Showing 141001 words to 144000 words out of 158267 words

Chapter 48 - Dan Adam Book 1 Complete Hausa Novel

fadi ba. Wallahi mata suna nan suna harin miji irin naki basu samu ba, amman Allah Ya damk'a maki ba don wayonki ba, ki watsar da kunyar komai ki rungumeshi hannu bibbiyu. Shikenan dai ni zan wuce sai munyi magana ta whatsapp."
Ummi cike da jin kwarin gwuiwa ta yi mata rakiya iyakar kofa, daman yanzun kusan ma ta rage kunya-kunyar don salo-salon Faruk kadai ya isa sanyata dainawa domin kuwa shi babu ruwanshi koyaushe janta ya ke yi. 
   Ba shi ya shigo gidan ba sai bayan sallar isha'i adalilin rakiya da ya yiwa Daddy wani wuri. 
    Tana jin tsayuwar motarsa, ta ruga daki a guje ta kara gyara fuskarta ta fesa turare sannan ta fito ta budemishi kofa, sak ya yi yana dubanta, ta yi kasa da kanta gami da sa hannu ta kar6i ledar hannunsa.
"Sannu da zuwa." Ta fada gami da ba shi hanya. Ya shigo ya tura kofar ya rufe har da mukulli, har lokacin dubanta ya ke yi don ya kasa cewa uffan, ya ja hannunta zuwa falon ta ajiye ledar saman tebur, ya riko kafadunta. 
  "Mamaki fa ya k'i saki na, Ummin Faruk ce kuwa?"
  Ta na murmushi amman ta kasa magana saima ta sa tafin hannu ta rufe fuskarta. Ya janyota jikinsa.
"Kinyi kyau fiye da zatonki, ina kara sonki Ummina, ki dunga yimin irin shigarnan ina so."
  Ta gyada kai kawai don ta tsorata da ganin yanda ya susuce tasan babu sauki. 
  Ai kuwa janta ya yi sai sashensa. 
        
   Washegari suka samu bakuncin Haidar da Intisar, Haidar nan ya bar Intisar suka wuce masallaci tare da Faruk kasancewar juma'a ce, Ummi ta saki jiki da Intisar ganin yanda itama ta saki jiki da ita, daman ta riga da ta kusan kammala girkinta, ta taimaka mata suka karasa tana labartamata yanda rainon ciki ya ke da kuma sanadin kumburin kafafunta.  "Kai, mata na fama wallahi, Allah dai Ya rabaku lafiya."
. Cewar Ummi jiki a sanyaye dalilin tunanowa da Ummanta, yanzun ko awane hali Saude suke ciki? Allah Masani. 
  "Amin kedai, fatanmu Allah Ya bamu mai sauki."
"Amin."
Bayan sun kammala suka dawo falo, suma sallah sukayi sannan suka yi zaman hira, kusan ma Intisar ce mai yin rabin hirar. A haka kuma ta gangaro zuwa ga maganar dake sosa ranta inda ta soma magana.
  "Ummi ina neman wata alfarma gareki akan kanwata Ikram."
Saida ta ji gabanta ya fadi batare da tasan dalili ba, ta dafe kirji.
  "Gareni kuma Anti?"
Ta gyada kai.
"Kwarai kuwa."
Ta girgiza kai.
"Ai a duniya babu abinda za ku nema na kasa yi gareku matukar baifi karfina ba idan har Allah Ya bani ikon yin."
  Murmushi Intisar ta yi. Ta soma labartamata yanda akayi tun farko tasan Ummi na son Gidado har zuwa kadan daga hirarsu kwanaki ta dora da fadin.
"Don Allah Ummi ki taimakawa kanwata, na gaskata tana son Gidado da gaske ba wai iyaka baki ya tsaya ba, nasan kuma wannan jarrabawa ce babba ta iso gareta."
   'Anya ba mafarki nake ba?' Ummi ta jefawa zuciyarta wannan tambayar....!!
 
 

  
[2/8, 10:05 AM] ‪+234 803 862 6581‬: DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

122

Ta kasa gaskata lamarin, gani ta ke yi kamar ba idanunta biyu ba, dafa hannunta da Intisar ta yi ne yasa ta dago kai tana dubanta kamar wata wawuya.
"Kar ki yi wani zargi akan haka, nasan wacece Ikram, wallahi da ace karya ta ke yi da maganar kafin ta iso kunnenki ta ruguje don bazan amince mata ba saidai iyakar gaskiyarta ta nuna kuma ta furtamin na ji."
Ummi ta numfasa kafin ta dora daya hannunta saman na Intisar tana murmushi.
"Anti da ki ke kiran Ikram da kanwarki, nima 'yar uwa na dauketa, ina mata kallon jinina, wallahi ko kusa ba wani zargin nake ba, kawai dai abin ne na ji shi banbarakwai saidai tunawa da na yi Allah Shi ke da wannan ikon, yasa na ji zuciyata ta wanku kuma na kara gaskata faruwar hakan. Na tausayawa Ikram matuka kuma in sha Allahu zan taimakamata, saidai ta saka a ranta shi aure nufin Allah ne, idan Allah Ya yi matarsa ce ita to ba makawa zata zama idan kuwa ba matarsa bace..."
Sai ta yi shiru, Intisar dake kallonta kallo na burgewa tana mai kara jin kaunar halayya irinta Ummi wanda ya sha bamban da mafi yawa cikin mutane ta fadada murmushin.
"Karki damu, munsan komai kaddara ne, in sha Allahu na tabbatar ba za mu ji kunya ba."
Ummi ta murmusa. A kasan ranta ta shiga damuwa, ta ina zata faro? Tasan sanarwa Gidado abu ne mai sauki saidai kuma da wane ido zata dubi Hafsa matarsa? Batasan kalar nata kishin ba, kada fa ta rik'eta a zuciya?
'Komai na Allah ne, zai taimakemu.' Cewar wani 6angare na zuciyarta. Shigowar mazan ne ya katse tunanin kowaccensu, dukkansu cikin fararen kaya, sunyi kyau hakanan kamanninsu ya kara bayyana sai hira suke yi har suka karaso falon. Suka yi musu sannu da zuwa, nan suka zauna, ba kunya Faruk ya zauna kusa da matarsa gami da riko hannunta.
"Ummina na dawo, kinsan addu'ar da na yi mana?"
Kunya ta kamata, Haidar ya ja guntun tsaki yana dariya.
"Daman haka ka ke? Ina maka kallon wani mutum da baisan komai ba, ashe-ashe?"
Faruk ya shafi sumarsa yana taya Intisar dariyar da ta ke yi. Ummi kuwa kanta na kasa tana murmushi gami da kokarin zare hannunta cikin na Faruk saidai hakan ya gagara.
Baice mishi komai ba saima ya sanya bakinsa saitin kunnen Ummi.
"Addua na yi akan Allah Ya bamu twins."
Ai da sauri ta mike ta na fadin.
"Nan za'a kawo muku abinci ko acan za ku ci?"
Su Haidar da ke dariya suka mike yana taimakawa matarsa.
"Ina zamu wahalar da ke? Wannan Angon naki ba shi da ta ido gwara muyi-muyi mu tattara mubar gidannan."
Faruk ya shagwa6e fuska.
"Kai brother."
Cikin dariya Intisar ta dubi mijinta.
"Don Allah ka kyaleshi hakanan." Ta yi maganar cikin kasa da murya don har lokacin ba wani sabo ta yi da Faruk ba, ya ja karan hancinta yana dariya.
"Ke bakisan waye wannan ba da ba zaki tausayamishi ba."
Murmushi ta yi kawai suka rankaya gaba daya wajen tebur.
Bayan gama ci da sha kuma suka dawo falon inda Haidar da Faruk suka wuce sashen Faruk din suka barsu, nan kuma hira sosai suka shiga yi, Ummi ta sake sosai da Intisar wannan karon har suna kyakyata dariya. Sai kara yabawa da halin Ummi ta ke yi, ashe haka ta ke da dadin sha'ani?
Ba su suka bar gidan ba sai yamma, tana zaune itama Faruk ya ce ta shirya su fita. Har tsalle ta yi don murna ta fada daki, mayafi kawai ta dora saman maroon lace din dake jikinta ta sanya takalmi mai tudu mai kalar bak'i da maroon. A kofa sukayi kici6us da gogannata, bai chanja kaya ba, ya karemata kallo, ta yi mishi kyau ta kara haske. Ya shafi gefen fuskarta.
"Bazan gaji da fadamaki ina sonki ba."
Murmushi ta yi cikin jin wani sanyi a ranta.
"Nima haka."
Ya dago ha6anta.
"Kema me?"
Ta lumshe ido tana murmushi.
"Ina sonka."
Ya ji dadi gami da sumbatar le66anta.
"Nagode Ummina, muje ko?"
Yana rike da hannunta suka fita, kai tsaye wajen ice-cream suka nufa, nan suka siya suka yi zaman sha, saidai ko mintuna uku basu yi ba ya kasa jurewa ya ce ta taso su sha a mota, gani ya ke yi kowa a wajen ita ya ke kallo, kusan ma baisan ta fishi murna da hakan ba don kuwa gani ta ke yi yan matan gaba daya na wajen idanunsu akan mijinta suke. Bayan mota suka zauna kamar zai shige jikinta, yana bata tana ba shi, ba zato aka kwankwasa musu gilashi, suka dubi wajen kadan daman suka bude, ya karasa sauke gilas din batare da ya matsa daga jikin matarsa ba, wata budurwa ce sanye cikin kananun kaya kanta ko kallabi babu. Ta daga mishi yatsu tana mishi wani kallo bayan ta dubi Ummi dake gefensa. Irin zaman da sukayi ya nunamata alakar dake tsakaninsu, wato dai matarsa ce. Sai ta ji ta kasa maganar da ke bakinta.
Fuskarsa kamar bai ta6a dariya a duniya ba, ita kanta Ummin fuskarta daure tamau tana jin zuciyarta na wani zafi, ashe haka kishi ya ke?
"Lafiya dai?" Cewar Faruk cikin kakkausar murya. Duk saita daburce, ganinsa dazun yana murmushi ta dauka bazai yi wuyar aminta da ita ba, yanzun kuwa sai ta raina kanta.
"Sorry, na dauka wani face da na sani ne, ashe ba shi bane."
Ya dan daga gira kadan bai kara kallonta ba ya daga gilas ya rufe! Sum-sum tabar wurin gayu na mata dariya.
Ya ja tsaki.
"Mata kenan, sun maida kansu tamkar karnuka."
Ummi dai ba ta ce komai ba, jin shirun ne yasa shi dubanta, ta miko mishi ice-cream dinta.
Ya hada har hannun ya rike ba tare da ya saki ba ya ce.
"Lafiya dai?"
Ta girgiza kai tana murmushin yak'e.
"Bakomai ya isheni ne."
Ta fada tana kokarin danne hawayen da ke son zubomata, duk da ranta ya yi sanyi da irin yanda ya yiwa budurwar nan saidai ta kasa fidda kishin a ranta. Ya gane hakan, ta kuma kara burgeshi, ya juya ya cigaba da shan ice-cream din, cikin kara son zolayarta ya ce.
"Haka fa yan matannan suke tsareni ko a ofis, saidai ni ba ruwana da kowaccensu. Bakiga ma wata ba kyakkyawa da ita.."
Bude kofar da ya ga ta yi ne yasa shi yin shiru, fita ta yi ta dawo gaba ta zauna. Ba tare da ta dubeshi ba ta soma magana cikin rawar murya.
"Don Allah mu tafi kaga Magriba ta kusa."
Baice uffan ba har ya kammala shan ice-cream dinsa, ya goge bakinsa da tissue kafin ya tsallako gaba ya zauna mazaunin direba.
Ya dubeta bayan ya sanya bak'in gilashinsa wanda ke kara mishi kyau.
"Wai ni fushin nan na menene?"
Ta girgiza kai.
"Bakomai."
Ya rausaya kai kawai ya tada motar ya ja, har suka isa gida rediyo ne kawai ke aiki.
Suna shiga ta fada dakinta ta ajiye mayafi sannan ta shiga bandaki ta dauro alwala ganin an soma kiraye-kirayen sallah, shima ganin haka yasa bai bi ta kanta ba saida ya je ya yi alwala ya fice masallaci. Bayan ta idar ta yi ta rokon Allah akan ya sauwaka mata zafin kishin da ta ke ji a ranta game da Faruk. Babu abinda ke tayar da hankalinta face furucinsa na a ofis dinsa ma ana mata na takura mishi. Kenan ma abin dadi ya ke mishi ko? Ai kawai sai ta sanya kuka. Jin motsin mutum ta yi a kofar dakin, hakan yasa ta saurin goge fuskarta. Ya karaso ciki ya zauna a kasa gefen dardumar da ta ke zaune.
"Ni ne ko?"
Ta kauda kai gami da kokarin mikewa, ya ja hannunta ta koma ta zauna suna fuskantar juna.
"Ki yi hakuri, Ummina da ace zasu burgeni da tun kafin na ganki na soki su zan fara so saboda nasha ganin ire-irensu, amman babu daya da ta ta6a kwantamin cikinsu, sam ba su daga cikin kalar matar da nakeson aure infact ma ni ban ta6a son wata ba bayan ke, bana fatan kuma Allah Ya jarabceni da son wata din bayan ke."
Ta ji ranta ya yi sanyi, tasan banda ma abin kishi ina ita ina wani kishi da wasu bayan tasan matsayinta wajen mijinnata?
Ta sauke kanta kasa tana murmushi, abin ya ba shi dariya.
Ranar kam sai a hankali....!!!

"Allah Sarki." Shine furucin da Amina ta yi bayan gama sauraron jawabin Ummi game da Ikram. Amina ta cigaba da magana....!
  DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  123

"Kinga yanda Allah ke jarraba bayinSa ko Ummi? Kiga dai yanzun kin zame musu wata abar, kinga ikon Allah wannan karon wajenki Ikram ke neman alfarma ko? To don Allah kar ki rikesu da komai duk kuwa na tabbatar ba ki rikesu a rai ba. Yanzu ni bansan me zan ce miki ba akan wannan abu, saidai gaskiya inajin tausayin Ikram kamar yanda rayuwar Gidado da Hafsa ta burgeni, anya kuwa ba za mu yi musu shishshigi ba?"
Ummi ta dan cize le6anta na k'asa gami da mikewa tsaye daga zaman da ta yi a gefen gado. 
   "Shine nima wallahi Anti, wannan ne matsalar, da ma ace Yaya Gidado ba shi da mata ne, da babu abinda zai hanani sanarmishi, kawai..."
  "Ko za ki jarraba fadawa Yaya Abubakar? Watakil shi yasan shawarar da zai bada."
   Ta gyada kai jin abinda Amina ta ce.
"Kuma fa hakane."
Suka tsaida wannan shawarar kafin kuma suyi sallama ta yi kiran Abubakar. Bai daga ba sai ya yi saurin yankewa ya kirata. 
"Innota ya akayi?"
Murmushi ta yi sannan ta gaisheshi ya amsa gami da tambayar lafiyarta da ta maigidan.  Bayan gama gaishe-gaishe ne ta fadamishi maganar Ikram, ta kara da fadin.
"Ni kuma wallahi ina kunyar Anti Hafsa, banaso wani abu..."
  "Kar ki damu, shi aure ai nufin Allah ne, idan Allah Ya yi sai ta zama matarsa to zata zama din. Yanzu dai abin yi bai wuce na a sanarmishi ba, ai ko don halaccin da mutanen nan suka yi mana na rikemana ke amana ba tare da sunsan komai naki ba ya kyautu mu yi musu abinda yafi haka muddin bai fi karfinmu ba, zan nemi shi Gidadon, batun kuma wai Hafsa karki damu kanki, Allah ne Ya bamu damar yin fiye da daya matukar zamu yi adalci tsakani." 
   Ita dai ta yi tsuru da idanu ta rasa abin cewa banda um don kuwa tsoronta bai wuce daukar da Hafsa zata yi mata ba. Abubakar ya ce kada ta damu daga haka ya tambayeta ko akwai wata matsalar ta amsa da babu sannan suka yi sallama. Koda ta shaidawa Amina yanda sukayi Amina ta amsa da cewa.
"To, sai mu tayasu da addu'a, idan akwai kaddarar aure tsakaninsu, Allah Ya hadamishi kansu, Allah Ya kawo lamarin da sauki."
"Ameen." Daga haka sukayi sallama.

  A washegari kuwa Abubakar ya kira Gidado ya sanarmishi, dariya Gidado ya yi don zatonsa wasa kawai Abubakar ke yi.
"Banda abinka, ina diyar birni wacce ta tashi cikin daula ina ni dan kauyen Jar Kwami? Haba dan uwa, gyara zancenka."
   "Kada ka dauka wasa na ke yi Gidado, I'm serious. Ka yi tunani akai please."
Gidado ya yi shiru, daman fa ya tsargu da irin yawan kallon da ta ke mishi hakanan kuma da yawan murmushinta gareshi saidai ba shi da kakkarfar hujja, to shi me zai iya yi mata? Alal hakika babu wacce ya ke so kamar Hafsa, kuma ace ko yanzu ko shekara basu yi ba ya tashi neman aure? Auren ma wacce yasan zai sosa zuciyarta fiye da auren wata a kauyennasu? Ya girgiza kai tamkar Abubakar na gabansa.
  "I'm sorry Abubakar, gaskiya..."
"Karka yanke hukunci da gaggawa mana, ka yi tunani don Allah, ko don irin rikon da suka yiwa Ummi ai..."
"Ya isa, karka sanyo batun wannan don Allah, ana magana ne fa ta aure wanda ya kasance raayin mace da namiji."
"Idan Allah Ya kaddaro fa?" Abubakar ya tari numfashinsa. 
  Ya sauke ajiyar zuciya wanda har kunnen Abubakar.
"Wannan kuma kaddara ce, sai ayi."
"To haka nake so ka saka a ranka, idan Allah Ya kaddara aurenka da Ikram sai fa anyishi koda ace babu son ranka ciki. Ka barwa Allah za6i sannan don Allah zan aikomaka lambarta ka dunga kiranta, mai sonka ai yafi makiyi, don Allah dan uwa ko gaisuwa ce ka daure ku dunga yi, yarinyar na wahala ne akanka."
Dariya Gidado ya yi don abin mamaki ma ya ke ba shi, to me ta gani a jikinsa da har ta ji ya burgeta?
  Haka Abubakar ya cigaba da yi mishi magiya har saida ya aminta da hakan sannan suka rabu. Ko mintuna uku baayi ba ya aikomishi lambar ta whatsapp. Koda ya adana ta cikin wayarsa, ya bude hoton da ta dora, hotonta ne na bikin Haidar da Intisar, da k'ibarta a hoton, tana dariya ta rungume Amarya da Ango aka dauka, ya kuramata idanu, bata da makusa saidai bai ji wani sonta a ransa ba illa tausayi da ta bashi na kamuwa da son wanda ba ya sonta. Ya yi mata sallama gami da cewa.
"Kina magana da Gidado, ina fatan mutanen Abuja lafiya?"
  Daga haka ya rufe wayar ya maida aljihu inda ya cigaba da sauraron (customers) dinsa da ya bari suna cinikayya da yaron shagonsa. 
   Sak'on bai iso ga Ikram ba sai Magriba bayan ta dawo daga islamiyya, ta zauna da zummar duba litattafan makaranta sakamakon jarabawarsu ta karshe da ke k'aratowa, ta janyo wayar ta bude. 
   Ta yi mamakin ganin bak'uwar lamba ta whatsapp dinta, saidai me? Tun bata bude gaba daya ba idanunta ya hango mata sunan da ya ambata nasa, wato Gidado sai kuwa hotonsa da ya dora, hannu na rawa yayinda gabanta ke bugu da sauri-sauri ta soma da budo hoton don gaskatawa, ai batasan lokacin da ta diro daga saman gado ba tana buga tsalle hakanan hakoranta a waje ta kasa rufe bakin tsabar murna har da hawaye farinciki, ta dafe kirji. Oh yanzu ya zata ji idan ya furta yana sonta tunda ganin ya kulata kadai ma ya sanyata farinciki, to wai ma a ina ya samu lambarta? 
'Ummi.' Cewar wani 6angaren zuciyarta. 
  Ta k'ara tsalle tana ihun farinciki wanda batasan da karfi ta ke yi ba saida aka murda kofar aka shigo.
"Lafiya?" Jin muryar Hajiya yasa ta nufarta gami da rungumeta tana murna. 
Hajiya cike da mamakin na abinda yasa Ikram wannan farincikin ta dagota daga jikinta tana dubanta, can kasan zuciyarta hamdala ta yi domin kuwa ta mance rabonta da ganin irin wannan fuskar fara'ar ta Ikram, to amma hawayen na menene?
  "Meyafaru ki ke mana ihu?"
Cikin zak'uwa ta ce.
"Yau Yaya Gidado ya yimin magana, ki tayani addua Allah Ya..."
  Dif ta yi don gaba daya ta mance gaban wacce ta ke, idanunta sun riga sun rufe. Ita kuwa Hajiya ta tsareta da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login