Showing 27001 words to 30000 words out of 176055 words

Chapter 10 - Wutsiyar Rakumi Book 1 Hausa Novel Complete

07 Jan 2025

853

fahimci hakan, ta dafa hannunsa tana kallon fuskarsa dake kuma dulmiyata a ƙaunarsa, “Love Daddy yana sonka, yanajin haushine saboda katsewar karatunmu ni da kai, amma zuwa nan gaba kaima zaka fahimcesa, dan yanda yake sona kaima haka yake sonka”.
Badan ya yardaba ya ɗaga mata kansa kawai, daganan suka shiga hirar shirye-shiryen bikinsu.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Garin ɗilaufa ya kuma ɗaukar sabon zance akan ɗaurin auren Ummukulsoom, harma wani bayajin zancen wani. Yayinda jama'ar da suka halarci ɗaurin aure suka fara barin garin.
A cikin gida kuwa zuba ido ake aga ango ya shigo gaida iyaye kamar yanda aka saba, amma sai sukaji tsit, nanfa abu yazama abun kace nace har ran inna laraba ya ɓaci matuƙa tahau zazzaga tsiya cikin taro, da faɗin ai badai dole sunga angoba, idan sun daka ransu a inuwa shekarama kwanace indai mijin Ummukulsoom ne zasu gansa duk daren daɗewa.
Wannan hayaniyace ta tashi Ummu a barci.
Da ƙyar ta iya haɗa bayanan masu tsogumi waje ɗaya, harta fahimci abinda ke faruwa, jikinta rawa kawai ya farayi, dan ƙafafunta suna neman gaza ɗaukar gangar jikinta, ta zame a hankali ta zauna tana sharar ƙwala da tunanin miyasa baba bai karɓi uzirintaba ya yarda ya aura mata mutumin da kowa ke tsoro......
Tunaninta ya katse saboda kiran da inna harira ke mata, ƙwallanta ta share kafin ta miƙe tafito bakin ƙofa inda Inna harira ke tsaye.
Inna harirah dake kallonta tace, “Sako hijjabinki zaki gaisa da baƙine”.
Komawa tayi da baya, ta ɗauki gyalen Aziza dake aje a tabarma jikin ts duk a sanyaye. Inna Harira ta kama hannunta suka fito tsakar gida, kanta a ƙasa ta kasa kallon mata dake cike da gidan ƴan biki da ƴan gulma. Gashi dama sun zuba mata ido tamkar yau suka fara saninta.
Soron gidan malam Habu inna harira ta kaita.
Alhaji Mahmud ne zaune a tabarma shida wasu abokansa biyu shaƙiƙai, sai Ameer dake tsaye gefe yana cika da batsewa, dagani kasan yazo ɗaurin aurenne dan tilas.
Ummukulsoom ta durƙusa a gabansu ta gaishesu muryarta na rawa, ga hawaye na zuba danma gyale ya kare fuskar.
Duk sun amsa mata cike da kulawa, tareda addu'ar zaman lafiya da samun zuria ɗayyiba, suka ɗora da saka mata albarka itada mijin nata da bata saniba, bakuma taga alamar yazoba.
Alhaji Mahmud yataso yafito waje yana kiranta. Tasowa tai ta biyoshi, can gefe suka koma inda babu jama'a, amma dukda haka saida aka saka musu ido har wasu na zargin koma shine mijin?.
Shi dai Alhaji Mahmud ko a jikinsa, fuskarnan kuma babu fara'a tamkar ko yaushe. Ya kallli Ummu dake durƙushe a gabansa,
“Kiyi haƙuri ɗiyata, kizama cikin mutane masu karɓar ƙaddara aduk yanda tazo musu, insha ALLAHU zakiyi farin ciki a ƙarƙashin jinina, ki manta da komai daya faru a baya, ki fuskanci sabuwar rayuwar da zakiyi yanzu. Mun gama magana da mahaifinki da a yau zamu wuce dake, amma saboda wasu ƴan dslilai muka bar tariyar taki sai satin sama idan ALLAH ya kaimu, aidaita haƙuri da rayuwa kinji, zan aiko Isa da saƙo zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, tashi ki koma ciki, ALLAH yay miki albarka”.
Kai kawai ta iya kaɗa masa, kafin da ƙyar tace, “Amin Dady, na gode da karamcinka gareni, ALLAH ya ƙara girma da lafiya mai amfani, ya sakanka maka da mafificin alkairi”.
Karo na farko danaga yayi wani ɗan guntun murmushi wanda saika saka masa ido zaka fahimci yayisa, idonsa a kanta yace, “Tashi kije ciki, muma wucewa zamuyi yamma tayi”.
Nanma kanta ta ɗaga masa tamiƙe tana tangaɗi da ƙyar ta iya isa inda Inna harira ke jiranta.

Tunda Ummukulsoom ta koma ciki saita ƙunshe kanta a ɗaki tana cigaba da tunanin yanda rayuwa zata gudana a gidan Alhaji Mahmud, yanzu haka tana kula yanda Ameer yake jifanta da kallon ƙyama da tsana, ta rasa miyasa Alhaji Mahmud yagaza fahimtar wutsuyar raƙumi tai nesa da ƙasa tsakaninta da ɗansa, sannan baba yagaza fahimtar ita abinda take hangowa.
Har yamma tana ɗaki, sai ƴan biki dakan leƙo su gaisa irin ƙawayensu da sukai rayuwar yarinta, waɗanda mafi yawansu a yanzu idan ka gansu saika ɗauka yayun Ummukulsoom ne, wasuma tamkar sun girmeta sosai, su Azima kansu dake aure a birnin duksun wani tsofe mata a ido, dan Azima ma fama take da ƙaton ciki na huɗu yanzu haka.
Zuwa yamma su Murja suka saka waƙa a redio sunaji ana kwasar rawa da guɗa, tareda shewa da dariyar yaran mata.
Sune ma sukaje suka kinkimo Ummukulsoom daga ɗaki dole ta fito tsakar gidan dake cike da mata, saboda anan inna laraba ke karasunta matsayin Uwar ƴa tunda babu mahaifiyar Ummukulsoom a duniya.
Ga ƙatuwar tukunyar tuwo masara fari ƙal anata tuƙi, sai miyar taushe da kunun zaƙi da zoɓo, duk dai dangin mahaifiyar Ummu ne sukayi dan itama tayi farin ciki, karkuma tayi kukan rashin Uwa.
Cigam ɗin dasu Murja suka siyo itadasu Aziza sukazo kan Ummu suna zuba mata suna tiƙar rawa, wai cingam ɗin shine matsayin kuɗin liƙi.
Batare da Ummukulsoom ta shiryaba tasaki murmushi tana ture murja dake callara mata buɗa a kunne, yayinda Aziza da Nusaiba da Hadiza ke zuba mata cingam.
Manyan iyaye irinsu baba yalwa da gayyar ƴan biki suna kallonsu, wasu kuma na aikin abinci, yayinda wasu ke gulmarsu group-group, irinsu baba yalwa kuwa danne zukatansu kawai sukeyi, dan wani sashe na murna wani sashe na baƙin ciki.
Har dare kusan tara gidan anata kujiba-kujiba irinta biki, yayinda wasu ke kwasar ƙafafunsu suna wucewa gida ana barin ƴan uwa irinsu Murja da suka cigaba da cashiyarsu.
Itadai Ummu tunda tagudu ɗaki sallar magriba bata sake dawowa ba ma. Sai wajen tara da rabi yunwa ta isheta ta leƙo kozata hango Aziza, amma tagaza ganinta, danma garin ƙwanyar yake da hasken farin wata kasancewar yau daren sha biyar.
Ruwa ta ɗiba a buta tanufi bayi, tafitone ta hangi Murja can gefe tana wankema ɗanta Amadu kashi tana masifa saboda a wando yayi.
Ƙarasawa Ummu tayi taimata dundu a baya, Murja ta ɗago tana sosa wajen zatai masifa saitaga Ummukulsoom ce.
“Kai kai wlhy dama ance ƙashin amare ƙwarine dashi, amarya karki ƙarasani kijama mijina salalan tsiya”.
Ummu ta harareta tana ɗaukar Amadu daga gabanta ta ƙarasa ɗauraye masa jikin da butar hannunta, cikin dusashshiyar muryarta da kuka ya dishe tace, “Kindawo nan kinama yaro mugunta, ALLAH ya isarmu”.
“ALLAH Umma bazaki ganeba, tunfa ɗazun nace yaje ya hau fo amma yay kunnen uwar shegu dani, dan wulaƙanci da wayonsa yay kashi a wando, dashi zanji koda Sa'a?”.
Ummu data kammala masa ta ɗaukeshi a hannu tana faɗin, “ƙila to baiga fo ɗinba, kinacan kina tiƙa rawa zaki nutsu ki bashine, mizan samu a gidannan inci nasha magani, yunwa nakeji”.
“Tab aiko sai tuwo, kuma kinsan yagama hucewa, ba ɗazun naga Halima da kwanoba tace kezata kaima fura inji baba furera?”.
Ɗan yamutsa fuska Ummu tayi tana gyara tsayuwa, “Kinsan bancika damuwa da furaba Murja, kuma lokacin banajin yunwa, da Jummai tashigo itada kishiyarta naga ƴarta nata kallon kwanon shine nace ta zauna tasha”.
“A to lallai bakida mankai, to yanzu da furar haki ce kumafa? Ke bakisan shegan son banzar Jimmai ba ashe, itada bata wuce tayi duk gidan data shiga saboda shegen kwaɗayinta datayi sallama ake kife kwano da murfi”.
Karo na farko da Ummu tai dariya har haƙoranta suka bayyana tunda tadawo garin ɗilau, “Kai Murja ALLAH ya shiryaki, nidai samomin ko tuwon ne naci dan ALLAH”.
“A'a ba ayi hakaba amarya da cin tuwo, bara na mayi ango tunda baya kusa, ina zuwa naba Kamilu ya siyo miki shayi wajen idi na bakin yara”.
Duk kiran da Ummu take mata akan karta bada bata sauraretaba, ta karɓi Amadu daga wajenta dantaje ta saka masa kaya.
Ummukulsoom ma wuce yaran dake rawa tayi takoma ɗaki, bayan yunwa ma har wanka tanada bukatar yi kodan nauyi da jikinta yay mata, rabonta da wanka tunna safe bayan sun dawo a sibiti, da yamma ma dazata canja kaya daga alwalar la'asarne tashafa mai ta canja kayan.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Su Alhaji Mahmud sun iso kaduna gab da magriba, baima shiga gidaba ya tsaya masallaci, saida yay har sallar isha'i sannan ya ƙarasa ciki.
Duk ƴan uwan hajiya Jamila da sukazo sun wuce, daga ita sai ƴaƴanta yanzu a gidan harda Ummi babbar ƴarsu Aneesa, saikuma ƙannen Alhaji Mahmud su uku da sukazo daga Ajiwa, da wata tsohuwa gwaggonsu. Kasancewar ba sakewa suke a gidanba idan baya ciki duk suna ɗaki, saisu Aneesa dake a falo suna kallo da hajiya Jamila da ƙanwarta Mansura dake aure a kano, dama tun jiya tana gidan, ita keta kuma tunzurata akan ƙin auren na Amaan da Ummu.
Duk nutsuwa yaran sukai suna masa sannu da zuwa, fuskarnan tashi babu walwala kamar kullum ya amsa, Mansura ma ta gaidashi damasa ALLAH ya sanya alkairi.
Ganin babu danginsa a falon ransa ya sosu, harya kama kafar benen zai hau ya juyo yana kallon hajiya jamila da gabanta yafaɗi lokaci ɗaya saboda yanda taga idanunsa.
“Su su Faɗima suna ina? Naji banji motsinsu ba?”.
Cikin inda-inda hajiya jamila tace, “Sallar isha'i sukashiga yi, da duk muna zaune a falo muna hira”.
Yasan halinta sarai, kuma yanayinta yasashi sanin karya take, baice uffanba ya ida haurawa yabarta nan tsaye tana binsa da kallo. Saida taga ya ɓacema ganinta sannan ta juyo suka haɗa ido da Mansura suna wani ƙyaɓe baki.

Koda ta biyoshi harya cire kayansa zai shiga bayi wanka, ko kallonta baiyiba ya shige abinsa, dukda taji takaici haka ta zauna a bakin gado zaman jiransa.
Wayarsa data fara tsuwwa alamar kira ta kalla, ganin sunan *Fodio* ya sata ɗaukar wayar ta ɗaga kiran.
Daga can Jarumar muryarsa ta fidda sautin sallama tareda faɗin “Dad kun dawo gida lafiya?”.
Takaici yasaka hajiya jamila miƙewa tafita da wayar falo dan kar Alhaji Mahmud yaji mizata ce, a falonma saida taje can ƙarshe kafin tace, “Lallai Fodio, nadai lura kai bama ka kishin kanka akan aurennan ko?, ɗazun kuma na kiraka kaki amsamin waya saboda ka maidani ƙawarka”.
Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke daga can yana lumshe manyan idanunsa daya gada a wajenta, kafin yasa hannu ya dafe kansa, “Momcy Ina yini”.
“Lafiya lau” ta amsa a ƙufule.
dukda yaji yanda ta amsa saiya basar yace, “Dad fa?”.
Cikin gatse tace “Na dafashi na cinye, Fodio banason wulaƙancinka fa na basar da abu, namaka magana baka bani amsaba kana kawo wata tambaya daban”.
Muryarsa mai nuna tsantsar jarumtarsa daya gada ga Alhaji Mahmud da nutsuwa ya kuma sanyayawa, “Momcy banida abin faɗane shiyyasa”..
Haushi ya ƙara kama Hajiya jamila, tace, “Ni wlhy Fodio dama kurma ALLAH yayoka danafi jin daɗin haka, koba komai nasan kurma na haifa, dan iskanci mutum yamaka magana goma ka bashi amsar ɗaya”.
Rasa abinda zaice mata yayi, sai yace “Yi haƙuri to” abinda kawai yace kenan yay shiru, danshi mutumne bamai yawan magana ba, sunema yake ɗan daurewa yay magana mai tsawo dasu itada dad.
Jin kamar motsin fitowar Alhaji Mahmud yasata komawa ɗakin da sauri tana faɗin, “Yana wanka, amma gashinan fitowa”.
Fodio dake saurarenta daga can ya yanke wayar kawai yana sauke numfashi tareda gyara kwanciyarsa a doguwar kujera..
Alhaji Mahmud baibi takantaba yahau shiryawa cikin jallabiya doguwa.
Ganin hakan ne yasata cewa, “Fodio ya kira kana wanka, gakuma abinci yana jiranka”.
Batareda ya bata amsar farkoba yace, “Bazanci abinci ba, akwai fura da muka dawo da ita a ɗiba a dama min”.
“Fura kuma? Yanzu Abban Fodio duk irin munin ƙauyennan da Ameer ke faɗamin haka zaka iya shan furar da akayo daga can, inama laifin afita asiyo maka mai tsafta wajen Hamza”.
Wata banzar harara ya watsa mata, ya tsallakota ya fito abinsa.
Tamkar zata makesa tabiyo bayansa da sassarfa. A falo ta iskeshi yana ƙokarin kiran Fodio. Ganin yanda ya kuma kicin-kicin da fuska yasata ƙokarin ficewa ta cika Umarninsa.
“Ki turomin su Asiya”.
Wani takaicinne yakuma rufeta, ta amsa da kyar tana fita, gata a gidan amma dan wulaƙanci zaice ta turo masa ƙannensa. Shiyyasa bataso suzo gidan kwata-kwata.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Washe gari ma ancigaba da ƴar hidimar biki daba a rasaba, dukda babu ango babu danginsa, zuwa yamma kuma baba yace Ummu ta shirya gidan gwaggo Hinde kakarta zata koma da zama har zuwa rar tarewa. Tayi murna da hakan sosai, dan ta lura zaman gidansu babu abinda zai ƙara mata sai baƙin ciki da damuwar tunawa da basiru, dan habaici da gugar zana kawai ake zuba mata tun jiya akan fasa aurenta da yayi, tun tana hawaye akan ƙananun maganganun harma zuciyarta ta dake tabar jin kukan. Musamman ma dayake Aziza na kusa da ita a ko yaushe tana ɗebe mata kewa.
Da daddare tareda Aziza suka tafi gidan gwaggo Hinde, dama kayanta dukta tattara ankai can tunda yamma.
Wannan komawa gidan Gwaggo Hinde da Ummukulsoom tayi yajawo ƴar hayaniya tsakanin Baba da matansa, wai wani munafuncin yake shiryawa shiyyasa yace Ummu takoma gidan kakarta.
Banza yaymusu yaƙi kulasu, dan ya lura hassada ke cin ransu kawai, da akace an fasa auren Ummukulsoom da basiru ai cikin farin ciki suke, ko jiya da safe dasukaji zancen ɗaurin aurenta da wani basu damuba, saida sukaji labarin yawan motocin da sukazi ɗaurin aure da manyane mutane sannan hankalinsu ya tashi, dukda sunjin daɗin angon baizo ɗaurin aureba.
Shirun baba yakuma sasu takaici, saisuka zauna da ƴaƴansu su Nusaiba suna gulma. Zainaba ce dama kawai babu ruwanta, dan ita harga ALLAH tana ƙaunar Ummukulsoom matsayin ƴar uwarta Uba ɗaya.

★★★★★

Komawar Ummukulsoom gidan gwaggo yaɗan sake bata nutsuwa, yayinda gwaggo ta duƙufa gyarata da maganin sanyi, ko yaushe suna tare da Aziza dan suma basu komaba sai randa za'a tafi da Ummukulsoom.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Kwana biyar da ɗaurin auren Ummukulsoom sai ga Baseer ya danno ɗilau da dalleliyar motarsa fara sol.
Yawani ƙara ƙyau da ƙiba ɗan zaman dayay na kwana takwas a gidansu Suhailat.
Sai wani faɗi yake da fankama, yayinda yara suka zagaye motar suna kallo.
Baba yana zaune a ƙofar gida yana kallonsa, ya gaza cemasa uffan sai ido daya zuba masa ko ƙyaftawa bayayi.
Gabansa yazo ya durkusa yana gaidashi ido a ƙasa.
Baba ya amsa yana faɗin ”Kaiko Basiru ina kashige haka dan ALLAH?, kana ganin wannan rayuwar ta dace dakai? Kofa sallama bakai manaba kabi mutuminnan saboda yafimu yanzu a wajenka ko?”.
Ɗan juyawa Baseer yayi gudun kar wani yaji abinda baban nasa ke faɗa, ganin duk taron yarane saiya juyo yana kallon baba cikin ɓata fusaka yace, “Please baba kabari mushiga daga ciki zan maka bayani ai”.
Kaɗa kai kawai baba yayi yacigaba da rubutunsa da yakeyi a allo. Basir kuma yamiƙe yashiga cikin gida yana ƙunƙunin baba yaƙi ya waye, arziƙi na kiransu amma suna rintse ido.........?

NO. 10

Inna dake tsakar gida tana surfen ƴar masarar tuwonsu ta ɗago ta kalli basiru batareda ta amsa masa sallamarsaba, harya ƙaraso gareta bata iya janye idontaba, hannunta ɗaya da taɓarya ɗaya kuma tana ƙokarin janye kan akuya dake saka kai a turmin da take dakan, ƙarasowa yay yana girgizama Inna makullin motar hannunsa, fuskarsa washe da murmushi.
“Innata kuma fa ALLAH ya kaiku matsayin dawani mahaluki bai taɓa takawaba a garinnan”.
Ɗauke idonta tayi daga kallonsa tacigaba da dakanta tana faɗin, “Nagani kam, yaka baro su baban naka?”.
Duk da maganar tata ta doki zuciyarsa saboda fahimtar gatse tamasa amma saiya basar ya amsa da “inna suruki dai, iyayena kam ai kune, amma suna lafiya lau, sunce na gaidaku da ƙyau, wani satin zasuzo maganar auren”.
Inna tasaki murmushin takaici da jinjina maganar a ranta, gidan mazane ke zuwa neman aure,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login