Showing 93001 words to 96000 words out of 176055 words
gida suka isa, sosai komai ke ƙayatar da Baseer, part ɗinsa da ban shida matarsa Meenal, waddama suna ajiye kaya bai sake ganin ƙeyarta ba ta shige cikin ƴan uwanta, zamanne ya ishesa shima ya ce bara yaɗan fita ko tsakar gidane yasha iska. Sai dai yana taɓa ƙofar yajita gam, Meenal ta kullesa, wani haushine ya kamasa, kishin meenal yayi yawa, ya tabbata dan karya fitane tai masa haka, ya furzar da iskar bakinsa yana komawa ya zauna a falon.
Son da yake matane yake sanyashi shanye duk wani iskanci da take masa, harga ALLAH yana ƙaunarta sosai.
Bata dawo sashenba sai dare, ta rungumeshi tana faɗin, “I miss you my bobo”.
“Ƙyace hakafa tunda kin shige cikin ƴan uwanki kin manta dani, danma wulaƙanci harda kulleni”.
Dariya tayimasa tare da gwalo, “Hhhh bana buƙatar kowa ta ganarmin miji, ai harma a gama taron nan bazakaga wajeba”.
Baki a hangame yake kallonta, “To inkuwa hakane ki barni na wuce garinmu nima naga su Innata”.
“Lah wasa nake maka fa, indaima ka fita to sai tare dani”.
Yanzu kam murmushin yaƙe kawai yay mata bai iya cewa komaiba.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
A ɓangaren su Zaid kam da dabara suka ɗakko Gwaggo hinde daga ɗilau, lokacin da suka iso cikin kaduna har tara na dare yayi.
Kai tsaye gidan Hajiya yaya suka nufa, dan sunsan su Abba ma dai duk suna can, tunda bayan tafiyarsu Abba ya kira yaya Zaid yana tambayar suna ina a rikice.
Shine yace masa sunje wani wajene amma insha ALLAH zasu dawo a yau, babu yanda Abba baiyi ba dan yasan inda sukaje amma sam Zaid yaƙi faɗa, hakane yasa duk bayan wasu awas sai Abban yakira yaji wane hali suke, sai faɗa yake musu akan fita basu sanarba.
A galabaice suka iso da Gwaggo Hinde kaduna, dan bata taɓa doguwar tafiya irin hakanba, iyakar yawonta baya wuce Zaria😂.
Tunda motarsu ta tsaya Ummi da Abba da Attahir suka fito.
Ganin su Zaid da babbar mace waddama tafi Hajiya yaya tsufa saboda jin daɗi ba ɗayaba ne ya basu mamaki, Attahir daya gaza haƙuri yace, “Kai wai wacece kuka kawo wannan?”.
“Yaya mu shiga daga ciki, zamuyi muku bayani”.
Babu wanda ya sake magana, Ummi ta matso ta taimaka musu wajen shigar gwaggo hinde ciki.
A falo Zaid sai waige-waigen inda zaiga Ummukulsoom yake da hajiya yaya, dukda Ummi ta fahimta sai batabi ta kansa ba, saima shayi da taje ta haɗoma Gwaggo hinde.
Bily ma da ta matsu taga Ummukulsoom ce ta kasa hakuri itakam, matsawa tayi wajen yaya Attahir a hankali tace, “Yaya Ummukulsoom fa?”.
“Tayi barci Bilkisu, dan ta fama ƙafarta saboda ruɗewa da tashin ciwon Hajiya, sai da aka sake nemo mai gyara yay mata, shine Ummi tai mata allurar barci danta huta”.
Cikin damuwa Bily tace, “ALLAH sarki bestie na, ALLAH ya basu lafiya itada hajiya”.
“Amin bily. Wai wacece wannan?”.
“Yaya zaku sani, amma kuyi haƙuri ba yanzu ba”.
Bai sake ce mata Uffanba, haka suma su Abba basu sake tambayarsu wacece Gwaggo Hinde ba, itakuma jigartar datai tasata yin tiɓis, burinta kawai ta kwanta ta huta.
Hakanne yasa tana kammala shan tea din da Ummi ta haɗa mata saita bata wasu magani tasha aka rakata inda zata kwanta ta huta.
Suma ɗin Abba cayay su koma gida, shi zai kwana anan shi da Ummi.
Attahir yace, “A'a Abba, ka gafarceni kuje ku ku huta, ni zan kwana anan ɗin kawai”.
Bily ma tai caraf tace, “Abba nima dan ALLAH, kaga fa Bestie na nan”.
Murmushi kawai Abba yay yana girgiza kai, yace, “to indai hakane kai Attahir kuje gida kawai harda Zaid, ita Bilkisu saita kwana dasu, ni da Umminku ma anan zamu kwana”.
Duk yanda sukaso dole sukabi Umarninsa, suka wuce gida su uku akabar Ummi da Bilkisu nan, ɗakunan dake can gefe Ummi da Abba suka tafi, bayan Ummi ta kuma duba su Ummukulsoom ta tabbatar babu wata matsala.
*_WASHE GARI_*
Alhmdllh kowa ya tashi, musamman ma Hajiya yaya da ciwon nata yake tamkar iska dama, Ummukulsoom daice keɗan ɗangyasa ƙafarta, amma dai Alhmdllh batajin ciwo kamar jiya.
Ummi da kanta ta tashi ta shirya breakfast da zai dace da cin kowa na gidan da taimakon mai aikin hajiya yaya, sai Bily dake ƙoƙarin tsaftace ko ina.
Tunda garin ALLAH ya waye hankalin gwaggo hinde a tashe yake, burinta taga ta inda Ummukulsoom zata ɓullo, amma taji tsit. Gashi bata zaƙeba ta fito a gidan mutane batasan ina zata dosa ba.
Tana tsaka da wannan tunaninne Bily ta shigo ɗakin da sallama Ummi na biye da ita.
Daɗi ya kama Gwaggo Hinde, bayan sun gaisa Da Ummi cikin girmamawa ta ce, “Bilkisu ni banga ƙawar takiba ai har yanzu, ko sai ta gama mini yangane”.
Dariya sosai Bily keyi, cikin tsokana tace, “Gwaggonmu ta mutunci, What Are you eating na baka na falling down ne, yanzu zakiga Bestie na harda babban abun mamaki wanda nasan zan samu ƙyauta ta musamman a gareki”.
“Tofa ƴar nema, ina jiran ganin wannan abun mamaki kuwa”.
Ummi dai na jinsu tana murmushi kawai, tunaninta ya fara hasaso mata labarin da Abba ya bata a daren jiya, amma dai zatabi yaran nata dan ganin manufarsu, ba zata zama mai musu ƙutseba.
Bily ta haɗama Gwaggo hinde ruwan wanka mai ɗumi, sai da ta taimaka mata tashiga bayin saboda karta zame a tiles tunda ba sabawa tayiba, dama da asuba itace tazo tai mata jagora tai alwala. Kafin Gwaggo hinde ta fito Bily ta gama gyara ɗakin tsaf ta saka mata turaren wuta tareda ajiye mata man shafawa.
★★★★★
“Waini bestie ina kiketa shiga da fitane? Nagama kamar baki damu daniba”. ‘Ummu ta faɗa a shagwabe’.
Dariya Bily tayi tazo tana rungume Ummukulsoom, “Oh sorry dear, in banji ciwonki ba wama zaiji a gidannan, jima nake kamar ya dawo kafata, ai Yaa Amaan yasa ina jin haushinsa wlhy akan wannan abu”.
Baki Ummukulsoom ta cije tana ƙwafa, amma sai batace komaiba.
Hajiya yaya duk na jinsu amma sai bata tankaba, dan ranta duk a jagule yake, sosai take ƙwaɗayin son ganin wani nata taji koda labarin ahalin tane, tasan dai kam da wuya ace mahaifinsu nada rai yanzu, sai dai tana tsoron tambayar Ummukulsoom komai a yanzu ma............
“Lah Gwaggo hinde!”. ‘Cewar Ummukulsoom cikin tsananin murna, hakanne ya katsema Hajiya yaya tunaninta cikin tsitstsinkewar zuciya ta ɗago ta kalli bakin ƙofar ɗakinta da Gwaggo hinde ke tsaye bayanta Zaid.
A zabure ta mike tana nuna Gwaggo hinde hannunta na karkarwa, hakama bakinta, “Hin...hinda....tu kece da gaske?”.
“Yaya!” ‘Gwaggo hinde ma ta faɗa tana zazzaro idanu tareda ture Ummukulsoom data shige jikinta’.
Ai tuni ɗakin ya harmutse, babu mai jin zancen wani, Hajiya yaya da Gwaggo Hinde duk sun rungume juna sunata rusar kuka, Abba ma sai sharar ƙwalla yake da babbar riga.
Bayan wasu mintuna kusan arba'in komai ya natsa, Hajiya yaya na kwaƙume da hannun Gwaggo hinde kamar za'a sake rabasu, har yanzu hawaye yaƙi tsayawa a tsakaninsu, kowanne na mamakin hukuncin ALLAH, musamman ma Gwaggo hinde da ta daɗe kamannin Zaid na rikitata ainun, hakama kamannin Bily da Ummukulsoom.
Ummi ce cikin lallashi ta lallaɓasu suka ɗanci abinci, tabama hajiya yaya maganinta tasha sannan akai zama na musamman a falon Hajiya yaya, kowa kagani yana cikin wani yanayi na farin ciki da girmama ikon ALLAH mai tsara yanda yaso ga wanda yaso, akuma lokacin da yaso....
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Dad daketa zagaye falonsa bayan tafiyar su Ummukulsoom yaji motsi a bayansa, juyowa yay yana kallon Momcy da itama ta kafesa da ido cike da damuwa, ɗauke kansa yay tamkar bai gantaba, saima ya nufi hanyar bedroom ɗinsa saboda daga ita har ɗan nata takaicin ganinsu yakeyi....
Da sauri ta katsesa ta hanyar faɗin, “Dan ALLAH Abban Fodio kayi haƙuri, mu ɗauki hakan a matsayin kuskure, kasan hakannan da gangan bazai cutar da itab......”
“K! Jamila ki kiyayeni wlhy, inba hakaba daga ke har Fodio zan saɓa muku a gidan nan, idan ke baki san wacece itaba aishi daya aikata ya sani, dan haka ki fita daga idona kafin na rufe dake a ciki wlhy kinji na faɗa miki”.
Sosai ta tsorata dashi, dan tasan halinsa balle idan ya fusata, tarasa minene yasashi ɗaukar zafi akan wannan yarinya? Kodai kawai dan kar Fodio ya aure ta ne?.
A wannan tunanin ta zauna, tasan dai bai wuci yace zai horasa akan yay masa aure ya saki ba, zai dinga bin hanyar da duk tazam ta sanadinsa ya daƙile idan Fodio ya samu matar aure mai dangantaka dashi, musamman wannan da suke da alaƙa mai ƙarfi tsakaninsa da Alhaji Abubakar, tai murmushi tana kallon ƙofar da ya shiga,
“Alhaji kenan, to ai hanyar ALLAH yawane da ita, insha ALLAHU wannan ɗin sai ta zama matar Fodio, zanbi ta hanyar Hajiya Na'ima (Ummi), sannan nasa Fodio yay farautar zuciyar yarinyar, inhar so ya shiga sai naga ta inda zaka hana, tunda kai baka manta abinda ya wuce a rayuwarka.
Oho shi baima san ta nai ba.
Amaan kuwa dake a sashensa Momcy na fita shima ya hau haɗa kayansa, a yau ɗinnan zai koma Lagos koda ta motane, bazai taɓa barin wannan tunanin yay barazana da ransa ba, danshi shirmema ya ɗauki sosayyar tun tuni, shiyyasa bai taɓa yin taba...............✍🏻
NO. 33
.........“Yaya kin ɓata ɓat, baba yasa anyi nemanki daga baya har an gaji, wani yaro Sallau har danfarar sa yay ya saida ƙaramar gonarsa ta bakin fadama ya bashi kuɗin akan wai ya ganki a Legas zai je ya kawo ki gida, amma yaron nan tunda ya tafi bai sake dawowa ɗilau ba sai da baba ya rasu”. ‘Gwaggo hinde ta ƙare maganar da fashewa da kuka’.
Itama Hajiya yaya kukan takeyi jin Baba ya rasu, “Hindatu kina nufin ALLAH yay ma baba rasuwa?”.
“Eh yaya baba yarasu tun bayan Auren wannan ƴar (Inna Laraba, bata faɗar sunanta saboda ƴar fari ce), bayan tafiyar ki a zuwan da kukayi baba ya ɗau zafi sosai, ashe Iyami ce ta tunzuro shi, sai da inna haule ta dawo daga tafiyar da tayi katsina, kinsan sanda kukaje baku isketa ba, to bayan dawowarta taji abinda ke faruwa tazo har gida ta sake tambayata, ban ɓoye mata komaiba na sanar mata, itace taje ta samu baba ta warware masa komai har yanda kuka gudu, aiko baba yayta kuka yana dana sanin korarku da yayi, tunda ga nan yashiga nemanki, itakuma iyami ya saketa, amma sam sai ba'a daceba harya kwanta ciwo, kusan shekararsa ɗaya yana jiyya ALLAH yay masa rasuwa, sai dai yace ko bayan ransa aka ganki a shaida miki ya yafe miki duniya da lahira, kema ki gafarcesa keda mijinki”. Kuka sosai Hajiya yaya da Gwaggo hinde sukeyi, sai da ƙyar suka tsagaita, Gwaggo hinde ta nuna Ummukulsoom da itama ke kuka tana faɗin, “Wannan jikarmu ce, ɗiyar Hassana ce data bari, sunanki aka saka mata”.
Hajiya Yaya ta kalli Ummukulsoom tana murmushi da zirar da hawaye a lokaci ɗaya, “ALLAH sarki, ashe Hassana rabuwar har abada mukayi da ita daga ita har baba, na gwada zuwa ɗilau yafi a ƙirga, amma kalaman baba ke hanani, ALLAH ya gafarta musu, Ummukulsoom zonan kinji”.
Matsowa Ummu tayi ta shige jikin Hajiya yaya dake hawaye har yanzu, ji take tamkar tana tare da ɗiyarta Hassana.
Bayan an sake samun nutsuwa Abba yay gyaran murya tareda jaddada godiyarsa ga ubangiji da ban haƙuri ga iyayen nasa, ya ɗora da faɗin, “Ubangiji sarkin hikima, ashe ni ƴata nake riƙo ban saniba, nayi murna da hakan sosai nakuma ji daɗi, a ƙiyasi mahaifinmu ya riga ƴar uwata rasuwa, dan haka tana da gadonsa kenan, dukiyar daya bari yazama ni kaɗaine magajinsa a yanzu hakan ya canja, dole za'a fiddama Hassana haƙinta a damƙasa ga ɗiyata mai sunan Hajiya tunda itace magajiyarta”.
Ummu na hawaye tace, “Ni dai A'a Abba na yafe maka, ganinku ya fiyemin komai”.
Murmushi Abba yay yana faɗin, “Mai sunan Hajiya ai haƙƙine, dolene kuma a fitar, ke dai ALLAH yay miki albarka, a yanzu saimu fahimci kuma duk abinda ALLAH ya jarabci bawa dashi badan baya sonsa baneba, na tabbata kinshiga ƙunci mai yawa sanadin matsalarki da Fodio, to ashe wani babban mabuɗin alkairinne ke bibiyar ki, ƙila da hakan bata faruba da wannan sirrin bazai taɓa buɗuwaba, har sai mu bar duniya da tabon a ranmu”.
“Wannan gaskiyane Abubakar, dolene mu ƙara nuna godiyar mu ga ALLAH, kaima Attahiru ALLAH ya saka maka da alkairi, domin girman da ALLAH ya baka ka riƙe shi, ALLAH ya sake baka wuyan ɗauka”.
Da amin kowa ya amsa, daga nanfa aka ɓarke hira, zuciyar kowa ƙal da farin ciki.
Abba kam ai neman Dad yay a waya ya zayyane masa abin farin cikin daya faru.
Rasama mi Dad zai faɗa yayi saboda al'ajab da farin ciki, a lokacin ya baro gidansa zuwa gidan hajiya yaya.
Hajiya yaya sai ƙara zuba masa albarka takeyi, domin ƙyautatawar sa akan na ƙasa dashine da ƙyaƙykyawar zuciyarsa ta zama sanadi, da ace bai haɗa Ummukulsoom da Fodio aure ba da duk hakan bata kasanceba. Hajiya yaya sai kuma ƙarfafa musu gwiwa take akan su cigaba da zama masu adalar zuciya, domin hakan basusan alkairin da zai janyoma rayuwarsu ba.
A dai ta ƙaice ranar saita zama anyi wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan biki a gidan, dan sai dare su Abba suka koma gida, aka bar Gwaggo Hinde da Hajiya yaya suna cigaba da hirar zuminci.
Musalta muku farin cikin da Ummukulsoom ta tsinci kanta a cikima ɓata lokacine, amma kowa ya ganta yasan yau ɗin ta musamman ce, ga albishir da Dad yay mata na komawarta makaranta nanda sati ɗaya, zataje Law school, ta birnin ikko (Lagos) ta ƙarasa shekara ɗayanta da zai tabbatar da ita a matsayin cikakkiyar Barrister..
Sai daren ranar Attahir yasan Amaan baya ma garin ya koma Lagos, murmushi ƙeta yayi dan kuwa abinda ya gudar mawa zaije ya iskeshi, da Ummukulsoom zasu tafi Lagos, kuma a gidansu zata zauna harta kammala.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Su baseer ansha shagalin bikin rantsarwa, yaci gayu yanata basarwa sai kace shine ɗan gwamna ɗin, danma Meenal ta kafa ta tsare saboda kar yayma wata mace magana....
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Zaune suke a katafaren falon gidansu, ta canja tamkar ba Suhailat matar baseer ba, ta kuma cika da girma dan batafi sati uku da dawowa ƙasarba ma, tana Germany karatu, waya take latsawa hankalinta kwance, yayi da su Mom ɗinta ke kallon labarai.
Kamar ance ta ɗago sai ta kalli TV jin Daddynta tana kwarzanta bikin rantsarwar dayake shima yaje saboda mahaifin Meenal abokin sane.
Ƴar zabura tayi tana kuma ware idanunta akan tv n, “Kam bala'i, Baseer!!”.
Atare Mom da Daddyn ta suka kalleta tareda cewa, “Baseer kuma?”.
“Ƙwarai kuwa Daddy, wannan Baseer ne ya gama magana a matsayin surukin gwamna, Daddy yaran Alhaji Ɗalha nawane mata?”.
“Eh to, kamar guda biyu ne, ɗaya ce kuma tai aure shekara kusan biyar data shige, kinsan anyi bikin lokacin bana nan shiyyasa ban jeba sai Salman na wakilta”.
“To aiko lallai Abba shegen nan ne Baseer mijin”.
“Ya zakice haka Suhailat? Tayaya kika san haka?”.
“Mom ko shekara nawa nayi banga Baseer ba na gansa saina ganesa, Daddy kana da
Invitation ɗin bikin?”.
“Za'a iya samu Suhailat, amma fa kinsan kusan shekara biyar kenan, ganesa sai ansha wahala”.
“Daddy bazanji wannan wahalar ba, zanje na duba inda kake tara invitation card ɗinka yanzu nan, dan rayuwar yarinyar tana cikin haɗari, na tabbata itama ba sonta yake ba, kamar yanda yay min zai mata ya gudu”.