Showing 78001 words to 81000 words out of 158267 words
Dakta saidai kunya ce ta hanashi zuwa gidansa ya ba shi hakuri, wai shine ya nemi yi mishi rashin kunya akan ya ta6a matar da ya ke ji cikin zuciya da gangar jikinsa. Maganar Haidar ta katseshi.
"Batu kuma na Ihsan, wannan ba yanda ka iya, ka zamo mai biyayya ga umarnin iyaye ko don ka cika d'a nagari. Ka yawaita addua akan neman za6in Allah ka ji?"
Ya zauna a karshen matattakala batare da ya bude kofa ya shiga ba falonnasa ba, murmushi dauke saman fuskarsa na jin dadin maganganun dan uwansa ya ce.
"Na ji Brother, zan yi yanda ka ce, bari na yi wanka nayi breakfast, zan je gidan Dakta idan ma ban sameshi ba zan shiga asibitin."
Ya ji dadin maganarsa.
"Yauwa that's my lovely brother, haka nake son ji. Nasan anjima zai shigo, gwara ka je kafin shigowarsa, nima ina nan tafe bayan Magriba idan Allah Ya yarda, don na k'ara ganin surukartamu da akai mana 6oyon fuskarta."
Dariya Faruk ya yi kafin suyi sallama ya mik'e ya fad'a d'akinsa.
*** *** ***
RINGIM
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
72
A farfajiyar gidan suka hadu da Anti Amarya wacce ta dawo daga gidan wata kawarta, ta lura da yanayinta saidai baki kawai ta saki tana kallonta, Hajiya Mama itama ganinta ne yasa ta dan saita kanta duk da kuwa bai hana komai 6oyuwa ba. Anan kofar gidan ma Adnan ya dawo daga yiwa wasu abokansa sallama sakamakon tafiyarsa da ta k'arato nan zuwa kwana biyu ya ci karo da ita, daga yanda ta amsa sallamarsa ma yasan ba lafiya ba, ta shiga mota direba ya ja suka bar wajen. Hawayenta ya kasa tsayuwa, wannan wane irin rana ce ta zo musu? Kamar yanzu ne suke wasa da dariya da kanwartasu, ace har lamari na aure ya had'asu rikici na ban mamaki. Wai yau Madina ce ke kiran sun ci amanarta, ta nuna suna mata son kai, wannan abu da me ya yi kama? Har take nuna basu suka haifi Ihsan ba ga da ga.
Ran Hajiya Mama ya k'ara jagulewa, ta kasa hadiye kukanta, haka hawayenta ya yi ta zubowa tana daukesu da mayafinta. Babu abinda ta fi tunowa sai yanayin shakuwarsu tun suna k'anana har zuwa girmansu, yau sa6ani ya shiga tsakaninsu akan auren Ummi da Faruk.
Ta runtse ido.
'Madina ina kika mance tarbiyyar da iyayenmu suka bamu? Yaushe kika chanja daga kyawawan d'abi'unki? Ya akayi kika bari son 'yarki ya rufemiki ido har haka? Wannan abu abin kunya ne ya shiga kunnen iyayenmu. Abin kunya ne gareki idan Hajiya Babba ta ji wannan lamari.' Tana dukkan wadannan maganganun ne cikin zuciyarta. Akan hanya wayarta ta yi k'ara fiye da sau biyu amman ta kasa d'auka, tsoron dagawar ma takeyi, me zata iya cewa Hajiya Babba? Sam bazata iya da wannan abin kunyar ba wanda ta ke ganinsa tamkar a mafarki.
Adnan cikin sauri ya shiga wajen Maminsa, saidai bata falo hakan yasa ya nufi dayan falonnata, nan ma batanan, a karshe ya yanke hukunci shiga dakinta. Gefen gado ya sameta zaune tana kuka. Hankalinsa idan ya yi dubu to yau ya tashi, ya isa gabanta ya durkusa.
"Mami meke faruwa ne? Ga Hajiya Mama ta fita hankalinta a tashe tana hawaye, kema ga ki na tarar dake kina kuka, rasuwa akayi ne?"
Ta share hawayenta.
"Da rasuwa ce to da sauki don ansan tana kan kowa, wannan yafi mutuwa k'ona zuciya Adnan. Yau akan Ummi har Hajiya Mama ta mareni, sai nace tun tasowarmu da ita sa6ani irin haka bai ta6a shiga tsakaninmu ba."
Kansa ya danyi dum, ya kasa tantance tak'amaiman yanayin da ya shiga.
"Ummi kuma?" Ya furta yana dubanta.
"Kwarai kuwa." Ta kwashe maganat ta gayamishi, ya dan ji hankalinsa ya kwanta, daman ba yau ya fahimci akwai wani abu a zuciyar Faruk game da Ummi ba, shi yasan daman irin haka zata faru wataran, Faruk ya ce zai auri Ummi. Saidai Ihsan fa? Bai ta6a kawowa tana son Faruk ba. Tabbas shi bai ga aibu a had'asu ya auresu ba.
"Kayi shiru?"
Ya dago ya dubi mahaifiyarsa.
"Mami shi fa lamari na aure Allah ne Ya tsara abinsa, babu wanda zai chanja kaddararsa. Kuma..."
"Tashi ka ficemin! Shashasha kawai da baisan kishin nasa ba."
Sum-sum ya fice don ya lura ta shiga cikin zafi, da alama babu abinda zai iya fadamata a yanzun ta fahimta. Har ace ta manta irin gwagwarmayar da ta sha a baya wajen Abbansu, har ace zata mance komai na duniya rubutaccen al'amari ne, idan Allah Ya yi za'ayi, za'ayin?
Ya waigo yana mai dubanta, waya ya ga ta dauka ta na kokarin kira. Gabansa ya fad'i kada fa ta ce zata kira Hajiya Babba. Da sauri ya isa gareta ya rike hannunta.
"Don Allah Mami karkiyi haka, ki duba zumuncinku, kada a sanadin abinda bai kai ya kawo ba ki 6ata kyakkyawar alak'arku da yan uwanki wadanda kowa ya gani sai ya yi sha'awarta." Sai kuma jikinta ya danyi sanyi, ta dubeshi fuskarta har lokacin a daure.
"Tashi ka ficemin Adnan tun ban kai ga ta6a lafiyarka ba."
Ya tashi jiki a sanyaye ya fice, bata fasa kiran ba saidai jin da ya yi Ihsan ta kira ta ke tambayar ko ta taho, hankalinsa ya dan kwanta.
*** *** ***
ABUJA
Hajiya Babba duk ta bi ta damu akan rashin amsa kiranta da Kanwarta Sadiya bata yi ba, batason kiran Mami tukunna.
Ihsan ta shigo da sallamarta ta yi shirin tafiya don tuni an fita da kayanta, sam lokacin ma batasan anfasa tafiyar da Ummi ba. Ganinta yasa Hajiya sakin fuska tana dubanta.
"A'a, d'iyata har an fito?"
Fuskar Ihsan ba walwala sosai ta amsa.
"Eh Hajiya, an fita da kaya ma."
Hajiya ta gyada kai.
"Zo ki zauna mu danyi wata magana."
Ta zauna a gefen Hajiyar kamar yanda ta umarceta.
"Ihsan inaso kiyimin kyakkyawar fahimta akan maganar da nakeson yi dake. Zamanki anan tare da mu yasa na fahimci kamar kina son Sadauki, ban tabbatar da hakan bane saida naji daga bakin Ikram. To sai kuma Sadauki ya zo mana da zancen Ummi tashi guda da sunan ita ya ke so da aure. Saidai ya amince zai hadaku tare ya aura. Ina fatan baki da matsala akan hakan?"
Takaici ya hana Ihsan magana, lallai ma ta yaya ake zaton za ta yi zaman kishi da 'yar aikin gidansu? Wannan ma jawowa kai raini ne wallahi. Haushin Hajiya ma ya hanata cewa uffan har lokacin kanta yana k'asa.
Hajiya ta yi shiru tana karantarta, sai kuma ta numfasa.
"Ki je Ihsan ki yi tunani, bazan matsamaki ba. Ke tawa ce, bazan k'i farincikinki ba kema, bazan kuma so k'untata miki akan wata ba. Dake da Sadauki abu daya na daukeku, babu wanda zanso shiga hakkinsa."
Ihsan ta sauke ajiyar zuciya.
'Kedai kome za ki ce daga baya ne kin riga kin nuna son danki fiye da kowa."
Cewar Ihsan a zuciya. Shigowar Binta ce ya katse maganar. Suka amsa sallamarta.
"Ya ce ta fito."
Ta mike Hajiya na mata adduar komawa lafiya itama tana godiyar abubuwan alherin da suka bata. Saida zata shiga motar ne ta dubi Ikram.
"Wai bada Ummi za mu tafi ba?" Kafin Ikram ta amsa Hajiya ta amsa.
"Ki je zata zo."
Ran Ihsan ya k'ara yin bak'i, kenan plan dinsu da Ikram ya tashi a banza? Niyyarsu da zarar ta koma Kano a koreta sai aga ta aurenta da Faruk, ranta ya yi wani irin daci, a fusace ta shiga motar ta banko murfin. Mamaki ya kama Hajiya, anya babu wata a k'asa? Daman ta lura kamar bata yi na'am da maganganunta ba. Haka ta bi bayan motar da kallo, tuni haushi da 6acin rai yasa Ikram juyawa ciki. Watakil nan gaba ma Ummi ta zama mai mulkar kowa a gidan, don taga alama ta samun kar6uwarta wajen Hajiya da Daddy. Acewarta DAN ADAM tara ya ke bai cika goma ba, zasu ga hali na butulci da Ummi za ta yi musu nan gaba indai akayi auren. Don ta sha jin labaru na irin hakan.
Ummi duk tana kallon abinda ke faruwa, daman tun jiya da dare Hajiya ta sanarmata an fasa tafiyar da ita, sannan Faruk ya kira ya bata tabbacin kada ta sake ta shirya da zummar komawa Kano, ta daina aikatau daga ranar.
Ta saki labulen kicin din gami da sauke ajiyar zuciya ranta ya danyi haske, ko babu komai alwashin da Ihsan ta ci akanta bazai tabbatu ba. Yanzu ita ina tasan zata ta samu motar garinsu idan suka korata? Saidai da tambaya kam. Ita har fargabar komawarta Ringim take, ko wane k'alubalen zata fuskanta a wajen Saude da Babanta?
"Ke!" Ta firgita matuk'a ta juyo idanunta a zare kirjinta a sama don ji tayi har numfashinta ma kamar yana barazanar daukewa. Ganin Binta yasa ta dafe kirjinta gami da rufe ido tana sauke ajiyar zuciya. Dariya sosai Binta ta sanya, Ummi ta girgiza kai.
"Wallahi ba ki ji yanda na tsorata ba, kai Binta saiki kashe mutum."
Binta cikin dariya ta daga mata hannu.
"Yi hakuri, daman cewa nayi bari nagani ko za ki tsoratan, na manta yanzu ke fa a tsorace kike da kowa ma."
Ta yi murmushi tana tattare tafarnuwar da ta zubar a k'asa don kid'ima.
"Na yi zaton Ikram ce ko Ihsan din ce ta dawo."
Sukayi dariya. Kafin kuma Ummi ta cigaba da 6arar tafarnuwa.
Binta ta dubeta sa'ilin da ta janyo robar kifin da ta saka a ruwa don ya yi kankara ta soma kokarin gyarawa.
"Wai ni don Allah meyasa ban ta6a jin kin fad'i wani daddad'an kalami na soyayya ba game da Yalla6ai? Sai nake ganin kamar ya fi sonki fiye da yanda ke kika daukeshi."
Wannan tambaya ta Binta, yasa Faruk cin burki daga kofar kicin don ya zo ne daman da niyyar tuhumar Ummi dalilinta na barin waya a daki ga shi yana ta kira.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
74
RINGIM
Bud'a ne ya cika gidan Baba Habiba sakamakon auren da aka daura na Zahraddeen da Khadija. Yawanci gaba daya danginta ne suak halarci bikin, daidaiku ne cikin dangin Malam Yahuza suka zo, wadanda zuwansu ma ba amfani awajen Baba Habiba don acewarta sun zo kwasar rahoto da gulma.
Ita da aminiyarta Saude sun yi shiga ta sutura har kala uku ana yi ana chanjawa, Amarya kuwa kusan kala biyar ta yi domin wannan ranar. Da yamma Amarya na cikin taron jama'a suna gaisawa, wata yar uwarsu ta zo kiranta.
"Kizo kinyi bak'i fa daga Kano." Ta bi bayanta da mamaki don iyakar saninta bata da kowa a Kano. Gabanta ya bada wani bugu mai karfi ganin Raihana cikin shiga ta wata shegiyar shadda mai tsadar gaske, daidai da sark'ar da dan kunnenta abin kallo ne, ballantana kuma idan ka dubi agogo da awarwaronta kasan na gwal ne. Tana da 'yar k'iba hakanan doguwa ce, ba laifi tana da kyau daidai gwargwado, wacce suke taren itama ta ci nata adon har ta gaji da haduwa. Murmushi Raihana ke jifanta da shi da wani dan iskan kallo wanda bai kyautu a matsayinta na yar uwarta mace ta yi mata ba. Ta daure ta k'ak'alo murmushin yak'e ganin cewa cikin mutane ne.
"A'a, Raihana kece a garinnamu? Sannunki da zuwa."
Raihana da har lokacin bata bar murmushi ba ta amsa.
"Yauwa Dijat , ke kuma haka akeyi?"
Dija ta rude gudun kada ta ce wani abu da mutane zasu dagosu, tana shirin kwa6arta Baba Habiba ta karaso wajen duk ta had'a zufa saboda shiga da fita. Ganinsu yasa ta washe baki kamar gonar auduga, ta bisu da kallo daga sama zuwa k'asa sannan ta dubi Dija.
"Wadannan fa?"
'K'awayena ne na yanar gizo, sun zo tayani murna ne."
"A'a sannunku kun ji ko? Ina wuninki?"
Ba kunya ta gaishesu, kasancewar suma yan duniya ne sai suka amsa.
"A'a baza'a barsu anan ba kinga nan a cike yake, kaisu gidan Saude su zauna. Bari na kar6o muku muk'ulli."
Daga haka ta karasa ga Saude ta Kar6o ta damk'awa Dija.
"Jeki can na kawomiki kazar ma ki ci acan kinga asiri a rufe." Ta fada cikin k'ank'an da murya. Dija ta murtuke fuska.
"Aa, ki barshi sai dare.". "To shikenan."
Ta ja su Raihana zuwa gidan Saude. Bayan sun zauna Raihana ta rik'o hannunta idanunta sun kada tsabar kishi.
"Ba ki kyautamin ba Dijat, yanzu wannan kwalliyar duk don Deen kikayi ba don ni na ganki na ji dadi ba? Haba Dijat, ba ki ta6a yimin kwalliya irin haka kin aikomin na gani ba." (Wa'iyazubillah)
Dija ta daure fuska gami da zame hannunta.
"Ki bar wannan magana mana Raihana, ke meyasa kike da sa6a alk'awari? Ban gargadeki kada ki zo gidanmu bane?"
Raihana ta yi raurau da fuska.
"To ya na iya tunda dai kin kashe wayarki kwana biyu bana samunki, ni kuma hankalina duk ya tashi na ji tsoron kada ki juyamin baya shine na zo."
Dija ta ja tsaki sannan ta mik'e.
"Ina zuwa." Daga haka ta fice, Raihana da abokiyar tafiyarta, Saima, suka bita da kallo cike da shaawa.
Saima ta maido dubanta ga Raihana.
"Ashe dai a kauye ana samun mata har haka? Ke kam kinyi dace."
Ta daure fuska.
"To meye naki ciki?"
"Aa, bakomai ranki ya dade, ni mamakin ma da nakeyi ya zaayi kamarki ki zauna wai wannan ta gagareki juyawa? Haba Hanah, dubun da suka fi ta ma kin shawo kansu ta hanyar malamai balle kuma ita?"
Raihana ta numfasa.
"Ni wannan so nakeyi mata na gaske, ba don ta kafe akan wannan shegen Deen din ba da har aurenta zan so yi. (Waiyazubillah) saidai ya zo yana son yimin shigar sauri."
Saima ta jinjina kai, lallai ba karamin so take yiwa Dija ba, banda haka, manyan mata nawa ne suka so samun wannan damar amman ta k'i basu sai ita?
Duk yanda taso ta shawo kan Dija abu ya ci tura don kwata-kwata bata bada fuska ba, ta ce ko menene sai ta je Kaduna, haka gwuiwa a sake Raihana ta juya bayan ta bata makudan kudade da suka girgizata.
Washegari aka tattarata aka mik'a Kaduna gidan Deen, har lokacin Munira bata dawo ba tana Ringim don ta ce bazata iya ganin rawar kan da mijinta zaiyi akan yar uwarta ba da ta ci amanar yan uwantaka.
Gudu ta ke yi itama tana binta a guje suna k'ara runtumawa cikin dajin da babu gida gaba babu a baya, har ya kai ta taka k'aya, ta zube a wajen tana numfarfashi, takobi ne shar6e6iya sai kyalli ta ke, doguwar mace kyakkyawa ce rik'e da wuk'ar kafin akan idanunta ta fuskarta ta rikid'e zuwa kalar kore.
"Saina kasheki! Saina kasheki ke Makira!!"
Tana ihun kuka tana fadin kiyi hakuri na tuba Hasiya karkimin haka don Allah. Amma ina bata ko saurareta ba ta daga takobin nan, ai kuwa ta fasa k'ara.
Yi ta ke babu kakkautawa duk ta hargitsa mutanen dakin, suka rirrik'eta, fadi take. "Zata kasheni! Wayyo zata kasheni wallahi! Ku taimakeni!" Cikin gigita Saude ta kai hannu ta toshemata baki.
"Ke Habiba shiga taitayinki, mafarki kikayi?"
Sai lokacin Habiba ta gane ta farka, ta dubi jama'ar dakin 'yan rakiyar amarya Kaduna ta sauke ajiyar zuciya gumi yana ta tsastsafowa daga goshinta, ita kuwa Habiba idanunta a zazzare, rashin gaskiya ya bayyana k'arara akan fuskarta. Tana jin matan na fadin addua ya dace ta dungayi idan ta yi mafarki. Har dai kowa ya koma makwancinsa. Dabara ta fadowa Saude.
"Tashi muje ki sha ruwa."
Suka mike suka fita zuwa kicin, ta dakata gami da rike kafadar Habiba.
"Gayamin wane irin mafarki kika yi?"
Habiba wacce har lokacin jiki ke rawa ta zayyanemata komai, hankalin Habiba ya tashi, ji ta yi hanjin cikinta sun kad'a.
"To, meke shirin faruwa haka? Mun shiga uku."
"Ba ke kika shiga uku ba Saude, ni da na ganta ganin idona ai ni ce da shiga uku."
Saude ta dubeta da idanunta da sukayi kwalkwal.
"Kada fa allura ta tono garma?"
"Kar ki damu, da zarar mun koma zanje wajen bokanya, ko menene zata sanarmana sai a dauki mataki."
Saude ta jinjina kai cike da gamsuwa. A karshe suka koma makwancinsu batare da ko ruwan Habiba ta iya sha ba.
*** *** ***
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
75
KANO
Da yamma suka isa, direba na fakin, ta sauko daga motar a hargitse, tana rataye da jakarta ta hannu. Sukayi kici6us da Iklima wacce ke shirin fita zuwa makwafta, daga ita sai doguwar riga(fitet gown) da mayafi karami kalar kayan. Ta watsamata kallon tara saura.
"Akwadaita an dawo?"
Ihsan ko kallonta bata yi ba ta gifta ta wuce. Iklima ta bita da kallo gami da sakin dariya, batasan meyasa yanzu gaba daya ta tsani Faruk ba, wani mugun so ta ke yiwa dan wata k'awar Hajiya Binta, Mu'azzam, shima sonta ya ke yi tamkar ya mutu.
Ihsan bata zarce ko'ina sai sashensu, tuni Fahad ya isar da zuwanta ga Mami wacce ke kicin tare da Ramma suna aiki, saidai duk fuskarta babu digon walwala. Jin zuwa Ihsan yasa ta fito, Ihsan na shiga itama uwar ta hau kwalawa kira. Suna yin kici6us ta fad'a jikinta gami da ruk'unk'umeta ta soma hawaye. Mami ta lumshe ido tana mai rungumeta, ta riga tasan meke damunta.
"Aa lale da manyan gari." Maganar Ramma ya katse tunaninsu, jin hakan Mami sakinta.
"Shiga ciki ina zuwa."
Bata ko amsa sannu da zuwan Ramma ba, ta yi gaba abinta, wannan ya bawa Ramma tabbacin akwai matsala kenan. Mamin tasa Ramma mik'amata kayan sama. Tana jin Ramma na fadin. "To ita kuma Ummin tana ina?" Saidai babu mai amsamata, koda ta shiga dakin Ihsan harara ta samu da ta kulata. Ramma ta kama baki.
'O'o, ko ta yi gamo ne a hanya?' Ta tambayi zuciyarta don tasan ba mai amsamata. Ta fice tana jimamin wannan lamari na sauyin da aka samu daga uwar