Showing 93001 words to 96000 words out of 158267 words

Chapter 32 - Dan Adam Book 1 Complete Hausa Novel

bayan yan uwansa sai ya wuce dakin da aka saukesu. 
    Ita dinma da sauri ta yi ciki, yau wani Faruk din ta gani ba wanda ta sani ba, wannan Faruk din ya tsorata ta. 
     Koda ta koma sama, a falon daga Hajja sai Hajiya Babba zaune suna hira sai kuwa Modibbo dake gefe yana jan carbi. Ta wuce a sannu ta yi dakin da aka basu don kwana. Gaba daya masu kwana tare da ita basu nan sai Baba karami(mai sunan daddy), Amal da Yasmeen. (Yaran Babban Yaya) da kuma Ma'aruf da Ahmad (Yaran Dakta) suna wasansu saman gado.  A dakin kusa masaukin su Jidda ne ta jiyo shewa da hirarrakinsu. 
  Zata zauna saman gadon ne ta ji Ma'aruf na fadin.
"Ke! Karki zauna a gadon nan, wari ki ke yi."
  Ta yi shiru tana kallonsa, ba laifi bane don ya yi mata, ya danganta da abinda aka fadamasa a kanta.
"Lala lala, sai na fadawa Grandma, ka manta abinda ta ce mana? Ita fa Uncle Faruk zai aura." Cewar Baba Karami kenan. 
  Ta dubi fuskar Ma'aruf ganin yanda ya ke yamutsa fuska.
"Ai Momi ta ce mana 'yar aiki ce, ko boko ba ta yi ba ko?"
  Ya fada yana duban kaninsa Ahmad wanda ke yin doki da filo, Ahmad ya gyada kai.
"Eh, Momi ta ce kuma kada mu dunga kulata."
   Amal a guje ta yi hanyar waje tana fadin.
"Sai naje na gayawa Grandma."
Da sauri Ummi ta rikota tana murmushin yak'e.
  "Dawo kinji, rabu da su."
Amal cikin kalar tausayi ta ce.
"Gashinan sun sanyaki kuka."
Ummi a wayance ta share fuskarta.
"Ba kuka nake ba abu ne ya shiga idona."
"Lah Uncle fa ya ce mu daina k'arya kuma kin yi."
  Cewar Amal, yarinyar ta burgeta, ta yi murmishi har cikin ranta.
"To na daina, jeki ku yi wasanku bazan zauna saman gadon ba."
  Gefe ta zauna tana danna waya saidai zuciyarta cike fal da damuwa, Amal ta matso.
"Lah Anti kina da game?"
Ta yi murmushi kadan.
"Akwai, za kiyi ne?"
"Eh."
Nan ta kunna mata, suma yaran duk suka matso zasu yi, Ma"aruf yana gefe yana kallo, yana son ya ce zaiyi saidai ba dama, sai kuma ya mike ya nufi waje yana fadin.
"Ai nima Momina tana da game bari na amso wayarta."
Murmushi kawai ta bishi da shi har ya fice. 
    Haka sukayita jagwalgwala wayar tana kallonsu har chaji ya kusan k'arewa sannan ta kar6a ta jona ta. Tana jin bacci saidai batason hawa gadon ace ta yi laifi, haka ta kwanta nan saman darduma. Har ta soma bacci ta ji wayarta ta dauki k'ara, mikewa ta yi tana salati, har lokacin basu shigo ba, yaran ma sun gaji da wasa sun kwanta. Ganin Faruk yasa ta yin murmushi kafin ta dauka duk a gajiye don muryarta ma ta nuna. 
  "Bacci ki ke yi wai?"
"Eh."
"Shikenan bari na kyaleki saida safe." Ya fada cikin dauriya don shi kam tunaninta ya so ta6a nasa baccin, suka yi sallama daidai lokacin su Ikram suka shigo. 
  "Wai yarannan bacci suka yi anan? Lallai ma, ke kuma kina kallonsu idan suka yi mana fitsari fa?"
Fadin Ikram kenan. Baraka ta dubi Ummi don ita sam bata ko lura da ita ba ma.
"Tashesu su wuce dakinsu."
  Bata ji ko darr a ranta ba, don ita bata jin kanta a wata har yanzu ballantana ta musa musu, haka ta tashesu ta mik'asu wajen iyayensu inda akayi musu shimfida a k'asa, saidai ta sanyasu fitsari kafin ta kwantar da su, tuni Intisar ta yi baccin don ga gajiya ga kuma ciki. 
  "Saida safenku." Ta fada bata ko saka ran zasu amsa ba sai kuma ta ji sun amsa din sannan ta rufemusu kofa ta koma dakinnasu. 
   Nan ta kwanta k'asa gami da yin filo da hannunta, babu wanda ya ce mata uffan, tana ji suna yara fulatancinsu suna dariya, sai ta juyamusu baya don duk ta tsargu.
  Basu jima da hakan ba sai ga Hajiya Babba ta shigo. Suka amsa sallamarta, ta shigo ciki sosai. Daman tasan hakan zai iya faruwa, ta daure fuska.
"Ke kuma mene na kwanciya a k'asa? Tashi ki hau gado. Ku kuma kuna ganinta ku ka kyale?"
"Ita ta za6i nan fa." Cewar Baraka.
    Harara kawai ta samu daga Hajiya Babba wanda yasa ta jan baki ta yi shirun dole. Ba ita ta bar dakin ba saida ta tabbatar Ummi ta hau gadon, kafin ta juya harshe ta gargadesu sosai sannan ta fice. 
  Ummi dai tun tana jin hirarsu har mijin Baraka, Sa'ad ya kirata suka hau hira, sama-sama ta ke jinsu har bacci ya yi awon gaba da ita. 
    Washegari....
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
  86

Washegari da misalin karfe sha biyu na rana, Hajiya Mama da iyalanta suka dira a gidan Modibbo. Ummi tun gaishesu da ta yi ta sauko. Ido hudu sukayi da Antinta Amina dake tsaye a kofar kicin suna gaisawa da Larai. Da sauri Amina ta juya ta fita, itama Ummi cikin saurin ta karasa sauka daga bene ta fita, tsaye ta ganta a baranda ta sunkuyar da kai. Cikin sanyin jiki ta karasa gareta ta dafa kafadarta fuskarta dauke da matsanancin farinciki.
"Anti."
Koda Amina ta dubeta ta razana da ganin hawayen dake saman fuskarta. 
  Hankalinta ya tashi.
"Anti ki yi hakuri don Allah, ban.."
  "Meyasa haka Ummi? Meyasa bakya tausayawa kanki da rayuwarki? Anya kuwa kinsan hatsarin da ki ka jefa kanki? Kina sane cewar a sanadinki zumuncin dake tsakanin Mami, Hajiya Babba da Hajiya Mama ya raunana?"
  Gabanta ya fadi, Amina ta koramata bayanin duk abinda ke faruwa ta dora da fadin.
"Ina jiyemiki tsoron abinda zai je ya zo. Karki dauki maganganu a baibai, ni mai kaunarki ce, ba kuma zan so wani abu ya sameki ba sanadin auren Yaya Faruk, saidai kishi tsakaninki da Ihsan?"
Ta yi shiru tana mai girgiza kai kafin ta share fuskarta. Bata kara komai akai ba ta yi gaba, Ummi hankalinta ya yi mugun tashi, duk wannan abun ya faru ne sanadinta? Ya akayi bata da masaniya? To wa zai fadamata, bata ji daga bakin kowa ba, ta tuno dai sadda Hajiya Babba ke kokarin yi mata magnar Faruk ya shigo wanda hakan yasa Hajiya katse maganar da ta yi niyya alokacin. 
   Durkushewa ta yi awajen sai kuma ta ji kuka mai karfi ya tahomata, da sauri ta zagaya dan lungun gidan ta durkushe ta soma shek'asa, duk a sanadinta hakan ya faru, anya bata zama mai son kai ba? Tana ina akayi hakan? Meyasa babu wanda ya sanarmata? Sai gaba daya ta ji kunyar kanta ya mamayeta, ya za ta yi da wannan abu? Da wane ido zata kalli Mami a yanzu?  Don ita sam Ihsan bata gabanta kamar Mami, Mami ta fi ji. Acan kasan zuciyarta kuwa tana ji kamar ba zata iya rabuwa da Faruk ba. 
   Ta jima anan har saida ta ji Amina na cigiyarta sannan ta taso ta zo tana mai amsawa. Ganin yanayinta ne yasa Amina jin wani mugun tausayinta, ta janyo hannunta suka zauna a baranda.
  "Anti wallahi ba ni da wannan labarin, bansan da shi ba da babu abinda zai kaini ga amincewa hakan."
  Amina ta yi murmushi cike da tausayawa Ummi, tana kaunar yarinyar ko don hakurinta. Ita kanta ta yi mamakin yanda aka ce Ummi ta yarda da batun auren Faruk batare da wani tunani ba. 
  "Karki damu kanki Ummi, Ubangiji Ya fi kowa sanin dalilin hakan, idan kuma Ya kaddaro aurenki da Yaya Faruk to babu makawa sai an yishi. Kawai dai ni na yi mamaki ne daman yanda akayi ki ka amince har haka."
  Ummi ta dubeta sai kuma ta shiga bata labarin dukkan abubuwan da suka faru bayan tafiyarta, Amina tana murmushi ta tsaida idanunta kawai tana duban Ummin. Har saida Ummin ta shiga damuwa, ga wani gumi da ta ke yi sakamakon iska mai zafin dake kadawa haka kuma garin hadari ne kwance. 
  "Ki godewa Allah da Ya hadaki da mutum mai matukar kaunarki irin Yaya Faruk, lallai kin yi sa'a."
  Kunya ta kama Ummi, ta sunkuyar da kanta don har lokacin hankalinta bai kwanta ba. 
  Kiran da Larai ta yi musu ne ya katse hirarsu, abinci ne. Ta dubi Ummi sadda ta mik'awa Amina filet din abinci.
"Sama za ki hau ai, kya ci a anan?" Cewar Larai.
  Ta ji babu dadi.
"Kai Larai, to ni wacece da ba zan ci da yar uwata ba? 
  Larai zata yi magana Amina ta rigata.
"Ai nasan halin kanwata ko wane matsayi ta taka ba zata wulakanta DAN ADAM ba."
  Larai ta jinjina kai tana mai kya6e baki.
'Inama ni na samu damarki.' Ta yi furucin a ranta, a fili kuwa hannu ta mik'awa Amina.
"To kawo na k'ara muku." Bayan ta k'ara Ummi ta kar6a suka koma falon dake k'asa suna ci suna 'yar hira anan ne Ummi ke jin batun saka ranar Amina wanda aka daga sai bayan azumi don lokacin watanni biyu ya rage azumin.  
         
   Misalin karfe uku kusan kowa ya iso har Mami. Ummi kasa zuwa ta yi gaida Mami, wajen Amina ta wuce har lokacin da aka bude taro da addua suka soma abinsu.
  Ummi da Amina na nan zaune suka ji sallama, suka dubi kofar suna mai amsawa. Wani saurayi ne dan dogo bak'i saidai kana kallon sumarsa Kaga bafulatanin mutum(lol) yana sanye da shadda fara k'al sai hula da ya dora a kansa. Shima idanunsa a kansu musamman ma Ummi wacce ya k'urawa ido har ta tsargu da hakan ta sunkuyar da kanta. Suka shiga gaisheshi, ya amsa, kafin su yi wani yunkurin Abba da amininsa Alhaji Kabir Jimeta sun shigo, kai a kasa Ummi ta gaishesu don kuwa tana tsoron kallon da zata samu daga Abban wanda bata mance irin rabuwar da ta yi da gidansa ba duk kuwa da ance komai ya wuce. Kafin su kai ga cewa komai sai ga Babban Yaya da Dakta sun sauko daga sama, su suka jagorancesu zuwa saman. Abubakar Kabir Jimeta har ya soma taka benen bai bar waigen Ummi ba shi fa kallon sani ya ke yiwa fuskarta saidai ya kasa tuna ko a ina yasan fuskar! Zai so Baffansa ya gani saidai kuma sam bata k'ara dago kanta ba. 
   Acan sama kuwa bayan an zauna aka gaggaisa, Modibbo cikin harshen fulatanci ya ke tambayar Alhaji Kabir Jimeta mutan gida. Bayan gama gaisuwa Abba ya gabatar da Abubakar matsayin wanda ke son Ihsan da aure. 
  Banda Hajiya Babba da ta riga tasan zancen da kuma Faruk da shima ya riga da ya sani a bakin Hajiyarsa, babu wanda bai girgiza da jin wannan batu ba sai ko Hajiya Mama dake murmushi kawai. 
  ((Ku yi hakuri da wannan, kaina ne ciwo...))
             ***   ***   ***
  DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  88
   Misalin karfe goma na dare, Ummi kwance saman gado tana tunane-tunane, ta ji shigowar su Ikram, wannan dalilin ne yasa ta rufe idanu tamkar mai bacci. Tana ji suna faman hirarsu kafin Ikram ta ce.
"Wai wannan isashshiyar har ta yi bacci? Lallai yau ko ta jira a yi mata iso kan gadon? Um, kan mage ya waye."
  Baraka ta dara.
"Ai ko bata hau ba dole ma ta komo, ni banason abinda zai ta had'amu da Hajiyarmu muna 6ata ranta kan abinda mukasan mun fishi."
    Ikram ta ta6e baki gami da mikewa. Cikin muryar rad'a ta ce. "Bari yau dai na bincika wayar nan nata." Ta mike tsaye tana mai zagayawa 6angaren da Ummi ta ke, Ummi na jinta ta dauki wayar a hankali, can kuma ta ja tsaki.
"Wallahi nasan aikin Yaya Faruk ne don wannan illiterate din ba zata iya ba."
  "Me kenan?"
"Wai pattern lock yasa mata."
Baraka ta yi dariya, za ta ajiye wayar ne hankalinta yakai ga zoben dake yatsar Ummi, ta zaro ido tana karemishi kallo kafin ta dubi yar uwarta da muryar rada ta ce.
"Kinsan zoben gwal ne a hannunta."
Baraka ta mike tana mai soma takowa wajen hadi da fadin.
"Wasa ki ke."
Sai kuma ta kama yatsan a hankali ta kurawa zoben ido itama, kafin kuma ta saki yatsan.
"Lallai abin babba ne, a ina ta samu?"
Yar harararta Ikram ta yi suna kokarin barin wajen.
"Wa ki ka san zai bata bayan Yaya Faruk? Ai inaga nan gaba ma (salary) dinsa gaba daya akanta zai k'are. Har tausayi ya ke ban, Allah dai Ya karya wannan sihirin tun ba'a kai ga aurennan ba, idan kuwa aka yishi ba karamin mijin tace zaayi ba."
   Haka sukayita hira akanta tana jinsu hakanan tana ji kamar ta yi kuka har suka gaji suka gangaro kan Ihsan. Inda Baraka ke fadin tasan mijinnata, don kuwa saurayin wata kawarta ce a baya, ta tabbatar shi din yana da yanmata kala-kala acewarta saidai Ihsan ta yi hakuri ta kauda idanu akan wannan tunda har ta nuna ta ji ta gani. 
      Tun tana jinsu har bacci ya yi awon gaba da ita.
   Cikin dare aka yi ruwa sosai wanda bata da masaniya sai washegari bayan tashinta daga bacci. Ruwa duk ya shigo ya jik'a labulen dakin, ta dubi inda su Baraka ke kwance, har lokacin (karfe shida da mintuna) basu tashi ba, murmushi ta dan yi, tasan jiya sun jima basu kwanta ba. 
   Kai tsaye wanka ta fad'a sanin cewa da wuri zasu wuce don Hajiya Babba ta ce kafin takwas zasu tafi. Tana fitowa ta iske Baraka zaune bakin gado, itama bandakin ta shiga tana mitar Ummi bata ko tashesu sun yi sallah ba, ita dai hakuri kawai ta bata daman ita fashi ta ke. 
   Garin ya yi sanyi-sanyi hakanan har lokacin akwai hadari bai gama yayewa ba duk kuwa da cewar duhu bai gama fita ba. Ta shirya cikin wani bulun Swiss Atamfa mai haske, tana da adon manyan fulawoyi wanda acikinsu aka yi kwalliya da kalar bulu mai turuwa. (Lol..ku nemi Aysha ku siya). Dinkin riga da siket ne, rigar simple akayi mata mai hannu (3 quarter) ta zauna das a jikinta, hoda da kwalli kawai ta shafa, lokacin har Baraka ta fito ta yi sallah ta shiga wanka, ita kuwa Ikram na saman darduma tana addua saidai idanunta na satar kallon Ummi don duk hassadar mai hassada bazai k'i aminta da kyawun da ta yi ba. Ko ita kanta shigarta ta burgeta saidai ba fa zata nuna ba. 
   Ummi ta tattara kayanta a jaka sannan ta soma gyara saman gadon bayan ta dauke musu wayoyinsu, tana kokarin share dakin ne Intisar ta shigo da sallama. Bayan sun amsa ta zaro ido tana duban Ikram don ita tuni ta yi wanka ta saka doguwar riga 'yar kanti mai mayafi. 
  "Ke Ikram, ko wanka ba ki yi ba?"
Ikram ta mike tana cire kayan jikinta.
"Wallahi yanzu zan shiga yau sanyin da gari ya yi yasa mun makara sallar Asuba ma."
  "Kedai fadi gaskiya tun daga can dakin muke jin hirarku fa har muka yi bacci." Intisar ta amsa lokacin da ta shigo dakin sosai. 
   Ummi ta gaisheta, ta amsa fuska a sake tana kallonta, kwarai shigar Ummi ta burgeta don ta yi kyau ainun, ga dirin jiki da Allah Ya bata. 
    Fitowar Baraka ce ta katse tunaninta, Ummi ta fice don dauko tsintsiya da tsumman tsane ruwan da ya shigo ta windo. 
     Babu kowa a falon sama, kai tsaye ta sauka k'asa, nan dinma ko fitila ba'a kunna ba, ta karasa hanyar kicin inda anan ne ta gano haske, Larai ce ke faman soye-soye tare da Hafsatu sabuwar mai aikin Hajja, ta gaishesu Larai ta kama baki.
"Oh ni, Ummi kinga yanda ki ka haska kuwa?"
Ta basar da zancen tana  dan murmushi lokacin da ta ke kokarin daukar tsintsiya da abin kwasar shara.
"Larai tsumman guganku yana ina?"
"Me zaki yi 'yar nan? Ke ai kin wuce aiki yanzu."
Ummi ta dan daure fuska.
"Ni wallahi bana son hakan da ki ke yimin."
"Jimin 'ya, Hafsatu ko karya nayi ne? Ina Ummi ina aiki?"
Hafsatu dake mikawa Ummi tsumma ta yi dariya kawai, ai kuwa Ummin na kar6a ta fice da sauri don dagaske Larai ta bata haushi.  Tana jin dariyarsu. Ta soma taka matattakala ta ga an kunna fitilun falon, hakan yasa ta kai dubanta ga mai shi. Ido hudu sukayi da shi yana sanye da riga da wando yan kanti sai jacket da ya dora bak'a a saman rigar wacce kana hangota fara k'al, hakanan farin wando ne dogo na jeans a jikinsa. 
    Idanunsu suka sark'e cikin juna, wani kyau ta ga ya yi mata na daban duk da ta lura da jan da saman hancinsa ya yi can kuma ya saki atishawa, ya rufe bakin ta hanyar amfani da dan hankicif din dake a hannunsa. Kafin ya kai ga cewa wani abu, Haidar ya shigo shima sanye cikin kananun kayan, da sauri ta haye sama bata bari ko gaisuwa ta shiga tsakaninsu ba. Ya numfasa yana duban Haidar wanda ke kokarin zama.
   "Wai murar ce haka? Ai saida nayi-nayi akan ka kashe fanka ka nuna kai zafi ka ke ji."
   Shima zaman ya yi yana mai dan ta6a karan hancinsa da ya ke ji yana mishi zafi. 
  "Daban da murata na zo saidai ba ta yi karfi haka ba sai yanzun."
"Ya dace ka nemi magani ka sha."
Haidar ya amsa yana kallon hanyar sama.
"Wai kada dai basu tashi ba? Muna da ayyukan yi fa."
  Ya tuna hasken idaniyartasa wacce shigarta ta yau ta daukemasa hankali, murmushi ya danyi.
"Sun tashi mana."
  
Acan kuwa Ummi ta tarar har Baraka ta shirya sun fice daga dakin ita da Intisar, ta goge inda ruwa ya 6ata kafin ta hau shara. Tana cikin yi itama Ikram ta fito, bayan ta kammala ta fito. Anan falon ta iske Hajiya da su Hajja sai kuwa Larai da Hafsatu dake jera kayan karin kumallo.
  Ta ajiye ta karasa ta gaishesu kanta a kasa, suka amsa, Hajja ko ciki-ciki ta amsa tana karewa yanda yarinyar ta chanja ta wani murje. 
  Har Ummi ta bar wajen da kallo ta ke binta. Kafin ta kya6e baki.
  "Wannan yarinya nan gaba sai ta ce bata sanmu ba.". Ta yi maganar ne da harshen fillanci ganin su Larai dake wajen ga kuma su Amal dake dudubniyarsu. Hajiya Babba 'yar dariya kawai ta yi na wayancewa don ita har ga Allah tana jin kaunar Ummi a ranta. 
    Ummi kasa sauka kasan ta yi jin muryoyin yan samarin Hajiyar tare da su Intisar ana hira, jin suna kokarin hayowa ne yasa ta juyawa da sauri har suna karo da Hafsatu. Ta numfasa.
"Don Allah Hafsatu taimaka ki karasamin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login