Showing 21001 words to 24000 words out of 153675 words

Chapter 8 - Kyawuna Jarabta Ta Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

15 Dec 2024

599

yau anfito waje" juyoda kanta tayi takalleshi washemai baki tayi tana murmushin nan mai tafiyar da imanin mutum tace "Ya Hamad rabon dana fito waje wlh harna manta nafi shekaru" murmushi yamata yace "this is a chance da Allah yabaki, remember abinda nafada miki duk wanda yadogara ga Allah to Allah ya isar masa, cikin sauki tashi daya Allah yacireki daga kuncin gidan mu, so babu abinda yagagari Allah muddin ki kayi imani, just always thank Allah kinji and be a good girl" gyadamaikai tayi kaman mai tunani tace "Ya Hamad nifa nama manta kamannin Maman Mami fa Grandma, tun ina karama da Mami ta taba zuwa dani ban kara zuwa ba, saidai muyi magana awaya, su Aneela ne suka santa" dan murmushi yayi hankalinshi nakan hanya yace "grandma dinki is one of the nicest person I know in this world, tanada kirki gatada son mutane, duk naje Abuja sainaje na gaidata, you are so lucky to have her as grandmother" shiru Du'a tayi kaman tana tunanin maganan shi saikuma chan ta kalleshi tace "Ya Hamad maisa kai u are different agidan mu? baka biyema su Mum da Ya Nana, kafisu kirki duka" yana kallon hanya still yace "let's say sabida ni namiji ne I see life differently daga yanda mata keganin life, and Abba yabani tarbiyan da nakan iya banbance right from wrong" murmushi tayi takalli kulan kan cinyarta tashiga budewa name ne soyayye da Irish da plantain. "bani nama naci" turo baki tayi tadauko nama daya takai tasamai akan hannunshi dayake bata, murmushi yayi ya wurga abaki yana taunawa yace "wow girkin Mami always taste different" nama daya itama ta dauka tamaida kulan tarufe sanan tahauci tanamai hira kadan kadan harta cinye sai bacci, kallonta yayi ganin yanda take bacci yasa yay murmushi gabgarawa gefen hanya yayi yay parking Sana yadan taso yasaukar mata da kujeran sanan yakoma mazaunin shi yatada motan yana bata wuta.



Wuraren 1 suka kai Abuja, tadata yayi ta hanyar kiran sunanta. "Du'a, Du'a" bude idanunta tayi kadan, hararanta yayi yace "duk uban baccin dakikayi jiya bai isheki ba yarinya saison bacci" tashi tayi yace "gyara kujeran" gyara kujeran tayi yataso sanan takalli hanya yace "kinga yanda Abuja keda kyau kalli titi ba irin na Kanon Kuba" murmushi tayi tace "mun kuwa kaiwa gidan" gyadamata kai yayi yace "takirani yafi sau uku duk kina bacci" shiru tayi tana kallon ko'ina kaman zata hadiye garin da idanunta saiwani irin sanyi da shauki takeji har sukakai wani estate mai suna Presidential Estate. zaro ido tayi tana kara kallon ko'ina ganin gidaje masu suna gidaje ba muna gidaje ba, tasha ji idan su Mum na gulman su tana yawan cewa ai Abba sabida ya rainata yar gidan masu kudi yaje ya auro mata, itama yarinyar kaman mayya itace kawai ta auri talaka mahaifiyarta tabarta ne sabida ita kadaice yarta mace, ita bazata iya tuna gidan dasuke zuwa a dan memory dinta na Grandma sonta lokacin tana yarinya akazo kuma aka dena zuwa da ita saidai su Aneela da Muhammad da Mudasir.


Shiga Estate din yayi yana tafiya ahankali ganin yanda Du'a is enjoying the view din, agaban wani lafiyayyen gida Hamad yay horn, wani security yafito ganin Hamad yasa yace "barka da zuwa yallabai Hajiya ta sanar dani zuwanka" gyadamai mai kai Hamad yayi yana murmushi shikuma yakoma ciki yabude musu Gate din, Jan motar ciki yayi Du'a ta kwalalo idanu tace "nan ne gidan Grandma Ya Hamad" murmushi kawai yamata yana karasa parking motansu acikin jerin motocin dakenan gidan wanda babu mate din seinna su, bude motan yayi yafito sanan yamata alamu data fito gyadamai kai tayi daidai security yagama kulle gate yazo yace "akwai akwati ne Yallabai" "oh yeah" Hamad yafadi yana budemai booth daidai lokacin Du'a takaraso wajen tsayawa chak security yayi yana kallonta ganin haka yasa Hamad yace "ga akwatin" dasauri yajuyo yakalli Hamad hannu yasa yadauki akwatin yawuce Hamad kuma yarufe booth din yajuyo daidai lokacin wata hadaddiyar mata wacce kana ganinta kasan ba yarinya bace dan ta ijiye jikoki tafito, tana sanye da bubun atampa ajikinta gatanan black beauty da akalla zatakai 70.


"oyoyo oyoyo, su maigida an iso" jin muryanta yasa dasauri Hamad yajuya washe baki yayi yace "Hajiya wanan kwalliya haka, bazaki barma yara ba" dakuwa tamai tace "kaci gidanku, yanzu dani dasu idan akaje gasan kyau basai akwasheni sau dari baza'a kwashe suba" karasawa yayi har inda take sanan cikeda girmamawa yadan runtsuna yace "ina yini Hajiya" hannu tasa tashafa kanshi tace "kasha hanya Soja na maigida, jekai wanka kahuta kaida komawa kano sai gobe" tai maganan tana kallon Du'a dake bayan Hamad kanta akasa tana wasa da hijabinta kunya yahanata dago kai. "Du'a" matar takirata ahankali, ahankali Du'a kaman wacce ke tsoro tadago kanta takalli kakanta fess tagane ta danga kamanninta da Mami nan, black beauty abinta yar gayu, ganin takasa magana yasa dasauri tabude mata hannu tace "zonan zoki rungumeni, taho taho" ahankali Du'a taje dasauri tashige jikinta takankameta kankameta Hajiya tayi tace "Alhamdulillah Alhamdulillah, Du'a sannu, sannu kinji, akwai abinda ke miki ciwo"?girgizamai kakan nata kai tayi, dagota Hajiya tayi tasa hannu tai cupping face nata tana kallonta kaman yanda Du'a me kallonta ahankali rasama mezatama yarinyar tayi hakan yasa ta manna mata kiss a goshi sanan takama hannunta tarike tace "muje nakaiki dakinki kiyi wanka"


Ciki tashiga da Du'a falon wani irin hadadden gaske gashinan Duplex sai yan aiki guda biyu dataga suna gyara dinning suna ganin Du'a duk suka bitada kallo suna gaidata. "welcome Du'a" murmushi Hajiya tayi tace "kingan su suke tayani aikace aikacen gida, wanan sunanta Shema'u, dayan kuma sunanta Razika, duk sun sanki, jeki musu sallama" gabansu taje ahankali sai kallonta suke kaman basu taba ganin mutum ba, hannu tamika musu cikin muryanta mai dadi tace "Assalamu Alaykum, nice to meet you" dasauri suka karbi hannunta suna murmushi Razika tace "you are so beautiful" tsayawa tayi turus tana kallonsu Hajiya dake kallonsu tace "tell them thank u sunce kinada kyau" ahankali tace "thank u" sakinta sukayi itakuma Hajiya tasauke ijiyan zuciya sanan tace "taho mutafi" dasauri tajuyo kaman jira take dama stairs sukayi sukai sama saitaga ashema kasan baida kyau wani daki tabude dakin mai kyau sosai saiga hoton ta datana yarinya tana rarrafe kusada Hajiyan dasauri tashiga dakin tana kallon hoton, murmushi Hajiya tayi tace "lokacin kina yar tatsitsiya keda Mamanki kunzl ganin gida, little Du'a, jeki yi wanka kizo kici abinci zan baki labarin anjima" gyadamata kai tayi sanan tacire hijabi ahankali tawuce zuwa kofan datagani wanda ta tabbata bathroom ne saida tashiga sanan Hajiya tafita daga dakin.


Saida tayi wanka sanan tafito daure da towel,
akwatin ta dataga anshigo dashi tabude tadauki wata doguwan riga wanda yawanci kayanta dogayen riguna ne daidaikune riga da skirt, saka rigan tayi sky blue ce mai kyau sanan tasaka hijabi salla tayi sanan tazauna tana tunanin maganan Hajiya datace tasauko, tashi tayi ahankali tacire hijabinta ta ijiye sanan tabude kofa tafito, ahankali take sauka daga stairs tana karabin gidan da kallo, daga sama sama takejin maganan Hajiya da Hamad saikuma takarasa suna ganinta sukai shiru. "kin idar tahonan" tauna mata kusada ita akan dinning hakan yasa ta taho zama tayi wajen Hajiya tace "debi abincin ki kici" dasauri Hamad yace "kafin namanta banfada mikiba kuran nama tazo gidan nan ba" turo baki tayi Hajiya ta harareshi tace "karkaga kana maigida kanemi samin jika kuka sama zamu hau nidakai, ci abinci ki kinji kome kikeso" gyadama Hajiya kai tayi sanan tadebi rice da stew da plantain da fish tanaci, bini bini Hajiya ke kallonta hartaci rabin abincin sanan tasha ruwa haka



💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫


✍️M SHAKUR

EPISODE 1️⃣3️⃣
Har dare hira suke Hajiya da Hamad, kagansu zaka dauka Hamad jikan ta ne, Hajiya wata irin mace da idan kana tareda ita you have no reason or what so ever to hate her ne, kodan sabida yaranta biyu kachal aduniya saisa takeda son mutane haka oho, danta na farko yaranshi uku dukansu Maza kuma kanana dan Mami tariga shi aure yana UK achan yake aiki sai Mami dakeda yara hudu tana aure a kano, Bayan Mami ta haifi wata tarasu, Hajiya is very very educated, lawyer ce babban gaske amman yanzu tai retire saidai she's still an advocate na Human right, batun yauba taso tadauki Du'a, akwai lokacin data kusan kulle Maman Abba wato Kaka, sabida kukan da Mami tamata ne tana rokonta yasa tahakura daga lokacin tai fushi da Mami ta shareta, saisa koda wasa bata taba taka kafarta agidan Abba ba dan batada daukan nonsense and zasuga yanda zata maida yarinyar nan, Du'a tariga tabar gidan nan kenan har abada saidai in bata raye.


Ganin Du'a na gyangyadi akan kujera yasa ta tadata. "Du'a Du'a tashi kije ki kwanta adaki" ahankali ta tashi murya chan kasa tace "saida safe Grandma" murmushi tamata tace "kiyi alwala sanan kiyi addu'a kafin ki kwanta kinji" gyadamata kai tayi sanan tawuce, dakinta tabude tashiga tamaida kofan tarufe, bayi tashiga tadauro alwala kaman yanda aka umurceta sanan tafito, fadawa kan gadon tayi tana karanto addu'an bacci sanan taja bargo ta lulluba tana rufe ido fuskan mutumin nan tagani yay flashing a idanunta dasauri tabude idanunta tana yaye bargon tafito da kanta waje tanabin dakin da kallo, mutumin daya ciro ta daga rijiya she just saw fuskanshi, lumshe ido tayi ahankali still tana ganinshi saikuma ta girgixa kanta kaman tana kokarin koran abin dan bataso tana ganinshi, ahaka bacci yay awon gaba da ita......


Hajiya tashigo dakin da asuba ganin wutan dakin A kunne, karasawa gaban gadon tayi, zama tayi atabaki bakin gadon tana kallon fuskanta, Du'a is just different! ahankali takai hannunta ta kwashe gashin daya sauka a gefen fuskanta, shafa gefen fuskanta tayi tana kiranta ahankali. "Du'a, Du'a atashi daga bacci asuba tayi" bude idanunta tayi ganin kakanta yasa taji kunya murmushi tayi dasauri Hajiya tace "na tabbata yau zata yalwatu da ni'ima a gareni, wanan kayataccen murmushi dakika gaisheni dashi Du'a, Masha Allah jikata is very beautiful, barakallahu fiki, tashi kiyi alwala kizo kiyi salla kifito kuyi sallama da Hamad yashirya zai tafi" gyadamata kai tayi Sanna tasauka daga gadon ahankali bathroom tashiga itakuma Hajiya tawuce tafita.


Saida tai salla sanan tafito sanye da hijabi, a falo tagansu suna zaune Hamad na rike da mug yanashan coffee, karasowa tayi ta tsugunna ahankali tace "ina kwana Grandma" "kintashi lpy Du'a ya kwanan Abuja" murmushi tayi tace "I love here Grandma, Ya Hamad good morning" "morning dama ke nake jira zantafi" yatashi bayan ya ijiye cup dinshi, Hajiya tace "sa takalmin ki kiraka yayanki" tashi tayi tasaka slippers din da Hajiya ke nuna mata sanan tabi bayan Hamad suka fita daga falon sauka suke daga matattakala kaman daga sama yace "ya akayi kika fada rijiya Du'a" dawani irin sauri takalleshi ta tsaya batare data cigaba da tafiya ba hakan yasa shima ya tsaya yana kallonta yace "answer me" murya chan kasa tace "Muhsin din Ya Nana ne yazo" dawani irin sauri cikeda mamaki yace "Muhsin"gyadamai kai tayi tabashi labarin komi iya wanda tasani, shiru yayi saikawai yay kwafa yace "muje" binshi tayi harwajen mota, sanan ya tsaya yace "be a good girl kinji, kinga yanda rayuwanki take kasancewa awajena maza so be careful kinji" gyadamai kai tayi shafa gefen fuskanta yayi yace "wuce ki koma ciki bye" waving hannu tamai tawuce shikuma yashiga mota yatada yabar gidan bayan security yabudemai gate.




Ahankali da sallama tabude falonsu tashiga, Hajiya na zaune kan kujera tanacin fruits dake cikin bowl akan cinyanta, ganin Du'a ta shigo yasa tanuna mata gefenta tace "zoki zauna anan Du'a" murmushi tayi takaraso wajen tazauna, bowl din tanuna mata tace "zaki sha fruits"? gizgiza mata kai tayi tace "na koshi" murmushi tamata tace "karki damu nariga namiki friends sunje kano ne but maybe tsakanin yau ko gobe zasu dawo zaki gansu yanmata kaman ke zadan su girma miki but I'm sure u will like them" murmushi tayi tace "thank you Grandma" murmushi tamata sanan tace "yanzu abinda ke mind dina is school, banso kishiga secondary school dan kinyi girma saidai lessons, koda wasa bazakiyi rayuwan kullen nan dakikayi agidan ubanki ba, don't worry I will think of what to do akanki, yanzu dai zansa driver na yadauke ki Razika zata biki kije saloon ama gashin nan lafiyayyen gyara ko amiki kalba ko kitso duk wanda kikeso, sanan amiki gyaran farce right" gyadamai mata kai tayi tana murmushi, Murmushi itama Hajiya tayi tace "answer da naki stop nodding head be acting like a big girl okay" murmushi tayi sosai wanan karan tace "okay Grandma" "good girl, jeki shirya kiduba wardrobe dinki akwai kaya awajen kisa daga nan" harzata gyadamata kai saida sauri tace "Tom" wuce wa sama tayi Grandma tabita da kallo harta bace mata.



Wardrobe din dakin tabude hadaddun karyane wanda mostly abaya ne, dogayen riguna kala kala daban daban, ahankali tadaura hannunta kan wani baki fitodashi tayi daga leda tana kallon rigan kaman Grandma ta aunata shiryawa tayi cikin rigan saikuma dagudu tai wajen madubi tana kallon kanta yanda taga tayi kyau ko Nana su bata taba ganin tasaka doguwan riga mai tsada nan ba, murmushi tayi tadaura dan kwalin saman tadauki hijabinta akai tasaka tafito tasauko kasa Hajiya na ganinta tace "ina gyalen abayan Du'a" dasauri tace "nadaura akai Grandma" dan dariya Hajiya tayi saikuma ta mike tace "zokiga" karasowa gabanta tayi Hajiya ta yaye hijabin dan kwalin ta warware sanan ta gyaramata parking gashin, takalli Razika dake wajen tace "he daukomata handbag a dakinta Razika" da sauri tai sama, taimata rolling gyalen saitai kaman wata balarabiya, saukowa Razika tayi da jaka mai kyau, Hajiya ya karba tabata tace "perfect oya kutafi to driver na waje yana jiranku" takalli Razika tace "stay by her side, saikun dawo, bye Du'a" juyowa Du'a tayi tamata waving hannu alamun bye sanan suka wuce suka fita sai murna take basabamba, mota suka shiga direban yajasu.






💫 KYAWUNA JARABTA TA 💫


✍️ M SHAKUR

Free page
EPISODE 1️⃣4️⃣
Bini bini direban Hajiya dake sanye da uniform ke kallonta tamadubi, hakan yasa Razika takalleta, ganin yanda take kalle kallen hanya tana murmushin nan dake karamata wani kalan kyau nadaban yasa Razika tace "is this ur first time a Abuja Du'a?" juyowa tayi tazubama Razika mayun idanunta dakesa mutum yaji wani kwanciyan hankali harzata gyadamata kai ta tuna maganan Hajiya hakan yasa tace "eh" murmushi sosai Razika tayi tace "Abuja ai nada kyau, nima Hajiya tadaukoni daga kauyen mu takawo ni nan, sanan akwai lesson teacher dake zuwa mana karatu duk asabar da lahadi, Hajiya nason yara, kinga tunda nake a Abuja bantaba ganin yarinya mai kyau kaman keba" dan murmushi tayi saikuma tadauke kanta tamaidashi kan titi tana kallon motoci dan kunya takeji taji ance tanada kyau bamataso adinga cemata haka, ahankali tace "thank you" "yauwa munkawo" Razika tafadi ganin driver yay kwana yashiga wani babban Plaza, parking yayi hakan yasa Razika tace "sauka muje" bude kofa tayi ahankali tafito tana kallon wajen yanda akwai mutane kowa na shiga da fita abinshi, ko yanda takebin mutanen datake gani da kallo ne yasa taga suna kallonta itama oho dasauri tarike hannun Razika gam data fito tace "muje" tana rikeda hannun Razika suka wuce suka shiga wani hadadden saloon dake nan first floor, ma'aikatan suka taso suna gaidasu kafin Razika tamusu bayanin me za'amata nan aka shiga yi mata gyaran gashin.


"inje insiyomana ice cream a wanchan shagon Du'a" ta tambayi Du'a da ake wankema gashi, murya chan kasa tace "eh" tashi Razika tayi tafice daga saloon din daidai angama wanke ma Du'a tulin gashin aka nannade mata gashin da towel matar tace "tashi muje dryer" tashi tsaye tayi tawuce taje tazauna ana sliding kofan saloon din aka shigo, juyowa tayida sauri tazaci Razika ce, wani Alhaji tagani yaci babban riga milk na shadda dake kyalli da akalla zaikai 60yrs baki dashi mai kyau ga gemu kadan tareda wata mata kana ganinta kaga yar duniya ga hujin hanci akan hancinta guda uku tana rikeda jaka tana taunan cingum tana sanye dawasu kaya dabasu da maraba da babu ajikinta, suna shigowa masu aikin suka taresu. "welcome Alhaji, welcome Hajiya" gyadamusu kai yayi yanabin matan saloon din da kallo one by one, zama matar dake taredashi tayi kan kujera tawani kamo hannunshi ganin ba ita yake kalloba da sauri yajuyo yakalleta jinta kamamai hannu, kashemaai idanu tayi tace "Baby kagaya musu style din da za'a min" washe baki yayi yace "kai wlh mata kun iya rigima yanzu style ne sai an tambayani, ninasan kan style ne" kallon yar aikin dake gabansu yayi wacce ke jiran bayanin su kafin sufara aiki yadan lashe baki sanan yace "okay bari muga" juyawa yayi yacigaba da kallon yan shagon, Du'a yanuna da akema rolling gashinta a roller za'a sata a dryer yace "how about that fine baby style, Zinariya kinason style din"? yamata tambayan still yana kallon Du'a da akema gyaran gashi wacce ko kallonsu ma batayiba madubi take kallo tana kallon abinda ake mata akai wanda is new to her tabama kofa baya, ganin inda yake kallo yasa Zinariya tace "katafi meeting din dakake dashi Sweet, idan kagama saika biyo kadaukeni" tai maganan tana shafamai hannunshi still datake rikedashi, dan juyowa yayi yakalleta kaman wanda ya manta da abinda ke gabanshi yace "ohh meeting dinan, to,to bari inje, saina dawo" yay maganan yana juyawa bude kofan yayi harzai fita saikuma yadawo dasauri yawuce wajen kujeran Du'a ya tsaya tagaban wajen yana facing nata directly yakare madubin datake kallo yana murmushi yana kallonta kaman yanda takedan kallonshi atsorace yace "nace nawane kudin gyaran kan Zinariya"? Ya tambayi mai gyaran kan Du'a yana kallon Du'a kaman wani tsohon maye wanda baitaba ganin mace ba sai akan Du'a, Mai gyaran gashin Du'a dake kallonshi ne itama cikeda girmamawa tace "all payments are done to Christy Alhaji gatachan the cashier" tanunamai wacce ketare da Zinariyan shi data daure fuska tana kallonshi, yana kallon Du'a still yace "in that case ba matsala, by the way young lady ur hair is beautiful" yama Du'a magana yana wani kalan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login