Showing 171001 words to 174000 words out of 176055 words
matar dana fara aure, daga baya kuma sai muka rabu”.
“ALLAH sarki, to malam basiru bayan ita Suhailat ka ƙara wani auren kafin Meenal ne?”.
Shiru Basiru ya kasa amsawa, sai hawaye dake zirara a kumatunsa, wani irin kunyar Ummu yakeji da nauyinta....
Ummukulsoom ta sake mai-maita masa tambayar yayinda take taku a hankali cikin kotun.
“Malam basiru kai muke saurare fa”.
Sake daurewa basiru yayi ya shiga zayyano bayanin aurensa da Lubna, harma da Fannah kafin ya rabu dasu ya auri meenal. Kotu tayi tsit kowa na saurarensa, al'ajabi ya cika iyayensa da talatuwa, su dai duk basusan yayi wannan aure-auren ba, lallai lamarin basiru sai addu'a kawai.
Bayan yakai aya ne har inda faɗa ya haɗasa da Meenal aka kaisa jail ya kuma sharce hawaye.
Ummukulsoom ma numfashi ta sauke tana jinjina kai da kallon alƙali, “Yamai girma mai shari'a wannan shine gaskiya lamari daya faru har basiru ya tsinci kansa a prison, dan inada shaidu kwarara akan hakan da tabbatar da gaskiyar maganarsa, kaf matan da basiru ya aura suna nan, kuma sun tabbatar min da sune suka ɗanama basiru tarko tsakaninsa da meenal, badan komaiba sai dan su rama abinda yay musu”.
Alƙali dake kallon Ummukulsoom yana wasa da pen akan hancinsa yaja numfashi, tare da sunkuy da kansa yay ɗan rubutu ya ɗago yana bada umarnin bayyanar matan basirun duka.
Suhailat dama ta fito, dan haka itama lubna ta fito itada Fannah, mamaki al'ajab ya gama kashe Meenal, sam bata taɓa kawo hakan a ranta ba koda da wasa akan su Lubna.
Tambayoyi aka shiga musu suna bada amsa tamkar yanda basiru ya faɗa, suka kuma tabbatarma kotu sune suka kafama Basiru tarko ya afka, badan komaiba sai dan gujema Meenal shiga irin halin da suma suka shiga ta dalilinsa da matan da zai iya yaudara a bayanta, idanun basiru sunyi tsiru-tsiru, sai hawaye da yake malalarwa yana kallon ɗiyarsa ta wajen Lubna. alƙali ya gamsu da dukkan bayanan da suka gudana, ya kuma wanke basiru daga zargin kisan kai da ake masa, wahalar da yasha na zaman jail kusan shekara uku ba tare da an yanke masa hukunciba ne yasa ya samu sassauci daga kotu, zaije gida ya cigaba da jiyya, sai tara da zai biya su Suhailat, tare da maida dukiyar maharfin Suhailat da yaci, da kuma biyan dukkan kuɗaɗen da aka lura da ƴarsa tun daga goyonta har kawo yanzu data zama ƴar babba kusan shekara takwas.
Kuɗin dake accaunt ɗin basiru aka kwaso, basukai adadin abinda ake buƙata ba, dan haka Abba da Dad suka cika, sai dai Lubna tace ta yafe na rainon Amal, amma har abada babu ruwansa da Amal, yasa a ransa bai taɓa haihuwa ba, kuka mai cin zuciya basiru ya saki, wanda ya sanyaya jikin mutane da dama a wajen, son zuciya dama ai ɓacin zuciyane.
Basu bar kotunba sai da aka bama kowa haƙƙinsa, ya saki meenal daketa tsine masa da jifansa da kalmar ALLAH ya isa, yayyen Suhailat kansu badan sunga ruwa ya ƙarema basiru ba da saisun wajiga rayuwarsa, amma yanzu a cewarsu sun barsa da sakamakon daya samu daga ALLAH.
Haka suka wuce ɗilau inna da baba da talatuwa sunata sharar ƙwalla, Zaid ne ya kaisu har gida. Ummukulsoom kam gida suka wuce da A'i data maƙale musu, da Bily harta hana aje da ita sai da Ummukulsoom ta lallaɓeta.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
A'i kuka take sosai da shartar hawaye tana gurfane gaban Ummukulsoom da duk tausayinta ya kamata, dan azahirin gaskiya A'i ta kuma tsufa da fita hayyacinta, saikace ba itaba.
“Ki gafarta mini uwar ɗakina, na kasance azzaluma wadda ta jagoranci mutuwar aurenki, wlhy sam mijinki bashi da laifin komai akan sakinki, dan kuwa dai harda asiri a lamarin, saboda mahaifiyarsa tayi-tayi ya sakeki yanata mata yawo da hankali saboda baison saɓama mahaifinsa, ni ce na bata shawara akan ta bishi ta ƙasa kawai, dan maganar da take masa bata da amfani, munyi haka da kwana biyu saiga yarinyarnan data taɓa zuwa gidan harya doketa tazo (Bukky) kuɗi ta bani naira dubu ɗari akan na saka wani abu a gadonki, wannan abun kuma irin mugun asirin nan nasu ne na yarabawa, wanda idan har sukai maka ikon ALLAH ne kawai zaisa ka dawo dai-dai. niko na amince mata zan saka saboda ganin waɗannan maƙudan kuɗi, a yanda taimin bayanin asirin dama sai yallaɓai ya fara sakinki sannan, daga nan asirin zai fara tasiri, dan ance inhar kina gidansa ko wani daya shafesa to bazai aikin komai a jikinki ba. Kina wanka na lallaɓa na saka miki wannan abu a ƙasan gado kamar yanda ta umarceni, sannan na saka wanda shi maigidanki zai taka, bisa tsautsayi kuwa ina gama sakawa ya shigo gidan, daga nan kuma ne na kira mahaifiyarsa na sake tunzurata itama ta kirashi ta tunzurasa da barazanar koya sakeki kota tsine masa. Munso kafin ya sakeki yaci mutuncinki sosai, sai dai hakan bai kasanceba, magana kaɗan ya faɗa miki wadda ni a wajena bata gamsu ta zafi ba, nifa dukkan wannan abu da nakeyi burina shine ɗiyata Aina'u ta shigo gida ta auri yallaɓai bayan k kin fita, sai kuma hakan bata faruba, dan asirin da akai miki ALLAH ya taƙaita miki wahala kika zauna wajen babban Aminin mijinki Attahir, asirin jikin yallaɓai sai baiyi wani tasiriba yabar jikinsa cikin kwanaki uku kacal da rabuwarku, shinefa ya biyo sawunmu nan kaduna, kai tsaye niya tunkara, ya titsiyeni saina faɗa masa gaskiya, niko na dage babu komai, aiko aranar ya saceni daga gidansu aka koma dani lagos, Wlhy Uwar ɗakina nasha wahala hannun mijinnan naki, saida nayi dana sanin zuwana duniya, a take na zayyane masa komai harda amincewar mahaifiyarsa, itama Bukku take ko wa? Aranar aka kawota inda nake, tare yayta hajijiya da rayuwarmu saida mukai tiɓis ya maidata gidansu tare da gargaɗin da mahaifinta ya tabbatar idan yallaɓai yay wani motsi komai nasa ya rushe, shinefa yasa basu ɗau matakin komaiba, nima ya maidoni gida can ƙauyenmu, yajamin dogon gargaɗi akan inhar ya sake ganin kafata a kaduna nasan sauran, wannan yasa ban sake zuwa ba sai wannan ganin da kikaimin, shima ƴata Aina'u ce kishiyarta ta ƙonata da ruwan zafi shine ake shari'a, anma yankema kishiyar hukunci. Naga rayuwa uwarɗakina, wadda nasan ko alhakinki ya isa hanani zaman lafiya, dan ALLAH ki gafarceni, a kullum dake nake kwana nake tashi, dan duk muguntar da nai miki saita dinga dawowa kan Aina'u........”
“Ai hakan shine dai-dai tsohuwar banza kawai”. Aziza ta faɗa tana harar A'i.
A'i ta kuma fashewa da kuka tana sake sabon gurfane a gaban Ummukulsoom dasu Aziza. Da sauri Ummukulsoom ta dakatar da ita tana faɗin, “Nikam baba na yafe miki, ALLAH ya yafe mana baki ɗaya, idanma ban yafe mikiba ashe ban godema ALLAH tarin ni'imomin da yayminba kenan, tunda gashi sanadin rabamun naga dangin mahaifiyata, na koma makaranta nasamu ilimin da yake amfanar al'umma, daga ƙarshe na koma gidan mijina, iyayensa da ƴan uwansa suna sona, nazama *Wutsiyar raƙumi* ga wanda yay min butulci da ahalina dama ƙauyenmu gaba ɗaya, A'i bake ba dukkan wanda yay min wani abu a yau ni Ummukulsoom buhari na yafe masa, nima ALLAH ya yafe mini nawa kura-kuran”.
“Ameen ya rabbi” su Bily suka haɗa baki wajen faɗa har Ummi dasu hajiya yaya, yayinda itama A'i taketa zuba godiya tana share hawaye da bakin zani.
Koda A'i taci ta ƙoshi sai su Ummukulsoom suka bita asibiti inda Aina'u ke jiyya, dukda tama fara warkewa abin babu ƙyan gani, su Ummukulsoom duk saida sukai hawayen tausayi, sunma A'i alkairi suka tafi, Ummukulsoom ta bata Number ta akan konan gaba wani abu ya taso ta nemeta zata taimaketa da ita abinda ALLAH ya ni'imtata dashi itama.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Basiru ya zama abin kallo da kwatance a ƙauyen ɗilau da kewaye, har niƙo gari ake zuwa kallonsa daga maƙwaftan ƙauyikan ɗilau, yayinda ƴammata suka haɗa masa waƙa a dandali, wadda tuni ta shige bakunan yara da samari, wani lokacinma da biyu ake zuwa jikin dannin gidansu ana rairawa, kokiji mata nayi cikin liguden daka.
Ƙiri-ƙiri fitowa koda ƙofar gida a ƴar wheelchair ɗinsa ta gagaresa, wasiƙar da Ummukulsoom tai masa randa za'a wuce da ita gidan Amaan itace ta zame masa abar karantawa safe da yamma yana kuka, yanzunma yana daga jikin bishiyar dalbejiyar dake tsakar gidansu saboda zafin da akeyi, zaune yake akan tabarma da ƙafarsa ɗaya da rabi, ya jingina da bishiyar yana karanta takardar, murmushi da hawaye na fita daga garesa a lokaci ɗaya.
*_Assalamu alaika_*
_Nasan a lokacin da wannan takardar zata iso gareka babu komai a ranka sai ƙarin tsanata Basiru, banga laifinka ba, dan kuɗi sunsha juya zukatan al'ummar duniya, sun kawo saɓani a tsakanin abokai, sun kawo saɓani a tsakanin ma'aurata, sun kawo tsakanin iyaye da ƴaƴa, sun kawo tsakanin masoya tamkar yanda suka zama sanadi a tsakanina da kai, koban faɗaba a yanzu nasan akwai ranar dana sani daga gareka, dan kayi kuskuren yarda duniya ta aureka iyayenka na fushi dakai, wannan shine kawai babbar damuwata, dan ALLAH basiru kafin ka auri wadda kakeso yanzu, ina roƙonka ka sasanta kanka da iyayenka, wannan kaɗaine zai zame maka hasken cin duniya hankali kwance, na manta dakai har abada, koda kuwa sonka zai zama ajalina, sai dai kai inason karka manta dani har ƙarshen rayuwarka, wannan halaccin kawai kaimin ya wadatar dani._
Talatuwa ta zare takardar tausayin ɗan uwanta na sake ratsata, wannan takarda ta Ummukulsoom ta zame masa tamkar wani karatun salla, tanada tabbacin harya gama haddaceta ma. Zama tai tana lallashinsa da bashi baki akan yakamata ya saki ransa zuwa yanzu, ya fiskanci yau ɗinsa, dan kuwa jiyansa ta wuce bisa rubutaccen alƙalamin ƙaddara da babu hannun dake gogewa, a yau ɗinsa yake, wadda tazo masa da sakamakon bashi damar duƙufa neman gafarar ALLAH da iyayensu domin yaga ƙyaƙykyawan sakamako a gobensa a duniyarsa da lahirarsa.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Kamar yanda Amaan ya alƙawarta yana dawowa ya biyo kd suka wuce da Ummukulsoom, ya dankara mata kyauta mai tsoka irin ta masoya, dan taci nasara kamar yanda yay fata, iyayensu nata sanya mata albarka, sannan ta kara daraja da kima a idon mutane.
Haka rayuwar taci gaba da shurawa Ummukulsoom na jan cikinta da cigaba da aiki, yayinda busy yaketa ƙaruwa ga Amaan, lokacin da cikinta ya tsufa dole ta koma gidan Attahir da zama kusa da maman Ahmad, idan kaga taje gidanta to Amaan yana a gari.
Yana tafiya kuma zata koma can, dukkan wani tattali dai tana samunsa daga maman Ahmad, sai da cikinta ya ƙara tsufane Momcy tazo har lagos da kanta ta ɗauki abarta suka koma kd, dan tagaji da yawo da hankakin da Amaan ke mata.
Kowa tausayin Ummukulsoom yake a gidan da tattalinta, hatta da Ameer da ayanzu ya maidata abokiyar shawararsa, kuma Aunty sama aunty ƙasa, ita dasu Aneesa kuwa ai bama ajin kansu, kowane motsinsu aunty Ummukulsoom, idan suna son abu a hannun Amaan ta hannunta sukebi, idanma taga babu yawa saita musu ba tare da takai masa kukanba, sai dai yaji suna masa godiya ba tare da yasan akanmi ba, daga bayane yake fahimtar abinda Ummukulsoom takeyine da sunansa ashe. Rasa mima zai mata ya nuna jin daɗinsa yayi, dan aganinsa magana da fatar baki bazatayi ba saidai yayta mata addu'ar gamawa da rayuwa lafiya har ƙarshen numfashinsa.
Kwanan Ummukulsoom huɗu a gidan ta tashi da nakuda a safiyar alhamis, babu bata lokaci sukai asibiti da ita, tasha wahala kafin ALLAH ya sauketa lafiya ta sunkuto ƴarta mace mai kama da ita tamkar tayi kaki ta tofar.
Faɗa muku farin cikin da wannan ahali suka tsinci kansu ɓata lokacine, tun a wannan ranar zancen haihuwar ya isa ɗilau.
Kasancewar baby da maijego lafiya aka tarkatosu zuwa gida, dan Momcy ta kafa ta tsare Ummukulsoom na kusa da ita.
A ranar da yamma shima Amaan ya isa garin, daga Cameroon yake, duk rashin fara'arsa ranar saida jama'a da yawa suka gane yana tare da farin ciki na musamman.
★★★★★★
Yana zaune gefen Ummukulsoom dake kwance a kan gadon Momcy ya rungume ƴarsa a ƙirji idanunsa lumshe, shi kaɗai yasan abinda yakeji a ransa, yau shine da ƴa matsayin mallakinsa har abadan, duk inda ta shiga za'ace jininsa ce.
A hankali ya buɗe idanun tare da kai bakinsa ya sumbaci goshin yarinyar yanajin wata irin tarin ƙaunarta na shiga har cikin ɓargonsa, baki Ummukulsoom ta taɓe tana juya masa baya, ita adole kishi takeyi, dan tunda ya shigo baibi takanta ba ta ƴarsa yakeyi.
Ajiye Babyn yay yana murmushi, ya kwanto jikin Ummukulsoom yana mata raɗa a kunne. Ture kansa tai tana sake turo baki gaba da faɗin, “Anki ɗin, kuma karka sake kulani wlhy”.
“Tab, akwai matsala kenan ai Beauty, kece Amaan fa, daga sanda kika bar kula Usman fodio ai babushi sai hotonsa, ALLAH yay miki albarka, ya baki ladan rainon ciki dana naƙuda, tare da bamu ƙwarin gwiwar tarbiyarta bisa ka'ida da dokokin addinin islama”.
“Amin ya rabbi” Ummukulsoom ta faɗa tana rungumesa itama, bakinsa yakai kan nata ya sumbata, yakuma maidawa zai ƙara Momcy ta shigo.
Sallallami ta fara da rike haɓa, daga karshe ta kora Amaan yabar ɗakin da masa gargaɗin karta sake ganin ƙeyarsa.
Murmushi kawai yayi ya fita yana shafar keya, itako Ummukulsoom kunya ta hanata yarda su haɗa ido da Momcy dake mata faɗa itama akan ta kiyayi biyema Amaan danshi bashida matsala, ita zai ta ɗurama ciki ya bari da aiki shi yana gefe yana barcinsa harda nashari.
Ita dai Ummukulsoom batace ƙalaba, Amaan ma tun daga ranar sai ya kiyayi shigowa saboda ma kullum su Bily anan suke yini, zaizo dai da safe su gaisa hakama da yamma, idan magana yake bukatar suyi saiya kirata a waya taje sashensa kosu haɗu a harabar gidan, dan sashen nasuma sau ɗaya yace taje akan wani muhimmin magana da sukayi, shima kuma Momcy tasan da zancen.
A haka akaci kwanaki bakwai na zaman bakwai, inda Dad da Momcy suka nuna bajinta a kayan barka, hakama ƴan uwan Amaan suma alkairin da yake musu tun suna ƙananunsu da wanda Ummukulsoom ɗin take musu duk basu mantaba, dan sunyi hidima da jikinsu da aljihunsu.
Hakama baba daga ɗilau yayo tasa bajinta shi da su baba yalwa dasu murja, ananma su Attahir sunyi tasu, hakan yasaka Ummukulsoom da kara tabbatar da itafa ƴar gatace ta gaske a wajen ƴan uwanta, kowa burin share mata hawayen maraicin rashin uwa yake wanda ta fuskanta tana karama. An raɗa suna bayan sallar asuba inda baby taci sunan Jamila (anma Momcy takwara kenan) kuma Dad ne yayi, dan shi Amaan ya bama zaɓi, shi kuma sunan iya marigayiya mahaifiyar Dad yaso a saka, amma hakanma baiyi baƙin cikiba, dan yasan Dad yanada dalilinsa. Aiko sai gashi Momcy harda hawayenta tayi.
Za'a dinga ma baby alkunya da suna *_Noor-ur-Rahman_*.
A ranar dai kam ba'a cewa komai, dan an raƙashe an kwalle, inda maijego da baby suketa shan gayu, zuwa yamma mata sukasha shagalinsu a cikin gida, Suhailat, Lubna, Fannah harda Meenal saida sukazo wajen suna, dan yanzu sun ɗinke sun zama ƙawaye suda Ummukulsoom, sudai sunce birgesu take, komai nata na masu ajine da nutsuwa, gashi bata da girman kai.
Hayaniya tayi yawa a gidan, inda dole Amaan yabar gidan, dan bazai iya da wannan hayaniyarba, bai dawo gidanba sai kusan 12, lokacinma harsu Ummukulsoom sun jima dayin barci, sai zuwa safiya ya gansu.
Kwanaki biyu dayin suna ya koma lagos ya barsu wankan jego. Haka Ummukulsoom taci gaba da shayar da Noor-ur-rahman cikin amin ALLAH, gefe kuma tana wankanta na jego Momcy na gyarata gyara na musamman irin na ƴan gata, itama Ummi nayin nata, hakama su hajiya yaya da gwaggo hinde tsoffin kwarai, kamar yanda suka gyara su bily haka itama Ummukulsoom akai mata.
A haka su Ummukulsoom sukai arba'in, taje ɗilau tai kwankinta huɗu da taho, wannan gani ma da basiru yay mata har kuka yayi, musamman daya ɗauki Noor-ur-rahman, yarinya kyakykyawar abin son kowa, daka ganta kasan Ummukulsoom ce ta haifeta saboda tsabar kamannin da take da ita. Ganin zaman banzan da basiru yake Ummukulsoom ta bashi shawaran ko zai dinga sai da kayan miya anan ƙofar gidansu.
Jiki na rawa ya amince yanata zuba mata godiya da sake neman gafararta, itadai tace yabar mata wannan godiya haka komai ya wuce a gareta, bata baro ɗilau ba saida taba wani yayanta Surajo kuɗi yaje ya saroma Basiru kayan miya a zaria, aka kafa masa tebir a ƙofar gida yanda zai dinga samun taro da kwabo na taimakon kansa da iyayensa. Haka Ummukulsoom ta barosu suna kuka da saka mata albarka shidasu Inna, Noor-ur-rahman kanta tasha du'ai kala-kala. basiru jiyake kamar yace kar Ummukulsoom ta