Showing 138001 words to 141000 words out of 158267 words
kala-kala da ta aikomata na daurin dankwali.
Saida ta kammala ta feshe jikinta da turaruka masu dadin kamshi kafin ta fita zuwa kicin ta soma kiciniyar hada musu karin kumallo, tana cikin yi ta ji mutum a bayanta. Har saida ta firgita ta juyo, ganinsa yasa ta sunkuyar da kai tana murmushi.
"Bana ce karki wahalar da kanki ba?"
Ya fada a shagwabance. Ita kam batasan ita da shi wa zai rarrashi wani ba...!
((Sorry yau na fita ne...manage))
[2/6, 1:41 PM] +234 703 962 5239:
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
120
"Ka yi hakuri gani na yi..." Sai kuma ta yi shiru. Murmushi ya yi ya ja hannunta zuwa dinning table ya zaunar, ta dubeshi ya sanya yatsansa a baki alamu na ta yi shiru.
"Shii! Yau aikina ne ba na ki ba."
Daga haka ya yi hanyar kicin yana murza hannuwansa. Ta bishi da kallo kamar ta yi dariya, yana sanye da riga tshirt marar nauyi sai kuwa wandonsa 3 quarter. Tunaninta ko zai iya tace ruwan shayin, sam batasan ma akwai kayan abinci ba da ta soyamusu kwai.
Shi kuwa sanin akwai din yasa shi tsayawa gami da rike k'ugu bayan ya ciro kwai guda bakwai a firij. Toh ya zaiyi? Me da me ake sanyawa acikin kwai idan za'a soya? Ya ta6e baki don yasan bai wuce maggi kawai ba sai a yanka albasa. Nan ya tace ruwan shayin ya sanya a filas kafin ya koma ya dauko (bowl) ya soma fasa kwan, ya bi wata kofa dake cikin kicin din wanda ya kasance store, ya dauko albasa guda daya. Haka ya na gyarata yana hawaye, idanunsa a rufe ruf, ji ya yi an rike hannuwansa. Ya bude idanun dakyar ya na duban Ummi wacce jin shiru ta biyo baya, ta hadiye dariyarta.
"Kawo zan karasa don..."
Ai bata karasa maganar ba ya sakarmata albasa da wukar ya fita da sauri-sauri yana fadin. "Ina sonki fa."
Saida ta tabbatar ya yi nisa kafin ta tuntsire da dariya ta yi mai isarta sannan ta soma aikin.
Shi kuwa gogan yana bandaki ya na fama da wanke idanunsa, saida ya wanke hannunsa tas da handwash kafin ya soma da fuskarsa, bayan ya kammala ya goge da karamin tawul, sai kuma ya tunano da Umminsa wacce ya ce ba zata shiga kicin ba, ya dan daga gira. Toh ya zai yi? Daman fa ba ta6a shiga kicin din ya yi ba, shawarar Haidar ya bi wanda ya ce a ranar farko ya yi mata karin kumallo da kansa. Alokacin dubansa ya yi ya yamutse fuska.
"Kasan dai ba shiga kicin na ta6a yi ba ko?"
Haidar ya yi dariya ya daki kafadarsa.
"Koya za ka yi for the sake of love."
Alokacin murmushi kawai ya yi.
Sauke ajiyar zuciya ya yi gami da ajiye tawul din a ma'ajiyarsa, kai tsaye ya fito falon, kamshin suyar kwai ya cika falon, k'arar kwankwasa kofar da akayi ne yasa shi fasa shiga kicin din ya nufi wajen kofar. Malam Ado direban Hajiya Babba ne rike da kwando. Ya gaisheshi da girmanawa, Faruk ya amsa kafin yasa hannu ya kar6i kwandon da ya ke mik'o mishi.
"Gashinan, Hajiya ta aikoni na kawo."
Murmushi Faruk ya yi, da yasan zata aiko ai da bai wahalar da Umminsa ba, ya mishi godiya sannan ya sallameshi.
Ummi da ta ke jera kayan kari a saman tebur ta soma bin hannun Faruk da kallo ganinsa rike da kwando. Ta karasa bayan ta ajiye tiren hannunta, ta kar6i kwandon alokacin da ya ke fad'in.
"Kinga Hajiya ta aikomana da abin kari kuma."
Murmushi kawai ta yi.
Farfesun kaza ne sai kuwa ruwan shayi a filas, farfesun ta zubamusu, suka yi zaman sha. Yanda ya ke tarairayarta tamkar wata bebi abin har ya soma daina bata kunya don ta lura kamar halinsa kenan idan zata tsaya kunyarnan sai ta cuceshi kamar yanda ya sha fadamata kenan, ba ya son kunyarnan idan sun yi aure.
Karfe sha daya da mintuna suna zaune a falo ya sanyata jikinsa suna hira inda ya ke k'ara yi mata albishir da zai nemamata Malamar da zata dunga zuwa har gida domin koyar da ita, wannan albishir da ya ke yawan yi gareta yafi komai sanyata cikin farinciki. Hon da aka yi ne yasa hankalinsu ya koma ga waje, maigadin ya bude aka shigo, hakan yasa shi mikewa gami da lek'e ta windo. Murmushi ya yi sannan ya dubi Ummi.
"Yan uwanmu ne fa 'yan Gombe." Jin haka batasan sadda ta mike tsaye ba tsabar d'oki ta nufi hanya don budemusu.
"Tsaya mana." Muryarsa ta katseta. Dankwalinta ya mik'omata ta yafa a kanta suka sakarwa juna tattausan murmushi kafin ta nufi kofar da ake kwankwasawa don ta bude shi kuwa ya koma sashensa.
Anti Halima ce ta soma shigowa sai kuwa Hajiya Salma a bayanta da sauransu. Ta rasa ina zata sa kanta don farinciki, wannan ya rungumeta wannan ya shafa kanta, duk sai ta ji kunya ta cikata. Abu ta yi mata rada a kunne.
"Har kin chanja." Ta harareta, ta tuntsire da dariya.
Haka suka shiga suka zauna. Nan wadanda basu samu zuwa ganin gida ba suka hau zagaye, Faruk ya fito wannan karon sanye da dogon wando maimakon gajere ya durkusa yana gaidasu. Ummi ta dan dubeshi.
'Ashe yasan kunya.' Ta fada a ranta. Bayan gaishe-gaishe ne ya fita jin cewar da Gidado suke. Hajiya Salma ta ja Ummi har d'aka, wasu kayayyakin ta kara damk'amata sannan ta bita da nasihu masu ratsa jiki da jini. Karshe ta rungumo kafadarta yayinda kwalla suka cicciko mata har saida suka zubo.
"Ina ganinki tamkar Zahra Innon Abubakar, ina kaunarki har cikin zuciyata Ummi. Ki rikeni matsayin uwa kamar yanda na rikeki nake miki kallon diyata kinji?"
Ummi dake hawayen farinciki itama ta gyada kai tana murmushi mai bayyana hakora.
"In sha Allahu Mama (Kamar yanda ta ji Abubakar da kowa ma suna fad'a) za ki sameni mai yin biyayya gareki irinta d'a da uwa."
Hajiya Salma ta share fuskarta yayinda ta ke ji kamar da Zahra ta ke magana, ta rike hannun Ummi.
"Allah Ya albarkaci rayuwarki Ummi. Tashi ki adana wadannan kafin wani ya shigo."
Ta amsa da to sannan ta mike ta bude sif ta bude dirowar dake cikinta daga tsakiya ta zubasu.
Sun jima suna hira da mutan Gombe sannan sukayi shirin tafiya.
*** *** ***
Ikram kwance saman gado bayan dawowarta daga makaranta ta yi shiru tana jin takaicin rashin sallamar da basu yi ba da Gidado hakanan bata samu ta kar6i lambarsa ba har ya tafi. A haka Ihsan ta shigo tana sanye da riga da siket yan kanti, su sai gobe zasu wuce. Ta dubeta duban kurilla kafin ta zaune gefen gadon cike da damuwa.
"Na tsani na ganki cikin wannan yanayin wallahi 'yar uwa, ji na nake yi kamar zazza6i. Ke kuma ga shi nayi-nayi ki fad'amin damuwarki kin k'i, karki manta a baya kece mai bani shawara kan na cire damuwar komai cikin raina game da Yaya Faruk, yanzu kuma da Allah Ya yayemin sai ke ki ke neman jefa kanki cikin damuwa wacce jikina ke bani kamar damuwar irin tawa ce."
Ikram ta dubeta da mamakin yanda akayi ta d'agota da sauri haka. Ta numfasa kafin ta mike zaune ta matso gareta jiki a sanyaye.
"Ki yi hakuri Ihsan, banaso sanyaki damuwa shiyasa ban fadamiki ba, wallahi son..."
Sai kuma ta yi shiru tana mai jin nauyin furucin. Ihsan ta dubeta cikin zak'uwa.
"Inajinki ki yi magana."
Ikram ta sadda kanta.
"Wallahi Soyayyar Gidado yayan Ummi ne ya maidani haka, bansan..."
"What?!" Cewar Ihsan hankali a tashe cikin daga murya, wannan yasa Ikram kasa cewa komai ta yi shiru kawai. Ko me Ihsan ta tuna sai kuma jikinta ya yi sanyi ta buga tagumi ta yi shiru. Batasan sadda ta soma hawayen bakin ciki ba.
"Mun shiga uku Ikram, mun shiga uku, ya akayi muka k'are a fadawa tarkon jinin Ummi? Kin kamu da son Gidado wanda bai fiki da komai ba, asalima kin ketareshi a aji, ga shi ina shirin auren Abubakar wanda a baya nake hura hanci nake tunk'aho nake kuma gani kamar na yi miji na nunawa sa'a wanda yafi Yaya Faruk komai na jin dadin rayuwa, ashe tunk'aho nake yi da dangin Ummi, yarinyar da tun farkon ganina da ita ban ta6a jin digon kaunarta ba, yarinyar da nake kishi a kanta. Saidai zuwa wannan lokacin na makaro don ban isa na tunkari Abba nace bana son Abubakar ba, ban kuma isa na ce hakan ba koda a karon kaina ne don yanzu inason Abubakar Ikram, ina jinsa a raina sai nake ganin abin tamkar a mafarki duk da cewar jinin Ummi ne, kinsan kuwa Abubakar koyaushe mukayi waya ba shi da hira sai ta Ummi? Sai ince miki wallahi ko matarsa Badiyya, ba ya yimin maganarta kamar yanda ya ke min ta Ummi a yanzun, koyaushe cikin kwatantamin yanayinta da Innonsa ya ke yi, ya na yawan cemin ya na jinta kamar Innonsa, sai ince miki tun jiya da na 6ata ransa a wajen fatin Yaya Faruk akan Ummi har yanzu ya k'i kiran wayata balle na samu damar ba shi hakuri, ni kuma gani nakeyi zubda aji ne na dauki waya na kirashi akan wata Ummi. Don Allah Ikram kada ki sa mu ji kunya, ki barmu ma da wannan da muke sha sanadiyyata, kuma naga kin soma shigewa Ummi, don Allah ki fita hanyarta."
"Kuskure babba da ku ka tafka a rayuwarku."
Suka tsinci murya daga bakin kofa, gaba daya suka juya ga kallonta. Intisar ta karasa shigowa ta rufe kofar don kuwa a dazun Ihsan bata karasa rufeta ba. Ta tako a sannu sakamakon kumburin da kafafunta sukayi ta isa garesu ta janyo kujerar gaban madubi ta zauna kafin ta dubesu a tsanake fuskarta a daure sannan ta soma magana....
[2/8, 12:30 PM] +234 703 962 5239: [2/7, 10:35 PM] +234 703 663 6364: DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
121
"Kin 6ata wayonki Ihsan, kin kuma bani mamaki sosai wallahi, ban yi zaton a duniya za ki iya zurfafa kiyayya ga DAN ADAM ba. Wannan jahilci zan kirashi ko kuwa dai hauka? Tabbas akwai ban mamaki, na daya, idan a baya hujjarki Ummi 'yar aikin gidanku ce, to yanzun ta tashi daga wannan matakin. Na biyu Ihsan, idan rashin dangi yasa ki ke uzzura rayuwar baiwar Allahn nan, toh fa wallahi a yanzun idan bata nunamiki yawan dangi ba, ba za ki fita ba. Ki ji tsoron Allah Ihsan, yarinyarnan Allah Ya kaddara dole zata shiga cikin zuri'armu, kar kuma ki manta Kawunta (Alhaji Kabiru) aminin kut da kut ne da mahaifinki, kinga kuwa babu, babu ta yanda zaayi ki gujewa auren dan uwanta Abubakar saidai idan Allah Ya kaddara ke da shi ba za ku kasance ma'aurata ba. Ihsan ko Annabinmu sallallahu alaihi wasallam ya hanemu da zurfafa kiyayya har haka, akan wane dalili za ki dasawa zuciyarki muguwar tsanar Ummi? Toh wallahi Ummi 'yar halak ce, ta kuma wuce a kirata da Butulu mai mance halacci, Allah Ya bata baiwa ta hakuri, haba jama'a, ki tuna irin wulakancin da ki ka sha yi mata tun zuwanta gidanku har kawo lokacin da akace ta zama matar Yaya Faruk, ki kuma tuna irin yanda hakan baisa ta rik'emu ba a zuciyarta, asalima har yau bata bar bamu girman da ta ke bamu ba, shi DAN ADAM yana da matsala, ya na manta cewar shima halitta ce mai daraja har kiga wasu lokutan yana wulakanta kansa ta hanyar biyewa sharrin zuciyarsa ya yi ta aikata 6arna alhalin a karon kansa yasan cewa lallai 6arnar ce. Ba ku kadai ba, daidai da su Anti Jidda basu kyautawa kansu ba da a baya suka zagi baiwar Allahn nan suka tsangwameta, Yaya Faruk ya burgeni burgewa da bai fasa ja baya ba har ya kai ga cimma burinsa da taimakon Allah, ya auri Ummi. Idan wannan bai isheki ishara na ai ya kamata ace gujewa Yaya Faruk da ki ka yi ki ka za6i Abubakar kuma ya zo ya kasance jinin wacce ki ke ikrarin kin tsana, ya isheki ishara. Saidai na yi mamaki yau da na saurari maganganun da ke fitowa daga bakinki, anya Ihsan kina da imani kuwa? Toh ko kina da shi ba ya tasiri akan Ummi, ina fatan shiriya gareki, Allah Ya ganardake. Ke kuma."
Ta juya ga Ikram wacce ke faman hawaye ga gumi da ta had'a sakamakon da na sani marar misaltuwa da ya k'ara shigarta gami da kunyar Ummi da ta ke gani kamar tana gabanta, bata mance marin da ta yi mata akan an mareta da tozarcin da ta yi mata cikin shago.
"Ki zauna nan ta zugaki ta baro ki, kuma kinsan Allah? Inaji a jikina soyayyar Gidado sai ya wahalar da ke kamar..."
Da sauri Ikram ta toshemata baki da hannu, ta soma girgiza mata kai tana kuka sosai.
"Don Allah karki yimin baki, ki dubi daraja ta zumuntakarmu Sis."
Ta sauke hannunta gami da rike kanta tana kuka.
"Na jima da gane laifina, na jima da neman gafarar Ummi, bana fatan soyayyar da nake ji game da Gidado ta fi yanda nake ji a yanzu, na tabbatar zan iya mutuwa aduk sadda ya k'i aminta da soyayyata, in sha Allah shi ba MIJIN MACE DAYA bane, ku tayani addua."
Ta kara fashewa da kuka, dan uwa rabin jiki, duk sai ta karyamusu zuciya, Ihsan ji ta ke da ace tana da iko da ta raba Ikram da wannan makahon son, da ta raba zuciyarta da son Abubakar. Hawaye kawai suke yi, Intisar ta daure ta hadiye nata kukan don batason kara karya zuciyarta. Ta dafa kafadarta.
"Allah Yana tare da ke, mu cigaba da mika kokenmu gareShi, zanyi miki taimako daya, zan samu Ummi da kaina na sanarmata na tabbata ba zata bamu kunya ba, ita zuciyarta ba irin tamu bace, ta fimu hakuri."
Tana kaiwa nan ta mike jiki ba kwari.
"To tsaida hawayen mana Matar Gidado."
Cewar Intisar tana riko ha6anta, dariya sukayi banda Ihsan wacce ta kasa gane hakikanin abinda maganganun Intisar suka sanya ta ji.
*** *** ***
A gidan Ango da Amaryarsa kuwa, babu abinda sukeyi sai dirzar amarci hankalinsu kwance, kwanaki biyun da suka yi sai bak'i suke samu, a rana ta uku ne suma 'yan Adamawa suka je gidanta, Hajiya Salma tuni ta bi yan Gombe har Abubakar sun koma don shi Alhaji Kabiru kwana biyar ya yi ya juya Adamawa. Basu jima gidanta ba suka wuce su dinma a ranar suka tafi. Gidan ya rage su kadai a koyaushe, babu ranar da basa waya da mahaifinta da su Dada, hakanan Hajiya Babba kullum saita kirata sun gaisa. Hatta su Hajiya Mama da Mami Ummi kiransu ta ke yi hakan ba karamin dadi ya ke musu ba. Tsakaninta da mijinta sai sam barka don kuwa kullum soyayyar junansu k'aruwa ta ke a zukatansu.
Haka har suka yi kwanaki shida suna tare, ita kadai ce zaune wajejan karfe uku, Faruk bai jima da cin abincin rana ba ya fita zuwa gaida su Hajiya Babba. Zuwansa na uku kenan tun bayan auren, ta ji ana kwankwasa kofar falon, koda ta bude ta yi mamaki na ganin Husna da kanwarta karama Siyama. Batasan sadda ta daka tsalle ta rungumeta suna dariya ba. Sai bayan sun shiga ciki hira kuma ta 6arke, Husna sai kod'a irin chanjin da ta ga ta yi ta ke, Ummi banda murmushi babu abinda ta ke. Sun jima, ta taimakamata hada abincin dare kafin ta dubeta.
"To sai wanka ko?"
Ummi dariya ta yi, ba musu ta fafa wanka, bayan ta fito ta soma shiri suna hira da Husna wacce ke zaune saman gadonta tana kallon hotunan biki gami da yaba irin wankuwar da sukayi harda daukar wanda akayi musu su biyu, can ta dago ganin Ummi na kokarin sanya wata atamfa dinkin riga da zani rafa ta dan harareta.
"Kar ki cemin tun zuwanki kwalliyar atamfa da lesuna ki ke yi? Gaskiya yau ki sanya kananun kaya."
Ummi ta murmusa.
"Ke wallahi don ba ki ga kananun kayan ba ne duk kama jiki sukeyi, kusan iyakar tsawon rayuwata ban ta6a sanya kananun kaya ba banda riga da siket su kuma ba matsastsu ba."
Husna ta mike tsaye.
"Shiyasa fa na cewa Amina sai mun dunga sanyaki a aji don duk abin Amina wallahi ta fiki wayewar kai, matsa kiga ina suke na za6o miki? Ai nan gidan mijinki ne ba haramun ki ka aikata ba, ko ba ki ji yanda Anti Jamila Bappa ta group ke yawan magana akai bane? Duk kuma litattafan da na ba ki ai anyi bayaninsu."
Daga haka ta shiga duba kalolin kayan, kananun kaya ne masu kyau matuka da tsada, wata abokiyar kasuwancin Hajiya Babba ta aikomata na Amarya da kuma kudade wanda ta ce na Ango ne.
Wata riga (purple) mai hannun shimi ta dauko da wando bak'i dogo mai kama jiki ta dubi Ummi tana mai mik'amata.
"Kar6i ki saka wadannan."
Ummi ta zaro ido saidai hararar da ta samu daga wajen Husna yasa ta darawa.
"Wannan kallo sai kace na ce bazan saka ba?"
"Ki ce din ma mana mugani."
Suka dara kafin ta fita ta bata wuri don ta shirya, tana zaune falo Ummin ta fito.
"Masha Allah!"
Shine furucin da ya fito daga bakin Husna ganin irin kyan da Ummi ta yi. Batasan sadda ta mike tsaye ba, rigar har taso matseta hakanan ta fiddo da halittarta sosai kamar yanda shima wandon ya zauna d'abas a jikinta. Fuskar ta sha kwalliya, ta tufke kitsonta da ribbon sai kuwa dan mayafi na pashmina da ta dan daura akanta da kuma dan kunne fashion mai kyau.
"Kai Ummi, kin fito wallahi kamar ba ke ba."
"Anti Ummi kinyi kyau." Cewar Siyama.
Ummi ta murmusa kadan tana jan riga.
"Nagode, saidai anya zan iya bari ya ganni haka?"
Tsaki Husna ta ja don haushi ta dauki mayafinta don daman ita ta ke jira ta fito su yi sallama.
"Matsalarki, wallahi da kinsan waye mijinki da ba ki tsaya wannan kauyencin ba, tuni wata a waje ta yi miki sakiyar da ba ruwa, koda su Fati na kafa miki misali ya isheki, ga ki da dan karen kishi kuma kina ja baya wajen gyara, don Allah Ummi ki k'ara sakin jikinki, wallahi duk abinda ki ka yi ga mijinki ba ki