ne"? dasauri ta gyadamai kai alamun eh hakan yasa yace "amman your mum is different ko?" sake gyadamaikai tayi tace "Mami ce Mum dina" yanda take magana da muryanta kaman na yara tsabagen dadi bala'in tafiya dashi yake she talks kaman yar yarinya kuma kaman ashagwabe, ahankali yace "Yaya akayi to bansanki ba?" ahankali tace "Abba baya barina infita" yanda take maganan gabaki daya taki kallonshi sai gefe take kallo yasa yasake binta dakallo tundaga gashin kanta har zuwa kirjinta da yake hango tudun boobs dinta da kyau wowwww! dan he could have a clear sight saman sabida yanayin wuyan riganta dakuma yanda tadan rankwafo ta gabanshi, tana kallon gefe still tace "dan Allah kasakeni in tafi I don't know you, idan wajen Ya Hamad kazo kaje side dinshi Abba kadai ke zama anan" murmushi yamata ganin da gaske takasa kallonshi sai gefe taketa kallo tana magana this girl is not use to men! yay maganan aranshi sanan yace "ni wajenki nazo sonki nake" girgixa mai kai tayi dasauri tace "wlh bani bane banama fita baka sanni ba please kasakenmini hannu nakoma cikin gida ba'a san nafitoba wlh" yanda take maganan yake mugun burgeshi baisan lokacin dayace "antaba gayamiki u look beautiful whenever you talk? Is this ur natural hair"? yakai hannunshi zai taba kanta dasauri takoma baya saikuma tasaki kuka shima binta yayi tana komawa baya yana kokarin biyota zai taba mata gashin sukaji karan fadin abu dasauri dukansu suka waigo baya.
Nana ce tafito taci uban gayu sai kamshi take zubawa tadauko hadadden tray da jug din cold zobo da cups kekai dukta sakesu akasa jug din yafashe zobon nabin kasa.
💫 MY BEAUTY MY CURSE 💫
✍️M SHAKUR
Free page
EPISODE 4️⃣
Ganin Nana yasa takara karfin kukan tace "Ya Nana kinga wanan mutumin ko yarikeni yaki yasakeni tundazu" juyoda kanshi yayi yana kallon yanda take magana kaman zai cinyeta yace "inda nasan akwai kyakkyawan yarinya irinki agidan nan I wouldn't have wasted my expensive time on this your sister yanuna Nana" wani irin kwalalo idanu tayi sai yanzu tagane saurayin Nana ne wanda zata aura, rawa jikinta ya shigayi tana kallon Nana tana kokarin fizge hannunta daga nashi, ganin yanda ta daburce yasa yasaketa yana murmushi looking so damn happy, dawani irin gudu ta kwasa tama kasa komawa ta hanyar data biyo dazatazo kawai ta zagaya takoma ta compound tabude kofan falonsu ta shiga da gudu tai sama.
Binta yayi da kallo harsaida yadena hangota sanan ahankali yakalli dankwalinta dake wurin da novel dinta yadauka sanan yakai dan kwalin kan fuskanshi yana wani shakan kamshinta sanan ya janyesu daga kan fuskanshi yakalli Nana dake tsaye takasa kwakkwaran motsi yace "so kinada this beautiful sister baki taba gayamin anything about her ba, in fact you've never mentioned her to me ma" tattaro courage dinta tayi tasakinmai murmushi kobakomi akwai one thing data koyo daga wajen Mum dinta is kirsa, karasowa tayi kusada shi tazauna akan carpet din data shimfidamai cikeda salo irin na siyasa tace "ko Abban mu dudda yarshi ce baya acknowledging nata cikin yaranshi, bama Abba ba har uwarta Mamin ta data haifeta ma, bakaganta ba kaman mayya, Mamanta kafin tai aure tanada aljanu namijin dare, kafin acire mata aljannun akwai wanda ya aure ta so ance shine yamata cikin wanan yarinyar saisa gatanan daban, gabaki dayan danginmu ita kadaice fara, ita kadaice daban, kamanninta komi nata daban, Kakanmu ta tsaneta, she has been nothing but a bad luck duk inda tashiga saitai causing trouble saisa Abba yay grounding nata, ba boko ba islamiyya ko this our compound she's not allowed to come out, iya kanta daki, ko kitchen ba'a bari tashiga kartaje ta kashemu, I don't think ko hot water ma ta iya boiling, she has been grounded like this for years ba tun bayan JSS2" tunda take magananan yake kallonta don shi mugun dan gayu ne dan boko yaron dan gata dan masu kudi wani irin tabe baki yayi yace "you people are being sarcastic, young innocent preety girl zaku kulle haka agida sabida she's different kamanninta daban that's illiteracy, gatanan so pretty my lord, her body is so soft, ga gashi, just look at her snatch waist, ka auri wanan ai zaka more rayuwa da itane kasha miya kasha miya harka gaji" murmushin yake tayi tace "common Muhsin mubar maganan yar Aljanun nan" mikewa tsaye yayi yace "I'm being serious ni, wai kinzaci wasanake, wlh naganta inaso nafasa aurenki, bari naje nasanar da Dad, this ur beautiful sister nakeso wlh ita zan aura, gata so young daga gani batafi 20 ba" tashi tayi dasauri kirjinta na bugawa uku uku dan arayuwanta tana bala'in mahaukacin son Muhsin kaman zata haukace, yarone ga kudi ga gata ga kyau, dawani irin sauri takama hannunshi tarike tace "please Muhsin inma wasa kakemin this joke is way too expensive, bikinmu duka duka baifi 1month bafa saikace kafasa aurena kanwata kakeso daga ganinta yanzun nan don't you see what's going on abinda yasa ake cewa ita yar aljanune, minti nawa da ganinta har kaji kana sonta u are willing to risk our relationship damuka raina for years when we are finally about to get married, dan Allah karkamin haka, kataimakama rayuwana Muhsin kasan yanda nake sonka please Baby" fizge hannunshi yayi yace "stop talking nonsense, wlh bazan aureki ba kinjima na rantse, ni Du'a nakeso ita zan aura" yajuya zai tafi dawani irin sauri tasha gabanshi ta zube ta hanyar kneeling down tahade hannayenta tana kuka tace "please stop saying kanwata zaka aura, please stop saying that, wlh karabu dani zan iya mutuwa Allah kuwa Muhsin dan Allah karkamin haka, you know how much u mean to me eh, me zakayi da ita? babu abinda banfitaba kawai saidai ta nunamin haske" zaro ido yayi yace "what! are you crazy, karki kara comparing kanki da yarinyar nan dan wlh tafiki komi, nima daman zan aureki ne because u are full dan banson mace ramamma, kinada big boobs da ass you know that's what I like, but damn!!!! Du'a shape is bura'uba! her shape is life threatening, idan bansami yarinyar nan namore rayuwa da itaba I can die, ke kinga ass da boobs wane naki, see maddd flat tummy, see snatched waist, I don't think kugunta yakai 10, ke abeg go gefe we are talking about Kim Kardashian anan danko Kim taga Du'a she go run go hide" dasauri tashiga hade hannayenta zatai magana hankadeta yayi yabita gefenta yawuce yace "saikuma kiyi bayan nagama rantsuwa cewa bazan aureki ba kome zakiyi saidai kuma kiyi ni kanwarki nakeso wlh, am off zanturo Dad anjima da night" yana maganan yay gaba zuwa compound dinsu yaje yashige hadaddiyar jeep dinshi mai gadi yabudemai gate yawuce yafita abinshi.
Takai morethan 15min awajen kuka take sanan wani irin zuciya yadibeta ta tashi tai ciki ta kofan kitchen tabi Mami na kitchen tana kwashe abinci amman ko kallonsu batayiba tana kuka tawuce fuuu ta tafi falo tashiga Mum dake zaune tareda Hawwa suna magana ne sukaga shigowan Nana tana kuka sosai bamata luradasuba tai hanyar stairs dasauri Mum tamike tace "Nana ke lafiya gani nan anan, menene kike kuka haka"? dawani irin sauri tajuyo tadawo batai wata wataba tafada jikin Mum tazube sai kuka, daga Mum har Hawwa rudewa sukayi, Hawwa tace "Ya Nana menene fada kukayi da Muhsin ne" cikin kuka sosai tace "Mum Muhsin yace yafasa aurena wai Du'a zai aura" chak Mami datafito rikeda kula ta ijiye kan dinning ta tsaya dubus awajen tana mamakin mekuma yakawo sunan Du'a a zancen su. Mum dama tarude sabida yanda yarinyar ke kuka tace "Du'a kuma, ta ina Muhsin yasan wata Du'a dahar zaice miki zai aureta iyye, kinsan mekike fadi kuwa"? Mum tai tambayan sounding so confuse and shocked dan batagane kan zancen yartataba, cikin kuka sosai Nana tace "Mum bayan nadauki zobo naje kaimai ajikinshi naga Du'a suna hira haryanama tabamata gashi taciremai dankwali, kuma idan karya nayi kije garden tama barmai dankwalin ta har novel dinta awajen ma" cikin wani irin mugun zuciya jikin Mum har kyarma yake tashiga kwalama Du'a kira.
"Du'a! Du'a!!! ki sauko kasan nan dakanki kafin nazo dakin nan wlh dan na lahira zai fiki jin dadi" bude kofa tayi ahankali tashiga saukowa idanunta sunyija sabida kuka tashiga saukowa daga stairs hada ido tayida Mami dake tsaye a dinning tana kallonta kaman yanda itama take kallon Mami, kasa karasa saukowa tayi Mum tace "zaman lafiyanki shine ki amsa tambayan dazan miki batare dakinmin karyaba inba hakaba yau saina kusan nakasaki wlh, kin sauka kasa ko baki sauka kasaba"? kama jikin skirt din lace dinta tayi gam gam tsabagen tsoro tana kallon Mami tsabagen tsoro sanan ta kalli Mum tace "bayan nai salla shine ta window na leka naga su Aneela nawasa a compound shine nasaci hanya ta kitchen nafita, to naji muryanku a kitchen shine na kwasa da gudu sabida kada ku ganni wlh wlh ni bansan da mutum a garden ba tuntube nayi dashi zan fadi shine yataroni" fashewa da kuka tasakeyi sosai tace "wlh wlh ni banma sanshi ba Allah kuwan Mum"
Cikin wani irin bakin zuciya Nana tai inda take a stairs wani irin finciko gaban riganta tayi ta chakumeta tace "karya kike baki sanshi ba, kinji ina waya dashi jiya da daddare munyi zaizo yau saisa yau harda cin kwalliya haka sabida ki kwacemin wanda zan aura ko, baki sanshi ba ubanme mikikeyi ajikinshi"? Cikin kuka sosai tace "wlh Ya Nana niban shiga jikinshi ba hannuna yarike kuma inata kokarin na kwace yaki sakina, shine yazo zai tabamin gash......" wani irin kishine ya kwashi Nana tawani kaimata mugun duka abaki bata cire hannu ba sai jini bakinta tasake fashewa da kuka, kimarta Nana tashiga yi baji bagani Mum tace "yima shegiyar yar Aljanun mugun duka Nana, yimata jina jina, itada uwarta sunga kinyi miji daga gidan arziki shine aka turata tayomiki kwace tarabaki dashi, duniya inhar baka mutuba baka gama ganin abin kallo ba, kimeta da kyau kyan datake takama dashi ki chanza mata halitta" yanda Nana ke dukanta tana bubbugata da kome tasamu yasa tafara ihu tana mika hannu tana kwalama Mami kira dan bata iya fadaba bamatasan yanda zata fara dukan yartaba kwata kwata, ahankali Mami tajuya tacigaba da arranging dinning table din datake, kannensu dake wasa ihun dasukaji yasa duk suka shigo ciki suka cika falon, Aneela tafashe da kuka sosai ganin yanda ake dukan yayarta.
Juyawa Mum tayi takalli dining ganin Mami tajuya tacigaba da arranging dinning abinta yasa tai wani irin murmushin mugunta tace "barka mata shegen rigan nan dataje tana kokarin kwacemiki miji dashi kannenta suganta taji kunyan duniya" wani irin bugata da tiles Nana tayi jikake kum Nana tawani juyarda ita tawani yage zip din riganta tanajan rigan zata ciremata, rike rigantayi tana kuka sosai tace "Ya Nana yakuri, Mamiii" tasake kwalama Mami kira dan mugun kunya take aganta, Mum da ranta fess dan tadade tanason gumama Mami amman tarasa ta yanda zatayi saiyau Allah yabata dalili mai kyau tace "fizge rigan duniya da kannenta suga abinda take boyewa, haka akema yan iskan yara masu son kacema yayyinsu mazajen dazasu aura, fizge rigan kannenta suga nonuwan marasa fasali" fizge rigan Nana tayi tayar Mum tace "yara ku kalleta kumata woyiiii" su Muhammad sukahau woyiiii dan basusan meke faruwaba yarane, throw pillow kan kujera taja takankame tana boye kirjinta, Nana tawani sake dauketa da mari tahau ruwan cikinta tana nausa daidai lokacin Abba da Hamad suka shigo dakin, shiru yaran dake woyi sukayi jikake dakin kaman andauke wuta sai muryan Du'a da baima fitowa da kyau tana kiran Mami Mami take, awani irin zuciye Abba yay wajen wani irin dago Nana yayi tsaye sanan yakai mata lafiyayyen mari Pau!!!!!!
Dasauri Mum tace "idan duka zakayi Alhaji ni zaka daka danni nasa Nana tama shegiyan makiran yarinyar nan duka tacire mata riga kannenta sumata ihu" wani irin kallon Mum yake kafin yabi kowana dakin one by one da kallo sanan idanunshi suka sauka kan Mami dake dining tana arranging kula cikin kakkausan murya yace "Zainab kina nan wajen kina tsaye zasu kashe Du'a can't you intervene, wani irin banzan hali ne wanan" juyowa tayi takalli Abba idanunta sunyi ja sosai cike da tsananin kunci tace "Dadyn Hamad mekakeso nayi eh? mekakeso nayi? Ya zanyi da raina?Tun ranan dana tsugunna na haifo wanan yarinyar duniya nake shiga bala'i kala kala? Babu kalan shairin da ba'a yimin ba kan haifo yarinyar nan, tunda na haifi Du'a ban kara samin kwanciyan hankali ba, kome yasameta ita tajama kanta kahanata fita waje ubanme yakaita garden? Gasu gatanan idan suka kasheta kaga kowama yahuta daman tun ranan dana haifota tazamema kowa kashi a wuya ankasa taunata, ankasa fitoda ita, ankasa hadiyeta, nima nagaji I am tired of everything, I'm tired" kawai saiga kuka yazo mata dasauri tabar dinning din tawuce sama tabude dakinta tashiga abinta.
Juyoda kanshi Abba yayi yakalli Mum da Nana dake kuka itama yace "kuwuce kuje kujirani adakina" wucewa sukayi sama, sanan ya kalli yaran yawani daka musu tsawa yace "to your room dukan ku" dasauri kowa na falon ya watse, Abba yajuyo yakalli Hamad yanunamai riganta yace "bani riganta" wucewa yayi yadauko rigan shikuma Abba ya tsugunna yatallabota zuwa jikinshi yana kallon fuskanta yanda goshinta ya kumbura ga bakinta jini, gefen fuskanta yay ja sosai, bashi rigan Hamad yayi Abba ya karba sanan yakama hannunta yasamata rigan kafin yarufe mata kirjinta dashi sanan yaja throw pillow data rufe kanta dashi ya yar sanan yasamata dayan hannun rigan yadagota zai saka mata zip tafashe dawani wahalallen kuka sosai ahankali Abba yace "ina ke miki ciwo"? Cikinta ta nunamai, daga riganta yayi yakalli cikin ga alamun naushi nan duk sunyi jajja, Hamad dake tsaye kansu yace "Abba bazamu kaita hospital ba kuwa what if tanada internal bleeding" girgiza mai kai Abba yayi yace "get me a towel and hot water da rob" wucewan kitchen yayi dasauri yakawo ruwan zafi da towel.
Karba towel din Abba yayi sanan yasa a ruwan zafi yaciro yadaura kan cikinta yana matsamata fashewa da mugun kuka tayi tarike Abba tace "wayyo Abba zafi, Abbbaaaa" sosai ran Abba yabaci kuma yay alkawari saiya mugun sabamata, tun tana kuka yana fitowa harya dena saidai hawaye, saida yagasa harda goshinta da bakinta sanan yashafa mata rub din tass, sanan yakalli Hamad yace "kaje phamarcy and get drugs for her she can't go to hospital" gyadamaikai Hamad yayi sanan yawuce yafita shikuma Abba yatashi daukanta yayi tana jikinshi dantamayi bacci kwantar da ita yayi kan gadonta sanan yasa bargo ya lullubeta