Showing 51001 words to 54000 words out of 158267 words

Chapter 18 - Dan Adam Book 1 Complete Hausa Novel

bar..."
  "Ki bar me? Lallai nima kinaso na juya da yunwata kenan."
  Ta zaro ido tana dubansa fuskarta dauke da murmushi.
  "Ina zan so haka? Muje."
Ya bita da murmushi sannan suka dunguma zuwa tebur. 
   Da kansa ya ja mata kujera ta zauna tana jin dadi a ranta tamkar ta mike ta daka tsalle. 
    Ya zauna ya yi (serving) dinta shima ya zauna ya zuba nasa sannan ya dubeta da murmushi har lokacin dauke saman fuskarsa yana kasheta da wani irin kallon da tun da suke bata ta6a ganinsa a tare da shi ba sai idan yana tare da Munira. 
   "Bismillah."
  Itama ta kasheshi da nata salon kallon sannan ta murmusa ta soma ci, tana ci amma ta lura shi sam hankalinsa baya kan abincin. Ta dubeshi cikin alamun tambaya, ya sauke ajiyar zuciya.
  "Kinga nakasa cin abincin ko? Naga kinmin kyau ne."
   Ta yi dariya.
"Kai Deen, ba fa wani kwalliya nayi ba."
   Ya kashemata ido d'aya.
"Anya? Kamar kin yi kurkur kin shafa jan baki da kwalli, haka nake ganinki a idona."
Suka tuntsire da dariya lokaci guda. Ta shagwa6e fuska.
  "Abin har da tsokana?"
Ya yi dariya gami da lakuce hancinta.
  "Ba zancen tsokana."
Ta yi soror tana dubansa, tamkar fa a mafarki ta ke gani, anya kuwa ba mafarkin bane? Cikin dabara ta kai hannu ta mintsili fatar hannunta.
  "Wash!" Ta fad'a a fili, a rikice ya dubeta.
"Meyafaru?"
Ta dan dara.
"A'a bakomai, gaskiya ka ci abinci idan ba haka ba nima zan daina ci."
  Ta karashe gami da ture farantin, ya maida mata filet din gabanta.
"Na tuba, zan ci. Don Allah karki fasa ci."
  Sukayi dariya suka hau cin abinci. A ran Dija murna fal ya cikata, ashe akwai sauk'aki'yar hanya da zata samu zuciyar Deen amma ta tsaya shirme da wahala?
  Deen ji yakeyi kamar ya rungumeta don tsabar so da kauna, bayan sun kammala ta rigashi mikewa ta koma falon, ya bita da kallo cikin shaukin so.
    Da biyu ta koma falon tasan dole ya bita da kallon. Wayarta ta janyo ta tarar da missedcalls har goma, kasancewar a (Vibration) ta sanyata ne yasa basu ji k'arar ba. Ta dauka ta duba, duk daga Raihana ne, dogon tsaki ta ja, tabbas Raihana dagaske ta ke. Kafin ta yi yunkurin ajiye wayar kiran ya k'ara shigowa. Saida ta waiga bata hangi Deen ya taho ba sannan ta d'aga.
  "Ina jinki."
  Raihana ta marairaice murya ta hau yi mata magiya akan ta sanarmata dalilin da yasa ta k'i d'aga wayarta da wuri. Wani bakinciki ya tokare zuciyar Dija, sa'ar da Raihana ke ci awajenta bai wuce na ita din itace silar taimakonta wajen samun Deen ba. Ta daure ta 6oye 6acin ranta.
  "Kiyi hakuri, ina tare da Deen ne."
Wani bakinciki da kishi ya turnik'e zuciyar Raihana, ta daure ne kawai don tana taya masoyiyarta son abinda take so. Ta daure ta ce.
"Allah Sarki, ya ji dadinsa tunda yana samun kulawar da bansamu ba."
  Dija ta ji kamar ta shak'eta. Motsin da ta ji na Deen ne yasa ta fadin.
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

  50
  "Zan kiraki karki k'ara kirana." A hankali yanda bazai ji ba, wannan muryar ta k'ara kashe Raihana da dadi. (Wa'iyazubillah) ji ta yi kamar ta shiga wayar ta rukunkumeta, dole ta yi mata sallama ba don taso hakan ba.
     Deen ya karaso, ya kammala shirinsa zai koma ofis, ya dubeta lokacin da ta ke k'ok'arin ajiye wayar. Suka yiwa juna murmushi.
  "Har zaka koma?"
  Ta tambaya cikin kankan da murya.
Ya gyada kai.
"Zan koma, ga shi basu dawo ba kamar kada na tafi nayi zaman tayaki hira."
   Ta kasa jurewa ta dubeshi fuskarta na nuni da tsantsan farin ciki.
  "Wai don Allah kaine kuwa? Ashe akwai ranar da za ka nuna kulawarka a kaina har haka?" Sai kuma ta yi shiru a tunaninta ta yi azar6a6i, amma sai bai bata kunya ba ya amsa.
   "Idan ban kula da ke ba ai bazan iya kula da kaina ba kenan Dija, bakisan yanda nake jinki a zuciyata ba wallahi."
  Ta lumshe ido don jin dadin maganarsa gami da murmusawa. 
  "Nagode Deen, yanzu kayi hakuri ka tafi ofis, ai idan ka dawo ina gidan."
   Ya nok'e kafad'a kamar wani k'aramin yaro. 
  "Aa." Sukayi dariya. Ya kar6i lambar wayarta don a baya ba shi da, sannan sukayi sallama. Ai yana fita ta hau doka tsallen murna, daga wancan kujerar sai wannan tana yi tana dariya. 
   Ba ita ta nutsu ba saida su Munira suka dawo bayan la'asar alokacin har kiranta saida ya yi suka sha hira. A gefe Raihana na faman jaddadamata cewa ta rik'e amana ta cika alk'awari ta yanar gizo. Banda toh babu abinda ta ke cewa a fili kuwa ta ja tsaki don haushi. 
                   ***   ***   ***
                       ABUJA
  
   KB ya ji haushi matuk'a akan abinda Faruk ya yi mishi, kuma ya tabbatar muddin ya ce zaiyi wani yunkurin na daukar fansa, to fa Faruk ba karamin aikinsa bane ya tona mishi asiri. A karshe ma sai ya ga menene abin tayar da jijiyoyin wuya akan wacce yasan ya ketare a komai, saidai ya fahimci tabbas akwai wani abun a zuciyar Faruk akan Ummi. Ya yi murmushi a yayinda ya ke kwance saman kujera da misalin karfe uku na rana.
  'Baka san wacce ta dace da wacce bata dace ba Faruk, duk abina bazan ta6a ajiye 'yar aiki a matsayin matata ba. Zubda aji kawai.'
  Ya ayyana a ransa sannan ya ja tsaki a karshe ya shafi goshinsa wanda ya kumbura ya yi dariyar da shi kadai yasan manufarsa.

Misalin takwas na dare, gidan babu kowa sai kalilan cikin iyaye da kuma yan aiki, sauran duk an tafi raka Amarya Baraka gidan mijinta. Amina na hanyarta ta komawa sashensu bayan ta yi aikin da Hajiya Babba ta sanyata na watsawa gaba daya jikokin nasu ruwa da sanyamusu kayan bacci, ta gyaresu tsaf ta shafa musu hoda sannan ta barsu anan falon k'asa suna kallon(Cartoon), alokacin Faruk ya sauko da zummar neman mai kira mishi Ummi, cikin sa'a ya had'u da ita, ita kanta Amina saida gabanta ya fad'i.
  'Ina Ummi ina wannan babban goron? Tab!' Ta ayyana a ranta, a fili kuwa durkusawa ta yi ta kwashi gaisuwa ya amsa yana mai dubanta.
  "Lafiya, idan kin shiga ki cewa Ummi ta sameni a inda muka had'u jiya."
   Ta amsa da to sannan ta bar wajen, tana shiga ta tarar da ita sai faman danne-danne takeyi a wayar ita Aminan, Amina ta kwace tana jan tsaki.
  "Kefa yanzu sai ki hargitsamin ita, ya kamata ki koyi sarrafa waya sai bala'in son wayar amma babu abinda kika iya ciki."
  Sukayi dariya, Amina ta bar dariya, fuskarta ya nuna alamun damuwa da kulawa.
   "Ummi ke din kina da babban matsayi gareni wallahi, ina son don Allah ki kula ki kuma dauki dukkan abinda na gayamaki. Nasan tabbas kina son Faruk shima kuma yana sonki , saidai ki dunga tunanin ke wacece ki kama kanki. Yanzu ki tashi ki je yana kiranki, yace ki sameshi a inda ku ka had'u jiya."
   Ummi ta yi dumm ta tabbatar dukkan abinda Amina ta fad'i gaskiya ce, hakazalika kauna ce ta sanya ta kwa6arta. Ta jinjina kai tare da yin murmushi.
  "In sha Allah Anti zan yi aiki da shawararki. Daman nima ina tsoron shiga kowace matsala adalilin Yaya Faruk."
  Amina ta yi murmushin jin dadin irin wannan matsayin da ta samu wajen Ummi wacce a shekaru bai fi biyu ko daya ta bata ba. 
  "Nagode Kanwata, sai kin dawo."
Daga haka Ummi ta zura hijabinta ta fita bayan ta duba babu wanda ya ganta. Kai tsaye wajen (swimming pool) na gidan ta nufa ta murda kofar ta shiga. 
   Zaune ta sameshi yana waya, ya juyo yana dubanta yana cigaba da wayar, alama ya yi mata ds ta rufe kofar, hakan yasa ta juyawa gami da rufewa, itama zata fi son hakan kada wani ya iskesu tare. 
   Tana kokarin durkusawa ya ja hijabinta hakan yasa ta dubansa.
  Da ido ya yi mata alama da ta zauna gefensa akan daya kujerar. Ta numfasa gabanta na dukan tara-tara ta zauna. Ko kamshin turaren Faruk ta ji, takan ji sauyi a jini da tsokarta, ballantana akai ga jin muryarsa da kuma kallonsa. 
     Tunda ta zauna bata dubeshi ba, shine ma ya karkato yana amsa waya yana karewa fuskarta kallo. Ga dukkan alamu da ogansa awajen aiki ya ke magana, ganin yanda ya ke bawa mutumin girma hakazalika batu ne na kudade da wasu takardu sukeyi. Maganarsa tafi yawa da harshen turanci.  A jikinta ta ji yana kallonta, ta dan juyo ta saci kallonsa, ya kuwa kafeta da ido kafafunsa saman kujerar ya tankwashesu. Ta kauda kanta ta yi shiru, ji ta ke tamkar ba zata iya rabuwa da Faruk ba, saidai hakan dole ne agareta, ko ta karfi ko kuma ta lumana. Ta karfin kuwa, daga yan uwa da danginsa ne, wadanda a karshe zasu ci zarafinta su korata kauyensu, ta lumanar kuwa shine ta bi shawarar Antinta wanda idan har ta kiyaye to fa baza'a kai ga sauran matakan ba masu ciwo. Saida ya kammala wayar sannan ya ce.
  "Bari kiga na kashe wayoyinnan, ko waye zai k'ara nemana saidai ya hakura na kammala da iyalina ko?"
  Kanta ya yi dumm, jin kowanne kalamansa ta ke yi tamkar sun fi gwal da daham tsada a wajenta. Da a bata komai na jin dadin rayuwa ta gwammace a mallakamata Faruk a matsayin mijinta, saidai me? Wutsiyar rak'umi ta yi nesa da k'asa.
Tunaninta ya katse sa'ilin da ya dora wayoyinsa a saman cinyarta. Ta dago ta dan dubeshi fuskarsa babu alamun wasa hakan yasa ta maida kanta ga duban wayoyinsa biyu manya wadanda ta tabbatar masu tsada ne saidai hankalinta yafi karkata ga son son jin abinda zai fito daga bakinshi.
   DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  53
   Washegari kuwa tun safe mutane suka soma tafiya, yan Adamawa kaf dinsu suka fice, Gwaggo surukar Mami bata zo wannan karon ba saidai ta aikowa Mami tsaraba hakanan ta aikowa Hajiya Babba g2udunmuwa. 
     Sai bayan Azahar su Mami suka soma shirin tafiya. Ummi suma sun kammala hada komai nasu ta tsinci sak'on kira daga Mami. Mamin na daki daga ita sai Ihsan wacce jin cewar zata karasa hutunta a gidan su Faruk ya sanyata kasa rufe baki don tsabar farinciki. A haka Ummi ta shiga ta riskesu, Mamin na faman kimtsawa don tafiya. 
   Bayan an gaisa ta ce. "Gani Mami."
Mami ta dubeta.
   "Yauwa Ummi, anan za ki zauna har muga abinda hali ya yi, saidai bayan komawata tukunna."
  'Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!' Shine abinda Ummi ke ambata a can kasan ranta, ta ya ya zaayi a barta a gidan su Faruk, ina laifin ma idan sun je Kano ta je koda gidan su Hajiya Mama ne ko gidan su Inna?
  'Ai ba danginki bane.' Cewar wani sashen zuciyarta. Ta ji babu yanda ta iya don yan uwannata basu ma damu da sha'aninta ba. 
   "Wai bakya ji ne wani sabon wulakanci ana ta yi ma ki magana kin yiwa mutane banza kamar tsararki?"
  Maganar Ihsan kenan wacce ta maidota hayyacinta batare da shiri ba.  Ta dubi Ihsan din wacce a take ta watso mata harara kamar idanunta zasu zazzago, gaba daya bakin cikin jin cewa har Ummi itama anan zata zauna ta ke, kamar ta shak'eta haka ta ke ji, tsaki ta ja ma a karshe ta fice daga dakin cikin kunar rai. 
    Ummi ta maida hankalinta ga Mami.

"Toh Mami. Allah Ya kaiku lafiya, Ya gyara lamura."
    Har cikin ran Mami ta ji dadin addu'ar.
   "Amin. Kina iya tafiya."
  Ta mike jikinta babu kwari ta fita, tana zuwa dakinsu ta fad'a saman katifa ta yi tagumi. Haka Amina wacce ta fita kai kaya mota ta shigo ta risketa.
  "Aa ya ki ka zauna, yanzu fa zasu fito."
  A sanyaye ta dubeta ta sanarmata yanda Mamin ta ce. Amina ta numfasa.
  "Allah Ya sa alheri ne ya tsayar da ke Ummi. Nidai fatana ki kiyaye dukkan nasihuna gareki, ban zama mai cutarwa gareki ba."
   Ummi ta yi yak'e tana duban Amina.
"Wallahi Anti babban ma fargabata bai wuce Ihsan ba, na tabbatar zan sha wulakanci daga gareta."
  Amina ta girgiza kai da dan murmushi saman fuskarta wanda na yak'e ne.
  "Karki damu Ummi, Allah Yana tare da ke. Kedai kiyi takatsantsan da lamura, bari naje kada su Hajiya Mama su rigani fitowa."
     Ummi ta mike sanye gami da zura hijabinta a saman riga da siket na koriyar atamfa ta bi bayanta. 
     A fusace ta shiga dakin babu ko sallama, hakan yasa su Ikram, Intisar harma Anti Aisha da Rahila dubanta.
  "Ke lafiyarki kuwa? Ku ganemin yarinya kamar mai iskokai yanzu kika fita kina murnar za'a barki garin masoyinki, kin shigo kuma kina fushi, meyafaru?" Cewar Rahila kenan.
   Ihsan ta zauna gefen gado inda Aisha ke sanyawa Tahir famfas ta ja tsaki.
"Wai don Allah meyasa Mami ta ke yin haka ne? Ya zaayi don nima zan zauna anan ace itama Ummi nan zata zauna? Wannan abun ya isheni, Mami bata da masaniyar yanda na tsani yarinyarnan wallahi da bata soma cewa ta zauna inda nake ba."
   Mamaki ya bayyana a fuskokinsu.
"Sannu sarauniyar wauta, sai akace zamanku a rumfa daya yana nufin matsayinku daya? Kai wallahi har gobe banga randa kuruciya zata fita kanki ba Ihsan."
  Fadin Rahila kenan kafin ta fice daga dakin rataye da jakar kayanta.
   Dariya sauran suka sanya, Intisar ta ja rigar Ihsan kadan.
  "Kina bani mamaki, kodai kishi kikeyi don Ummi ta fiki kyau ne? Wannan tsana haka?"
  Ihsan ta yamutsa fuska, kusan ma har da hakan saidai ita kanta tasan da abu k'alilan zata fi Ummi, shi dinma wuyarta Ummin ta samu hutu kamar yanda ta ke samu. Saidai kuma ta fusata sosai da zancen Intisar. Ta mike a fusace ta fita suna mata dariya wanda hakan ba karamin k'ara rura wutar kiyayyar Ummi ya yi a ranta ba.

    Amina da Ummi sune suka taimaka wajen fidda jakunkuna, Ummi a sace sai sharar hawaye take yi don har cikin zuciyarta bata so zaman garin Abuja, ga kuma fargabar kada Faruk ya yi wani abun da zai janyo mutan gidan su fahimci manufarsa a kanta. 
   Haka suka tafi banda Adnan wanda ya ce ko zai koma ba yanzu ba. Mami dai ganin bai gama hucewa ba ne yasa ta kyaleshi. 
    Ummi ta juya jikinta a sanyaye zata koma ciki, Ihsan da suka hada ido harara da dallara mata, Adnan kuws murmushi ya sakarmata.
  "'Yar Abuja." Ya fada cikin tsokana, murmushin yak'e ta yi mishi. Tana shirin barin wajen ta tsinci muryar Ihsan bayan Hajiya Babba ta riga ta koma ciki tana fadin.
  "Rashin dangi ne yasa ta ke yawo daga nan zuwa can, duk dai abin mutum bazai chanja iyaye ba. Kauyen dai da ake gudu nan ne asali."
   Daga haka ta tsinci muryar Adnan yana mata sababi bayan ya kai mata bugu ta kauce. Daidai da su Intisar basu ji dadin abinda ta aikata ba.
  "Bansan halin wa kika biyo ba, don danginmu ba ma wulakanta mutum, muna girmama DAN ADAM daidai gwargwado." Cewar Intisar kenan sannan ta juya ciki ranta babu dadi.
  Haka suka watse suka bar Ihsan cike da k'ara jin haushi da tsanar Ummi a nata ganin duk a kanta akeyi mata hakan. 
    Ita kuwa Ummi duk yanda ta so shigewa daki kai tsaye don kanta da ta ke ji yana sarawa ga kuma wani kuka da ya ke tahomata hakan bai samu ba sakamakon kiran da Hajiya Babba ta yi mata. Ta karasa ta durkusa cikin ladabi.
  "Gani Hajiya."
Hajiya ta dubeta fuska a sake.
"Yauwa Ummi, sai kuma kika ga an barki a wajena ko? To ina so muyi zama na tsakani da Allah da ke, daman na riga nasan da kyawawan halayenki daga bakin Madina, ki k'ara a kan hakan. Gyaranki na dakina ne sai falon sama da kuma wannan na k'asan. Sauran dakunan kuwa suna karkashin kulawar Binta. Girki daman ba aikinku bane da wanke-wanke, kinji ko? Akwai mai yi na kwanaki ma ganin bak'i da yawa yasa nake cewa ku shiga, fatan kin fahimceni?"
  Ummi ta jinjina kai, ranta ko digon farinciki babu sakamakon har lokacin ranta a tsananin 6ace ya ke. 
     "Na fahimta Hajiya kuma in sha Allah zan kiyaye zan kula."
    Hajiya Babba ta ji dadin furucinta ta sakarmata murmushi.
  "Na lura dai ranki bai miki dadi ba akan zaman da za ki yi anan, karki damu, na dan lokaci ne, da zarar na sanya an samomin wata za ko tafo, mai yiwuwa ma tare da su Ihsan."
   Jin an k'ara ambaton Ihsan sai ta ji duk zancen ya gundureta, ta daure ta k'akalo murmushi.
  "Lah bakomai Hajiya, ai can da nan din duk daya ne."
   Daga haka Hajiya ta sallameta. Tana shiga daki ta zube saman katifa, a hankali maganganun Ihsan suka dawo mata kawai sai ta fashe da kuka sosai har tana sheshshek'a. Wannan rayuwa ta soma isarta, Ihsan ta soma kaita bango, abin nata yana neman wuce gona da iri, ko don tana ganin ita din bata da wani karfin ikon da zata kwaci 'yancinta ne? To wane 'yanci ma ta ke da shi a yanzun tunda ba wani babban jigo abin tunk'ahonta wanda zai iya yin wani kata6us akan lamuranta? Kewar mahaifiyarta yafi komai damunta, ko babu komai ta tabbatar ba zata watsar da ita kamar yanda Mahaifinta ya yi ga rayuwarta ba. 
   A karshe dai wani sashe na zuciyarta ya yi ta nusar da ita da muhimmancin Yarda da Kaddara, haka har dai zuciyarta ta danyi sanyi ta mike don d'auro alwalar La'asar.
         
   Yana zaune saman kujera a ofis cike da dumbin tunani da damuwa, ya daga kai ya dubi agogon bangon dake a ofishin nasu, agogon ya nuna karfe hudu saura mintuna uku, ya ja guntun tsaki gami da dafe goshinsa. Ya san zuwa wannan lokacin sun wuce, tabbacin farin cikinsa ta tafi saidai hausawa sun ce garin masoyi baya nisa, yasan ko yaushe ya yi niyya muddin ranar babu aiki zai iya kai mata ziyara. Saidai zai so matuk'a tafiyar ta kasance babu ita.
  'Akan wane dalili?' Cewar sashe na zuciyarsa, ya runtse ido gami da jingina kansa jikin kujera.
 
   
   

 
         
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

51
   "Ummi, ina muka kwana a zancenmu na jiya? Abin nufi me kika

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login