Showing 150001 words to 153000 words out of 158267 words

Chapter 51 - Dan Adam Book 1 Complete Hausa Novel

har ankon bikin Amina, Mami ce ta bada a dinkamata. Har ta cika kwanakinta babu wata jituwa tsakaninta da Ihsan duk da ita Ummin bata dauki gaba da ita ba don duk wayewar gari sai ta gaisheta matsayin yar uwarta musulma, a dakile Ihsan ke amsawa. 
  Saida Mami ta soma biyawa da ita wajensu Hajja suka gaisa, har Hajja ta matsa akan sai ta kwana, dole ta barta anan ta yi musu kwana daya daman acewar Mamin, ya dace ta kwanarmusu, a wannan kwanan saida Hajja ta kara neman afuwar Ummi don shakka babu ta ji kunya musamman jin cewa Ummin na dauke da juna biyu, tabbas idan Rabo Ya Rantse to duk kiyayyarka da auren sai an yishi. 
    Ummi ta ji dadi ta nunamata babu komai, sun sha hira kwarai har da dariya da su Modibbo wanda ke jikinsa ya matsa mishi a yan kwanakin, washegari ta wuce gidan Hajiya Mama.  
  Nan ma ta ga kulawa da tarba mai kyau daga iyalan Hajiya Mama har ita kanta. Su Maryam kamar su hadiyeta.
  Amina Amarya ta yi kyau ta gyaru tsaf, anan gidan zaayi yinin biki, kwarai Hajiya Mama ta yi musu kara. Acan gidan Innar Amina, yan uwan babansu ne na Nijar da na Innarsu anan Kano suka cika gidan. Amina ta sha mamaki jin cewa Malam Balarabe da kaninsa Baffa zasu zo daurin aurenta, ta hadata da Dada ta waya inda ta bata hakuri gami da nunamata ta so zuwa saidai bata samu dama ba, Amina ta nuna babu komai. 
    Da dare suna zaune a dakin su Maryam gaba daya suna hira da dariya, wayar Maryam ta yi k'ara, ta mike da sauri ta fita. 
  "Mene na gudun? Ai munsan mai kiran, Adnan ne."
   Cewar Rukayya cikin daga murya. Amina da Ummi suka dara. Amina ta cafe.
"Kai ke kuma ba'a sirri dake." 
  Dariya Rukayya ta yi.
"Ai naga sai wani 6oye-6oye sukeyi kamar bamusan komai ba, gwara mu nunamusu mun d'agosu."
  Ummi da mamaki ta ce. "Wai don Allah soyayya su ke yi?"
"Ba ki da labari? Gaskiya Amina kinci amanar kauna da ba ki fesamata ba, ai kullum suna mak'ale da juna ta waya duk da wani 6oye-6oyen da sukeyi munsan komai, daidai da Hajiya Mama ta sani."
  Ummi fara'arta ta karu.
"Kai na ji dadi wallahi, Yaya Adnan ya yi dace kam, Maryam ba ruwanta halayenta na burgeni. Sun dace wallahi."
"Karshe ma." Cewar Rukayya daidai lokacin da Maryam ta shigo ta mikawa Ummi wayar.
"Ga Yaya Adnan ku gaisa."
Ta kar6a tana tsuke baki. Ta yi sallama ya amsa gami da fadin.
"Allah Ya kiyayemana ke ranki ya dad'e."
   Ta hadiye dariyarta.
"Ai ni na yi fushi Yaya Adnan, ka daina nemana kuma ko na kira layinka yanzu ba ya shiga."
"Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun! Na ji kunya biyu. Na farko kirana da Yaya Adnan da ki ka yi, na biyun kuma, kiran da ban yi miki da sabon layina ba kasancewar wancan ya fad'i sai na barshi. Ki yi hakuri Ranki ya dade matar bestie."
  Sukayi dariya a tare, ta girgiza kai.
"Har abada, Yayana ne kai wallahi. To na hakura, ya fama da biro da takarda?"
  "Gashinan sai kuyita tayamu da addua. Kinga surukarki ko? Ta yi ko akwai gyara?"
Ta daga idanu ta dubi Maryam da su Rukayya ke tsokana ta yi dariya.
"Ta yi 100%."
Ya yi dariya cike da mamakin yanda tasan wani 100% domin ko kusa ba shi da labarin ana mata darussa. Saidai kuma bazai iya tambayarta ba.
   "Yauwa Ranki ya dade, ai da kince akwai matsala tuni zan dakata."
"Wace ni da fadin haka?"
Suka dara kafin su yi sallama.

  An soma bikin Amina lafiya, ana gobe daurin aure Malam Balarabe suka zo, sun sha hira da diyarsa har ya rasa inda zai sakata don tsabar farinciki. Ita ta yi musu jagora har wajen Inna don yi mata fatan alheri, wani abu ya darsu a zukatan tsoffin sadda suka yi arba da juna. Bayan an daura auren ne Malam Balarabe ya kasa jurewa har saida ya sanarwa Baffa kaninsa don daman ya samun labarin cewa yanzu Inna bata da aure, hakanan yana iya cewa tun bayan Hasiya babu wacce ya kara gani ya ji yana so ya karashe rayuwarsa da ita matsayin mata kamar Inna Bilkisu. Baffa ya ji dadi kwarai kuma zai so hakan. Abinka da batun manya nan suka tuntu6i babban Yayan Bilkisu, Mahmuda, nan ya nunamusu jin dadinsa a fili don kwarai ba ya son zaman kanwartasa haka babu aure duk da cewa ta aurar da yara biyu Fiddausi da Hauwa, sai Amina ta uku, ga kuma autanta Ahmad mai shekaru goma sha daya a yanzu, ya yi musu alk'awarin tuntu6ar Inna Bilkisu. A karshe sukayi musayar lambobin waya sannan a karshe sukayi sallama da kowa suka tafi, Ummi har hawaye ta yi don kewa, shi kuwa babanta dadin yanayin da ya ganta ya ji don ta yi k'iba ta kara kyau. 
   Inna ta ji lamarin banbarakwai duk kuwa da cewa a ganin farko da ta yiwa Malam Balarabe ya kwantamata, ba musu ta amince da hakan. Nan ya kira ya shaidamusu, basu yi wata wata ba suka sanarwa iyayensu, Malam ya ji dadi haka ma Dada wacce ke tausayawa dan nata. Aka tsaida magana nan da sati biyu za'a je a daura aure. 
  Su Anti Hauwa sun ji abin banbarakwai, wai Innarsu aure. Tun basu ji ko waye mijin ba suka nuna rashin goyon bayansu, acewarsu da shekarunta na arba'in da takwas me ya ragemata banda ibada? A bakin matar Kawunnasu suka ji waye manemin auren, hankalinsu ya kwanta suka ji dadi, kusan Amina ta fisu jin dadin lamarin don a take ta bugawa Ummi wacce ke shirin komawa Abuja.
    "Albishirinki." Ummi ta ware ido.
"Goro fari k'al Antina."
  "Inna zata zama matar Babanmu."
Cikin rashin fahimta ta ce.
"Anti inace kin cemin Baba ya rasu."
Ta ja tsaki.
"Dallah can, babanmu fa na Gombe."
Daskarewa ta yi a tsaye ta bar ninke kayan. Ita abin kamar mafarki haka ta jishi. 
"Ke ya ki ka yi shiru, wallahi dagaske ne." Tiryan-tiryan ta labartamata abinda ta ji. Hawaye kawai Ummi ta shiga fitarwa tana kara jin kaunar Amina da yan uwanta. Banda hamdala babu abinda ta dunga nanatawa a fili. 
   Bayan komawarta Abuja ta sanarwa Faruk wanda shima ya ji dadi ainun, ya sanyawa lamarin albarka. Kowa ya ji sai ya sanya albarka ciki. Koda ta kira mahaifinta, dariya kawai ya yi ya ce.
"Lamarin Allah kenan Hasiya, a tayamu addua."
Farinciki fal cikin ranta haka suka sha hira suka yi sallama.
                ***    ***    ***
        BAYAN WATANNI BIYAR
Ayau ake bikin yaye su Ikram daga sakandire, acan Kano ma su Ihsan na nasu shagalin don lokaci guda aka yi bikin yayesu. 
   Duk yayyun Ikram sun je mata banda Baraka dake wankan jego ta haifi danta namiji wanda ya ci sunan mahaifin Mijinta suke kiransa da Abulkhair. Ummi ma da cikinta dan wata bakwai katon gaske haka ta zo. Fuskarta duk ta chanja, tana sanye da wata tsadaddiyar abaya Faruk na rike da hannunta. 
    Ikram duk bata tare da walwala sai lek'e-lek'en wuya ta ke faman yi. 
"Wai me ki ke nema haka?" Cewar Fadila wacce ta kasa shiru. Ikram ta dubeta, kafin ta yi magana suka ji sallama a gefensu duk suka waiga, mamaki karara ya bayyana a fuskokinsu. 
  Yana sanye da doguwar riga da wando na shadda dark green wacce ta sha aiki, ya dora hula mai fari da koren din sak'a, ya yi kyau kuma ta haskakashi ainun. Sai murmushi ya ke faman dokawa.
  "Yaya Gidado?" Ummi ta furta da tsantsar mamaki kafin kuma ta saki fara'a sosai. 
Ya bita da murmushi kafin ya karasa ya soma mikawa Mazajen Hajiya Babba hannu suna gaisawa. Suma sun saki fuskokinsu, Fadila da Jidda suka yi turus suna kallon ikon Allah, sun kuwa gane waye shi amman idan ka ganshi saika rantse ba daga kauyen Jar Kwami ya fito ba tsabar iya daukar wanka. 
  Ikram ta kasa rufe baki, zuciyarta na kara nutsawa cikin kogin so da kaunarsa, babban abinda yasa ta ke kwadayi da mafarkin zuwan wannan ranar kenan don kuwa ya bata tabbacin zai zo mata da kyakkyawan albishir duk ranar da ta yi Candy. Toh yau ga ranar ta zo. 
    "Ashe kana tafe ba ka sanarmana ba mu yi maka kyakkawan tarba?"
  Cewar Faruk cikin sakin fuska. Gidado ya danyi dariya.
"A yi hakuri surukina, ai gani yanzu ma bata 6aci ba."
  "Lallai kam, saidai kamar zuwan ba namu bane na kanwarmu ne ko?." Cewar Haidar wanda ya riga yasan dawan garin daga Intisar., ya fada yana duban Ikram.
   Suka yi dariya, kunya ta kama Ikram.
"Eh to, kusan hakan."
  Cewar Gidado, shi kuwa babban Yaya da Ridwan mamaki sukayi don basu zata ba , hakanan Faruk shi kansa bai ji daga matarsa ba. Ya dan matse hannunta ta yi karamin kara. 
  "Shine ko ki gayamin?"
Ta waro ido.
"Babu wani abu fa tsakaninsu."
Murmushi kawai ya yi.
  Har aka tashi taron Gidado bai samu ke6ewa da Ikram ba sai bayan sun koma gida, bayan ya gaisa da su Hajiya suka ke6e da ita a dakin bak'i. 
Ya fiddo wani akwati daga aljihunsa ya mik'amata.
"Ga kyautar da na zo miki da ita, ki yi hakuri babu yawa.". Ta kar6a tana washe baki.
"A wajenka ne babu yawa."
Sukayi dariya. 
  "Ba za ki bini bashin zance ba Ikram, yau zan sanarmiki abinda ban ta6a sanarmiki ba. Haka kuma zan cika alkawarin da na daukar miki."
  Ta lumshe idanu ta budesu.
"Ina jinka Yayana."
  Shiru ya dan biyo baya kafin ya cigaba da magana.
"Karambanin so ke neman kaini inda aka fi karfina, duk iya kokarin da na yi na dannewa da kaucewa faruwar hakan, saidai ya gagara, bazan iya hana Allah zartar da hukuncinSa, ban isa ba ban kuma kai ba. Wallahi na kamu da sonki Ikram, so na gaskiya, a rayuwa ban ta6a zaton zan kara son wata diya nace ba bayan Hafsa, amma cikin ikon Allah da sannu-sannu kyawawan d'abi'unki da kuma hakurinki suka rinjayi zuciyata na afka cikin kogin son wacce ta fi karfin dan kauyen Jar Kwami."
  Ta kasa motsi, ta kasa gaskatawa, ta kuma kasa tantance hakikanin yanayin da zuciyarta ta fada. Kallonsa kawai ta ke tamkar wata doluwa. Ya kai yatsa kamar zai tsone idonnata ta yi saurin lumshewa, sai kuma ta yi kasa da kai tana murmushi. 
  "Wannan kallon fa ya tsoratani, ko ba'a sona?" Ya fada don jin ta bakinta kawai bawai don baisan cewar tana sonsa ba. 
   "Bance ba, saidai na yi mamaki ne kawai ace kamar ka kana sona?"
  "Kina neman ki ce kinfi karfina ko?"
Ya fada a raunane. Ta yi saurin girgiza kai kamar mai shirin kuka ta ce.
"Wallahi aa, ni don Allah ka daina bambanta kanka da ni, kaima cikakken DAN ADAM ne mai daraja, ina girmamaka hakanan ina sonka tsakani da Allah."
    Ya murmusa gami da sunkuyowa saitin fuskarta cikin muryar rada.
  "Za ki iya zaman aure da ni a Jar Kwami?"
   Ta lumshe idanu gabanta na bugu da sauri-sauri.
  "Yayana ba Jar Kwami ba, koda cikin daji ka ke rayuwa wallahi zan iya binka muyi zaman aure, ina sonka fa." Ta karashe kamar za ta yi kuka, ai kuwa hawayen da ta ke makalewa suka kwaranyo.
   "Komai na Allah ne." Ta tuna furucin Ummi gareta a watarana da ta je gidanta da korafin yanda ta ke kara jin son Gidado a ranta kamar ta mutu. 
   "Idan Allah Ya kaddaro mijinki ne, za ku yi aure." Fadin Intisar a watarana suna hira ta ke kokawa bisa yanda Gidado kan share kwanaki ba ya nemanta koda ta waya sai idan ta nemeshi.

  "Na gaji da jin maganar Gidadon nan, don Allah ki hakura ki fiddashi cikin ranki, idan mijinki ne fa sai kunyi aurennan ko ba ya so." Cewar Hajiya a wataran da ta risketa tana kukan yanda ya ke yawan yi mata hirar matarsa wanda batasani ba wani zubin da gayya ya ke yi don kawai ya gwada ko tana kishinsa.

  Ta share hawayenta. Gidado zaune ya cigaba da fayyacemata irin son da ya ke mata ya kuma tabbatarmata ba da wasa ya zo ba, sonta ya ke yi tsakaninsa da Allah. Koda ta yi mishi batun Hafsa, ya nunamata wannan ba matsala bace, matarsa nada saukin kai tana son abinda ya ke so. 
Ranar saida ta yi nafilfilu don nuna godiyarta ga Ubangiji. Daidai da Hajiya ta taya diyarta murna hakanan duk wani masoyinta da yasan tana son Gidado, ko Ihsan ma ta dan ji sanyi ganewar ba yar uwarta kadai ke wahala ba, ashe shima yana so. 
  "Allah Ya ba ki sa'a." Shine kawai abinda Jidda ta fadi. 
   Ita kuwa bata biyemusu ba don ta gane yan adawa ne. 
           
   Kamar wasa, aka tsayar da maganar auren Ikram da Gidado wanda takanas iyayensa suka zo Abuja nema mishi bayan an samu an shawo kan Hafsa dakyar wacce ta dage akan saita bar gidan Gidado ta ya ya zai hadata kishi da wayayyiya kamar Ikram? Acewarta wannan cutarwa ce, da dai ya auri Ikram gwara ya auromata yar kauyen Jar Kwami irinta sun zauna. 
   Wasu cikin yan uwa suka goyi bayanta wasu kuwa ba su goya ba, hakanan a cikin dangin Gen. Ahmad Danzaki, wasu da yawa basu amince ba, acewarsu Ikram ba zata iya rayuwa a kauye ba da kuma dan kauye, ita kuwa ta dage lallai sai Gidado, to Daddy shima ya goyamaya baya ko babu komai autarsa ce yana ji da ita. Haka aka tsaida auren Ikram da Gidado wata uku ba da son ran wasu ba. 
     Aka shiga shirye-shiryen bikin Abubakar da Ihsan, sai Iklima da Musaddik, mijin da Abba ya za6ar mata akayi sa'a sun hada kansu, da kuma kanwarsu Hassana da Abdullatif. 
   Biki ya yi biki, dukkan yan uwa sun iso Kano, ciki harda KB wanda ya zo hutu daga Ghana, gaba daya ya chanja ya zamo na kirki kamar ba shi ba. Ummi ce ta samu dakyar Faruk ya amince da zuwanta, acewarsa cikinta ya tsufa babu yawo....!
    Ansha shagalin biki su Abida da sauran yan uwan Gombe na Jar Kwami duk sun hallara. Sai nan nan Hajiya Salma ke yi da Ummi, hakanan duk motsi da zata yi sai an tambayi ko akwai wata matsala. 
   Tana zaune ta sanya kayan ankon Party a gaba tana kumbure-kumburen fuska, Ikram ta dubeta.
"Allah Sarki Antina, yanzu shikenan ba za ki je ba?"
  Dariya su ka sanya gaba daya wanda ya kara k'ular da ita. 
  "Tana gani zamu wuce amma ba inda za ta je tunda Oga ya hana."
Cewar Baraka kenan. 
"Ke banda abinki, kina fama da wannan katon ciki haihuwar yau ko gobe ina ke ina wani dinner party?"
  Ta yi narai-narai da fuska.
"Nasan da wanda zan hadashi ai, bari na kira Yayana."
Sukayi dariya, ta kira Abubakar.
"Innota ya akayi na ji muryarki na rawa?"
  Daman kiris ta ke jira kawai ta soma kuka. 
"Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun, me akayi? Kinga kina ina yanzu?"
"Dakin Ihsan."
"Ok ina zuwa."
Ya katse kiran Faruk dake zaune gefensa a benci ya dubeshi.
"Me ya samu Innontaka?"
"Bari na je na gani."
Ya bi bayansa da kallo kafin ya ta6e baki don yasan zancen bai wuce na party ba.
  DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

128

Suna daga dakin suka ji falon ya dauka ga Ango ga Ango, da mamaki Baraka ta ce.
"Eh lallai yar gatan yayanta, kiga har ya shigo."
   Ihsan wacce bata jima da shigowa dakin ba batasan me akeyi ba, sai ganin Abubakar ta yi ya shigo. Tana zaune saidai ban ma lura da ita ba ya yi wajen kanwarsa. Itama tana ganinsa ta kara turo baki tana murmurza idanuwa. 
  "Ya Salam, meyafaru ne wai kanwata? Hankalina ya tashi wallahi."
  Ganin yanda duk ya rude yasa ta dan sassauta fuskarta, fuska ba walwala ta ce.
  "Ba shine ya ce wai bazan je dinner party ba."
  Ya dan runtse ido gami da numfasawa, hankalinsa ya dan kwanta.
  "Inji wa? Ai ya zama dole ku je don kafarki kafata. Barni da shi, kedai ki tabbatar kin shirya kinji ko?"
  "Yanzu bayanta za ka goya? Da wannan tulelan cikin ina ita ina wata dinner?" Cewar Rahila yayar Ihsan.
  Ya dan harareta don sun saba wasa da dariya.
  "Ina ruwanki to? Zuwa kuma ai ta yishi ta gama, atoh."
  Dariya sukayi banda Ihsan da ta k'ulu ganin kamar baisan da ita wajen ba.
  "Idan kaine mijinta ma ji ma gani." Ta kara fadi cikin dariya. 
  "Shima a tafin hannuna ya ke, surukai muke."
  Daga haka ya fice suna mishi tsiya. Ihsan jikinta ya yi sanyi, wane irin Ango ne mai fifita wata akan matarsa? Haushi ya cika zuciyarta saidai dole ta danne ta mike bisa umarnin Aisha wacce ta shigo kiranta zuwa kwalliya don Magriba ta gabato kuma ana sallar Isha zaa wuce. 
    Ya murza karan hancinsa gami da dora kafa daya kan daya kamar wani basarake yana dubansa.
"Ka ce me?"
Abubakar ya harareshi.
"Na ce idan Inno ba zata je ba to fa nima babu inda zanje, kafarta k'afata."
Wani murmushi mai burgewa Faruk ya yi kafin ya dubeshi.
"Shikenan, ai ba kai kadai ne Angon ba, sai muje mu sha shagalinmu."
Dariya su Haidar da Kb su ka yi don duk gaba daya suna zaune a babban falon na bak'i. 
  Abubakar cikin dariyar ya amsa.
"Kafata kafarta fa Malam, ai ba yawo za ta yi ba, wuri daya zata zauna."
  Baki Faruk ya ta6e baice uffan ba, yana ji Abubakar ya dauki waya ya kira Ummi gami da kara jaddadamata cewa ta shirya zuwa babu fashi don ya amince. 
   Ya kalleshi kawai ya kauda kai kawai. 
    Haka har aka tashi tafiya, idan kaga Amarennan saika k'ara kallonsu tsabar haduwar da sukayi domin kuwa wani arnen leshi suka sanya fari da silver ya zauna das a jikinsu., su kuwa Angwayen farin shadda k'al mai surfani ruwan toka suka sanya. Saura kuwa suka yi ankon bulun french lace mai ratsin ruwan toka sai silver head, yayinda tawagar samarin suka hade cikin (Sky blue)shadda, sunyi kyau har sun gaji da haduwa. 
Kowa ya shirya tsaf harda Ummi, ita buba ta yi na zani sannan ta dora mayafi ruwan toka-toka, ta yi kyau duk da cewa ta ajiye kumatu ga chanjin fuska da jiki sakamakon ciki. 
   Aka soma fita itama ta fito, Mami ta kama ha6a.
"Harda ke Ummi?" Hakan yasa sauran iyayen suka dubeta. Ta yi murmushi.
"Eh Mami."
  "To ki bi a hankali banda tsalle-tsalle don Allah ki zauna wuri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login