Showing 147001 words to 150000 words out of 158267 words

Chapter 50 - Dan Adam Book 1 Complete Hausa Novel

"Ai can na nufa ma."
Sukayi dariya, Ummi hankalinta ya tashi, kamar ta ce mishi kar su je, tasan kawai kunya zai sanyata gaban su Hajiya. 
Ai kuwa suna fita ta hau rok'onsa akan kada su je, baice uffan ba banda murmushi. Saida suka je din, Ikram ta tarbesu kamar ta hadiyesu don yanzu bil hakki tana kaunar Ummi, soyayyar Gidado ya shafeta.
   Hajiya ta yi murnar jin cewar Ummi na dauke da juna biyu, don Faruk da bakinsa ya fadamata, ta hau yi mata gargadi akan ta kula za'a samo mata mai tayata hidima, ta nuna a barshi saidai Hajiya ta dage sai anyi hakan. Faruk bai ce uffan ba don da ta raayinsa shi kansa bazai so ba saidai yana tuna maganar Dakta da ya ce ta dunga hutawa ya amince.
Da Magriba tana dakin Ikram sunyi sallah suka yi zaman hira, anan Ikram ke labartamata yanda sosai yanzu Gidado ke damuwa da ita har idan ya ji shiru bata hau online ba zai damu ya kirata a waya. 
"Ikon Allah." Shine kawai abinda Ummi ta ce, duk kuwa da cewar ta yi mata murnar hakan saidai kasan ranta tana tsoron abinda zai je ya dawo idan Hafsa ta samu labari. Ko da wane ido za ta dubeta?  
   A hakikanin gaskiya ko a baya idan Gidado bai jin wani abu game da Ikram to a yanzun yana ji, don ita kanta Ummin ta fahimta ta yanda duk sadda sukayi waya sai ya yi maganar Ikram, wataran ya ce suna hira wataran ya dunga yabon halin kirkinta . A bakinsa ne ma ta ji cewar suna chatting Abubakar ne ya bashi lambarta. Ko Abubakar din da kullum suke waya bai sanarmata ba. 
  "Ya karatun? Kina ganewa sosai ko?"
Ikram ta fada gami da katse shirun.
Murmushi Ummi ta yi.
"Ina fahimta."
"Allah Ya taimaka, ga Azumi ma ance nan da sati biyu ko?"
Ta gyada kai.
"Hakane, abin ba wuya, kamar yau ne muke lissafi da Anti Amina ta ke cemin bayan Azumi bikinta, yanzu har ga azumin ya zo."
  Dariya Ikram ta yi.
"Kina ban dariya idan kina ce mata Anti, sa"arki ce fa."
  Dariya itama Ummin ta yi kadan. 
"Ta cancanta, ita ta mayemin gurbin uwa kuma Yaya a gurina alokacin da bani da kowa cikin DAN ADAM dake son ya ra6eni, alokacin da kowa ya gujeni. Ita ke cemin na yi wancan mai kyau ne, kada na yi wannan babu kyau, ta zama Malama agareni tun ban kai ga soma zama a aji ba. Kinga kuwa ta cancanta na kirata da Antina."
  Ikram ta gyada kai, ita kam yanzu Ummi na burgeta, mutum ba zai san tana da shiga rai ba sai ya zauna da ita, daman bata tsaneta ba tun a baya sai sadda Faruk ya ce zai aureta har ya mareta akanta ga kuma taya Ihsan kishi. 
   "Lallai ta cancanta har ta wuce cancantar ma. Ni kuma nan gaba ina fatan zama yayarki."
Ta karashe da gwalo, Ummi ta gane, wato ta zama matar Gidado. 
Sukayi dariya lokaci guda.
   "Dagaske nake, kinsan kuwa Hajiya da Daddy sunce saidai nima na karasa jami'a a gidan mijina, da zarar mun gama jarabawarnan ta karshe sai aure."
   Ta jinjina maganar.
"Kice tare za mu sha bikinku da su Ihsan."
  Dariya Ikram ta yi sai kuma ta maida fuskarta kalar damuwa.
"Allah Yasa mu auri wanda yafi alheri garemu."
"Amin."
  
Sai bayan isha'i sannan suka bar gidan zuwa gidansu. Nan kuwa aka shiga rainon ciki babu wasa, yarinya karama aka kawomata, batafi shekaru goma sha hudu ba. Farkon kawota Ummi idanu ta zubamata tana kallonta cike da tausayawa sannan ta dubi wacce ke tare da ita wacce aka kira da mahaifiyarta da ko kusa bata ga kama ba.
   "Yanzu Baba wannan aiki zata dunga yi?"
  "Eh, aiki kowanne da ki ke so ki sanyata, babu wanda ba zata iya yi gareki ba."
  Ta k'ara duban yarinyar wacce ta yi wani firi-firi da idanu. Tausayinta ya kamata. 
  "Shikenan."
Jin haka matar ta hau washe baki tana gyara mayafi zata mike.
"To bari na koma tunda naga gidan, ke kuma Batula ki kula, kada inji kar in soma gani kin sa6awa uwar dakinki kinji ko? Hajiya don Allah ki dunga kula yarinyar akwai shegen munafunci."
  Ummi da ke jin kamar ta makureta ta ce.
"Wane irin munafunci kuma?"
  "Um, kada ta dunga yi miki la6e wai, to shikenan ai, sai anjima, Allah Ya kara arziki."
Ta karashe cikin basar da wancan maganar. Ummi ta bata dubu biyu ta hau mota. Nan ta hau zuba godiya ta fice. 
  Ta maida hankali ga yarinyar da aka kira da Batula.
  "Sannu Batula, inaso ki saki jiki da ni, ki rikeni tamkar yayarki, ni bazan cutar da ke ba, zan kuma rikeki bisa amana kinji ko?"
Cikin mamaki mai tsanani da rashin gaskatawa ta gyada kai don gani ta ke kamar wani salo ne na cutarwa, gida na uku kenan da aka kawota, wadancan biyun duk guduwa ta yi saboda matsi da takura.
   "Fadamin gaskiya Batul, mene alak'arki da wannan matar? Dagaske itace ta haifeki?"
Ta girgiza kai cikin raunin zuciya kiris take jira ta fashe da kuka.
"A'a, kanwar mamana ce uwa daya uba daya da ta rasu."
  Runtse idanu Ummi ta yi ranta na suya.
  "Meyasa ta ke kawo ki aikatau?"
"Babana ne ya aureta bayan rasuwar Mamana, ba da son ransa ta ke kawoni gidan aiki ba, ko yau da zamu taho da kuka muka rabu da shi. Kullum saita dakeni, komai ni nake yi mata."
  Hawaye Ummi ta shiga fitarwa, DAN ADAM kenan, ace 'yar yayarki ki ke yiwa rikon sakainar kashi? Duniya abin tsoro.
   Ummi ta tabbatar mata zata riketa bisa amana, ta bata kyakkyawan muhalli ta sanyata a makaranta. Ita da kanta ta wankemata kanta bayan ta tsefemata kitso, suna yi suna hira Batul na kara bata labarin kauyensu Maraba. 
   Cikin kayanta ta dauko wanda ya yi mata kadan ta bata ta sanya kasancewar yarinyar akwai tsawo nan suka zauna das a jikinta. 
   Koda Faruk ya dawo, ya yi mamaki, bai gane ko wacece ba ganin tana zaune a kasa suna hira da Ummi suna dariya. Batul ta gaisheshi ta yi ciki, ya zauna yana duban Ummi wacce ta tashi ta tarbeshi.
"Ummina wacece wannan?"
Da murmushi ta amsa.
"Itace wacce Hajiya ta turo zata tayani aikace-aikace."
Ya jinjina kai.
"Naga kamar wata kanwarki kunata hira ai."
Murmushin ta kara yi.
"Kanwartawa ce ma. Tausayi take ban."
Nan ta labarta mishi labarinta, shi kansa ya yi mamaki.
"Allah kenan, DAN ADAM babu mai iya masa sai Allahn da Ya halicceshi, Allah Ya datar da mu."
"Amin."

Tun daga wannan ranar Ummi ta riki Batul bisa amana, har makaranta an sanyata na Arabi. 
   Haka har azumi ya zo, nan ma komai tare sukeyi, cikin azumin ne kuma Intisar ta haihu diyarta mace. Kowa ya yi murna da hakan, ranar suna aka sanya sunan Hajiya Mama, wato Sadiya. Hajiya Mama ta ji dadin wannan karar da sukayi gareta. 
   Anci suna an kare lafiya kowa na yaba yanda Faruk ke nan nan da Ummi ko gaban mutane ne ba ya iya 6oye son da ya ke mata. 
  A ranar sunan ma ganin yanda Ummi ke yiwa Batul saida su Jidda suka tofa.
"Wai wannan inace 'yar aikinki ce ki ke mata haka?"
  Murmushi ta yi.
"Ni ina mata kallon mutum mai daraja."
"Don kema a baya yar aikin ce ko?"
Cewar Fadila.
Abin ya ta6a zuciyar Intisar da su Ikram, Ummi kuwa ko a jikinta ta soma bata amsa. 
  
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  126

"Ko bayan wannan, yan aiki mutane ne kamar kowa, hakazalika suma suna da nasu daraja da k'imar, da yawa cikinsu kan fito aiki bisa kaddara ba da son zukatansu ba, wasu anfi karfinsu ne wasu kuwa halin rayuwa ce. Ni Ummi bana fatan ranar da zata zo na wulakanta wani DAN ADAM a duniya, da yawa suna kuskure, sukan dauki kansu wasu har su dunga wulakanta masu tayasu hidima don kawai tak'amarsu biyansu su ke yi, sai yaronki karami ya budi baki ya zagi dattijuwar da ko ke ta haifa amman ba zaki kwa6eshi ba kasancewar kina mata kallon yar aikinki, sai ya zagi direba ko maigadinki duk ba za ki ji ko darr ba, asalima har ya kai ga kin shigarwa danki don kawai kina yi musu kallon kaskantu, watakil kuma sun fiki matsayi a wajen Allah. Ba ma akan masu aiki ba, kowaye kada ka wulakantashi don shakka babu bakasan mai yi maka rana ba, ko ya ya, bana mance halacci."
    Fadila da Jidda suka k'ulu da maganganun Ummi, musamman Jidda wacce ke ji kamar da ita ta ke, basu kadai ba har da wasu cikin gayyar sunan wadanda sun kasance suma sukan dauki yan aiki ba komai ba face kaskantu maganar Ummi ta shigesu, nan kuma wasu suka hau fadin ai yan aikin ma suna suka tara akwai mugaye. Ita kuwa Fadila bata kara cewa uffan ba don ta cika da mamakin yanda har Ummi ta yi kaurin wuyar mayarmata da martani.
  "Ku bar ganinta haka, yar aiki ce a baya shiyasa ta fiye wannan zakalkalewar, ai duk inda mutum wanda bai saba da arziki ba ya ke to fa sai kun gani ko a jikinsa ko furucinsa." Cewar Jidda a fusace.
Ummi ta dubeta, kamar ta ce wani abu sai kuma ta hadiye kawai tana murmushi.
"Kai don Allah Anti Jidda." Cewar Intisar kenan, Jidda ta watsamata mugun kallo.
"Na ambaci sunanki?"
  Ta rausaya kai.
"Ko ba don wani abu, ku yi duba fa da cewar cikin azumi ake..."
  "Please ya isheni, wani abin nace?" Jin haka Intisar ta ja bakinta kawai.
Wata hamshakiyar mace da ta hade cikin wani tsadadden leshi ta tofa.
"Kwarai Jidda suna haka, don wallahi wata yar aiki da kawata Mariya Sadik ta ta6a yi, ai kinsanta, yarinyar a dakin mijin ta kamata. Ai babu butulu kamar dan aiki saidai mata mu kiyaye."
Nan kuma babin ya koma hirar yan aiki, Ummi ganin abin nasu kamar da biyu ne, yasa ta mikewa ta bar dakin zuwa falo, Intisar da Baraka suka biyo bayanta har Ikram don abin ya 6ata ransu suma. Ta nunamusu ba komai ganin yanda suka damu. Ita kuwa damuwarsu akai ma kadai ta sanya komai gogewa a zuciyarta.

   Sai Magriba Faruk ya zo daukarta, anan ya sha ruwa da su Haidar hakanan suma nan ciki suka sha ruwa sannan  ya shigo ya ga bebi, anan ne Fadila da Jidda suka kai mishi k'arar Ummi akan ya ja mata kunne. Ya cigaba da danne wayarsa yana yiwa yarinya hoto, gefensa Haidar ne zaune sai Ridwan wanda shima bai jima da zuwa ba. 
  "Wai muna magana ka maidamu wasu shashashai." Cewar Jidda mai saurin fusata. 
"Wai meyafaru? Me Ummin ta yi muku?"
Cewar Dakta yana duban Jidda. Jidda ta yi kwafa. 
  "Mene idan ba rashin kunya ba har tana kiranmu masu raina mutane. Yaushe kan mage ya waye da har raini zai shiga tsakaninmu?"
  Faruk ya bar abinda ya ke ya dubi Jidda ransa a 6ace kamar ya yi magana saidai shigowar Ummi da Intisar falon Haidar ya katseshi, sanye ta ke cikin wani leshi bak'i mai adon orange flowers, sai mayafinta (orange) da ta yafa, hakanan jakarta da takalminta marar tudu. Idanunta akansa suka soma sauka. 
  Wani sassanyar murmushi suka sakarwa juna kafin ta karaso ciki ta gaida Angon karni da Dakta. 
   Faruk ya mik'awa Dakta bebin.
"Bari mu wuce."
  "Ai daman fuskar da ta samu wajenka ne yasa ta ke..."
  "Ya isa! Haba!" Cewar Ridwan ga Jidda wacce ke zak'alk'alewa. 
"A'a Dakta, babu batun ya isa fa, magana ta gaskiya."  Cewar Fadila tana taunar cingam da kallon banza. 
  "Ummi me ya hadaki da yan uwanki?" Cewar Dakta kenan, Faruk na tsaye hannuwa ciki aljihu kawai yana kallonsu. 
   Ta dan murmusa don ita bata ga abin daukar zafi ba.
"Ba abinda ya hadamu."
  "Karya ki ke yi uwar kissa." Cewar Fadila. 
  "Ya isa, Intisar me ya hadasu ne?" Cewar Dakta. 
Tiryan-tiryan ta fadi duk yanda aka yi, Faruk ransa ya yi mugun 6aci ya soma magana.
"Ku rike girmanku, ina girmamaku, kada ku janyo abinda zaisa nabar ganin girmanku. Duk wacce ta kara cin zarafin matata bazan lamunta ba, ko wacece cikinku komin girma da kimarta da nake gani zan yi watsi da shi wallahi!"
   Jidda da Fadila ba bakin magana, shiru sukayi sai faman harararsa sukeyi amma ba bakin magana, ko babu komai yana da kwarjini. 
  Haidar ya dubeshi.
"Ka yi hakuri mana. Gaskiya ba ku kyauta ba Maman Ma'aruf,  kune masu laifi ba Ummi ba, sai ku duba matsayinta a yanzu a Family namu, ku dunga sakaya bakinku."
  Shima Dakta cikin tsananin 6acin rai ya hau zazzagawa matarsa fad'a, Ummi dai ganin mijinta ya nufi hanyar fita, itama ta yi musu sallama ta bi bayansa. 
   A mota ta sameshi zaune yana jiranta, ta shiga gami da dubansa, idanunsa sun kada bai ko dubeta ba ya figi motar a guje, ganin Batul yasa ta yin shiru ba don taso ba, duk da haka saida ta mishi magana.
"Don Allah ka rage gudu."
Ta fada gami da dafa hannunsa dake rike da sitiyari. Ya lumshe idanu yana mai jin zafin abinda ya faru, ganin ta damu yasa shi sassauta gudu har dai suka isa gida, Batul ta yi shiru tana mai tausayawa uwar dakinta don kuwa ta ji kadan cikin abinda ya faru.
    Koda suka isa, dakinta ta nufa. Ta cire mayafi kenan ta isa gaban madubi da zummar cire dan kunne da sark'a ya shigo, ta dubeshi ta madubi suka hada ido.  Murmushi ta sakarmishi a kokarinta na 6oye damuwarta. Karasowa ya yi da sassarfa ya rungumeta ta baya yana sauke ajiyar zuciya idanunsa a runtse. 
  "I'm sorry." Ya fada a hankali, ta lumshe idanu, sai lokacin zuciyarta ta raunana, ta ji kamar ta zubar da hawaye saboda tsananin farinciki na samun miji kamar Faruk mai so da kaunarta. 
   Ta juyo ta dago fuskarsa gami da girgiza kai yayinda hawayen da ta danne suka shatato. 
   "Haba FAR HAS, don Allah ka daina  inajin wani iri wallahi."
Ta rungumeshi tana hawaye yayinda lokaci guda ta ke murmushi mai bayyana hakora na farinciki. 
  "Ko babu komai wannan kaunar da ka ke yimin ta zarce komai a wurina, ta isa wankemin dukkan wani 6acin rai dake zuciyata. Wallahi na yafemusu bazan kuma rikesu da hakan ba, DAN ADAM ajizi ne."
  Ya dago kanta yana murmushi gami da share mata fuska. 
"Shiyasa nake kara sonki Ummina, halayenki sunfi komai burgeni. Na damu ne don nasan koda ya miki ciwo ba za ki bari na fahimta ba, cin zarafi ne abinda suka yi gareki wanda wallahi Allah idan suka ce haka za su dunga yi gareki bazan lamunta ba, zan jure komai idan ni ka yiwa amman banda abinda ya shafi lamuranki. Kema kin sani ko?"
   Tun soma maganarsa ta zubamishi idanu tana murmushi gami da jin tamkar ta hadiyeshi don so, ya hure mata idanu hakan ya basu dariya.
"Eh mana naga kamar mai shirin hadiyeni, wannan kallo haka?"
Ta bugi kirjinsa tana kukan shagwa6a.
"Kai don Allah."
Ya ja karan hancinta yana dariya kafin ya taimakamata da abinda ta soma kokarin yi.
     
  Su Jidda daidai ga Hajiya saida ta nunamusu rashin dacewar abinda su ka yi, hakuri suka bawa Hajiyar kasancewa suna ganin girmanta ainun don bata kasance cikin surukai masu sanya idanu kan abinda ya shafi zamantakewar yaransu ba, ta kama girmanta hakanan bata daure musu fuska. 
   Bayan wucewar watan azumi aka gabatar da karamar sallah. Ko ranar da suka hadu da sallah a gidan Hajiya banda gaisuwa babu abinda ya hadasu duk kuwa da cewa basu bita da kallon banza ba. 
    Nan kuma ta soma shirin zuwa Kano halartar bikin Amina wanda dakyar Faruk ya aminta ganin tana fama da jikinta itama. Ko su Ikram sun zo zuwa saidai makaranta, itama Baraka na fama da ciki dan wata biyar babu damar zuwa. Da kansa ya kaita, kai tsaye gidan Mami ta soma zuwa inda zata yi kwanaki uku sannan ta wuce gidan Hajiya Mama har zuwa gama biki. Babu tarbar arziki daga Ihsan sai dai ta samu sosai daga Mami da sauran mutan gidan wanda yanzu suke zaman aminci. 
    Mami sai nan nan ta ke yi da ita, abin ya sanyata farinciki sosai. Ihsan kuwa kallo bata isheta ba, sai idan ita ta gaisheta ko ta yi mata magana sannan zata tankamata a dakile kamar bata so. Ga shi kuma daki daya suke kwana, wannan abin na bawa Ihsan haushi don dai ba yanda ta iya ne.
  Yau Ummi na kwance saman gadon Fahad wanda yanzun ya ke kwana dakin Adnan, tana tunanin yanda ita ke gyarashi a baya, lokacin sha dayan dare bata jima da gama waya da rabin ranta ba inda ya ke fadamata tsananin kewarta da ya yi. Ihsan ta shigo dakin daga falo, jin haka yasa ta yin makwas tamkar mai bacci. Itama duk a zatonta bacci ta ke yi, hakan yasa ta saka waya a handsfree tana amsawa.  Ita da Abubakar ne wanda rikici ne zalla.
  "Kasan ina sonka shiyasa, kuma kasan bazan iya rabuwa da kaunarka ba amma a yanda na ke jin labarin irin yanmatanka da tuni na yi watsi da lamuranka."
  Ummi ta yi shiru jin amsar Abubakar wanda ta ke mamakin inda ya bar matarsa a wannan lokaci.
"Ki kara hakuri da halina, ni nasan ina da son mata, ki yarda kawai wannan kaddar..."
"Kada ka karasa, wannan son zuciyarka ne. Daga waccan yarinyar ta sanka, sai waccan ta dora hotanka a dp dinta, na soma gajiya Abubakar, kishi na neman fasamin zuciyata."
Kawai sai ta sanya kuka, ya rude yana faman kiran sunanta da magiya kan ta yi hakuri, saidai ina, tuni ta katse kiran da ta ga bai bar kira ba, kawai sai ta kashe wayar gaba daya. 
Ta jima tana kuka kafin ta kwanta cike da tausayawa rayuwarta, yanzu idan suka yi auren haka zata dunga fama da shi? 
  Ummi ta ji babu dadi kwarai, tana ganin Abubakar kamar bazai aikata irin haka ba, ashe kusan jirgi daya ya kwasosu da Kb dan uwan su Faruk, koda bikinsu bata ganshi ba ta ji ance yana Ghana karo karatu. Ta tausayawa Ihsan ainun, ta dan juya ta dubi gadonta, ta bata baya saidai ta tabbatar bacci ya kwasheta, juyar da kanta ta yi gami da numfasawa.
'Rayuwa kenan, kowa da kalar jarabtar da Ubangiji zai mishi, Allah Yasa mu dace, amin.' Ta fadi a zuciyarta kafin ta yi adduoi ta kwanta itama.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
  
  127

Kwananta uku gidan Mami

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login