Showing 81001 words to 84000 words out of 158267 words
har d'iyar, tana nan Hajiya Mama tazo saidai kafin ta je gida ta dawo ta tarar batanan.
Sai bayan Magriba, Mami ta yi wanka ta shirya tsaf da nufin zuwa turaka, alokacin ne ta shiga dakin diyarta ta inda ta tarar da ita tana goge jikinta alamun wanka ta yi. Ganin Mami yasa ta zama gefen gado, itama zaman ta yi.
"Mami kin ji..."
"Kar ki ma 6ata bakinki, nasan komai."
Cike da mamaki ta ce. "Au Mami har daman zasuyi mana wannan cin fuskar su iya kiranki su sanarmiki?"
Ranta ya dan sosu da jin kalma ta cin fuska da 'yarta ta jefi Hajiya Babba da shi, zata so ita ta kirata da komai amma bataso yaranta su rainasu.
"Kar ki k'ara fad'ar haka tunda ba ke ta ciwa fuska ba, ni ta yiwa. Kuma idan har muna raye zasu ga sakayya."
Ihsan ta yi kwafa tana mai jin zafi a zuciyarta.
"Wallahi Mami ni na hakura da Yaya Faruk, na ji na tsaneshi ma. Wai akansa aka ci zarafina, banda cin zarafi ta ya ya za'a had'ani kishi da 'yar aiki, wallahi nafi karfinnan."
Ta ji dadin kalaman Ihsan din, daman ita ta ke ganin zata bata matsala sai kuma ta bata mamaki. Cikin murmushi ta dafa kanta.
"Kin burgeni matuk'a, barni da su suna gani sai kin auri mijin da yafi Faruk komai da komai, sai sunyi mamakin mijinki Ihsan. In sha Allah kuma sai kin riga d'anta aure. Ita kuwa Ummi su jik'ata su shanye, mu ba'a koyamana yawan malamai ba, idan ita ta bisu don kawo mana rashin jituwa a zuri'armu to ta cigaba idan zaiyi tasiri."
Ihsan ta dan ji wani iri, so daban ya ke, anya zata so wani nan gaba irin son da ta yiwa Faruk?
Tana ji Mami ta gama maganganunta kafin ta mike bayan ta ce idan ta kammala ta zo ta gaida Abbanta, daga nan ta fice, Ihsan ta bita da kallo. Sai kuma ta dan ja guntun tsaki gami da cije le6e. Ummi kadai ce matsalarta fa, da babu ita, babu abinda zai hanata auren Faruk. Amma kuma Mami na da gaskiya, watakil fa ba banza ta bar su ba, ta yi kwafa.
"Babu abinda yafi karfin addua, za ki gane kurenki." Ta yi furucin a fili.
Saida ta kammala shiri cikin doguwar jallabiya ta fito, bayan kammala cin abinci da Fahad ta ja hannunsa zuwa ga Abbansu, Adnan tun maganar da sukayi da Mami ya bar gidan.
Abba ya yi farinciki da zuwanta, ita kuwa dadin sake ganin dariyar Abbanta ne ya cika zuciyarta, gani ta ke yi kamar a mafarki.
Sun jima suna hira kafin Mami ta umarceta da shiga sashen matan gidan a gaisa. Haka ta soma da zuwa sashen Hajiya Binta, babu kyakkyawar tarba daga gareta harma yaranta, itama ganin haka ta nuna yar zamani ce ta fito batare da ta k'ara kallonta daga gaisuwa daya.
Kai tsaye wajen Anti Amarya ta nufa, ta sakarmata fuska fiye da baya don ita bata da matsala a hakan, hakanan su hussaina yaranta, har Anti Amarya tayita janta da hira tana fadamata ta yi k'iba. Ihsan ta ji dadin zuwa sashenta kafin su yi sallama.
Haka halayen Anti Amarya ya ke saika rantse dagaske so na tsakani da Allah ta ke maka, takan yi iyakar kokarin boye ainahin sirrin zuciyarta agabanka. (DAN ADAM MAI WUYAR GANE HALI KENAN...!)
Hajiya Mama ranta duk a 6ace, Amina da yaran Hajiya Maman, Rukayya, Maryam, Na'im da autarsu mai shekaru goma, Mufida. Intisar ce babbat diyarta don Hajiya Mama bata samu haihuwa da wuri ba.
"Lafiya kuwa yau?"
Cewar Rukayya tana duban yan uwanta. Amina wacce suka zama kamar yan uwa ta jinjina kai.
"Nifa na lura tun dawowar Hajiya Mama daga gidan Mami bata cikin hayyacinta, Allah Yasa ba wani abun ne ya faru ba."
"Amin, ni duk jikina ya yi sanyi ma wallahi, bakuga wainar fulawar nan ta dazu ba gaba daya fita daga raina ta yi wallahi."
Rukayya ke maganar tana yamutse fuska cike da damuwa, duk da ita ce ma karfin cewa suyi wainar fulawa har ana rabon aiki, wannan ce zatayi suya a farko idan ta gaji waccan ta yi, wancan mai daka yaji.
"Allah Ya jishshemu alheri." Fadin Amina kenan.
Suka amsa da amin, ita kam Amina ko aka bata ta6a kawowa wani batun Ummi ne ya tashi da Faruk ba? To wa zai kawo hakan ma?
Suna nan zaune Adnan ya shigo da sallamarsa. Suka amsa, Maryam ta saki baki tana dariya.
"Ikon Allah, kodai mafarki nakeyi, ku mintsileni mugani."
Ai kuwa Amina da Rukayya harma da Mufida suka hau rige-rige, ganin dagaske suke ta yi tsalle ta ja baya suka sanya dariya gaba daya. Adnan ma cikin dariyar ya zauna, hankalinsa ya dan kwanta da yanda suka tarbeshi, ko babu komai ya ji dadin ganin Hajiya Mama bata sanarwa yaranta ba. Bayan an gaisa yake sanarmusu batun tafiyarsa gobe, Rukayya harda ihun murna, Maryam ta zaro ido.
"Dagaske?"
Adnan ya jefeta da kallon kauna don kuwa sun had'a kansu saidai a 6oye suke soyewa ta kafar sadarwa harda yiwa juna alkwarin rikon amana.
"Kamar baki sani ba?"
Sai kuma ta yi murmushi. Maryam ta ta6e baki.
"Ato, ai munsan komai saidai mu yi shiru."
Ya yi dariya da mamaki kafin ya dubeta.
"Ke kika sani malama, ina uwata?"
"Au, daman baku hadu ba? Daga gidanku fa take."
"Eh, ni na dan fita ne."
"Ayya, bari ayi mata magana."
"Kamar ba gidanmu ba?"
Ya fad'a yana hararar Rukayyar, sukayi dariya kafin ya wuce.
Sallama ya yi, Hajiya Mama ta amsa don ta ji maganarsu da yaranta. Fuska a sake tana mai kokarin danne damuwarta ta ce.
"Aa Adnan? Karaso mana."
Ya karasa jiki a sanyaye ga kuma kunyar abinda Maminsa ta aikata gareta ya russuna ya gaisheta. Ta amsa. Shiru ya biyo baya kafin ya soma bata hakuri kan abinda ya faru.
"Kayya, dama baka shiga ciki ba don kuwa wannan tsakaninmu ne. Karka damu, ka yiwa mahaifiyarka uzuri kasan ance mai d'a wawa, watakil son nata ne ya rufemata ido har haka. Amma nasan Madina ba lallai har zuciyarta hakan bane."
Ta fad'a ne kawai ba don har zuciyarta tana ganin hakan bane, saidai bata kaunar yaransu su shigo cikin maganar wanda dai da kamar wuya. Bazata so ya shafi zumunci yaransu ba da mazajensu.
Adnan shi kansa yasan Hajiya Mama ta fad'a ne kawai.
Ta share maganar.
"Ashe kuma gobe zaka wuce ko?"
"Eh." Ya fada yana mai shafar sumarsa.
Ta shiga yi mishi nasiha tamkar dan cikinta, da nunamishi sanya Allah a rai da kuma gujewa mugayen dabi'u da abokan huld'a. Adnan ya ji dadi matuk'a na shawarwarinta, ya ji dukkan damuwarsa ta warware daman ya dauka shikenan Hajiya Mama ta barsu kenan, sai ya ga ba haka ba. Koda ya ce zai wuce, dakatar da shi ta yi don saida ya ci abincin dare sannan ta kaishi har wajen Alhaji Haruna mahaifin su Intisar suka gaisa shima ya bishi da kyawawan nasihu da kuma addu'o'i kafin suyi sallama ya tafi bayan su Maryam sun tabbatar mishi zasu zo rakiyarsa zuwa(Airport) goben.
*** *** ***
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
77
RINGIM
Habiba da Saude suna komowa Ringim kai tsaye wajen bokanyarsu suka zarce. Suna isa bayan anmusu iso suka shiga gami da zubewa agaban Uwar Biyu mai bori. Habiba ta zayyanemata dukkan yanda ya faru a mafarki.
Ta mike ta soma jijjige jiggigenta da kad'e-kad'e kafin ta zauna fuska a murtuke sai kuma ta kyakyace da dariya wanda ya razanasu ya kada yan hanjin cikinsu. Maganarta ta katse tunaninsu.
"Karki damu kanki! Wannan ba komai bane sai shaida na cewar diyarta na nan tafe da wata gagarumar nasara a rayuwa wanda zai iya janyo tonon silili kala-kala ciki harda mutuwar auren daya a cikinku! Abubuwa da yawa a rufe su ke nakasa fahimta amman ina mai tabbatarmuku ba mai kyau bane gareku! Wannan duk ba damuwa bane idan ni Ade Mai Bori na raye to ba bazai afku ba ko kadan!"
Cikinsu ya k'ulle tsabar rud'u, Saude har fitsari ta soma a wando, Habiba da ta soma had'a gumi ga jiki da ya dauki rawa ta daure ta soma magana cike da dauriya.
"Mudai yanzu bokanya da ke muka dogara, ki taimakemu ki fiddamu wannan hatsari." (Waiyazubillah)
Dariya na hauka Ade Mai Bori ta yi kafin ta yiwa kanta kirari cikin karaji sannan ta dubesu fuska murtuke.
"Zan yi muku aiki fiye da yanda na rufemuku bakin shegu a baya! Me ku ke bukata?"
Saude ta riga Habiba magana.
"Idan da hali a kashe Ummi!"
Ta tsaya ta gama tsaface-tsafacenta kafin ta dubesu idanuwa a zazzare.
"A'a! Na duba wannan bazai yiwu ba!"
Saude da hawaye ya tahomata ta kasa magana sai rawar jiki, Habiba ta cafe.
"Bokanya nidai a haukatar da ita yanda bazata yi amfani ba koda ta zo."
Ta gama tabbatarwa da ba mai yiwuwa bane ba a hanyar tsafinta, saidai bata son ko kusa ta nuna gazawarta har karo na biyu hakan yasa ta kyakyacewa da dariya.
"Angama!!! Ko garinnan ba zata ta6a waiwaye ba!!!"
Ransu ya danyi sanyi, suka had'a duk kudaden dake jikinsu wanda ya kai dubu ashirin suka ajiyemata. Haka suka baro wajen hankali tashi, Saude suna fita ta ke6e bayan gini ta rage mararta, tana ji cikinta na kad'a saidai ta danne har su isa gida ta kasaye. A hanya babu wanda ya iya magana kowanne tunaninsa ya ke yi, duk tunaninsu ya basu cewar karshensu fa ya kusanto. Babu babban abinda ya k'ara hargitsasu sai mutuwar auren dayansu da Bokanya ta ambata.
Ko kan wa zai fad'a???
Koda suka isa a gidan Saude suka yada zango, saida Saude ta rage cikinta sannan ta samu zama don su tattauna, alokacin kuma Mariya ta shigo gidan daga gidan makwafciyarsu acan ta kwana.
"Habiba, kinji kuma sabuwar masifa ko?"
Habiba ta numfasa.
"Hum, bari kawai Saude, wallahi don ba ki ji yanda kwakwalwata ta dauki chaji ba, kai wannan jarabar da me ta yi kama? Da nasan akwai wannan ranar tafe wallahi da sadda na gama da shegiya lokacin zan gama da ita itama. Ni na yi zaton shikenan ta zama hanyar arziki ashe akwai sauran rina a kaba?"
Saude ta share gumi da mayafinta.
"Wallahi dadin da naji daya ne, na cewa da Bokanya ta yi zata haukata mana ita, kinga shikenan sai daga nan ta k'ara gaba, idan ma ta samu motar da ta kad'eta, mun huta."
Habiba ta saki fuska.
"Allah Yasa hakan."
"Ameen dai."
Nan suka cigaba da maganar, hankalin Saude ya kai ga diyarta Mariya da ta zura hannu a wando ta yi shiru tana kallonsu. Cikin tsawa ta ce. "Ke ciremin hannu daga nan tun ban bubbugeki ba!"
Habiba ta mik'e gwuiwa a sake.
"Atoh, ki ka sani ko k'aik'ayi ne?"
"Ai ina zaton haka, mantawa na yi ma ina son kar6omata maganin sanyi wajen Bokanya, wannan yawan soshe-soshen ya isheni."
"Yafi dai kam idan ba so ki ke ta diyarki ta 6aci tun yanzu ba. Bari na je na huta gajiyar bikinnan tunda hankali ya kwanta."
Saude ta taka mata har kofar gida kafin su yi sallama itama ta koma ga harkokin gabanta batare da ta k'ara maida hankali ga yarinyar ba....!
*** *** ***
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
76
ABUJA
Faruk kuwa yanda sukayi da Haidar ya yi, ya shirya ya wuce gidan Dakta. Bai iskeshi ba sai Jidda da ta hau shi da tsiya akan ta ji da auren wacce kuma ya 6ige.
"Amman wallahi ka bamu kunya."
Ya watsamata wani kallo yaso ya tanka sai kuma ya tuna maganganun Haidar, bazai so kam zumunci ya 6aci ba. Ya yi kwafa.
"Kin fa ci darajar yarana, da a yau za ki koma Ghana."
Ta yi dariyar k'ular da shi.
"Dad'in abun ba kauye na tashi ba ballantana na tsoraci komawa."
Bai ko k'ara kallonta ba ya fice yana murmushin kinyi kad'an.
Kai tsaye asibitin da Dakta Ridwan ya ke ya isa. Duk da ba ranar aiki ba ya shiga don duba wata mai nak'uda da ta samu 'yar tangard'a, ya yi nasarar ciro bebin lafiya yana cikin dinketa ne, ya hango kaninnasa daga jikin windo kasancewar windon gilas ne, ya dubi nos dake gefensa cikin fad'a.
"Ba ki da hankali ne? Ta ya ya za'a barmin windo bud'e ina aiki?"
"I'm sorry Sir."
Daga haka ta karasa cikin sauri ta saki labulen, murmushi Faruk ya yi ya zura hannuwa a aljihu kafin ya wuce kai tsaye ofishin Dakta. Zama ya yi akan kujerarsa yana kalle-kalle kafin ya ta6e baki.
"Wani aikin sai likita, duk wani jagwal suna gani."
Ya k'arashe kafin idanunsa ya kai ga dan karamin frame din dake saman teburin, su hud'u ne a hoton wanda akayi musu ran bikin Ridwan din. Idanun Faruk a rufe don lokacin ma bai zama cikakken matashi ba, su kuwa sun dubeshi suna dariya aka yi hoton. Murmushi ya yi, shi kam haka Allah Ya yishi bai fiyeson hoto ba. Duk da dai yayyunnasa sun ce bikinsa ne da baizo ba, muddin ya tashi aure watakil ma da kansa zai dunga kiran mai hoton ya dauka. Yakan yi dariya don yana ganin lamarin wasa kawai.
Baifi mintuna goma ba sai ga Dakta ya shigo. Yana ganinsa ya tsaya ya daure fuska.
"Get out of my office."
Ya fada yana mishi nuni da k'ofa. Faruk ya mike tsaye ya na dubansa fuskarsa dauke da damuwa. Ganin ba shi da niyya yasa Dakta soma tattara abin amfaninsa zai wuce gida don daman abinda ya shigo da shi kenan, da sauri ya sha gabansa ya rungumeshi.
"Please forgive me brother, kayimin dukkan hukuncin da kaga ya dace da ni." Ya dago jikinsa yana dubansa da idanunsa wadanda suke nuni da gaskiyar abinda ya ke fad'a.
"Amma kada ka hukuntani ta hanyar dauke fara'arka daga gareni da kuma fita harkata."
Jikin Ridwan ya yi sanyi, daman dauriya kawai ya ke yi don tun bayan barinsa gidan Daddy, ya ji babu dadi, yasan kaninnasu mai son farincikinsu ne, ta ya ya shi ya kasa kar6ar abinda yazo musu da shi da hannu bibbiyu ko don faranta ransa?
Ya dafa kafadarsa.
"Kamin laifi Lil, saidai na yi maka uzuri tunda baka ta6a yimin makamancinsa ba. Karka damu ya wuce."
Ran Faruk ya yi sanyi, tare suka jera suna tafiya, Ridwan na k'ara nunamishi dalilin da yasa ya nuna rashin goyon bayansa.
"Gani nake kamar ka wuce ajin yarinyar ne, na kuma yi tunanin kodai wani asirin ta yi maka? Amman ka yo hakuri."
Faruk ya yi murmushi.
"Babu abinda ta yimin, ka manta muna dagewa awajen adduar neman tsari? Duk da dai akwai kaddara, amma bama fatanta. Wannan kauna ce daga Allah nake jinta game da ita."
Suka dubi juna sukayi dariya, ya bugi kafadarsa.
"Lil ne da soyayya? Kamar ranar nan ba zata zo ba."
Faruk ya shafi sumarsa yana shagwa6e fuska. Hanashi wucewa ya yi suka nufi gidan Ridwan din da niyyar zuwa yamma su wuce gidan gaba daya. Ta (whatsapp) ya sanarwa da Haidar cewar sun shirya. Ya aikomishi da rawa na mace har abin ya sanyashi dariya.
Jidda ganinsu yasa ta hau cakar Faruk akan batun Ummi, shi kuma ya ce ta yi ta gama aure ne babu fashi sai idan Allah baiyiba. Shi kam Dakta na jinsu saidai baisa baki ba, saida ya kula da Jiddar na neman korar mishi k'ani yasa shi tsawatarmata dole ta saki hirar ta yi shigewarta daki da alama dai 'yar bayan Ihsan ce.
*** *** ***
. ABUJA
Hajiya Babba ce zaune a falonta tare da yaranta maza ana 'yar hira. Ta dubesu cike da farincikin ganin yanda Ridwan ya sakarwa Faruk fuska kamar yanda suka saba, fatanta Allah Ya cigaba da had'a kan yarannata haka. Suna zaune a saman kafet ga katuwar leda agabansu an shimfid'a sai kulolin abinci duk Ikram ta zuzzubamusu. Haidar ya sanyo batun auren Faruk da irin kyauta ta musamman da ya tanadar mishi.
"Mata biyu lokaci guda? Ai wannan ni kadai nasan tanadin da na yi ma."
Ya fada saitin kunnen Faruk , ya yi kamar bai ji ba ya cigaba da cin abincinsa. Babban Yaya na jin haka ya ajiye cokali gami da dan kora ruwa sakamakon kwarewar da ya so yi babu shiri.
"Wai wa zai auri mata biyu?"
"Oh, baka da labari fa ashe Dan uwa." Cewar Dakta.
"Abincin za ku ci ne ko hira zaayi?"
Suka tsinci muryar Daddy wanda ya katse hanzarin Haidar da Dakta masu zuci-zucin bawa Babban Yaya labari kamar wasu yara.
Ya karaso fuska a sake ya zauna.
"Ke kuma na lura duk ranar da 'ya'yanki ke gidannan kina mantawa da lamurana, ina ga dai na kusa hanaku irin wannan zuwan."
Ya karashe yana kallonsu, suka yi dariya har Faruk.
"Kai amma da na ji dadi Daddy." Ya fad'a yana kanne ido daya. Suka watsamishi hararar wasa banda Babban Yaya da ya ke dariya.
"Kwana nawa ne kaima?" Fadin Haidar kenan.
Daddy ya dakatar da su da hannu.
"Ya isa hakanan, a ci abinci a nutse. Idan kun kammala ina nemanku."
Daga haka ya tashi Hajiya ta bi bayansa.
Bayan sun kammala suka hadu sashen Daddy har Ikram. Ya soma da fadin.
"Ku amanar Allah ce awajena, ya kuma zama dole na dunga nusar da ku akan lamura na rayuwa." Ya cigaba da yi musu nasiha mai ratsa jiki kafin ya sanyo batun auren Faruk da Ummi.
"Idan Allah Ya shiryo hakan babu wanda zai hana, hakazalika kowa da kaddararsa a rayuwa."
A karshe dai ya kara nusar da su batu na hadin kai, akan ko bayan ransa yana fatan su rike zumunci.
Sun jima anan, Babban Yaya bai nuna wata alama ta k'in sha'anin ba, Ikram dai har lokacin zuciyar bata lafa ba, koda ta yi yunkurin hakan da zarar ta tuno da wacce zaa aurar sai ranta ya yi bak'i. Ko yar uwarta Baraka lamarin baiyi mata dadi ba, Intisar ma ta nuna rashin yardarta ga Hajiya Mama nan ta ci karo da fushinta, dole ta ja bakinta ta yi shiru ba don ranta naso ba, ga mijinta shima da ya goyi bayan dan uwansa.
Haka taro ya tashi zuciyar kowa a sake har Ikram don ta samu dama Faruk ya sakarmata fuska.
Bayan fitarsu Daddy ya sanarwa Hajiya cewar lokaci ya yi na dauke Ummi daga sashen yan aiki, itama daman ta yi tunanin hakan saidai tunanin da ya yi mata yawa akan k'in daga wayarta da Madina ta k'i yi duk kuwa da cewar ta samu magana da Hajiya Mama