Showing 126001 words to 129000 words out of 176055 words

Chapter 43 - Wutsiyar Rakumi Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

895

na sonki Ummukulsoom, halayyarsa kuma ba girman kai baneba, haka ALLAH ya haliccesa, wlhy duk wani hali da kikasan ALLAH ya halicci ɗan adam dashi babu mai iya canjashi, sai dai ya koyi wani abun, a wannan gaɓar ba kuskuren Ajiwa ya kamata ki kalla ba kota Momcy, Ƙyautatawar Dad da halaccinsa ya kamata mu kalla mu dukanmu, Dad ƙarfin hali kawai yakeyi, dan kaf ƴaƴansa yanason Ajiwa fiye da kowa a cikinsu, ba komai yakawo hakanba kuwa sai ƙaƙarin ƙyautata masa da yakeyi, dan kowacce zuciya nason mai ƙyautata mata, amma saboda adalcinsa a gareki ya haramtama ɗansa ke, bawaifa dan shima baya sha'awar tarayyarku baneba, kawai bayason ya shiga haƙinkine. Saboda ke ya saki uwar ƴaƴansa da sukai aure tsawon shekaru, Na baki damar ki zauna ki tunani akan maganganuna, kamata yay ki koma gidanki ki hukunta Ajiwa da kanki, ba ki barin farin cikin iyayensa dana ahalinsa yaci gaba da tafiyar hawainiya ba”. Yana gama faɗa ya miƙe yabar wajen.
Ko motsi kasayi Ummukulsoom tayi a wajen, ba komaine ya tsaya mata araiba sai adalcin Dad a gareta, tabbas zatayi wani abu akai, amma ba komawa gidan Amaan ba, ta riga da ta jingine babinsa gefe kuma har Abadan shikam, bakuma tajin zata sake zama dashi musamman zaman aure..........✍🏻


NO. 43

..........A nutse yake sumbatarta, babu wani rawar jiki ko hanzari a tattare dashi. Duk mutsu-mutsun da take bai bartaba sai da yay san ransa, a yanda yake mata kawai zai tabbatar maka da akwai huce haushi, gashi ya danna hannayen duka da nasa babu damar motsawa, ƙololuwar takaici Ummukulsoom tagama kaiwa.
Tsawon mintina uku suna a haka sannan ya janye bakinsa yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, Idanunsa da launinsu ya canja ya ɗago ya zuba mata su, sai taga sun kuma girma da kwarjini, sam bazata jure kallon cikinsu ba.
Ta kauda fuskarta gefe tana ƙunƙunan ALLAH zai saka mata da koƙarin haɗiye hawayenta.
Duk da sarai ya jita saiya basar, batare da ya ɗagatanba ya saka mata keys ɗin a hannunta na dama yana matso da fuskarsa daf da tata sosai tamkar zai kuma haɗe bakinsu, duk yanda taso kauda kanta yaƙi bata dama.
Magana ƙasa-ƙasa tamkar mai raɗa ko mai gulma yana gudun a jisa yace, “ko zaki sake gwada ihun?”.
Kamar zata shareshi saita kasa, ta dalla masa harara, Tana sake kumbura fuska da cuno baki.
“Idanma kin kira mutanen kece da kunya matar Uthman” yay manar da janye jikinsa daga nata gaba ɗaya.
Ajiyar zuciya Ummukulsoom ta sauke saboda jinta sakayau, aranta sai mita take akan uban nauyinsa.
Yanajin ƙunƙunan da takeyi amma sai bai tankaba.
Har tuntuɓe take da ƙafarsa wajen yunƙurin tashi ta gudu, ya bita da kallo ƙasa-ƙasa dariya nacin ransa, amma saiya haɗiye kayarsa ya miƙe tsaye kamar zai kamata, saiya waske yana gyara babbar rigarsa.
Tuni Ummukulsoom kam taje ga ƙofar bathroom dan ta zata kamata zaiyi, ganin zata shige yace, “Hajiya bani key kar aga na daɗe azata wani abun nakeyi”.
Harara ta zuba masa ta shige bayin.
Murmushi yayi yana kai hannu ya shafi girarsa, dama danta hararesan ya faɗa, harara na mata ƙyau, dan tana sake fiddo da manyan idanunta ne, har wani ƙyallin ruwa zakaga sukeyi, shikuma hakan na matuƙar tasiri agareshi.
Gaban Mirror ɗinsu ya nufa, ya ɗauki tissue ɗin dake wajen tare da pen yay rubutu kaɗan daga ƙarshen da aka warwara ya maida ya ajiye, sannan ya koma saman gadon ya ɗauki keys ya fice.

Tunda ya fito falon Attahir ya wani kafesa da kallon tuhuma, sarai ya fahimcesa dan haka saiya kuma haɗe face ya basar yana watsa masa harara, zama yay suka gaisa da Ummi tai masa ALLAH ya sanya alkairi.
A saman laɓɓa ya iya amsawa saboda jin nauyinta, kafin ya miƙe suka fice shida Attahir ɗin da dama zaman jiransa yake, Gwaggo Hinde da Hajiya yaya sai tsokanarsa sukeyi.
Sai Attahir ne ke karesa, amma shi ya gaza cewa komai.
Suna fitowa Attahir ya tsaya cak yana masa kallon sama da ƙasa, “Ajiwa wai mika aikata kayanka sukai wannan Squeezing ɗin haka? Kamar wanda yay danbe”.
Hararsa yayi yana ɗauke kai, tareda ci gaba da tafiya yana faɗin, “Shaƙeni na faɗa maka, inma danben nayi miye naka a ciki?”.
Sosai Attahir ya tuntsure da dariya, “Yanzu kam kasamu bakin min rashin kunya tunda na kaika inda aka ƙaromaka ƙarfi, ɗan rainin wayo nasan maganinka ai wlhy, sai next year zata tare”.
Juyowa yay ya kallesa, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru ya cigaba da tafiya zuwa falon baƙi inda ya tabbabatar su Abba na can.
Attahir ya bisa da kallo zuciyarsa fes, Ajiwansa kenan mai abin haushi da ban mamaki, duk wanda yay masa farin sani yasan yau yana cikin farin ciki, a kan laɓɓansa ya furta “ALLAH ya baku zaman kafiya”.


★★★★★

Duk da taji ya fita kasa fitowa tayi daga toilet ɗin, gani take kamar kowa yasan miya faru, ta cije baki wani haushi na kuma mamaye ranta, hannunta takai saman laɓɓanta da sukaci ƙaniyarsu, tai ƙwafa da faɗin ƙazantar banza......
Jin an kuma buɗe ƙofar sai da gabanta yaɗan faɗi, ita duk zatonta shine ya dawo, ta kuma ƙanƙame jikinta tana mannewa da ƙofar.
Bily data shigo idonta ya sauka akan gadonsu, haɓa ta riƙe tana danne dariyar dake neman taso mata, ta hau waige-waigen inda zata hango Ummu, ganin babu alamarta a ɗakin saita shiga ƙwala mata kira.
Ummu dake bayi ta sauke ajiyar zuciya tana buɗe idanunta da dafe ƙirji jin muryar Bily, ƙofar ta buɗe ta fito tana wani cin magani da kumbura baki dan karma bily tazo mata da ƙananun magana.
Bily dake kallonta ta kwashe da dariya, “Amarsu ta yaya Amaan, mi akaci aka rage a ɗakinne naga gadonmu duk a yamutse?”.
Kunya ta kama Ummukulsoom tamkar ta nutse, amma saita dake tana harar Bily.
“Yo miye na hararata? Gadon nan dai da gani Ya...”
Ranƙwashi mai azabar zafi Ummu tabama Bily akai, ta dafe wajen tana faɗin, “Muguwa kasheni zakiyi”.
Sosai Ummukulsoom tasa dariya tana ƙarasawa gaban mirror, tissue ta ɗauka da niyyar goge fuskarta data jiƙa kwalli yaɗan kwaranyo, sai taci karo da rubutu. har zata share a tunaninta shirmen Bily ne tayi, sai dai ta tsaya karantawa.
*_“Duk wayon Amarya wataran ƙirjin ango zata kwana. Amma fa kina ruwa babie, idan kika fito za'aji ƙamshin turarena a jikinki, idan kika canja kaya kuma kowa zai tabbatar ango yay......”_*
Da sauri ta yage tana dunƙulewa da ƙunƙuni dan kar bily ta gani, sai dai batasan tana a bayanta ba, tarema suka karanta.
Duk yanda bily taso danne dariyarta ta kasa hakan, dole ta barta ta fito, ta faɗa saman gadonsu tanayi iya iyawarta.
Ummu ta kuma kumbura da haushi, wani haushin Amaan na kuma ratsata, wlhy mutumin nan ya iya mugunta, ɗan rainin wayo kawai, saiya nemo mai kwana aƙirjin nasa......
_“Amma fa kina ruwa babie”,_ “hhhhh oh yaya Amaan ɗinmu na mutunci, ashe haka kake dunɗun dunkum ɗinnan bana banza bane, _Ango yay... Me?_ ƙarasa min naji dan ALLAH tawajena”. ‘Bily ta katse mata tunani da shaƙiyancinta’.
“ALLAH ya isa to” Ummu ta faɗa tana harar Bily ta koma ta sake shigewa bayin badan tasan abinda zataiba, sai sam batason bily taga hawayen da suka cika mata idanu.
Saboda tsabar jan magana irin na Bily saita bita jikin ƙofar Bayin, “Bestie kar dai wankan manya zakiyi?”.
Murɗa ƙofar Ummukulsoom tayi da nufin fitowa Bily ta kwasa da gudu ta fice daga ɗakin tana dariya. Itama ƙwafa tayi ta maida ƙofar ta rufe.

★★★★★

Sosai su Abba suka tasa Amaan da faɗa da nasiha akan a kiyaye gaba, badan mahaifin Ummukulsoom ba da iyayen Momcy dasu Hajiya yaya da Attahir ne duk ya kama kafa dasu, da Dad bai sakkoba har ya amince da sake ɗaurin auren nasu a karo na biyu.
Daya amince ɗinma cayay sai dai a haɗesa da nasu Bily ne.
Amma sai Baba yace a'a a ɗaura kawai kodan hankalin Amaan ɗin ya ƙwanta waje ɗaya, yakai maƙurar da ya kamata a tausaya masa kodan mugun ciwon dake tare dashi, suna gudun yaci gaba da takura kansa azo zuciyarsa ta buga a banza, bayan sunada damar share masa hawayensa, kuskurene dai anriga da anyisa, saikuma a tari gaba, ga Attahir dake ta masa fadanci.
Dukda haka kuma sai da Dad ya kira Ummukulsoom ya tuntuɓeta akan inhar batason Amaan ta sanar masa, shi bazai amince ai mata auren doleba.
Kunyace dukta ishi Ummukulsoom, ina taga bakin buɗewa tacema dad batason jininsa, cikin in ina tace “Dad na.. Na amin.. ce”. Tai saurin yanke wayar.
Farin cikin da Dad yashiga aranar bai musaltuwa, dan haka ya amince akan a daura, dama kullum fatansa da addu'arsa kenan, sai dai bayason shiga haƙƙin Ummukulsoom ne kawai.
To shine fa aka ɗaura auren a yau kamar yanda Hajiya yaya ta bada umarni, shikuma Dad ya roƙeta akan abar Ummu karta tare sai lokacin bikin su Bilyn da bai gaza wata ɗaya ya rageba, zuwa sannan ta kammala karatunta, dan baza'a shiga haƙƙinta ba itama.
Koma dai yayane shidai Amaan yaji daɗi, sai yaji Baban Ummukulsoom ya kuma daraja da kima a idonsa shida Hajiya yaya, duk abinda ya aikatama ƴarsu sai basu duba ba suka kalli halaccin mahaifinsa. Sosai yay musu godiya, tareda ƙara roƙon Dad ya yafe masa, da alƙawarin insha ALLAHU bazai sake wannan gangancinba, wannanma ƙaddarace.
A take Dad yace ya yafe masa, shi dama bai riƙesa ba, komai yana masane danya magantu.
Tashi yay ya rungume Dad yana sake jero godiya.
Attahir sai dariya yake ƙasa-ƙasa dan kar su Abba suji aci ƙaniyarsa.
Anja musu doguwar addu'ar zaman lafiya kafin kowa ya kama gabansa.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Tunda Ameer da Bassam suka dawo suka sanarma Momcy abinda ke faruwa saita hau kukan daɗi tana sanyama Ummukulsoom albarka. gaba ɗaya ta ƙagara Fodionta ya shigo gidan ta gansa, dan jitake tamkar an maida matashi sabon mutum yau.
Babu ɓata lokaci tashiga buga waya tana sanarma ƴan uwa da abokan arziƙi abin farin cikin daya sameta.
Su Baba Halima da sai yanzu sukasan mike faruwa daɗi dukya kamasu, Jud sai son ganin Umikusmu yakeyi, dan tunota yake sonyi randa Amaan yaji mata ciwon nan a ƙafa amma sam zuciyarsa taƙi yarda itace.
Cikin mintuna ƙalilan gidan yafara amsar ƴan taya murna na kusa, yayinda su Jud keta ƙoƙarin haɗa abinci mai sauƙi.

Sai da aka idar da sallar la'asar Dad da Amaan suka shigo gidan, kai tsaye sashen Momcy ya nufa kamar yanda Dad yayi.
Yana shigowa Ummayya Da Aneesa da Buhayyah sukazo suka rungumesa duk da kowa zuciyarsa a tsorace take da hakan.
A mamakinsu sai sukaga bai gwalesu ba.
Momcy tazo duk ta turesu ta rungume yaronta ta gefe.
Tattausan Murmushi ya saki wanda mutane da yawa da basusan yana yiba suka shagala a kallonsa, Dad ma daya shigo kallonsu yayi yay murmushi yana yunƙurin hayewa sama.
Momcy ta saki Amaan ta nufi mijinta da hanzari ta rungumesa hawayen daɗi na silalo mata a kumatu, sam ta manta da wasu ƴaƴanta da maƙwafta, burinta ta nuna masa jin daɗinta kozai sakko itama yabar fushin da ita hakanan, dan tunda ta dawo gidan baya kulata, ko magana tai masa daga sallama baya sake amsawa.
Hannayensa yasaka ya zagayeta dasu shima yanajin farin cikin gane kuskurenta da tayi da wuri, tare da jin ƙaunarta.
Ƴar ɓoye fuska aka shigayi a wajen su Ummayya, Amaan ma ya sunkuy da kai yana cigaba da murmushin sa, harga ALLAH abin ya bashi kunya. Sai da ya tabbatar sun saki juna harma sun haye sama sannan ya ɗago kansa tare da juyawa zai fita sashensa.

Wanka yake amma gaba ɗaya zuciyarsa naga Ummukulsoom, abinda ya faru a tsakaninsu kawai yake hasasowa, yakai hannu saman laɓɓansa ya furta ya shafasu, a hankali ya furta“Jan aji, nutsuwa, cikar haiba, kamala....” saikuma yay ɗan murmushi batare da ya ƙarasa ba ya haɗiye sauran a ransa yana ɗauraye jikinsa...
Koda ya fito sai bai zaunaba saboda jiyo maganar Momcy a falonsa, wando 3quarter ya saka da riga mara hannu yaɗan fesa turare ya fito hannunsa riƙe da wayoyinsa.
Zama yay kusa da Momcy da tun da ya fito take kallonsa bakinta washe da murmushi na tsantsar farin ciki.
“Babana Congrat fa, ALLAH ya sanya alkairi ya baku zaman lafiya na har abada, ALLAH ya kawomin jikokina anan kusa”.
“Amin” ya faɗa akan laɓɓa ba tare da ya yarda sun haɗa ido da Momcy ba.
Madai-daicin tiren data shigo dashi ta ɗago tasa a cinyarta, kallonta yay da mamaki, “Momcy wannan fa?”.
“Kai zakaci Fodio, na kula duk yau baka sakama cikinka abincin kirkiba, koma nace tunda matsalolinnan suka shigo kaima abinci yajin aiki, dan haka ɗura zan maka”.
“Ɗura fa Momcy?” yay maganar da ƴar shagwaɓa.
Tace, “Ƙwarai kuwa, yanzun nanma bara ka gani”.
Duk yanda yaso zamewa akan ya ƙoshi bata barshiba, a baki ta dinga bashi abincin, saboda tsabar son kar yaci saiya ringa mata shagwaɓar wai akwai yaji, shifa ƙirjinsa zafi.
“Ungo sha ruwa, indai yajine zai kwanta. Duk dai iya langyarenka saika cishi, sonake kafin wata ɗayannan da ɗiyata zata tare ƙibarka ta dawo, ina daɗi akai mata ango ramamme”.
“Momcy!...” ya kira sunanta a matuƙar sanyaye.
Eh kirani da ƙyau, ai gaskiya na faɗa, Dad ɗinku ma cayay nazo na saka gaba kaci abinci.
Zaiyi magana Aneesa ta shigo itada Aunty Ummi. Haɗiye kayarsa yay yana maida fuskarsa babu wasa, dama bawani uban sakewa yay mataba.
Zama sukai suna kallon ikon ALLAH ana bama yaya Amaan abinci a baki.
“Lafiya kuka samin ido?”
Yay maganar ƙasa-ƙasa saboda Aunty Ummy.
Dariya Momcy da Aunty Ummy sukayi, Aneesa kam ɓoye tata tayi dankar asamu matsala.
Aunty Ummy ce tace, “Kai da wane idon ka kallemu kasan muna kallonka? Dama cazamuyi mun wuce gidan Abba mu gaishe da ƙanwar tawa”.
Sosai ya haɗe fuska, dan a zatonsa wani abune daban zai kaisu.
Momcy ce ta fahimci ma'anar ɗaure fuskar tasa, dan haka tai saurin cewa “Kaga karka kawo komai a ranka Fodio, abinda ta faɗa shine gaskiyar magana”.
Baice komaiba, amma dai alamu sun nuna ya gamsu.
Godiya sukai masa suka fice.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

“Auntys ga dama ta samu, wannan bikin da za'ayi na yayan Meenal ya kamata kusan yanda kukai kuka ƙulla alaƙa da ita, a wannan ranar nima zanyi duk abinda ya dace Numbers namu su kasance a wayar shashashan naku” Zulfah ta faɗa tana wani far da idanu.
Ranƙwashi Suhailat ta bata, “ALLAH zan ɓata miki rai idan baki nutsu ba, kimana bayani yanda zamu gane”.
“Kai Aunty wlhy da zafi, minene abin rashin fahimta anan, komaifa a buɗe yake, Auntys L & F dan ALLAH baku ganeba kuma?”.
Fannah tace, “nidai na fahimceki sosai Zulfah, samun Number sa a garemu dakuma saka tamu a tashi shine mataki na biyu dazai cigaba da girmama saɓani tsakaninsa da ita, amma sai daifa zan sai wani layin dabanne nikam, koma nace kowannen mu ya tanadi sabon layi saboda wannan aikin, muna gamawa mu gimtsesu kawai”.
“Shawararku tayi hundred percent, sai dai tayaya zamu samu zuwa bikin?”. Cewar Lubna.
Zulfa tai saurin faɗin, “Ta hanyar Aunty Suhailat mana, tunda nasan za'a gayyaci Daddy dan abokinsane babanta”.
“Kai amma naji daɗin harkarnan gaskiya, saimu bada himma da shiri na musamman”.

★★★★★

Sosai su Meenal ke shirin bikin ɗan gata, abin ba'a cewa komai, sam babu mai saka Basiru a sabgar, idan kinga an nemesa wani abu za'a sayo, sai a bashi mota yaje ya sayo, musamman Baban Meenal, motsi kaɗan sai yace a bama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login