Showing 81001 words to 84000 words out of 176055 words

Chapter 28 - Wutsiyar Rakumi Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

892

take kuma narke murya tana zubama Baba shagwaɓa akan rashin zuwansa walimar, sannan babu ko ɗaya daga cikin yayunta da yazo, danma Inna harira da Aziza na nan.
Kasa jurewa da zuciyarsa tayine, yasakashi Buɗe idanunsa a hankali, akan bayanta data juya masa ya sauke, yanda rigar ta fita da ainahin surarta ne yasaka numfashinsa yin sama yay kasa saida yay kokawar tarbosa ya haɗiyi yawu dake neman daskare masa da a ƙirji, sam duk yanda yaso ɗauke idonsa ya kasa, babban burinsama ta juyo yaga wacece ita....
Isowar Zaid wajen batareda Ummukulsoom ta fargaba yasata tsorata ta ɗan zabura tana yanke wayar.
Saurin riko hannunta Zaid yayi ganin zata zube ƙasa saboda tuzguɗewar da takalman ƙafarta sukayi kasan cewarsu masu tsini..
Tai azamar son fizge hannunta ta dafa flowers ɗin dake wajen, dan bata buƙatar yaya Zaid ya taɓata, sai dai kuma aka samu akasi ɗayan takalmin ma ya tuzguɗe tai baya zata faɗi gaba ɗayanta.
Shi kansa baisan lokacin daya baro inda yake zauneba yazo yay azamar fisgota ta faɗo jikinsa saboda ganin Zaid na shirin haɗata da jikinsa danya bata taimako daga faɗuwar da take shirin yin.
Da ƙarfi Ummukulsoom ta rumtse idanunta saboda takaicin faruwar abinda take gudu fiyema da zatonta, sai dai abinda ya ɗaure kanta sam ba ƙamshin turaren Yaya Zaid take shaƙaba, jikinma yasha banban dana yaya Zaid ɗin zata iya cewa.
Ƙoƙarin janye jikinta tayi yay saurin fara tureta yana haɗe fuska fiye da ko yaushe, kafin yaja siririn tsaki batareda ya ko kalli fuskartaba ya raɓa gefenta yabar wajan yana harar Zaid dake tsaye kamar gunki yana kallon ikon ALLAH daga Yaya Amaan, shi sam baiga sanda yazo wajenba, sai Ummukulsoom daya gani kwance a ƙirji sa.
Baki hangame Ummukulsoom tabi bayansa da kallo, cikin takaicin tsoron da Zaid yazama silar bata tace, “Shikuma wannan dangin tsakar daga ina? Waya bashi lasisin taɓani ma?”.
Dukda yayi taku kusan biyar a tsakaninsu hakan bai hanashi jin abinda taceba, dan haka ya tsaya cak furucinta na dukan ƙahon zuciyarsa da ƙarfi....
Azamar saka hannu Zaid yayi a bakinta jin zata kuma wani magana, ya ja hannunta suka shige ƙofar kicin din Maman Ahmad dake a wajen.
Hakanne yasa koda Amaan ya juyo domin ganin wannan tsagerar yarinyar sai yaga shigewarsu ciki kawai, da ƙarfi ya rumtse idanunsa tareda shafar girarsa da ɗan yatsa ya yarfar da hannun.........
“Ajiwa dama kana nan naketa nemanka?”.
Haɗiye abinda ya tokare maƙoshinsa yayi sannan ya buɗe idanunsa dake a rumtse da harsun fara canja launi.
Attahir da yay maganar ne ya kuma kafesa da idanu saboda mamakin yanayin daya ganshi, “Ajiwa lafiya kuwa?”.
Batare da yasan maganar ta subuto daga bakinsa ba yace, “Yaushe Zaid yayi aure ban saniba?”.
“Aure kuma? Zaid ɗinne zaiyi aure baka saniba? To miyasama kamin wannan tambayar?”.
Fahimtar kato ɓarar da yake nemanyine yasakashi maidama Attahir amsarsa da harara ya raɓa gefensa yabar wajen.
Da kallo kawai Attahir ya iya binsa, yayinda yake juya kalmar auren Zaid ɗin da Amaan yayi a ransa, yaɗan ɗage kafaɗa da taɓe baki alamar shiyya sani yajuya shima yabi bayansa.

Su Ummukulsoom kam na shiga ta ture hannun Zaid dake kan bakinta tana fusge hannunta, “Yaya Zaid dan ALLAH kabar min irin haka banaso wlhy”.
“Yi hakuri Ummukulsoom wlhy nima bada niyya nayiba, gani nai zaki ƙwanto mana ruwa haka kawai, kinsan kuwa wanene kike jifa da kalmar dangin tsaka?”.
Cikin halin ko in kula tace, “Oho yaya Zaid, nidai koma wanene ai gaskiya na faɗa, haka kawai yakama mana tsaki wani yace ya taimakeni? Ya barni na faɗin mana ai dai jikinane, ALLAH ya isana ma taɓanin da yay wlhy”.
Sosai Zaid ya waro idanu yana hangame baki, sai dai kuma tai gaba ta fice binta tana gyara zaman ɗan kwalinta ranta duk a dagule, dolene ta cire kunya ta takama Zaid burki bisaga take-takensa da take gani, dan bazataso yazama sahun farko a cikin jerin mazan da zata ja a ƙasa ba kodan mutuncin ahalinsa a idonta.
Binta da kallo yay harta fice, ya dafe kai tare da zubewa cikin kujerar falon, shikam baisan wane irin so yakema yarinyarnanba, amma sam takasa fahimtarsa tunba yauba, dukda iyakar iyawa yana yaɗa manufofinsa a zahiri gareta.

Ummukulsoom kam na fita taci karo da Maman Ahmad data taho kiranta saboda ana bukatarta a wajen.......


Idan ka ga mutum yana tsarguwa da shiga cikin jama'a, shi maha'incine, idan kaga mutum yana fushi a wurin jayayya to maras hujja ne, idan ka ga mutum yana faɗa, ba shi da abin faɗi. Mai gaskiya mmba ya tsoron jama'a. Mai hujja ba ya fushi. Mai abin faɗa ba ya faɗa!.

NO. 28


..........Duk yanda yaso hana kansa zama wajen taron zuciyarsa sam taƙi aminta, burinta kawai taga a bincinta, shi kansa yana buƙatar ganin mamallakiyar muryar, danya fahimci tsagerace ta gaske.
Daɗin daɗawa kuma tunda ya ɓillo da Dad ya fara tozali, yay masa wani kallo wanda yasan bai wuci gargaɗi ba akan ƙauracema zama wajen taron da yay.
Tafiyarsa ya cigaba dayi a hankali har Attahir yazo ya iskoshi, babu wanda yacema wani uffan suka ƙarasa inda dama aka tanada dominsu.
Zamansu baifi da minti biyu ba Ummukulsoom da Maman Ahmad suka dawo wajen suma, sai dai fa yanzu Ummu ta yafo gyale a jikinta. Hakanne ya saka Bily dan ƙara mata harara dayin ƙwafa alamar zan kamaki.
Duk hidimar da ake a wajen taron Amaan yaƙi kallon kowa, sai faman latse-latse yake a waya, amma kunnensa yana a wajen gaba ɗaya.
Ummukulsoom ma dai hankalinta baikai gareshi ba, sai Zaid daya addabi rayuwarta da kallo shida wane dake kusa dashi wanda take ƙyautata zaton Ameer ne, dama taga Momcy da Buhayyah a wajen tuni, amma sam bata kawoma ranta ganin Amaan ba.
An basu damar yin ɗan jawabi a taƙaice itada Bily, dan haka Ummukulsoom ta fara miƙewa kamar yanda aka umarceta.
Tunda ta miƙe idanu suka sake yawa a kanta, duk sai taji jikinta yayi sanyi, dan haka idanunta suka gaza kallon kowa.
Da sallama ta fara kafin addu'ar fatan alkairi ga waɗanda sula halarci taron tayasu murnar, sannan ta fara jawabi mai ratsa jiki a sanyaye.
Tunda tai sallama jijiyoyin jikinsa suka saki, kasa cigaba da latsa wayar yayi, yatasa da wane sihiri yarinyarnan take aiki a cikin muryarta.....
Ummu taci gaba da faɗin, “Alhamdullahi ala kulli halin, Ubangijina shine ya dace na fara gode masa, dan shi mai ni'imane mai kuma rahama mai jinƙai, mai badawa ga wanda yaso akuma lokacin da yaso, ba wayonka yakesa ya bakaba hakama ba ƙarfin iko ba, ka gode masa alokacin daya baka sannan ka gode masa idan ya hanaka, bai kasance azzalumin sarkiba balle ragon tunaninka ya baka cewar rashin sonkane yasashi hakanaka, kokuma kaida ya bamawa kai tunanin kafi kowane acikin al'ummarsa shiyyasa ya baka, ilimi baiwace, dukiya jarabawace, mulki ƙalubalene, Aljannah rahama ce, iyayena ya yayyena da ƙawayena a zatonmu wannne mafi alkairi a cikinsu?. Da ace ALLAH zai ɗauke maka kowacce ni'ima, ya azurtaka data ilimi da nasarar aiki dashi, yay maka albishir da ƙyaƙyƙyawar makoma shin bazakafi son hakaba?. Akwai miliyoyin halittun Ubangiji waɗanda basu da aljihu, ba asusun ajiya ko a banki. Amma ba su daina cin arziƙi ba. Ƙwantar da hankalinka, arziƙinka yana nan ba zai wuce ka ba. Nemi halaliya, don ba ka wuce arziƙinka. Saurin nema ba ya kawo samu. A wata maƙabarta aka rubuta cewa, “Ba za a kawo ka nan da kuɗi ba, amma kana iya aiko su kafin ka zo”. Kenan ya dace mai arziki ya yalwata arziƙinsa da alkairi tunkan ya tsinci kansa a kabari, mai ilimi ya yalwata iliminsa wajen aiki dashi da fargar da waɗanda basu saniba tunkan ya tsinci kansa a kabari, mai mulki ya yalwata mulkinsa da adalci tunkan ya tsinci kansa a kabari, talaka ka yalwata talaucinka da bautar ALLAH, tunkan ka tsinci kanka a kabari, dan abinda ka shuka shi kaɗaine zaka tarar a makomar da ita kaɗaice gidanka na gaskiya. Da ace kowane mai arziƙi irin zuciyar Dad da Abba da Ummi ke garesu da bamu tsinci a halin da mukeba a yanzu, ku ƙafafune, sannan bangwayene, bayane goya marayu harma da masu iyayen, ƙyawawan halayyarku ya koyamin abu uku, *Kƴautata zato, kar kai kuɗin goro ga al'umma wajen jifansu masu zukata da hallaya iri ɗaya, ƙyautatawa na ƙasa dani da tausayinsa* harshena bashida kalaman miƙa godiya a gareku, sai dai naita muku addu'ar fatan alkairi kuda a halinku har randa numfashine zai yanke, Dad da Yaya Attahir kune fitilata mai haska gabana da bayana, kune........!”.
Kukane ya sarƙeta ta kasa cigaba, dan haka Ummi ta taso tazo ta rungumeta itama zuciyarta na karyewa da kalaman Ummukulsoom, ba Ummi kawai ba, da yawan jama'ar dake wajen kalamun Ummukulsoom sun girgiza zuciyarsa.
Dad ne da kansa yafara tafama Ummukulsoom, kafin duk wajen ya ɗauki tafi, yaya Amaan daya kasa koda ƙwaƙwararn motsine kawai yakasa yin tafin, danshi ba hanunsa ke tafinba zuciyarsace ke tafawa tareda dukkan magudanar jininsa da kowacce jijiya dake kai saƙo tsakanin zuciya da ƙwaƙwalwa, karan farko da mace ta birgesa, karan farko daya tabbatar da mace duniyace mai koyar da mutanen duniya ilimi, karon farko da darajar mace ya girmama a idsnunsa fiyeda da dacan da mahaifiyarsa kawai yake kallo da irin wannan darajar bayan salihan mata da suka gabata irinsu nana Aysha, a tunaninsa matan ƙwarai masu hikima sun ƙare, a tunaninsa kowacce mace dake a wannan duniyar mara tunanice, a tunaninsa kowacce mace dake rayuwa a yanzu mara hangen nesa ce, ashe sam ba haka bane.......
Girgizasan da Attahir yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana kuma tamke fuska ganin jin abinda Attahir ke faɗa masa.
“Haba malam irin wannan kallo haka? Kodai ƙanwata tayi satar zuciyane?”.
Harara ya balla masa tareda jan siririn tsoki yana lumshe manyan idanunsa tareda ƙokarin dai-daita tangaɗin da tunaninsa keyi, ina su Attahir suka samo wannan yarinyar? Dan shidai baisanta ba agidan sai yau?.
Ummukulsoom kam da ƙyar Ummi ta lallasheta tai shiru, tasa tishu ta gyara mata fuskarta sannan ta maida ta mazauninta suna sauraren jawabin bily dame faɗin “Nikam ai banida sauran abin faɗa, ƴar uwata tagama faɗar komai daya dace, sai dai fatana ALLAH ya bamu ikon amfani da shawarwarinta, yakuma sakama iyayenmu da alkairi duniya da lahira”.
Da amin aka amsa, tareda tafa mata itama.
Su Dad suma sunyi jawabi mai ƙyau dake ƙara nuna martabar zancen Ummukulsoom, kafin su da kansu sufara bada ƙyautar da suka shiryama ƴaƴan nasu guda biyu, wanda kuma aka gayyaci Amaan amatsayinsa na yaya shida Attahir su bada.
Jiyay tamkar yace bazai yiba, amma sam bashida ikon yin wannan jayayyar.
Haka ya tashi zuwa wajen shida Attahir, sai dai fa fuskarnan tana nan yanda kuka santa.
Koda ya amsa micrephone ɗin domin yin jawabi na jinjina gasu Ummukulsoom kamar yanda Attahir yayi, sai ya rasa abinda zai ce, kusan sakanni goma kafin ya lumshe idonsa ya buɗe, tareda kai hanni yaɗan safi girrarsa, ganin Dad ya kafesa da idone ya sashi kuma rumtse idanu, shikam yaga ta kansa, gashi duk ƴan wajen sun watso masa idanu, abinda ya tsana a rayuwarsa kenan (kallo), da ƙyar ya fisgo magana saboda taɓasa da Attahir yay alamar yace wani abu.
“Sun cancanci jinjina, ALLAH ya sanya albarka ga abinda aka samu, yakuma sakasu yin aiki dashi damu baki ɗaya”.
Kowa da Amin ya amsa, tareda ƙara jinjina miskilanci irin nasa, duk abin faɗa dake a wajen shi iya abinda zai faɗa kenan.
Shi kansa Dad saida ya girgiza kai yana murmushi, ya tabbata wannan jawabin an kaisa maƙurane shiyyasa yayisa har kusan kalmomi 80, “ALLAH ya shirya ka Fodio”.
Ƙasa-ƙasa Attahir yace, “Ajiwa kayi abunkai, tunda kakusa faɗar kalma 90”.
Hararsa yayi amma bai tanka ba, danshi yama ƙagara yabar gidan gaba ɗaya.
Tunda ya fara jawabi Ummukulsoom ta tsargu, sai dai bata buƙatar gaskata shine din koba shi bane, dan haka ta hana idanunta ɗagowa tama kallesa.
Koda akazo wajen bada ƙyautar haka kawai Ummukulsoom ta tsinci kanta a wani irin yanayi na tsinkewar jini, ƙin yarda tayi ta kallesa yayinda shima yaso tilasta kansa ƙin kallon fuskar kowannensu.
Sai dai kuma aka samu akasi, bayan karɓar ƙyautar akai musu hoto ba tareda kowa ya kalla ɗan uwansaba, sai Attahir dake kallonsu yana murmushi mai ɗauke da ma'anoni da dama.
Bayan yin hoton ta juya zata koma wajen zamansu itada Bily bazar ƙasan gyalenta ta maƙale a zoben sa na azurfa batareda ko wannensu ya lura ba, saida tai taku uku ta tsaya cak saboda jan dataji amma gyalenta.
Shima da yaji an fisgi hannunsa saiyay saurin ɗago ido, hakan yay dai-dai da juyowar Ummukulsoom domin son ganin abinda ya riƙeta. Atake idanunsu suka shige cikin na juna.
Atare zukatansu sukai wata irin harbawa, yayinda wani fushi yazo maƙoshin Ummukulsoom ya tokare saboda ganin wanda bata taɓa tsammani ba, a ranta take furta “dama shine?”, samun kanta tayi da danƙara masa hararar data nemi wantsalo zuciyarsa ƙasa saboda tasirinta a gareshi batareda yasan daliliba.
Shi sam bai ganeta ba, yay saurin tattaro yawun dake neman gujema harshensa ya haɗiye da ƙyar kafin ya janye manyan idanunsa cike da basarwa da takaicin tsagerancinta, ya cire bezar gyalen ya bar wajen jijiyoyin jikinsa na saki gaba ɗaya.
Itama juyawa tai tabar wajen a wani irin yanayi da ita kanta takasa fassarawa.
Attahir da abin nasu ya tsaya masa a rai kasa daurewa yay sai da ya dara, hakama Dad da komai ya wakana akan idonsa, sauran mutane da basuda ilimin sanin komai kam basu kawo komai a ransuba, dan bama kowa idonsa yakai ba, Dad ya fahimci Fodio bai gane Ummukulsoom ba, itakuma ya lura ta gane Fodion, hakan yamasa daɗi sosai kuwa(🤣👍🏻Dad ɗinmu na mutunci tarkonka ya ɗanu).
Har taron ya tashi lafiya tsakanin Ummukulsoom da Amaan sai aka koma ƴar satar kallon juna, idan suka haɗa ido a bisa kuskure ta dan ƙara masa harara, shikuma hakan saiya saka zuciyarsa fusata.
itakuma ya lura ta gane Fodion, hakan yamasa daɗi sosai kuwa(🤣👍🏻Dad ɗinmu na mutunci tarkonka ya ɗanu).
Har taron ya tashi lafiya tsakanin Ummukulsoom da Amaan sai aka koma ƴar satar kallon juna, idan suka haɗa ido a bisa kuskure ta dan ƙara masa harara, shikuma hakan saiya saka zuciyarsa fusata.
Haka dai taron ya tashi lafiya, kowa yatafi da tsarabar da zuciyarsa ta samu, wasu burin mallakan waɗannan ƙyawawan yaran ma shine a ransu, musamman abokan Zaid irinsu Ameer.
Hakama tsakanin Amaan da Ummukulsoom...........

Duk yanda ka yi sai wani ya zageka. Manta da mutane ka yi komai yanda ya kamata.

Yafema wanda ya cuce ka ni'ima ce. Tuna abin baƙin ciki da damuwa wahala ce. Manta alkairi butulci ne.


NO. 29

..........“Bestie wai duk gajiyarce haka?”.
Guntun Murmushi Ummukulsoom dake kwance a kan gado tun ɗazun tayima bily mai maganar tareda miƙewa zaune tana ɗan sauke numfashi.
“Wlhy Bily kin ganninan kaina kemin ciwo kaɗan-kaɗan, nasan dai bai wuci wannan hayaniyarba, kina ganin yanda Aziza ta baje”. Tai maganar tana kallon Aziza da tuni tai barci.
“A kwaifa gajiya, yaukam ansha bidiri, yanzu danaje ɗakin Ummi take cemin Yaya Amaan ma ya aiko mana da ƙyautar kuɗi dubu ɗari mu raba”.
Duk da Ummukulsoom ta fahimci wa bily take nufi saita ɗan yatsine fuska, “Waye kuma haka?”.
“O ashefa kina buƙatar ƙarin bayani, wanda ya bamu ƙyaututtuka shida yaya Attahir, shima yayanmune ai, ɗan gidan Dad”.
“ALLAH sarki, to kin gode. Kinga bara na haɗo ko tea nasha yunwa ta fara gallabar rayuwata”.
“Maganinki kenan ai, tunfa ɗazu nakawo tuwo da zafinsa amma kikace kin ƙoshi, kuma kikace na gode ke baki godeba kenan?”.
“Indai kin gode nima kamar na godene kinji bestie, bara dai naga mike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login