Showing 1 words to 3000 words out of 104589 words
Tambuwal:; December, 21
A Jikinta ya manna kanshi da cikinta kana kuma ya cusa fuskarshi acikin jikin nata.
Tare dasa hannunshi na dama ya damƙe mararshi.
Gaba ɗaya jikinshi rawa yakeyi tamkar mazari, wani irin ciwo cikinnasa keyi masa, wanda har hakan yasa numfashinsa, ke kokarin kwacewa.
Hannunshi na hagu yasa abayanta ya zagayeta, tare da riƙe ta gam-gam cikin gigitan ciwo da fitan hayyaci.
Hakan kuwa yayi masifar gigita Jannart, wanda gaba daya jikinta ya d’auki rawa, kamar yadda nashi jikin ke rawa.
Kana ya kwakumeta ya kanainayeta ya hanata ƙwaƙƙwaran motsi.
Jannart kuwa Ganin hakan yasa cikin firgici ta buɗe baki, murya na rawa ta fara cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun Mamy! Mamy!! Mamy!!! Kalli yadda yakeyi fa!!!!”.
Yayinda ita kuwa Mamy cikin tsananin tashin hankali da kidima, ta fara juyawa tsakiyar falon cikin rashin sanin abinyi taketa rabkawa Ramadan kira.
“Ramadan! Ramadan!!! Kazo!!! Rayyern ba lfy”.
Dr. Sulaiman ne wanda shi ya dawo da Rayyern din, ya turo ƙofar da hanzari,
baishigo da wuri bane kuma, saboda ya tsaya fadawa Baba Mauɗo cewar ciwon Rayyern ne ya tashi.
A hanzarce ya faɗo cikin falon,
Baba Mauɗo na biye dashi a baya.
Yayinda sukabar Hadi da Ari mai gadi kuwa tsaye a harabar gidan, sunyi jugum-jugum domin duk mai imani, muddin yasan yadda ciwon Rayyern ke yi in ya tashi tamkar zai tafi da ransa to tabbas zai cika da fargaba.
Hakan ne ma yasa Hadi zaro wayarshi ya kira Abba, yana ɗagawa cikin yanayin tashin hankali yace.
“Alhaji jikin Rayyern fa ya tashi”.
Cikin kidima Abba ya kalli mutanen da yake tare dasu tare da miƙewa tsaye yace.
“Rayyern ba lfy”.
Yana faɗin haka ya fita daga falon da bisa alamu duk mgnar sirri yakeyi.
Yana katse kiran Hadi ya kira Ramadan yana ɗagawa yace.
“Kai Ramadan kana ina”.
Da sauri yace.
“Abba ina Minjibir ne. Lfy kuwa?”.
Cikin bada umarni da tashin hankali yace.
“Maza ka wuce kayi gida yau kuma cikin Rayyern ya tashi”.
Cikin tsananin tashin hankali Ramadan ya mike tare, da barin duk wani abu da yakeyi, hankalinsa amatukar tashe yace.
“innalillahi wa innailaihi rajiun! Jikin Hamma Rayyern ya tashi? Yanzu Abba Hamma Rayyern din yana ina?”
Abba dake tsaye, cikin alhini da fargaba yace.
“Yana gida, kayi sauri kaje.”
Yana gama fad’in haka ya katse kiran.
Kana yaci gaba da tuƙin da yakeyi.
Shi kuwa Ramadan a kidime ya kalli Riyyam-nsra dake cewa.
“Hamma Ramadan meya faru”.
Ya ƙare .mgnar yana firfito da idanunsa.
Idanu Ramadan din ya rumtse da karfi, cike da alhinin abunda Abban ya gaya masa, ya kamo hannun Riyyam-nsra tare da jansa, suka nufi parking lot, hankalinsa atashe yace.
“Riyyam mu tafi gida yau kuma ciwon cikin Hamma Rayyern ya tashi,
abunda yafi shekara biyu ya kusa shekara uku bai tashi ba, amma yau gashi ya sake tashi mishi.”
“Innalillahi!”
shine abinda Riyyam-nsra ke ta maimaitawa.
Dai-dai lokacin da suka shiga mota.
A 360 Radaman ya figi motar yana cewa.
“Yah Rabbi, Yah Allah ka bawa Hamma na lfy, gaba ɗaya mun sakankance, da cewar ya worke tunda mukaga yayi shekaru bai tashiba”.
A nan gidan kuwa.
Cikin yanayi tashin hankali Mamy ta kamo hannun Dr Sulaiman, a gigice ta jawoshi zuwa gaban Jannart da Rayyern ke kwance kanta, irin kwanciyar nan ta rubda ciki.
Murya na rawa Mamy tace.
“Sulaiman duba min Rayyern yana raye kuwa duba minshi kaga fa baya motsi”.
Ta ƙare mgnar wasu irin masifaffun hawaye na kwaranyo mata.
Yayinda sai a lokacin kuma Jannart ta sunkuyo da kanta, ta zuba mishi ido tabbas kuwa ya daina motsi, duk rawa da karkarwar da jikinshi keyi ya bari.
Wani irin zaro ido tayi tana kallon Mamy dake cewa.
“Innalillahi wa innailaihi rajiun Sulaiman ka duba min Rayyern, kada ya tafi ya barmu akwai nauyinshi da bamu sauke a kanmu ba."
Shi kuwa Dr Sulaiman kamo hannunta yakeyi, yana son zaunar da ita amman ina, gaba daya ta gama gigicewa, ga hawayen dake ta Kwarara acikin Idanunta.
Baba Mauɗo kuwa da sauri ya matso gaban Jannart ya tsuguna, cikin kuma tashin hankali yasa hannunshi, akan wuyan RAYYERN sabida a kife yake, murya na rawa dattijon ya fara kiran sunanshi.
“Rayyern! Rayyern!! RAYYANU!!! Muhammad Muhammadu tashi.
Buɗe idanunka Mauɗona!!!”.
Ya ƙare mgnar hawaye na kwaranyo mishi.
Wanda ganinsu ne kuma yasa hawayen idanun Jannart tsinkowa.
Tausayin tsohon da Mamy ne sukayi masifar raunata mata zuciya.
A fili zaka gano tsananin tashin hankali da kidimar da suke ciki, kana da tsananin sonshi dake cikin kwayar idanunsu.
Shi kuwa Rayyern da yakejin kansa acikin wata duniya, mai dauke da tsananin azaba gami da radadi, sama-sama haka yake jiyo muryarsu.
Saidai kuma bazai taba iya amsawa ba, duk da yana jiyo kiran sunansa da Baba Mauɗo keyi, saidai baya da hakikanin cewa, ko yan siraran labban bakinsa zai iya motsawa, saboda tsananin ciwon da yakeji.
Dr Sulaiman kuwa cikin samar da kwanciyar hankali wa Mamy, ya samu ya ajiyeta bisa kujera kana a hankali yace.
“Mamy Rayyern yana numfashi fa, babu abunda ya samesa, Dan Allah ki kwantar da hankalin ki, Insha Allah zai samu lfy, na mishi allura tun a asibiti, yanzu haka ciwon ya fara lafawa, Insha Allah gaba daya zai daina”.
Dr. Sulaiman din ya kare maganar cikin, kwantar da murya da kuma son samawa Mamyn nutsuwa.
Dai-dai lokacin ne kuma Abba ya shigo.
Da sauri ya iso tsakiyar falon.
Sai kuma ya iso gefen Baba Mauɗo a kidime ya fara kiransa.
“Rayyern”.
Sai kuma ya juyo da sauri jin Dr Sulaiman na cewa.
“Abba dan Allah ku kwantar da hankalinku, ku barshi zuwa anjima kaɗan zai iya amsa muku, nayi masa allura Insha Allah zai samu sauki”.
Wani irin dogon numfashi Abba ya sauke, kana ya koma ya zauna bisa kujerar dake gefensa.
Yayinda Mamy kuwa har yanzu ta gaza tsaida hawayenta.
Gaba daya hankalinta yaki kwanciya, tsoro takeji kada wani abu ya samu Rayyern din, badon komai ba kuwa saidan sanin da tayi, cewar ciwon cikin baya tab’a yi masa da sauki idan ya tashi.
Jannart kuwa da tayi k’asa da kanta, tana jin yadda Rayyern din ke kwakume da ita da masifar ƙarfi, yanayin rikon da yayi mata, dinne kuma yasa kugunta ya soma sarawa, saboda ba wai riko ne na wasa yayi mata ba riƙone na neman mafita.
Ramadan da Riyyam-nsra kuwa kusan a jere da sassarfa suka shigo cikin falon, kowannensu hankalinsa amatukar tashe.
More especially Ramadan da yasan irin yanda ciwon, keyiwa Hamman nasu idan ya tashi.
Da sauri suka nufi kanshi, saidai basu k’arasa ba kuma suka tsaya, saboda ganin su Abba duk suna zaune.
Baba Mauɗo na zubda hawaye, Mamy ma haka kana Jannart da yake kwance lib a cinyarta kamar matacce, itama hawayen take tsiyayarwa.
Abba kuwa habarsa ya tallafe, saidai kallo daya zakayi masa, ka karanto tsananin tashin hankalin dake kwance akan fuskarsa.
Ganin hakanne kuma yasa, zuciyar Ramadan wani irin harbawa, lokaci daya kuma gaba ɗaya jikinsa ya fara tsuman tashin hankali, dan su a zatonsu Rayyern din ya rasu ne.
Cikin wani irin tashin hankali rauni gigita da kuma kidima.
Riyyam-nsra ya saki wani irin raunataccen kuka, tare da zamewa ya zauna aƙasa ya kife kansa bisa sawun Rayyern, cikin rauni murya na rawa kuka na danne abinda yake faɗa yake cewa.
“Innallahi wa innailaihi rajiun Mammy mutuwa zata hanani cika miki burinki,
Wayyoooooooo Allah na Mammy na inama kina kusa kizo kiga halin da tsatsonki yake ciki, Mammy wlh shine wlh sune”.
Su Abba kuwa, tsananin tashin hankalin da suke ciki, yasa gaba ɗaya basa iya fahimtar kalaman Riyyam-nsra, asalima basa jin me yake faɗa da kyau.
Sai dai shi kuwa Rayyern da tunaninsa ke kokarin gushewa, a sama sama yake jiyo kukan yaron, da kuma abinda yake faɗi.
Duk da bawai yana fahimtar kalaman sosai bane, amma yaji wasu daga cikin maganganun, wanda ayanzu baya cikin Lfy da kuma hayyacin da zai iya nazari ko hasashen kalaman.
Dr Sulaiman ne ya matso kusa da Riyyam-nsra, ya jawoshi jikinsa ya zaunar dashi tare da cewa.
“Kai Riyyam-nsra kabar kuka bafa rasuwa yayi ba, ciwon ne ya fara lafawa kaga Abbanku ma yayi shiru”.
Sai alokacin Ramadan ya sauke wani irin numfashin daya, sakar masa da wani nannauyan abu mai kama da dutse daya tsaya a ƙirjinsa.
Sabida gaba ɗaya ya fara rasa numfashin sa.
Shi kuwa Riyyam-nsra cikin kasa danne kukan sa yace.
“Yah Sulaiman, da gaske kake Hamma Rayyern dina, yana numfashi?”.
Kai Dr. Sulaiman ya jinjina, kana cikin sauri yace.
“Eh Riyyam-nsra bai rasuba gashi yana numfashi, nanda y’an mintuna zai tashi insha Allah.”
Ajiyan zuciya suka sauƙe baki ɗayansu.
Sai lokacinne kuma Mamy ta iya tsaida hawayenta.
Yayinda Baba Mauɗo Kuwa sam hawayen shi ya gaza tsayuwa.
Hakan kuwa shi yasa Jannart ta gaza tsaida hawayenta, saboda acikin rayuwar ta akwai rauni sosai, matukar zata ga hawayen Babba, To Lallai zuciyarta saita karye, ba kuma zata iya lallashin kanta ba.
Ganin duk sun d’an nutsu ne kuma yasa, cikin sanyi Dr. Sulaiman ya samu ya zauna, tare da d’go kansa ahankali yayi gyaran murya kana anutse yace.
“Kwata kwata abun bai wuce 30mnt da fara mishi ba, domin tun da ya fara mishi na fahimta, saboda naga yana ta haɗa zufa, kasancewar alokacin muna cikin meeting ne da sauran Doctor's din mu,
Akan wani course da muke son wasu daga cikin Doctor's ɗin namu suje suyi a Mascow,
So dana fahimci cewa, ciwon cikin nasa nason tashi ne, sai na bukaci da mu tashi taron, amma sai yaki bani dama, to kafin mu gama ma abin har ya fara tsanan ta.”
Idanu duk suka tsurawa Dr. Sulaiman din, saboda Jin abunda yake fad’a.
Shikuwa Dr. Sulaeman gyara zamansa yayi, tare da fuskantarsu, cike da son sake samar musu nutsuwa yace.
“Insha Allah Rayyern zaiji sauk’i, domin muna fita a meeting din nayi masa allura, saidai kafun nan ma tuni abin ya gama tashi, shiyasa ya ɗan wahal dashi amman Alhamdulillah, bayan 50mn idan alluran ta fara aiki zai dan ji sauƙi, wanda kuma zuwa yanzu inada yakinin, fara aikin allurar Dan shiyasa ma kukaga yayi shiru jikin ya daina bari.”
Cikin gamsuwa Ramadan da Abba suka gyaɗa kai, saboda wannan bayanine da likitocin suka saba yi musu, sudai fatansu shine samun saukin Rayyern din.
Baba Mauɗo dake zaune kuwa, ahankali yasa hannunshi ya shafa kan Rayyern din zuwa wuyansa.
Kana ya miƙe tsaye.
Tare da sharce hawayen sa.
Cikin tausayawa yace.
“Toh Alhamdulillah Allah ya bashi lfy yasa zakkan jikine, Allah ya daga kafadunsa.”
Ya ƙare mgnar yana nufar hanyar fita.
Cikin sauƙe numfashi Riyyam-nsra da Ramadan suka bishi da ido, da kuma wani kallo mai cike da wani irin so na musamman.
Abba da Mamy kuwa.
Numfashi suka fesar tare da cewa.
“Amin ya Allah baba Mauɗo”.
Shi kuwa Baba Mauɗo yana fita
Hadi da Ari sukayi kanshi, cikin girmamawa da kwarjinin dattijon suka hada baki wurin cewa.
“Allah rene ya jikin nasa?”.
A hankali yace.
“Alhamdulillah jiki da sauƙi.”
“Allah ya kara sauki.”
suka had’a baki wajen fad’a.
Shikuwa Baba Maud’o.
“Amin ya Allah”.
Yace yana mai wucewa cikin ɗan side ɗinsu.
Kai tsaye Bathroom ya wuce al'wala yayi kana yazo.
Ya dauki Kur'ani ya fara karatu wai ko zaiji sanyin zuciyarshi, da wani nauyi daya danne mishi ƙahon zuciyarshi.
Amma ina hakan ya gagara,
Hawaye kuwa tamkar an bude bakin famfo.
Allah ya sani yana jin wani irin azabebben son yaran a zuciyarshi,
Baya son gani ko jin duk wani abu da zai cutar dasu duk kankantarshi da yanada hali da ko kuda bazata sauka kan Rayyern ba.
Da ya dauka kawai dan kyautata mishi da sukeyi ne, kuma dan kasan cewarsu yaran uban gidansa.
Toh amman zuwan Riyyam-nsra yasa ya fahimci, kawai yana son duk wani abinda ya shafesu ne.
Wasu lokutan yakanyi tunanin ko dan kamar da Riyyam-nsra din, yakeyi da Rayyern ne yasa yake masifar sonshi ma din.
Hannun shi ya daga sama yana mai yiwa yaran addu'a.
A nan cikin falon kuwa.
Shiru Jannart tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa.
Yayinda hawayenta keta kwaranya ba ƙaƙƙautawa.
Tana ciwo amman bata taɓa ganin irin wannan tashin hankali a fuskar Daddy, kamar yadda ta gani a fuskar Baba Mauɗo da Abba ba.
Bata taɓa ganin makamancin gigitar da Mamy tayi a fuskar Mom ba.
Duk da tasan mom tana masifar sonta.
Wannan kawai ya isa shaidar son uwa da banne a duniya.
Mamy kuwa numfashi take ta saukewa kawai.
Riyyam-nsra kuwa miƙewa yayi ya haura sama.
Yana shiga kuwa ya kira Mammyn sa.
Abba kuwa cikin sauƙe numfashi ya tallabe haba.
Tare da cewa.
“Ramadan dagashi a kanta.
Sai ka gyara mishi kwanciyarsa”.
Cikin sauri Dr Sulaiman yace.
“A'a Abba barshi shida kanshi zai tashi in allurar ta gama ratsashi.”
Cikin sanyi Mamy tace.
“Ai kuma Jannart din zata gaji”.
Kai ya dan juya tare da cewa.
“Bazai dadeba zai tashi”.
Shiru sukayi.
Kana shi kuma Dr. Sulaiman miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
“Toh Abba ni bari in wuce gida anjima zan dawo.”
“Toh mun gode Dakta”.
Abba ya faɗa yana mai gyara zamanshi.
Shi kuwa Dr Sulaiman Ramadan ya kalla tare da cewa.
“Kasan idan ya tashi zai tashi ba ƙarfi illar alurar kenan, shiyasa ba'a cika son yawaita yiwa mutum itaba.
Zaijishi duk ba ƙarfi, so dole sai an taimaka mishi ka sani”.
Kai Ramadan ya jinjina tare da cewa.
“Eh na sani”.
Daga nan ya sallamesu ya tafi.
Su kuwa, shiru sukayi suka zauna jugum-jugum.
Ganin kuma yamma lokacin daura girki yayine, yasa Mamy miƙewa a hankali ta nufi Kitchen.
Bayan ta cire lallenta ne kuma ta fara aiki.
Ita kuwa Jannart gaba ɗaya ta kasa kwakwaran motsi.
Sabida masifar kunya da nauyin Abba da takeji, kana ga kuma nauyin zaratan namiji dake kanta.
Wanda agaba daya rayuwarta bata taɓa fuskantar makamancin hakan ba ga wani irin masifeffen ƙamshin jikinsa dake narkar da jikinta, tattausan sumar kansa da sajensa ta zuwa idanu.
Yanzu kusan 50 minutes kenan suke a hakan.
Yayinda kuma har yanzu hawayenta ked’an disowa kadan-kadan.
Suna mannewa ajikin gashin idanunta.
Shi kuwa Rayyern dake kwance a hankali ya ɗan ja numfashin wahala tare da fesar dashi.
Kana ya rumtse idanunshi da ƙarfi tare da taune lips ɗinshi, duka biyu saboda so yake ya tashi, amman gaba ɗaya jikinshi daga kugunsa zuwa sawun takawarsa sunyi lakwas.
Wannan abun shiyasa baya son allurar.
Dan muddin akayi mishi ita sai yayi kusan mako guda karfinsa bai dawo dai-dai ba.
Da sauri Ramadan ya matso kusa dashi.
Dai-dai lokacin kuma Riyyam-nsra shima ya sauko ƙasa.
A tare suka ɗan sunkuyo kanshi, ahankali ya buɗe idanunshi jin muryar Abba nakiran sunansa.
“Rayyern! Rayyern!!”.
Cikin wata iriyar sassanyar murya can ƙasan maƙoshi yace.
“Na'am Abba”.
Jin Rayyern din ya amsa ne kuma, yasa Abba cikin jin daɗi yace.
“Alhamdulillah! Alhamdulillah!!”
Rayyern kuwa cikin ƙarfin hali da jarunta ya tattaro ragowar kuzarin sa baki ɗaya.
Ya yunƙura alamun zai tashi.
Da sauri Ramadan yasa hannunsa zai tallabeshi.
Cikin sanyin murya yace.
“Barni zan iya”.
Cike da rauni Ramadan yace.
“Hamma Rayyern bazaka iyaba”.
Kar-kar haka jikinsa ke rawa.
Lokacin da ya samu ya juyo ya ɗago kanshi.
Da sauri ya rumtse idanunshi ganin kamar kan Jannart yake.
Haka yasa ya miƙawa Ramadan hannunsa.
Da sauri ya kamoshi kana ya yunƙura ya zauna.
Lokacin Mamy ma ta iso cikin jin daɗi tace.
“Alhamdulillah sannu ko Babana”.
Kanshi ya gyada mata.
Ita kuwa Jannart a hankali ta miƙe tsaye.
Cikin son tsaida hawayenta ta nufi Kitchen.
Tashinta ne yasa Abba matsowa kusa dashi.
Hakama Mamy nanfa sukayi ta mishi sannu.
Ita kuwa Jannart tana shiga Kitchen aikin da Mamy ta fara taci gaba da yinsa.
Su kuwa A falon cikin ƙarfin hali ya maida kansa ya jingina da jikin kujera, kana a hankali ya fara yunƙurin tashi tsaye.
Da sauri Abba ya tallabeshi gefen damanshi.
Kana Riyyam-nsra ya tallabe gefen hagunshi.
Ramadan kuwa da Mamy ido suka zuba musu, sunaga yadda yake taka kafafunsa da suke karkarwa.
A hankali suka fara take steps din da taimakon su Abba ya samu.
Suka haura.
Kai tsaye Bedroom dinsa suka wuce dashi.
Suna shiga suka kwantar dashi.
Sanin kuma allurar zata sashi bacci ne yasa Abba juyawa ya fita.
Shi kuwa Riyyam-nsra gefensa ya zauna.
Yana gyara masa pillow.
Rayyern din kuwa yana kwanciya, lokacin ɗaya bacci ya fara fuzgarshi.
Ramadan ko ganin sun haura sama ne, ya sashi fita kaitsaye kuma Mai-nasara pharmacy ya nufa, inda yaje ya d’auko magungunan da Rayyern din Kesha Idan ciwon ya tashi.
Ita kuwa Mamy Kitchen ta koma nan sukaci gaba da aikinsu ita da Jannart.
Bayan sallan isha'i.
A hankali Jannart ta dan juyo tana kallon kofar babban falon,
daga nan cikin falonta.
Da sauri kuma ta miƙe jin muryar mutumin nan da taji ana kiransa da Baba Mauɗo yana sallama.
Da alamun kuma babu kowa a main falon.
Da sauri ta mike ta nufo falon.
Baba Mauɗo Kuma tsaye yake bakin ƙofar, ya ɗan turota yana sallama da ɗan buga kofar.
A hankali tace.
“Wa alaikassalam Baba ka shigo mana”.
Dai-dai lokacin kuma Mamy ta fito daga side ɗinsu.
Cikin girmamawa tace.
“A'a Baba Mauɗo ka shigo mana”.
Cikin kamala yace.
“Toh”.
Kana ya shigo.
A hankali Jannart ta dan rusuna tare da cewa.
“Barka da dare Baba”.
Juyawa yayi ya kalleta cikin wani irin mamaki da nazarin fuska da kammanin muryar yarinyar yace.
“Barka dai, Ya mai gidan naki da jikin?”.
Cike da girmamawa tace.
“Alhamdulillah jiki da sauƙi”.
“Masha Allah. Allah ya ƙara mana sauki”.
Ya faɗa yana mai juyowa yana kallon Mamy dake cewa.
“Bismillah mu isa yana sama, Abbansu ma yana can”.
Hakan ne yasa ya nufi saman.
Ita kuwa Mamy juyowa tayi ta kalli Jannart, da idanunta suka dan yi ja cikin kulawa tace.
“Kinyi salla ko?”.
Kai ta gyaɗa mata alaman eh.
Ita kuwa Mamy.
Ba tare da tace mata komaiba ta nufi Dinning area.
Foodflask ta ɗauko wanda tasa mata,
Abincin da sukayi sakwara ce, da miyar agushi.
Miƙa mata tayi tare da plate da spoon tace.
“Gashi ki zauna kici abinci, ki kuma bar zubda hawayen nan haka kinji ko Mamana”.
Cikin sanyi tace to.
Kana ta amshi kular ta wuce ɗakinta.
Ita kuwa Mamy Kitchen ta koma tazo ta shiryawa su Ramadan nasu ta kai musu falon sama.
Anan ta samesu.
Baba Mauɗo da Abba Kuma suna cikin dakin Rayyern ɗin.
Ganin har yanzu bacci yakeyi ne, yasa suka fito.
Ita kuwa Jannart ajiye kular tayi a falon.
Ba tare da tayi niyar ciba, ta kwanta a ƙasa bisa carpet din, tana rike da wayarta.
Sam ta rasa me take tunawa,
saidai kawai ta fahimci cewa yau gidan babu daɗi dan ciwon Rayyern ɗin.
Sabida su Ramadan masu ɗebe mata kewa da Riyyam-nsra mai sata farin ciki duk yau basa da Gud Mood.
Tana nan kwance ahaka har tayi bacci.
A folon kuwa suna fitowa suka samu Dr Sulaiman ya iso.
Nan Abba ya koma dashi ya ɗan ƙara dudduba shi.
Kana ya sallamesu ya tafi.
Haka dai su Ramadan suka tafi dakinsu.
Mamy kuwa falon Jannart ta leƙa ganin tana bacci ne yasa ta wuce side ɗinsu.
Dan tasan yau Abba a dakin Rayyern zai kwana.
Haka
Hakan kuwa akayi.
Rayyern kuwa baccin yayi mai zurfi sai karfe uku da rabi ya farka.
Abba da kanshi ya hada masa ruwa yayi wonka,
Kana yayi al'wala.
Yana fitowa yayi ramuwar sallan magriba da isha'i, sannan ya dan sha tea ɗin da Abba ya hada masa da kansa.
Toh kuma daga