Showing 123001 words to 126000 words out of 158267 words

Chapter 42 - Dan Adam Book 1 Complete Hausa Novel

ma Yayanmu ne ya kawoki?"
Tsaki ta ja wanda batasan sadda ya fita ba, ta giftasu ta wuce, suka bita da kallo kawai. 
Husna ta lura kamar tana cikin damuwa, ta bi bayanta har kusa da kujerarta ta zauna gami da dafata.
"Lafiya kuwa Hasiya?"
Kamar jira ta ke yi kawai sai ta soma kuka, Husna ta rike kafadarta, ta duba ta ga ana kallonsu.
"Ki yi hakurin danne damuwarki, kinga idanuwa duk a kanki fa."
Jin haka yasa ta share idanunnata, ta daure ta nutsu, ayau ta ji kewar Antinta Amina kwarai, saidai itama Husna ta yarda da ita, tana da hankali, watakil ta samu shawarar da zata iya bata. .....
  DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

107

Saida aka tashi ne suka samu damar ke6ewa. Anan Husna ta yi shiru tana kallon Ummi, ganin haka yasa Ummi soma magana.
  "Wata shawara nake nema agareki."
Husna ta gyada kai cike da k'osawa don sau wajen biyar kenan tana furta hakan amman ta kasa magana. 
"Ina jinki."
  Dakyar ta samu ta labarta mata kadan cikin labarinta wasu abubuwan kuwa ta sakayasu, ta nuna mata kawai dai tana fuskantar matsala yanzu da saurayinnata da aka daura aurensu aka bar biki daga baya. Ta karanto mata matsalar a sakaye sannan ta k'ara da fadin.
  "Husna kin ganni ko? Ban budi ido naga mahaifiyata ba, sannan ban samu wata kulawa daga kishiyarta ba, har zuwa yanzu da aka zo batun aurennan, sannan ni duka-duka ma a Islamiyyar Kano da na ke fadamiki ban jima ina zuwa ba, wani sa'in idan wata fita ta zo shikenan bana zuwa.  Ina cikin tsaka mai wuya Husna, ina 6atawa mijin aurena rai, ki taimakamin da iya abinda ki ka sani, yarda dake ne yasa na sanarmiki abinda ban ta6a fadawa kowa ba a makarantar nan."
Husna wacce ta cika da mamakin wai Hasiya yanzu matar aure ce, ta numfasa bayan kalamanta na karshe wanda yasa ta jin tausayinta.Murmushi ta sakarmata.
"Ki sha kuruminki k'awata, in sha Allah daga gobe zamu soma. Saidai abinda nakeson ki sanyawa ranki, shi fa mijinnan wajibi ne gareki ki bishi sau da k'afa, karki bari damarki ta wuce, idan ance biyayya ciki har da ba shi hakkinsa na aure idan ya nema tunda dai ansan da igiyarsa akanki, wannan zamanin ba'a sakaci Hasiya,  mata da yawa neman mai aurensu su ke yi, wasu kuwa kamar su jawo namijin ya kwanta da su su ke ji, ballantana kuma idan mijinki wani hadadden ne, tuni za ki yi sake. A baya ne za ki ji duk iyayenmu na irin wannan kunya-kunyar, ansan tana da kyau saidai bisa shawara ki rageta, ki rungumi mijinki hannu bibbiyu. Karki damu, yanzu kinga dai anzo daukata, bari zuwa gobe zan taho miki da wani littafi SIRRINMU na wata tsohuwar marubuciya sai kuma wani  Sinadarin Rayuwa shima marubuciyar ta yi kokari matuka wajen koyawa mata salon kula da miji da gida, zan kuma k'ara miki a kai. Duk fa litattafan Antina ne matar Yayana da nake hannunta, zan rufa miki sirrinki Hasiya koda baki nemi hakan ba."
Ummi ta dan ji sanyi, ta yi mata godiya sannan suka zagayo farfajiyar makarantar, anan suka yi kici6us da Fati. 
"Yauwa, anzo daukarki fa tun dazu Anti Hasiya."
Ummi na jin haka ta daure fuska.
"Nikam karki kara kirana Anti banaso wallahi."
Fati ta rike ha6a.
"Ah, ai sai na kiraki da fin haka, kin kai wallahi. Sai ma idan kin hadani da yayannaki."
Dariya Husna ke yi ita kuwa Ummi tsaki ta ja kafin a fusace kuma ta bar wajen. Ganin haka Husna ta sha jinin jikinta, ta biyota da sauri gami da dafe kafadarta.
  "Wai Hasiya kodai shine mijinnaki?"
Ummi ta juya, ganin Fati bata biyosu ba sai ma dagomata hannu da ta yi alamun (bye-bye) ta juyo ga Husna, kai kawai ta gyada mata a sanyaye.
"Innalillahi! Kai Hasiya wallahi ban ta6a ganin irinki ba, kina da kamar wannan me zai hanani zage damtse wajen ba shi kulawa ta musamman? Kodayake..."
Sai kuma ta yi shiru don ta tuna kalaman Hasiyar a dazu ta kuma fahimci cewa ko karatun litattafai ba ta yi, ita kuwa har na yanar gizo yi ta ke yi, tana kuma cin karo da abubuwan karuwa na Matan Aure, wasu kuma idan sunfi karfinta bata karantawa kasancewar yayanta kusan kullum sai ya bincika wayarta yasa ta ke takatsantsan. 
    Ummi babu abinda ta ce saima haushin kanta da ta k'ara ji, lallai kam ta yi babban kuskure a rayuwarta. 
  Suka rabu Ummi ta nufi motar, direban gidansu Haidar ne, Ikram na zaune ciki sai faman cika ta ke yi da batsewa. 
Ummi ta shigo sannan ta gaida Direban, ta kara da fadin.
"Ku yi hakuri don Allah, bansan ya zo ba."
   Tsaki kawai Ikram ta ja sai direban ke amsawa da babu komai.
  Earpiece Ikram ta sanya a kunnenta tana jin wak'a , ita kuwa sai ta maida hankalinta ga kallon hanya cike da tunanin maganganun Husna, kwarai ta yi ganganci, tasan har da hudubar su Anti Abida da Halima ya taimaka wajen k'in sakarwa Faruk. Wanda sam bai cancanci haka ba, sai ta ji tana zuci-zucin gobe ta yi ko don Husna ta damk'a mata litattafan.
Har suka isa ba wanda ya cewa wani uffan, koda suka shiga kai tsaye sama kowannensu ya nufa. Nan suka iske daga Babban Yaya sai ko Faruk da Hajiya sai su Jidda kowanne na kawo raayinsa, lefe Babban Yaya da Hajiya ne zasu hada, na Faruk bai wuce kawai gani ba, kudin ma sunce ya barshi, sai batun dinner party da suke yi da kuma fiddo anko wanda Babban Yaya ya ce su fadi irin wanda zasu yi zai kawo musu su za6a. Duk wannan za su yi shi ne a cikin sati biyu, saboda zuwa Adamawa da zasu yi su kwana uku su dawo don Modibbo ya matsa akan lallai sai an tafi saboda wadanda tsoffinsu basu sani ba. 
    Shigowar su Ikram dinne ya katse su, Faruk idanunsa akan Ummi ya kasa daukesu, haka kawai ya ke jin kewarta ainun, wannan karon fuskarsa a dan sake,  suka gaishesu sannan Ummi ta yi ciki ta bar Ikram anan, itama tana jin batun da akeyi ta mike zuwa nata dakin inda ciki ta riski Intisar kwance saman darduma ta idar da sallah. 
   Wajejan biyar na yamma, Haidar da Ridwan wadanda suka je daukar yara daga makaranta suka shigo ciki, don daman direban suka hutar da sanyashi dauko su Ummi kawai. Nan gidan ya k'are kacamewa, Ummi duk ta takura har saida suka wuce, koda aka kirata cin abinci ta ce ta ci, akan haka har fad'a Hajiya ta yi mata  gami da nunamata kada ta sake irin hakan ta dunga ci tare da su. Daddy yana dawowa daga Kano inda ya je ta'aziyya matasan suka koma wajensa har Hajiya, nan ya ke jin dukkan shirye-shiryensu, ya yi na'am da hakan, ya kuma ji dadin yanda kansu ke a hade har kowanne ya dauki nauyin abinda zai yi. Haidar na buga I.v da rabo ya dauka, shi kuwa Ridwan na dinner party, yayinda Babban Yaya da Hajiya zasu yi lefe, karshe Daddy ya dauki alkawarin yiwa Ummi kayan daki da komai na mata, acewarsa ko don zaman da ta yi da su ta cancanta, bai dace su bar iyayenta da nauyi ba, ta zama tamkar jininsu. Faruk ya ji dadi matuka, bakinsa ya kasa rufuwa, bawai don wani abin ba sai don ganin kowannensu ke nuna kaunarsa da wannan auren, hakazalika hadin kansu ya fi komai faranta ransa, fatansa har mutuwa su kasance tare haka. 
      Washegari sam basu hadu da Ummi ba, sai ta waya ta kirashi, wannan karon bai gwanyata ba don ya amsa, ta gaisheshi ya amsa ba kamar jiya ba, a karshe ta rasa abin cewa kawai ta yi mishi adduar sa'a sannan suka yi sallama. Daga lokacin kullum sai ta gyara mishi daki tas. 
    Koda ta je makaranta Husna ta damk'a mata litattafan, shikenan kuwa ta samu abin karatu, koyaushe cikin karatu ta ke yi har ta soma gano kuskurenta kwarai, har sai gashi tun tana kunyar wanke mishi undies har ta gwada yi na rana daya sai ta kasa shanyawa kawai ta matsar da labulen dake wajen kwamin wanka ta shanyasu a karfensa. 
  Ranar Alhamis ta yi wannan aikin, yana dawowa ya ganewa idanunsa, ido ya fiddo yana kallo da mamaki, sun wanku tas, saidai anya Umminsa ce za ta yi? Ya kasa gaskatawa har ya gama wanka ya shirya cikin doguwar jallabiya fara ya nufo cikin gidan. 
    Hajiya na sashen mijinta, Ikram kuwa wacce ta dawo kenan, tana dakinta tana aikin makaranta. Wannan ya ba shi damar shigewa dakin Ummin. Sallamarsa ce ta sanya ta mikewa zaune da sauri gami da tura littafin kasan filo ta riko wayarta kamar ita take dannawa, ya dubeta sannan ya dubi hannunnata, ta yi kasa da kanta.
'Ya Allah, Ka bani ikon dauriya ga dukkan abinda Yaya Faruk zai zo min da shi.' Ta yi furucin a zuciyarta, a fili kuwa dan zamowa ta yi gami da mishi barka da zuwa, ya amsa sannan ya zauna gefenta, hannu yasa ya kar6i wayarta, ya gama bincikensa har open apps ya duba saidai ba abinda ta bude, ya ajiye wayar saman kafafunta yana dubanta fuskarsa cike da damuwa.
  "Ki yi hakuri Ummina."
Ta dubeshi ido waje.
"Hakurin me?"
Ya lumshe ido ya bude.
"Na 6ata miki rai kwana biyunnan, na yi miki laifi, ki gafarceni."
Ta girgiza kai da sauri.
"Wallahi ni ce mai laifi Yaya Faruk, don Allah ka yi hakuri, in sha Allah na daina yi maki abinda ba ka so..."
Ta karashe a dan kunyace, ya yi murmushi wanda ya jima baiyi gareta ba gami da riko hannunta ya dan murza.
  "Is ok, share wannan, ni yanzu dai ki gayamin, daman an iya wankin undies aka bar Faruk nata wahala?"
Ya fada a shagwa6ance, ji ta yi kamar ta nutse a wajen, ai fa kunyarnan sai a sannu zai saketa gaba daya. Ta hau sussunne kai tana murmushi, ya yi dariya yasa hannu ya karkato fuskarta gareshi, ganin haka ta lumshe idanunta batason su hada ido. Ya yi mata k'uru da nasa idanuwan. Can kuma ya numfasa ya sanyata jikinsa ya matse.
  "Ummina idan addua ki ke min ki rage yinta, don idan Faruk ne kin gama mamaye zuciyarsa, please ki ragwanta kinji? Ina jin kamar zuciyata zata fashe da sonki."
Ta bude idanunta tana numfarfashi, tausayinsa ta ji, ta yi amannar cewa son da Faruk ke yi mata bai kai wanda ta ke mishi ba, kuma ba hakan na nufin ita din bata son nashi bane. Tana ji bata iya hanawa ba, tana gani bata iya ta kwa6a ba, haka sakonnin suka yita shigarta, duk inda ya biyo bata ko tureshi, har abin ya kai ga fin karfin tunaninsu, sai kuma don kansa ya kyaleta yana dubanta. 
  "Za ki tayani kwana yau? Tsoro nake ji." 
Batasan sadda ta dan harareshi ba sannan ta kauda kai gami da dan turo baki, ji ta ke kamar ta nutse saidai batason 6ata ranshi, batason ya k'ara nisantarta. A kwana biyun nan ta wahala da shariyar da ya ke mata. 
   Ya hau gyara mata sutura yana fadin.
"Kinji? Please."
Shiru ta yi, kamar ta ture hannunshi don tasan ba a iya gyaran zai tsaya ba,  ai kuwa ta ji ya sumbaci hannunta.
"Lallen nan naki ya burgeni Ummina, ki dunga yimin please."
Ta gyada kai kawai, sallamar Hajiya yasa ta ja baya da sauri gami da rufe kanta, shi kuwa baya ya ja kadan ya gyara zamansa sannan ya amsa. Hajiya jin muryarsa ta yi mamaki, hakan yasa ta fasa shigowa don kuwa wani hadin ne ta kawowa Ummin na mayuka masu gyara jiki don ance in kana da kyau ka k'ara da wanka. 
   Ganin ta maida kofar ta rufe bata ko shigo ba yasa Faruk duban Ummi yana murmushi mai bayyana hakora.
"Kinji Hajiyata fa?"
A rude ta ke kallonsa. Ta karya wuya.
"Don Allah Yaya Faruk ka tafi kada ta dauka wani..."
Sai kuma ta yi shiru don gudun 6ata ransa, ya dan ja jelar gashinta da ya lek'o.
"Kada ta dauka me? To naji zan fita, amma kirani da wani suna banason wannan."
"To Sadauki." Ta fada da sauri.
Ya yi 'yar dariya.
"Aa, wannan Hajiyata kadai ke fada."
Ta marairaice fuska can kuma ta ce.
"Yalla6ai."
Ya ta6e baki ya girgiza kai.
"Chanja."
Kamar zata yi kuka ta yi shiru can kuma ta dubeshi, ko ajikinsa asalima dariya ya ke mata.
  "Um..um...toh Yaya Umar."
Dariya kawai ya yi ya mike gami da sumbatar le66anta sannan ya ce cikin rada.
"Ina sonki kamar na mutu." Daga haka ya juya ya fita, ta bishi da kallo tana murmushi har ya fice. 
   Daga ranar masoyan suka shirya....!!!
         [truncated by WhatsApp]

  DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

109

   Zirga-zirga ta ke yi a dakinta ko kayan makarantar ta kasa fiddawa, can dai ta k'arasa fisge dankwalinta ta ajiye gefe, har da ribbon din da ta ke tufke yalwataccen gashinta na fulanin usul, ta zaune gefen gado. 
  'Kai anya kina da hankali Ikram? Me za ki yi da DAN KAUYE?'
  Shine tambayar da wani sashe na zuciyarta ta jefomata. 
  Ta runtse ido sannan ta ja tsaki gami da mikewa tsaye.
  "Craziness!" Ta fada a fili sannan ta rage kayan jikinta ta fada wanka. 
     Bayan fitowarta ne daga ita sai tawul ta tarar da kira har sau uku a wayarta, ta yi saurin dubawa, biyu daga wani saurayinta ne Khalid wanda kawai ta ji ba ta yi murna da kirannasa ba, ba kamar a baya da ya ke dan burgeta ba, ta shareshi ta bi bayan kiran 'yar uwarta Ihsan wacce itace ta kira sau daya. 
  "Ke ina ki ka shige ne ina nemanki?"
Cewar Ihsan. Ta dan dara,
"Yi hakuri baiwar Allah, wanka na shiga fa. Ya akayi, ya su Mami?"
  "Mami ta fita siyayyar tsaraba na mutan Adamawa, ke ni bugowa na yi na ji ko da waccan munafukar za'a je?"
   Murmushi Ikram ta yi.
"Babu inda za ta je, gobe ma zata koma kauyensu. Ina Man dinki?"
  Ta ja guntun tsaki.
"Yana can inda ya ke, na ji yana batun shima ba a soma bikin Yayannaki yana nan ba don zasu je dangin Abbansa."
Dariya Ikram ta yi karo na biyu.
"Me ye na tsakin wai? Kefa ki ka cemin kin soma sonshi."
"Bazaki gane ba, ya iya tsara kalamai wallahi, matsalar daya yana son sanyomin batun zai min kaza da kaza bayan aure. Haka fa zuwan da ya yi satin da ya wuce, wallahi har rungumeni yaso yi na kauce. Amma hakan bai hana ni sonsa ba, saidai banason hakan ne kawai."
  Baki Ikram ta ta6e,
"Sai hakuri da neman tsari daga sharrin shaidan, mai yiwuwa saboda shi kadai ya tashi gaban iyayensa shiyasa, kinga kuma yanda suke ji da shi."
   Tsakin dai Ihsan ta k'ara yi.
"Za ki yi ankon Yaya Faruk? An fiddo." Cewar Ikram.
"Allah Ya sauwake!" Cewar Ihsan cikin daga murya. 
Ikram ta ja tsaki sadda ta isa ga sif din kayanta da zummar fiddo na sanyawa. 
"Kefa wani zubin banza ce, rashin yinki bakisan kamar kin nunawa mutane har yanzu kina sonshi ne ba, ai wallahi gwara ki yi ki cekare abinki, ga Abubakar dinki a gefenki. Ke kanki kinsan hakan ma abin alfaharinki ne tunda gayen karshe ne shima a haduwa."
  Ihsan ta yi shiru sai kuma ta amsa.
"Barni tukun, sai na yi tunani. Bari na barki kada na cinye miki dan katin."
Daga haka suka ajiye wayar.

  Ummi kuwa tun a daren ta karasa shirin kayanta, sun yi waya da mutan Gombe ya fi sau uku a ranar duk su dinma d'okin zuwanta suke yi. Yau ko ta kan abincin dare bata bi ba don ta dage wajen shirye-shiryenta, daga ta rufa akwati sai ta tuna da wani abin ta bude ta sanya, kamar yanzu da ta ke kokarin sanya wasu kayanta da zata bayar, tana cikin jerasu ciki ne, Faruk ya yi sallama ya shigo.  Ta amsa tana mai duban kofar, fuskarsa cike da damuwa, kananun kayan da suka zame mishi jiki yau dinma su ya sanya. Cikin dauriya ta sakar mishi murmushi don kuwa ta fahimci sam tafiyar ce baya so saidai don babu yanda ya iya ne. Kafin ta yi wani yunkuri ya karaso ya kwantar da kai a kafadarta gami da rikota jikinsa ta gefe, ta lumshe ido batare da ta yi yunkurin hanashi ba don tuni ta daina wannan sai idan ta ga abin zai fi karfinta tukunna. 
   "Tafiya za ki yi ki bari mijinki?"
Ta sunkuyar da kanta tana duban hannuwansa dake cike da gargasa. Har lokacin murmushi ta ke.
  "Kaima ai tafiyar za ka yi."
Ya dago gami da sanya bakinsa saitin kunnenta. 
  "Ba zan samu rakiyarki ba kuma ko?"
  Ya fada a shagwa6ance, numfashinta sai safa da marwa ya ke yi, ta kasa cewa uffan kasancewar ya cigaba da sarrafata son ransa, haka har tsayuwa ta nemi gagararsu. 
    Can kuma ya dago kai yana dubanta da idanunsa da suka yi k'ank'an. 
  "Na yi? Kin amince?"
Ta zaro ido tana dubansa. Abin ya ba shi dariya, ya ja kumatunta.
   "Matsoraciya, kodayake na ga kin rage tsoron, oya tell me, ya akayi ya ragu?"
  Ya karashe yana mai zama gefen gado ita kuwa na saman kafafunsa. Shiru ta yi kawai tana murmushi, ya ja karan hancinta har saida ta yi 'yar k'ara. 
   "Wani 6angaren kunyarki na burgeni, yana k'aramin sonki sosai, ina son mace mai kunya, shine babban ado ga diya mace, yanmatan yanzu basusan wannan ba, za ki yi mamaki idan ki ka ga yanda mata ke tallata kansu ga maza, za ki yi mamaki idan ki ka hau yanar gizo yanda mata ke aika hotunansu babu ko rufin kallabi da sunan neman mijin aure alhalin basusan cewar sam mazan da suka san abinda sukeyi bazasu kallesu da daraja ba, ke har fa wajen biki kawo tallar kawunansu suke yi ga maza har kuwa inda suke, za kuma ki yi mamakin ganin mahaukatan da ke tallatawa mijinki surarsu."
Ta hade fuska kadan. Ya kara matsarta a jikinsa yana dan murmushi.
"Saidai sun yi kadan, tsarin Allah muke nema koyaushe daga sharrinsu, in sha Allah zai karemu. Kinsan a inda na tsani kunyarki?"
  Shiru ta yi ganin ya maimaita yasa ta girgiza kai. Saitin kunnenta ya yi mata rad'a. 
  Ai batasan sadda ta runtse ido gami da kokarin zamewa ba, saidai ba rikom ragon namiji ta samu ba. Dariya kawai ya yi mata. 
  Ya fi awa daya a dakin, daga an soma hirar arziki zai hau lalubenta, sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login