Showing 75001 words to 78000 words out of 158267 words

Chapter 26 - Dan Adam Book 1 Complete Hausa Novel

wacce ya ke yiwa bata jin yaren ba.  Ta runtse ido don a zatonta ma duka zai kawomata.
  "Ka yi hakuri don Allah."
Ta yi maganar cikin muryar kuka, ya sauke hannunsa gami da yamutsa sumar kansa idanunsa a runtse, baya son jin kukanta ko kadan. A tausashe ya kara fadin.
   "Naji, gayamin wa ya mareki?"
Ina, ba fa zata fad'a ba, batason tashin hankali ya k'aru a gidan sanadiyyarta. 
   "Idan kana kaunar Allah da Manzonsa (S.a.w) abar maganar, ni ba wanda ya mareni ma."
Yanda ta ke maganar gwanin ban tausayi yasa shi saukowa.
"Shikenan tunda kin 6oyemin, share hawayen fuskarki."
  Ba musu ta sa hannu ta sharesu.
"Meyasa ba ki sanardani yau ake shirin tura ki Kano ba?"
  Ta sunkuyar da kanta, dagaske ba kaunar Kanon nan take ba don ta tsorata da kalaman Ihsan. 
"Kin dauka bazan sani ba? To babu inda za ki k'ara takawa da sunan aikatau in sha Allah, idan kinga kin bar nan to fa sai da niyyar tafiya gidanku."
Jin haka yasa ta dubansa, ya gyada mata kai.
"Dagaske."
Kawai sai ta tsinci kanta da murmusawa, ta tuna Ihsan da alwashin da ta ci akanta, kenan dai Allah Ya yi nufin ku6utar da ita?
  "Tunanin me kike? Kin ma karya kuwa?"
  Kai ta gyada. 
"To yanzu wannan ruwan da ki ke faman tsoma yatsunki ciki, zai iya sanyaki mura, kinga tashi mu shiga ciki. Bala!"
Ya juya ya soma kwalawa mai kula da shukoki kira, mintuna k'alilan sai ga Bala ya iso, ya russina a ladabce.
"Ranka ya dad'e."
"Matse ka shanya wadannan."
"To."
Ya dubi Ummi da wani kallo wanda ta kasa jurewa.
"Muje ko?"
Ta kauda kanta ta soma tafiya. Bala ya soma wanki yana binsu da kallo cike da tunane-tunane a ransa da kuma mamaki, to me ya had'a kashi da fura?
  "Ikon Allah." Ya fad'a a fili sannan ya cigaba da abinda ke gabansa.  
                    ***  ***  ***
                        KANO
  
   Ta kama baki cike da mamaki sadda ta ke fitowa daga d'aki sai kuma ta saki fuska tana 'yar dariya-dariya.
  "Ikon Allah, ashe dai yaronnan da gaske ya ke, to, halan dai yau 6atan kai kikayi?"
  Hajiya Mama ta ja guntun tsaki tana dariya alokacin da ta cire takalmanta ta k'arasa har falon Mami na biyu tana fadin.
"Jimin ke da wata magana? Sai kace wacce ta kwashi shekaru bata lek'o ba."
  "Aa, ba zancen shekaru, saidai idan ban manta ba rabon da ki zo gidannan tun kafin bikin Baraka, saidai fa a waya ko kuma idan na je."
  Ta dan dara.
"To naji marar mantuwa, ai gani yau na lek'o."
   Mami ta zauna tana dariya.
"Na ganki kam."
  Hajiya Mama ta bi Mami da kallo cikin shak'iyanci ta ce.
"To wannan k'ibar kuma fa? Anya Fahad bai kusa samun k'anwa ko k'ani ba?"
  "Um, haka fa shima Abbannasu ke fad'i, wai duk na chanja kodai juna biyu gareni."
  Hajiya Mama ta gyada kai.
"Da alamu dai wallahi, amman ki je asibiti ki ji tunda ba kiyi girman da za ki tantance ko kina da ciki ko babu ba."
Ta k'arashe tana 'yar harararta, sai ma ta bawa Mamin dariya, suka dara. Sun dan ta6a hira sai kuma Mamin ke sanarmata cewar yau Ihsan zata dawo tare da Ummi. Alokacin ne Hajiya Mama ta taso da maganar da ya kawota. 
  "Ke, ni wata magana ma na zo miki da shi, aikoni Hajiya Babba ta yi wajenki."
  Cikin rashin fahimta Mami ta ce.
"Toooh, meyafaru? Ba dai wani abun na rashin d'a'a Ihsan ta yi musu acan ba."
  Hajiya Mama ta ja tsaki tana mai kokarin cire mayafi.
  "Kinji wata maganar kuma, to idan hakanne ai bata wuce Hajiyar da kanta ta lallasata ba, wa zai tsaya wani kawo miki k'ara?"
  Murmushi Mamin ta yi, tasan hakanne don ko kusa Hajiya Babba bata fiye daukar raini ba ba dai kamar Hajiya Mamar, wacce ita sha yanzu magani yanzu ce duk kuwa da cewar tana da mutunci kwarai.
   "Abinda ya ke faruwa shine..." Ta kwashe bayanin cikin hikima ta gayamata. Mami tunda aka ambaci Ummi aka jogana da Faruk ta daure fuskarta tamau, duk da Hajiya Mama ta lura da hakan, bata fasa cigaba da bayaninta ba saima kauda fuska da ta yi daga dubanta har ta kawo karshe da fadin.
  "Kinsan dai Yaya Fatima awajenmu da kuma yanda muka dauketa, ba zata so abinda zai ta6amu ba, nikam ban ga wani aibu a yin haka ba, duk da kema nasan babu wani abu da..."
  "A ina? Bazai yiwu ba wallahi. Haba Hajiya Mama, ban ta6a zaton zakuyimin haka ba, da ace ba ciki daya muka fito ba zan iya kiran haka da 'YAN UBANCI! Abin kunya abin turr ace keda Hajiya Babba jinina, ku ne kuka amincewa Faruk had'a Ihsan kishi da 'YAR AIKI? Ko don Ihsan ba ku ku ka haifeta ba? Wannan wane irin magana ce haka kika zo da ita?"
  Maganar ta ke yi a matukar fusata, idanunta ya rufe akan makahon son da ta ke yiwa d'iyartata wacce ita ta kasance mace d'aya tilo awajenta, wacce ta ci burika akanta da kuma ranar aurenta, ta ya ya tashi guda zaayi tunanin had'ata kishi da wacce bata isa ba? Lallai acewarta wannan tsagwaron cin amana ne da yan uwanta sukayi gareta. 
   "Kina da hankali kuwa Madina? Yau ni Sadiya ki ke yiwa haka? Anya kina cikin hankalinki?"
  Ta dubi Hajiya Mama da idanunta wadanda suka cika da 6acin rai. 
  "Ina cikin hayyacina wallahi, amman tabbas idan magana ce ta gaskiya wannan rashin kyautawa ne, Hajiya Babba ta nuna kaunar nata a fili."
  "Wallahi Madina kin ban mamaki, ashe haka kike?!! Ashe son diyarki zai iya chanjaki bansani ba? Aure ba kaddara bace? To wallahi bar ganin ana lalla6aki, ba fa tsoronki mukeji ba don ba kece sama da mu ba, aurene kuma yanda Hajiya ta fada hakan zaayi idan Allah Yaso, idan kin isa saiki hana!"
   "Ayi, amman ba dai da diyata ba, har abada ba zata yi zaman kishi da Ummi ba, abu ne da Ihsan ba zata ta6a aminta ba, ni na haifeta kuma nasan halinta, bazata ta6a son haka ba. Idan dagaske kaddarar ne, meyasa bai fad'o kan diyarki ba..."
   Bata kai ga karasawa ba adalilin marin da ta dauketa da shi.
  "Bansan ba ki da kunya ba sai yau, kuma wallahil azim muddin ina raye idan Allah Ya kaddaro babu mahalukin da zai hana auran Ummi da Faruk. Kina nan kuma itama 'yar taki tana nan tana gani za'ayi, ta je kada ki barta ta yi kishi da 'yar aikin da kike ikrari, akwai mazajen 'ya'yan masu kudi da mulki, kina iya had'ata kishi da su. Sannan ina mai tabbatar miki Madina, akwai ranar k'in dillanci, sai kinyi dana sanin wannan abu da kikayi, sai kinji kunyar kanki Madina."
  Daga haka Hajiya Mama ta dauki jakarta da mayafi ta kama hanya tana zubda hawaye, a haka ta shuri takalmanta har tana had'a hanya.
 DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

   70
                  ABUJA 
   Misalin takwas na safe, Ummi ta kammala gyara sashen Hajiya duk jikinta a dar-dar, burinta ta yi ta kammala ta bar wajen kafin wani ya risk'eta, saidai cikin rashin sa'a tana murnar har ta kammala za ta tafi ba wanda ya fito, Ihsan ta fito falon tare da Ikram. Daman tun jiya suke dakonta. Tsayawa ta yi kyam tana kallonsu, fuskarta alamu na rashin gaskiya ya bayyana, ta numfasa dakyar tana mai hadiyar yawu, suka k'araso har inda ta ke, idanunsu k'arara ya nuna alamun 6acin rai, babu ma kamar Ihsan wacce bacci 6arawo ne kadai ya saceta shima cike da mafarke-mafarke. 
  "Ina kwana..."
Bata kai ga k'arasawa ba ta ji an dauketa da wani zazzafan mari, ta rik'e kuncinta lokaci guda kuma ta saki bokitin hannunta tana duban Ikram fuskarta cike da tsananin damuwa, tuni hawaye sun soma sauka a fuskarta. 
  "Kinyi kad'an a mareni saboda ke ba kasa tararki na rama wallahi! Ke din banza! Sa'arki daya ma jiya a gaban wadanda suke da daraja aka mareni, da tun jiya na huce. To saidai mu din an koyamana tsayawa iyakar matsayinmu bamu saba ketarewa ba, ke kuwa da alama ba ki samu wannan tarbiyyar ba tunda har ya kasance kinyi tsaurin idon kai kanki inda aka fi karfinki. Banza mai kwadayi."
   Ikram ce ke wadannan kalaman tana mai jifanta da wani banzan kallo, ba ta ce uffan ba, ta sa hannu zata dauki bokitin Ihsan ta buge hannun da k'afarta.
  "Aiki kuma a gidannan ya k'are miki, sannan ki sa a ranki muddin yau muka isa Kano zamanki a gidanmu ya k'are, sai naga ta inda zaki auri Yaya Faruk din. Banza kawai!"
  Ummi da ta kasa dagowa daga durkushen da ta yi, ta runtse idonta cikin jin zafin wannan abu.
  "Meke faruwa ne?"
Suka tsinci muryar Hajiya, da sauri suka nutsu kamar ba su ba.
  "Bakomai Hajiya, k'arewa Matar Yaya kallo mukeyi."
Cewar Ikram tana dariya ta raini. Hajiya ta daure fuska.
  "Ku bar wajen nan tun ban sa6amuku ba."
Suka juya suna gunguni suka koma daki. Hajiya ta zauna saman kujera ta yi shiru tana kallon Ummi dake faman goge ruwan da suka zubar suka 6ata mata guganta, tana yi tana hawaye. Murya na rawa ta gaida Hajiya, Hajiya ta amsa mata.  Saida ta kammala sannan ta mik'e da zummar barin wajen, ta dakatar da ita ta hanyar kiranta, jin yanda Hajiya ta kira sunanta da sanyin murya, yasa ta dan ji sauki na rad'ad'i da kuma fargabar da ta cikata. Ta amsa a ladabce tana mai zama a gefe kanta a k'asa.
    "Kiyi hakuri Ummi, nasan daman tunda Sadauki ya 6ullo da maganar aurenki, dole irin haka ta faru koma fiye da hakan kafin a samu fahimtar juna. Ni ban ta6a k'in ki a zuciyata ba, haka kuma ina miki kallon mutum kamar kowa mai nata darajar ta daban. Ko yanzu hakurinki yasa kin k'ara samun wani gurbi a zuciyata. Ki sani, ni mai son abinda Sadaukina ke so ne matukar ba abin assha bane don haka kema na yarda da lamarinki da shi. Kar kice kuma zakiyi amfani da wannan damar ki cutar da d'ana, bazan ta6a lamunta ba. Idan kin d'ore a yanda kike yanzun to fa zamu shirya da ke. Sannan Ihsan..."
  Sallamar Gogan ya katse Hajiya daga maganarta, suka amsa suna dubansa. Idanunsa shima a kansu da mamaki, musamman ma na ganin yanda abar kaunarsa ke fidda ruwan hawaye saidai bayason cewa wani abu don gaban Hajiya ne, fatansa dai kada Hajiya ce ta sanyata kuka. 
  Ya karaso cikin shigar kananun kaya wanda ya nuna shaidar ya yi wanka, ya zauna gefen Hajiya yana mai gaisheta, ta amsa fuskarta a dan sake ba kamar jiya ba da ta daure mishi, hakan ya dan sanyamishi nutsuwa. Ummi ta gaisheshi batare da ta dubeshi ba, ya amsa yana bin fuskarta da kallo, yana son ya tambayi dalilin kukanta saidai babu dama. 
   "Je ki sai na nemeki, kin shirya kayanki?"
Ta gyada kai, Faruk ya yamutsa fuska yana duban Hajiyarsa cikin rashin fahimta, bayan fitar Ummi dauke da bokiti da tsummokarai, ya dubi Hajiya.
  "Ina zata?"
  "Kano zata koma mana, ko ka manta daga can ta fito?"
Ya daure fuska yana mai kauda kai.
"Idan har a matsayin yar aiki zata je don Allah ayi hakuri Hajiya."
Ya karashe fuskarsa cike da damuwa kwarai. Ta yi shiru tana dubansa, ta gama karantar ba karamin so ya ke yiwa Ummi ba, tasan halin d'anta, wannan magana har cikin zuciyarsa ya ke yinta.
   "To yanzu Sadauki za'ayita rike musu ita ne? Karka manta fa kawota akayi Kano aikatau asalinta ba ma'yar garin bace."
  Ya lumshe ido kafin ya bude.
"'Yar Ringim ce. Kuyi hakuri har ta cika watanta, idan wacce ta kawota ta zo Kanon, sai aje har Ummin ayiwa mahaifinta bayani don Allah Hajiya. Amma yanzu ba girma kuma ta cigaba da aikatau, a duba wannan lamarin Hajiyata."
  Hajiya ta gyada kai cike da gamsuwa.
"Shikenan, na ji zanyi tunani."
Bayan fitarsa daga falon ta rasa ma abin yi, mikewa ta yi ta nufi dakinta. Karshe dai ta yanke hukuncin kiran kanwarta Hajiya Mama, don ita har nauyin Hajiya Madina ta ke d'an ji a yanzu.
  Hajiya Mama ta dauka, bayan sun gaisa ta ce. "Sadiya kina jina?"
"Ina jinki Hajiya."
Ta koramata dukkan yanda ake ciki tun daga jiya da Faruk ya zo musu da maganar Ummi har zuwa yanzun da ya ce shi bayason komawarta aikatau Kano. Ta k'ara da fad'in.
"Ki ban shawara Sadiya, kwakwalwata ta cushe, na rasa abinda zanyi, ina kuma jin tsoron Madina ta ji maganarnan daga bakin 'yarta."
  Hajiya Mama da ta sandare don mamakin wannan al'mari ta numfasa.
"Allah Mai Iko, wannan shine ana zaton wuta a makera. Karki damu Hajiya, ni banga aibu a aurensa da Ummi ba matukar zai had'a har ita Ihsan din kamar yanda ku ka ce, don bazamu so wannan abu ya kawo matsala a zuri'armu ba. Amma don Allah kamar yanda Genaral ya ce, ku daure kuyi bincike sosai akan Asalin yarinyar nan, Ummi dai a halayya bata da aibu daidai gwargwado yarinyar akwai hakuri da sanin yakamata sannan har gwaje-gwaje ayi ko don gujewa wani abu da zai je ya dawo. Ki kwantar da hankalinki, daman yau zanje saloon, zan fasa idan yaso na sanarwa Alhaji na je gidan Madinan. Allah Ya za6a abinda yafi alheri."
   Cike da jin dadin kalamanta Hajiya Babba ta ce.
  "Kai da kuwa kinyimin babban taimako wallahi, nagode sosai."
  "Haba Hajiya, kina gaba da ni ai kin wuce haka, na tabbatar Madina ba zata kawo matsala ba in sha Allah."
  Ta jinjina kai.
"Ina fatan hakan."
A karshe sukayi sallama da zummar duk yanda akayi zata sanarmata.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

73

Ko wanka baiyi ba, hankalinsa na ga abar kaunartasa. Zai so jin amsar da zata bawa Binta. Hakan yasa shi yin cak yana mai zubamata ido don sun ba shi baya. 
      Ummi ta yi murmushi wanda har gefen  kumatunta ya lotsa. Batasan sadda ta soma magana ba.
   "Ni nasan yanda nake jin Yaya Faruk a raina Binta, akwai da yawa daga abubuwa wanda ba sai ka 6ata lokaci wajen bayyanashi ba, watakil ya nuna kansa wataran. Ina son Yaya Faruk fiye da kaina, zan iya sadaukar da nawa farincikin don kawai ya samu nasa. Binta me zance ga mutumin da ya daraja ni ya nunawa duniya ni din mutum ce mai daraja? Ke kuwa idan ban kaunaceshi ba me zan mishi?"
  Binta ta yi dariya.
"Tabbas kinyi gaskiya, kin kuma burgeni matuk'a. Allah Yasa wannan kauna taku ta d'ore har ku haayyafa ku tara zuri'a guda taku."
  Kunya ta hanata amsawa face murmushi da tayi.
  "Ameen." Jin muryarsa yasa duk suka juyo a razane, ta zaro ido duk ta bi ta diririce, shikenan ya ji abinda ta ce kenan? Ji ta yi kamar ta nutse a k'asa don kunya. Ita kuwa Binta tana yar dariya ta russuna ta gaisheshi, ya amsa fuska a sake yana duban Ummi. Ita dinma gaisheshi ta yi dakyar sakamakon harshenta da ta ji ya yi nauyi duk don tsabar kunya.
  Ya amsa yana ji kamar ya nufeta ya rukunkume don dadin da kalamanta sukayi masa.
     "Zo nan Ummi."
Ya fad'a gami da juyawa ya fita. Ta bi bayanshi da kallo, daga shi sai dogon wando da singilet bak'a. 
   Ta dubi Binta wacce ke zungurar kafadarta tana mata nuni da ta je. Ta yi murmushi mai bayyana hak'ora cikin muryar rad'a ta ce.
"Anya bai ji maganarmu ba?"
"Lallai ke dinnan, to meye idan ya ji? Daman kinason fadamishi kin kasa kinga ya hutar da ke."
Ta girgiza kai gami da wanke hannunta da handwash sannan ta mara mishi baya. 
  A tsaye ta tarar da shi wajen hanyar da zata sada ka da sashensa. Ya kura mata ido kamar ya hadiyeta. Ta kauda fuskarta ta karasa gareshi.
"Meyasa kike barin wayarki a daki sai nayita kira bakya d'agawa?'
Yana maganar cikin muryar shagwa6a kamar wani k'aramin yaro, abin ma sai ya bata dariya, idan yana wannan shagwa6ar wani kyau ya ke yi mata, ita dake mace ma bazata iya yinta ba.
  "Ka yi hakuri, aiki ne mukeyi."
"Naji, maimaita abinda kika fad'awa Binta yanzu a kicin."
Ta zaro ido tana kallonsa fuskarta dauke da murmushi, shima murmushin ya yi ya daga mata gira.
"Kinyi zaton ban ji ba ko? Na ji dukkab tattaunawarku, oya idan dagaske ki ke maganarki ki cemin 'Ina sonka Faruk' na ji."
'Innalillahi...' Ta karantota har karshe a ranta, gaba daya ta diririce. Shi kuwa dagaske ya ke, don tsayuwarsa ya gyara yana jiranta.
"Kinyi shiru."
Ta hau wasa da yatsunta, murya a raunane ta ce.
"Ni..ni ban ta6a fad'a ba fa."
"Shiyasa nakeso ki fad'amin, ya zama ni ne farko nine kuma karshen wanda za ki fad'awa hakan ok?"
  Ta runtse ido, yau ta shiga uku, ji ta ke yi kalaman sun yi mata nauyi da tsauri, bazata iya fad'a ba. Ya dan saka saman yatsansa manuniya ya zunguri hannunta.
  "Kin yi shiru Ummina."
Ta ja baya kadan ta hadiyi miyau. 
"Ka yi hakuri don Allah."
Ya lura a tsorace ta ke ma, sai kawai ya yi murmushi.
"Ki ka ce ba ki da abinda za ki biyani? Ke kuwa ki ke da shi, kawo kunnenki ki ji."
  Bata motsa ba, tuni shi kuwa ya matso da bakinsa dab da kunnenta. Maganar da ya fad'i ce ta rud'ar da ita, da gudu ta juya ta koma kicin. Ya bita da kallo yana dariya kafin ya juya ya soma tafiya. Wayarsa ta dauki k'ara, ganin Haidar ne yasa shi dauka da sallama. Bayan sun gaisa Haidar ya ce. 
"Ya Man, na ji ka shiru, ka kuwa fad'awa su Daddy?"
  Faruk yana taka matattakala yana murmushi ya shafi sumar kansa. Kafin ya soma kora mishi duk yanda akayi harma da rikicinsu da Dakta Ridwan da kuma cewar Hajiya na sai ya auri Ihsan ma.
   "I just don't know what to do brother, ban ta6a son Ihsan ba, ban kuma ta6a yi mata kallon budurwa ba, ina mata kallon kanwata wacce ban bambanta ta da Baraka da Ikram ba."
   Haidar wanda ya yi shiru ya soma magana.
"Duk wannan bai dameni ba, kamar yanda ku ka samu sa6ani da dan uwanka ba Faruk, zan so ka je ka sameshi har gida ku fahimci juna. Banason akan lamarin aurenka a samu rarrabuwar kai a family, it's something that never happen, so please don't let it now."
  Ya gamsu matuka da zancen yayannasa. Daman shima ya sauko daga fushin da ya yi da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login