Showing 102001 words to 105000 words out of 158267 words

Chapter 35 - Dan Adam Book 1 Complete Hausa Novel

ji hayaniya saidai bata gask'ata ba hakan yasa ta zo ganewa idanunta. Wata budurwa ta gani sanye da tsadaddun kaya durkushe tana kuka sai mazan dake tsaye a wajen.
Malam Balarabe aka kamashi ya zauna gami da jingina da bango.
"Sannu Baba."
Cewar su Babban Yaya, bai amsa ba sai binsu da ya ke yi da kallo kafin ya sauke idanunsa akan Ummi, da sauri ya runtse ido ya soma salati. Duk sai ya basu mamaki, babu kamar Ummi, mamakinta bai wuce na ganin wai mahaifinta ke tsoranta ba.
"Wai Malam lafiya?"
Saude ta yi maganar cikin rawar murya tana mai fatan ace Malam Balarabe ya koresu daga gidan matsayin ya ga fatalwa matarsa.
Ya nuna Ummi.
"Wai Hasiya ce dai ta dawo? Daman ba ta mutu ba?"
Tambayar da ya yi ne yasa hankalin su ya dan kwanta banda na Saude da Habiba wacce jin hakan yasa ta sulale ta koma gidanta, bata yi wata-wata ba ta dauki mayafi sai gidan Bokanya har jikinta na rawa tsabar firgici.
Acan kuwa, Yaha ta amsawa Malam.
"Aa Malam, wannan Hasiyar Ummi ce diyarka diyar marigayiya."
Ya kurawa Ummi idanu kamar yau ya soma ganinta, Ummi! Ummi!! Shi kuwa ina ta shiga kwana biyu ba ya ganinta?
  ((Ku yi hakuri, rashin chaji ke sa ku ji ni shiruuu..))
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  92
        
  Saude tana shiga gidan Bokanya ta yi turus sakamakom ganin Habiba da ta yi zaune itama tana faman kuka. Habiba na ganin Saude ta mike da sauri ta nufi wajenta. 
  "Yanzu Mai Bori ta ke gayamin kin tafe daman, munyi sake Habiba, lamura sun yi 6acin da gyarasu sai Bokanya. (Wa'iyazubillah)"
Saude ta wuce zuwa gaban Bokanya ta zauna. Bokanya tana dubansu tun soma maganganinsu tana dariyar k'eta. Kafin Saude ta ce komai ta rigata.
  "An sakeki Saude, Balarabe ya miki saki biyu ko? Hahaha."
Ta kyalkyale da dariya, Habiba ta razana da jin wannan, ta zaro ido ta dubi Saude ta koma duban Bokanya.
"Kunyi kuskure babba! Kun kasa kiyaye dokokina, yanzu ku ka soma fuskantar kalubalen rayuwa! Babu wani abu da zan iya, lokacin afkuwar ABINDA AKE GUDU ya iso!"
  "Karya ki ke wallahi! Ke din banza, idan ba ki yi mana aikin ba kin dauka babu dubunki?" Cewar Saude kenan wacce sam ba cikin and hayyacinta ta ke ba. Ita kuwa Bokanya dariyar keta kawai ta ke yi babu kakkautawa.
  "Allah Ya isa tsakaninmu da ke, ashe bokancin naki ya k'are tunda ki ka kasa gyara abinda ki ka san zai 6aci."
Cewar Habiba itama cikin kuka. Sai lokacin Bokanya ta dan tsagaita dariyarta tana mai duban Habiba.
"Kun yi kuskuren zagina! Sakamakonku zai biyo baya! Ke Habiba! Ke ki ka kashe Hasiya! Tare da taimakon Saude! Diyarki tana can ta fad'a harkar madigo! Aurenta zai mutu! Sai na karya duk aikin da na yi mata! Sai kun koma abin tausayi. Asirinku sai ya tonu! Ku tashi ku bar nan azzalumai!!"
  Ta karashe fuska a daure, suka mike don ko damar bata hakuri basu samu ba, Bokanya ta karanto musu laifinsu wanda duk a zatonsu asirinsu ya rufu ruf babu ta inda zai fito don kuwa su biyun cewarsu sun aminta da juna. 
  Suna tafe ga duhun Magriba, Saude fadi ta ke.
"Allah Ya isa tsakanina da ke, duk kece ki ka soma kaini wajen bokanyar nan yau ga shi nan abinda ya afku. Ga shi yau aurena ya mutu."
Habiba da ke kuka da tunanin tashin hankalin da ke gabanta na mutuwar auren diyarta ta dubeta.
"Au, haka ma za ki ce?  Kin mance dadin da ki ka ji a baya ta sila ta shine yau da akayi miki ba dadi za ki zageni? Lallai DAN ADAM mai mance halacci, DAN ADAM butulu, ban ta6a kashe rai ba sai akan kishiyarki, shi ne tsabar son ki nunamin ke kina cikin masu mance halacci za ki ce na cutar da rayuwarki? Ai babu wacce aka cuta sama da ni."
  Wannan kalamin na Habiba ya tunzura Saude, nan suka hau cacar baki suna tafiya, wannan ta fad'a, wannan ma ta maida martani, karshe haka suka rabu baram-baram, Saude kai tsaye ta kama hanyar gidan kawunta wanda shi da banza duk daya ta daukesu, sai kuwa a yau din da ta ke neman agajinsu kan su rok'i mijinta akan ya maidata dakinta.
    Habiba hankalinta idan ya yi dubu to fa ya tashi, babu abinda yanzu ke damunta kamar batun diyarta Dija, yanzu idan auren ya mutu ta yi ya ya? Ta dauki waya da zummar kiranta saidai ko kusa batasan yanda ake sarrafa wayar ba, sau da yawa idan za ta yi kira saidai ta shiga makwafta budurwar gidan ta danna mata. Tana nan zaune duk tunaninta ya jagule, Malam Yahuza ya shigo gidan da sallamarsa saidai bata ko amsa ba.
"Habiba, lafiyarki kuwa ina sallama ba ki ko kalleni ba balle ki amsa?"
  Sai lokacin ta dubeshi gami da jan tsaki.
  "To menene kuma? Za ka cikani da hayaniya, mtsw."
Ta karashe gami da jan tsaki.
"Habiba ni ki ke yiwa tsaki kuma? Toh bazan dauki wannan rashin kunyar banzar ba, ki kiyaye!"
  Sakato ta yi tana duban mijinnata, yau Yahuza ne ya samu 'yancin d'aga murya sama da nata? Tabbas Bokanya dagaske ta soma karya dukkan ayyukan da ta yi musu, ta yi tsuru don tsoro ma ya bata, ya kammala komai ya dubeta.
"Ina abincina?"
A sanyaye ta amsa.
"Ai ba ka bada kudin cefane ba."
Ya yi kwafa kafin ya mike ya fice zuwa masallaci. Ta bishi da kallo kafin ta dora hannu a ka ta hau kuka.
"Oh ni Habiba wannan wace irin bak'ar rana ce gareni?"
Ta fad'a a fili babu mai amsa mata.
                 
  Ummi farincikinta ba ya misaltuwa a wannan rana, ta yi sallar Magriba anan tsakar gidan, saida aka yi sallar Isha'i sannan Malam Balarabe ya shigo rike da leda, da sauri ta mike ta kar6a suna duban juna da murmushi saman fuskar kowannensu. Kauna ta da da mahaifi shi ke yawo a jinin jikinsu. Tarr ya ke ganin diyartasa sakamakon wutar lantarki da suke da shi don a baya sosai suna samun wuta a kauyen, sai ayi kwana biyu ba'a dauke ba, koda kuwa an dauke, to fa babu jimawa za'a maido musu, yanzun kuwa da aka shiga yanayi an dan rage samu kamar da.
    "Sannu da zuwa Babana." Ta karashe cikin jin wani irin sanyin dadi a zuciyarta, yau ga ta ga mahaifinta kamar yanda ta ke yawan mafarkin ta gani har ya damu da ita ya sakarmata fuska. Kwalla ta cika idanunta sa'ilin da ta ke kokarin ajiye ledar ya dakatar da ita da fadin.
"Sannu 'yar Baba, dauko faranti a ciki nama ne da gurasa ku ci."
Ta bi umarninsa, ta kawo ta juye, ta dubeshi.
"Baba mu ci."
Yana murmushi lokacin da ya ke share hawayen da suka zubomishi ya soma ci shima. Mariya itama ci ta ke sosai don daman da yunwarta.
   Bayan sun kammala ta debomusu ruwan randa mai sanyi suka sha kafin su yi zaman hira. Malam Balarabe ya dubi Ummi.
"Kamanninki da mahaifiyarki har ya 6aci, tamkar an tsaga kara an karya, hatta sanyin muryarta."
Ya danyi shiru kafin ya numfasa.
"Allah Ya jik'anta."
"Amin." Ummi ta amsa jikinta a sanyaye tana dubansa kafin ta ce.
"Baba kana da hoton Ummana?"
Ya gyada kai yana murmushi.
"Bazan rasa ba saidai yanzu nasan yana cikin kaya, sai zuwa gobe zan dubo miki. Bani labarin zamanki a hannun bayin Allahn nan."
Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta soma labartamishi tun farkon zuwanta har kawowa yau da suka taho nemawa dansu aurenta.
   Malam Balarabe dake ta faman jinjina kai, wani abin ya yi murmushi ya ce"Allahu Akbar" wani abin kuwa ya yi hamdala idan ya ji. Bayan ya kammala ya dubeta.
"Babu abinda zanyi na biya mutanen nan da shi sai addu'a. Hakika sunyi abinda Allah baiyi ni zan miki shi ba. Babu abinda yafi faranta raina kamar sanyaki a makaranta da suka yi basu barki kin zauna da jahilci ba.  Haka kuma rayuwarki bata lalace ba, har kuma suka tako daga Abuja zuwa kauyenmu don kawai su nemawa dansu aurenki, tsakanina da su sai addua, Allah Yasa aljanna ce makomarsu, in sha Allahu ba ki da miji sama da Umar. Zuwa yanzu na dakatar da maganar don nafison ki soma sanin dangina da na mahaifiyarki, ayi aurenki kina cikin dangi. Itama Amina Allah Ya yi mata albarka, Ya bata mijin da zai rik'eta rik'on Amana."
"Amin Baba." Ummi ta amsa da murmushi mayalwaci saman fuskarta, ai ko don zagin da su Ihsan ke mata, zata so ta hadu da dangin iyayenta, ta ga gatanta. Sai kuma ta dubi mahaifinnata, lokacin Mariya ta soma bacci saman tabarmar.
"Baba inason jin tarihinku da Ummana, ku din 'yan ina ne?"
Malam Balarabe ya murmusa kafin ya ja baya ya jingina da bango ya soma magana.
"Yanzu za ki ji takaitaccen tarihinmu da Ummanki, sauran idan munje kya ganewa idanunki."
Suka yi murmushi tare kafin ya cigaba da magana....!




 
 
  
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

93
  ((Wannan shafin naku ne yan uwa sis Aisha Samarou & Maman Adil))
 
"Da ni da mahaifiyarki duk yan gari daya ne, wato Gombe. Saidai ita din  ta yi rayuwa ne a kauyen Jar Kwami dake Gombe. Da mahaifinta, Malam Manu(Usman) da kuma mahaifina Malam Buba(Abubakar) aminan juna ne wanda amintarsu ta samo asali tun kan iyayensu wanda tarihi ya nuna suma haka suka taso kansu a hade. 
   Malam Buba  bayan aure ya koma cikin birnin Gombe da zama Unguwar Tudun wada tare da mahaifiyata Fatima wacce muke kiranta Dada. Yaransu bakwai, uku sun rasu, ya yi saura daga  Haruna, Baffa(wanda ya ci sunan Usman baban Hasiya) sannan ni Abdullah wanda hasken fatata yasa suke kirana da Balarabe sannan kuma kanwarmu Aisha. 
    Gaba daya danginmu bamu da yawa sosai don bamu kai yawan dangin mahaifiyarki. Mahaifinta d'a ne ga Muhammadu Lamido, tsohon Sarkinmu na kauyen Jar Kwami, kafin ya mutu yana da mata har hudu banda uku da suka ta6a rabuwa duk kuma sun ajiye mishi yara, mata sunfi yawa cikin yaransa, bayan mutuwarsa aka dora wani kan karagar mulkin don alokacin yaransa maza su uku duk basu kai minzalin rike mulki ba. 
   Koda lokacin ya yi, babban yayansa ne kawai  ke shaawar mulkin sam kakanki Malam Manu(dansa na biyu) ba ya so.  
    Gaba daya a gidan sarautar su ke zaune, manyansu da yaransu. Sai kuwa matan da aure ke rabasu da gidan, wasu cikinsu ma auren gida ake musu da yaran yan uwa. 
   Duk cikin yaran Malam Manu, mahaifiyarki ce k'aramarsu, babban dansa namiji ne, Ado sai Bilkisu, Safiya, Asma'u sannan Mahaifiyarki Hasiya saidai Boddo suke kiranta, wato mai kyau. Don Masha Allah duk cikin yaran Malam Manu babu mai kyawunta.  Innarsu Aisha da suke kira da Inna tun bayan haihuwar Hasiya suka koma kiranta da Inna Boddo. 
     Tun farko anso yi mana auren zumunci da mahaifiyarki tun ma bata isa aure ba, amma fir na k'i sakamakon soyayyar da muke yi da Saude diya a wajen wata mai siyar da abinci a tsohuwar kasuwa inda nan nake zuwa siye da siyarwa. Asalinsu yan Kano ne can kauyen Ringim, saidai aure ne yasa Atine uwa ga Saude  baro garinsu zuwa nan Gomben, bayan rasuwar mijinta ne ta fad'a harkar siyarda abinci. Saude kadai ce diyarta, nakan yawaita zuwa shagonnasu daga shagon yayana dake zuwa Kano saro yadikan maza,  haka har muka saba da Saude kafin kuma soyayya mai karfi ta shiga tsakaninmu. Kullum kwanon abincina na rana anan ya ke. 
   Ranar da na zo wa mahaifinmu da maganar auren Saude, sam bai aminta ba don kuwa ya ce shi fa ba ni da mata sai Hasiya, lokacin idanuna sun rufe na ce bana sonta, nan duniya  Saude kadai ce abar sona. 
   Akan wannan saida ran Malam ya 6aci ainun, ya budemin wuta sosai. Har ya yanke shawarar zuwa Jar Kwami don ayi wacce zaayi, hankalina ya tashi, ina gani babu wanda ya goyi bayan na auri Saude. Karshe kuwa da ni aka je Jar Kwami, koda Malam ya gama magana akan aurena da Hasiya, Malam Manu ya aminta kuma ya ji dadi sosai, saidai ya bawa Mahaifina hakuri inda ya nunamishi har lokacin Hasiya bata kai munzalin aure ba saidai ko ta zo a ta biyu. Malam fir ya k'i amincewa, ya jajirce akan lallai a daura aurenmu da Hasiya. 
  Koda na sanarwa Saude halin da ake ciki, ta shiga tashin hankali matsananci ga shi a wannan lokacin mahaifiyarta na shirin zuwa ganin gida can Ringim.  Ana gobe za'a daura aurena da Hasiya na bi Saude da babarta zuwa Ringim don kuwa a wannan lokacin ji mu ke yi idan ba mu auri juna ba to fa za mu iya rasa ranmu. A hanyarmu muka yi hatsari mahaifiyar Saude ta rasa ranta, har suma saida Saude ta yi don tashin hankali, inda ma aka ci sa'a Sauden tasan garin tana zuwa. Da taimakon jamaar gari da kuma kwatancen Saude, Allah Ya yi isarmu gidan Kawunta Isah, anan aka yiwa mahaifiyarta jana'iza bayan nan Saude ta gabatar da ni matsayin wanda za'a auramata, ta sanarmusu wannan ne musabbabin zuwanmu garin. Koda aka nemi sanin tarihina, muka rufe komai muka nuna cewar ni din maraya ne, dangi kuwa sun sakoni gaba, babu mai kaunar ya ra6eni. Kawu Isah bai so aurennan ba don yana ganin kamar mun 6oye wani abu bayan wannan, saidai ganin yanda Saude ta tada hankali ga kuma maraicinta da ya duba hakanan itama bata samu wani sukuni daga dangin ubanta ba, ya amince ya daura aurenmu, gidannan da ki ke gani nawa ne, a farkon zuwanmu gidan Kawu Isah muka zauna har na tsawon shekaru biyu kafin na samu abin hannuna ta hanyar sana'o'i daban-daban na gina wannan gidan ginin k'asa. Wannan na sumuntin duk na yanzu ne. (Ya yi nuni da bangon gidan sannan ya dora). Tun zamanmu tsawon shekarun nan Yahuza mijin Habiba makwatanmu ne, yanda na saba da Yahuza haka Saude ta saba da unguwar zoma Habiba kusan ma da ya ke su mata ne shakuwarsu ta fi namu.
   Ashe su kuwa acan da na tafi sun daura aurena da Hasiya, saida watarana tunanin gida ya addabeni tashi guda na ji inason komawa Gombe. Zuwana na ji labarin rasuwar mahaifiyarmu da kuma auren kanwata Aisha. Na yi kuka kwarai, Malam kuwa ko kallon inda nake baiyi ba. Gwara ma yayyuna sun saurareni, Haruna da kansa ya bani shawarar zuwa ga Malam Manu don shi kadai ne zai iya shawomin kan mahaifina ya yafemin. Banyi kasa a gwuiwa ba washegari na wuce Jar Kwami. Malam Manu kusan ya yi murna kwarai da ganina, yanda ya kar6eni har kunya na ji don ban ta6a daukar an daura aurena da diyarsa Boddo ba. Ya bini doguwar nasiha, karshe washegari muka wuce cikin Gombe. 
Malam ya tabbatar ya hakura muddin zan ba shi takardar Hasiya, ashe ma tun bayan auren aka kawota gidanmu saboda gudun maganar mutan gari.
  Malam Manu kuwa ya ce bai isa ba, babu mai kunce aurennan, ni kaina ba zanso hakan ba. Dakyar da sidin goshi Malam ya hakura saidai ya ce nan zan zauna da Hasiya. Nan ma ansha artabu kan ya amince da tafiyarmu Ringim da ita. Saida na yi sati uku kafin na taho da Hasiya da yayyunta da wasu cikin dangi duk don a ga waje. 
  Ina cike da tsoron irin kallon da Saude za ta yiwa lamarin, saidai ga mamakina ta nuna ta fini farin ciki, har da durkusawa ta yi ta nemi gafarar yan uwana acewarta itama ta yi musu laifi na rabasu da ni. Wannan abu ya k'aramata k'ima a wajena, haka suma yan uwana suka cika da farinciki fad'i su ke, "Balarabe ka yi dacen mace ta gari." Har suna kwatantawa Hasiya da ta yi koyi da Saude. Ko bayan tafiyarsu na barwa Hasiya dakina, daman dakuna uku ne a baya, daya a zaure sai biyun nan kafin yanzu da aka yi ciki da falo.  
  Zaman lafiya suka gudanar, hakurin Hasiya da kyawawan dabi'unta su suka sanya ni cikin shaukin so da kaunarta ainun, abin Allah sai Ya doromin so da kaunarta fiye da irin wanda na yiwa Saude. Dakyar nake kokarin kwatanta adalci atsakaninsu. 
  Alokacin ne kuma Saude ta soma nunamin damuwarta kwarai akan rashin samun ciki. Kullum cikin yi mata nasiha nake, saidai takan yawaita tambayata kudi na zuwa wajen wata mai maganin gargajiya da aminiyarta Habiba ta bata labari na wai tana bada maganin samun ciki. Duk yanda na so fahimtar da ita cewar haihuwa lokaci gareshi, bata fahimta ba. 
   Haka har Hasiya ta samu ciki, kusan Saude ta fimu nuna murnarta, har kuma ta raineshi Saude har ayyuka ta ke kar6amata, magungunan gargajiya duk da tasan zai amfaneta takan kawo, haka itama Habiba ta kyautatawa Mahafiyarki, Allah kadai yasan zuciyoyinsu, ko tun wancan lokacin da gaske suke nunawa Hasiya kauna, ko kuwa dai da biyu su ke yi? Ba zan ce komai akai ba don bani da tabbas. 
  Cikin ikon Allah cikin Hasiya ya kai wata tara, tana haihuwarki kuma sai Allah Ya dauki ranta."
  
Malam Balarabe yana kaiwa nan ya dubi Ummi ya na mai haska wayarsa sakamakon wutar da tuni aka dauketa. Ummi hawaye ta ke yi don ita tasan duk ba don Allah suka yi ba, ta sha ji suna hirar, Allah ne kadai ya yi itama za'a haifeta don tun tana ciki aka so cikin ya zube, cewar Saude kenan duk sadda ta ke goranta mata da zaginta a baya.
  "Hasiya ki gafarceni, bansan dukkan abinda ya biyo baya ba bayan mutuwar mahaifiyarki, don lokacin gaba daya tsanarki ce ta dirar min, su kansu yan uwana sai suka fita hanyata haka kema daga dangin mahaifiyarki babu mai zuwa su ganki. Sun aminta da Saude fiye da zatonki, kamar yanda nima na aminta da ita ta yimin halin DAN ADAM na butulci."
Ya karashe yana mai share hawaye. Murmushi Ummi ta yi gami da kamo hannun mahaifinta....
  ((Inda gyara kofa a bude ta ke [email protected] ko fcbk.. Rufaida Omar))
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

    94

"Idan kana bani hakuri bana jin dadi wallahi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login