Showing 63001 words to 66000 words out of 158267 words

Chapter 22 - Dan Adam Book 1 Complete Hausa Novel

Habiba ta murda kambunta.
  "Wani labari na ji a gari shine na zo don tabbatar da gaskiyarsa."
  Habiba murmushi kawai ta ke, Malam Yahuza ya kara tamke fuska, acan kasan zuciyarsa ko kadan bai jin dadin abinda ke faruwa saidai ba halin nunawa tunda yana gaban sarauniyartasa.
   "Wane magana kuma?"
"Wai Zahraddeen zai auri Khadija?"
Kafin ya yi magana Habiba ta amshe.
"Gaskiyar maganar kenan Bilkisu, yanzu nake shirin aikamuku cewar ku zo amsar kayan saka rana da lefe jibi, sai kuma ga ki da kanki don Allah ki aika a gayawa sauran dangi na kusa da ke."
    Bilkisu ta rasa me za ta ce, tsananin mamaki da tsoron hali na DAN ADAM su ne suka fi cikata. Ganin abin ta ke yi kamar almara, kamar dai a ire-iren litattafan da ta ke sauraro a shirin Rai Dangin Goro, ashe da gaske yana zama gaske?
   Ta mik'e tsaye sakamakon ruwan hawaye da ya soma kwaranyo mata a saman fuska. Ta dubi dan uwanta.
"To madallah, nagode kwarai da wannan cin amanar zamantakewar, babu abinda zance muku saidai duk wanda ya yi mai kyau kansa, akwai ranar k'in dillanci. Tabbas kun nuna hali irin na DAN ADAM na butulci, amma bakomai, Allah Yana nan."
  Daga haka ta sanya kai ta fice tana share fuskarta da mayafi. Tana jin sababin da Habiba ta ke yiwa yayanta akan yana ji ta ci zarafinsu bai dauki wani kwakkwarar mataki ba. 
   Koda Bilki ta isa gida saida ta sha fadan mijinta Malam Amadu akan dalilin da yasa bata bi maganarsa ba ta je gidan, ya kuma gargadeta akan kada ta sanarwa diyartasu tukunna har sai anga abinda hali ya yi. Daga wannan suka rufe maganar sai jimami da tunane-tunane. 
                  ***   ***   ***
                      ABUJA
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  61
                      ABUJA
  Tun wajejan uku na rana ta lura gidan kamar akwai wani shagalin da zaayi a dalilin gyara(decoration) da ta ga Ihsan, Ikram harma da Intisar (wacce ke fama da ciki wata uku) suke yi a (Garden). Abin kyalkyali suke sanyawa mai ban shaawa, ita tana gefe saidai a bata umarnin mik'o ruwan sha, mik'o balan-balan(balloon). Hada ido goma idan zasuyi da Ihsan, to fa saita watsa mata mugun kallo har dai a karshe ta raba kanta da kallonta. Hajiya Babba na zaune saman daya daga cikin kujerun da suka jera sai waya ta ke yi da surukarta(Jiddar Dakta Ridwan) akan batun (Cake) da(snacks) da suka bayar da oda. Abinci kuwa, Fadila matar Babban Yaya ce ta dauki nauyin girkawa a gidanta sannan ta zo. 
    Suka dauko wani tangameman hoton Faruk wanda ya ya juya fuskarsa yana dan murmushi, kamar dai wanda bai so akayi hoton ba saidai hakan da ya yi ba karamin kyau ya yi ba, yana sanye da riga mai hula sai dogon wando a farfajiyar gidan, ya yiwa Ummi kyau sosai. Hoton an kafeshi a daidai inda suka sanya teburin ajiye (cake). Bayan komai ya kammalasannan Ummi da Binta suka tattare ledojin da sauran takardun da aka zubar a k'asa.
     Haidar shine ya yi musu taimakon sanar da dukkan wasu abokan karatun Faruk da suke a garin, hakanan a 6angaren Ihsan ta gayyaci wasu kawayenta biyu mazauna Abuja domin su zo ta nunamusu mutumin da ta ke fatan ya zama mijinta. Ikram itama kusan dukkan kawayenta ta gayyata, bayan Magriba suka sanya fatin. 
    Duk wannan abu da sukeyi, Faruk ba shi da masaniya, zuwa dai lokacin yasan da cewa ranar ce ta(birthday) dinsa don tun sha biyun dare ya soma tsintar sak'onnin tayashi murnar cika shekaru talatin cif a duniya. Wasu ya basu amsa, wasu kuwa bai saman dama saidai ya aikamusu da alamar jinjina(like).
    Tun karfe shida, mutane suka soma zuwa, kowannensu ya ci ado kamar wani gagarumin biki akeyi musamman ma matan da suke zuci-zucin haduwa da Matasan yaran Gen Ahmad Danzaki ko wani cikinsu zai kyasa koda kuwa ace basu samu shiga wajen Faruk Danzaki ba.  
  Binta ta dubi Ummi.
"Oh ni Binta, ji yanda ake daukar kwalliya kamar baza"a mutu ba, ji sutura?"
  Ummi wacce har lokacin bata bar lek'en windo ba ta murmusa.
"Masu abu da abinsu?"
Ta6e baki Binta ta yi.
"Lallai kam, nasan dai duk don ya kyasa ne suke hakan, wasu ma ga dukkan alamu gayyar sod'i ne. To kwalelansu, Yalla6ai sai ke."
  Abin ya bawa Ummi dariya ta dara tana mai girgiza kai.
"Kai Binta, wai wa ya gayamaki hakan mai yiwuwa ne?"
   Binta ta yi kwafa.
"Ke kike ganin wuyarsa, amma na tabbatar karamin abu ne saidai kuma kin toshe kunnuwanki, ko kina da labarin Ihsan ma tana mutuwar son Yalla6ai?"
Ta yi kamar bata sani ba.
"Haba?"
  "Wallahi, jiya ina jinsu ita da Ikram tana zugata akan ta za6i kayan da zata sanya masu kyau sosai don ta burgeshi."
   Murmushi Ummi ta yi.
"Allah Ya tabbatar."
"Ba amin ba." Cewar Binta cikin sauri tana harararta, dariya kawai Ummi ta yi. Ta maida kanta ga duban windon inda ta nan suke lek'e, a ranta tana zuci-zucin ganin shigar da Ihsan din zata yi na sace zuciyar wanda ya riga ya fada tarkon kaunarta(ita Ummin).
   Misalin bakwai da mintuna kowa ya gama halartar wajen, ya yi daidai da dawowar Faruk gidan, ya yi hon yana duban kofar gidansu ganin motoci fin takwas a fake, mamaki karara ya bayyana saman fuskarsa, to me akeyi hakan?  Maigadi ya budemishi kofa ya shigo, a lokacin, kai tsaye wajen fakin ya isa, nan ma cike da mamaki ya ke duban(garden) din wanda a kusa da wajen ake fakin, duhu ne a wajen babu haske, haushi ya kamashi ganin ga shi akwai wuta, to meyasa Bala bai kunna fitilun wajen ba? Idan ma mutuwa kwayayen sukayi ai da sai ya sanarmasa tunda shi keda alhakin kula da komai na gidan, shi ya ke sanyawa a gyara, tun soma aikinsa ya daukewa mahaifinsa wannan nauyin. 
      Ya fito kai tsaye yazo giftawa zai shiga sashensa, hasken fitilu suka dallare shi sakamakon kunnawa da akayi, ya dubi wajen da sauri. Mamaki tsantsa ya bayyana saman fuskarsa na ganin yanda wajen ya dauki ado ga wani tangameman hotonsa a wajen har da cake babba. Bai gama shanye mamakin ganin hakan ba, ya tsinci muryar su Ma'aruf dan Dakta Ridwan da sauran yaran Babban Yaya sun fito, dukkansu yaran  maza da mata cikin riga mai (coat) da wando, suna fadin. "Happy birthday to you!" 
  Fuska a sake ya ke dubansu, bai kai ga gama shanye mamakinsa ba ya tsinci tafi da sowar tsoffin yan makarantarsu maza da mata wadanda basu kai ga yin aure ba da kannensa da kawayensu harma da yayyunsa maza suma suna masa wakar taya murna. Baisan lokacin da ya saki 'yar dariya ba.
   "What a surprise!"
Shine furucin da ya yi a fili na bayyana tsananin mamaki. Ko babu komai wannan abu ya burgeshi matuk'a, ya kuma ji dadinsa. Haidar ya dafa kafadarsa.
"Tafi ka chanja kaya, yau ranar murna ce."
  Ya yi murmushi sannan aka bashi hanya ya wuce. Ihsan wacce ta ci ado cikin doguwar riga(gown) kalar fari da ruwan hoda, gashinta mai tsawo an tufkeshi ko dankwali babu akanta ta yi kyau matuk'a, ta rungume Ikram tana ihun murna.
  "Kinga ni ko? Yaya Faruk ya ji dadin abinda mukayi."
  Ikram ta dara.
"Sai ma idan ya ji wacce ta kawo shawarar hakan."
Ta lumshe ido don dadi, suka sanya dariya. 
   Acan kuwa saida ya watsa ruwa, daman ya yi sallar Magrib dinsa, wasu sabbin kaya ya gani ajiye a saman gado,  coat ne fari k'al mai bulun 'yar ciki masu dankaren kyau. Sun kar6eshi matuk'a, daidai da turare sabo fil aka ajiye mishi a saman gado, ya feshe jikinsa da shi. Shi kansa yasan ya kai a kirashi da Namiji. 
   Tun da ya fito yanmatan suke binshi da kallo, ya karasa kai tsaye da Hajiyarsa ta rungumi kafadarsa tana jin kamar ta hadiyeshi don kauna.
"Kayi kyau Sadaukina."
Ya yi murmushi.
"Thank you Hajiyata."
Daga nan ya karasa ga inda aka tanadar mishi don zama, nan kuma shagalin ya soma. Aka kirashi ya yi jawabi na nuna tsansar farin cikinsa, sannan ya yi godiya ya koma mazauninsa yana k'arewa wajen kallo.
  'Ina Ummi?' Shine tambayar da ya jefawa zuciyarsa.
Baiwar Allah tana daga can wajen hanyar shiga dakunansu a tsaye tana kallo, tana gani Binta da karambani har da chanja sutura gami da karasawa wajen sosai amma ita ta ce sam bada ita ba, tana tsoron cin zarafin da Ihsan kan iya yi mata a cikin taron jama'a, tasan ba k'aramin aikinta bane ba. A can kasan ranta kuwa, tsananin kishi ne ta ke jinsa kamar ya kasheta na yanmatannan ta tabbatar kowaccensu shi ta ke hari, tana tsoron kadan ya zamana wata acikinsu ta burgeshi har ya ji yana kaunarta. Ganin da ta yi bazata jure ba ne yasa ta juyawa gami da komawa ciki.
      Shi kuwa daga nan inda ya ke zaune ya kasa nutsuwa haka nan ya ke daurewa kawai, ya yanke kek ya soma da sanyawa Babban Yaya a baki don tuni Hajiya ta koma ciki wajen mijinta, a ganinta taron na yara ne. Saida ya bawa yayyunsa kaf sannan suma suka bashi har suna 6ata mishi baki. 
Daga nan kuma aka tafi sallah, bayan an dawo aka saka (cool music) inda kowa ya zauna aka hau ciye-ciye, Faruk dai ba magana ya kasa cin komai, burinsa kawai ya sanya Umminsa a ido, yana so ta tayashi murnar wannan rana itama. 
  Tunaninsa ya katse sa'ilin da aka tsayar da wak'a, Haidar ne ya yi magana inda ya ce kafin a kammala ciye-ciye, za'a bawa Faruk dama ya zana musu macen da ya ke burin ace ta zama mallakinsa a rayuwa. Habawa, zo kaga ihu da sowa, kowa fadi ya ke hakan ya yi. Faruk ya yi wani murmushi kafin ya kai duba ga yanmatan da su ke zaune a wajen, kowaccensu da salon kallon da ta ke jifansa da  shi, har da masu chanja wajen zama yanda zai gansu sosai. Ya kai dubansa ga Ihsan wacce ta ke dubansa itama gaba daya kasan a tsorace ta ke. Duk waigensa bai ci karo da Sanyin Idaniyarsa ba, tunaninsa ya katse sa'ilin da aka janye teburin kek dake gabansa aka ajiyemishi karamin tebur mai dauke da alk'aluman zane da fente-fente. Sai(sketchboard) wacce aka sanya farar takarda a jiki.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
    
   63
    Ya dubi Haidar, duk wannan aikinsa ne, Haidar ya sakarmishi dariyar mugunta, sannan ya juya ga jama'ar ya bada umarnin kowa zai iya cigaba da ciye-ciyensa. Daga nan aka maida(cool music) din mai tashi a sannu-sannu. 
   A hankali ya zare(coat) dinsa ya dora a saman cinyarsa ta hagu sannan ya dubi jama'ar wadanda suna ci suna dubansa.
  Ummi wacce tun sanarwar da Haidar ya yi ta tsinci kanta cikin mugun tashin hankali da fargabar abinda zai faru, tana tsaye ta kasa zama a dakinta karshe ta bude labule kadan tana lek'ensa. 
   Cikin sa'a idanunsa ya sauka akanta, da sauri ta saki labulen gami da zamewa ta zauna kirjinta na luguden tara-tara na fargabar abinda ke shirin faruwa. 
    Ya lumshe ido yana murmushi kafin ya dauki fek'akk'an fensir ya soma zanensa.
   "Wa Faruk Danzaki zai zana?"
Shine tambayar da kowannensu ke yi a junansu saidai babu tak'amaiman mutum daya da ya sani. Daidai da yayyunsa sun k'agu su ga fuskar masoyiyar dan uwannasu wacce basu ta6a sanin koda sunanta ba...!

   Toh fa!!!!
  
    
 Ummi a rud'e ta k'ara d'agowa gami da lek'awa. Hankali kwance ya ke zanensa banda murmushi babu abinda kake gani a saman fuskarsa. Wasu ruwan hawaye ne suka zubomata, shikenan yau babu ita ba k'ara kwana a gidannan. Da sauri ta juya ta soma harhad'a kayanta don bil hakki ita kadai tasan iyakar rudanin da ta shiga. 
   Gogan kuwa, ya kwashi tsawon minti goma sha biyar kafin ya kammala ya mik'e tsaye, ganin haka yasa kowannensu mik'ewa, kowace budurwa awajen babu wacce kirjinta bai bugu da sauri-sauri don fargabar fuskar da zasu gani. Haidar ya k'ara tasowa ya iso gareshi, ya kai dubansa ga takardar zanen, ya k'urawa zanen ido, babu abinda kake gani sai manyan idanunta, ya yi alamun nikaf wanda ya rufe gaba daya fuskarta,  sai kadan daga siririn hancinta da ya dan fiddo mai dauke da karamin bak'in tabo daga sama. Ya kauda lasufika sannan ya harareshi.
  Haka mukayi da kai?"
Faruk da ke kokarin saka kwat dinsa ya daga mishi gira kadan.
"Ina kishin a ganta."
  Haidar ya jinjina kai yana dariya sannan ya kara duban hoton sosai.
"Kamar na ta6a ganin mai irin tabon nan, saidai bazan iya tuna a ina ba." 
  Faruk ya murmusa kafin ya k'ara daukar alk'alami, daga k'asa ya rubuta farkon sunanta.
"H"
Haidar duk iyakar tunaninsa bai ganeta ba, a karshe ya daga kafada kadan gami da maida dubansa ga jama'a wadanda ke jin kamar su tashi su warci hoton su sha kallo. Baice komai ba ya juya zanen ya nuna musu.
  "Ga wacce Kanina ya zana, sunanta da harafin H ya soma, ya dai yi mana kwalelan fuskarta inda ya ce yana kishin a ganemishi kyakkyawar fuskarta."
   Dariya matasan suka sanya, ita kuwa Ihsan ido ta k'urawa zanen, ta kasa gane ko wacece ita.
  "Wace kenan?" Shine tambayar da da yawa daga yanmatan. Ihsan ta dubi Ikram cikin rawar murya don har ta soma kwalla.
  "Wa ki ka sani mai farkon suna H?"
Ikram wacce tausayin Ihsan ya mamayeta ta daga kafada kadan.
  "Bani da masaniya akan kowacece, Hafsa kadai na sani sai Hadiyya, yanzu duk sunyi aure ma."
   Ita kuwa Ummi jin maganar Haidar ne yasa ta tsayawa daga abinda ta soma na watsa kayanta cikin yar jakarta. Ta mike da sauri ta lek'a, saidai bata ganin zanen yanda ya kamata, hakan yasa ta fitowa wajen, a daidai bayan bishiyar dogon yaro ta dan la6e tana hangen zanen. Ta dan sauke ajiyar zuciya duk kuwa da cewar akwai sauran rina a kaba, ta shafi karan hancinta, tabbas bakin a tabon nan yana nan inda ya ke wanda ta samu asanadin wani ciwo da ta ji awajen tun tana yarinya. Gabanta na dukan tara-tara ta zaro ido.
'Yanzu idan aka gane ni da wannan tabon ya zanyi ni Hasiya?' Ta tambayi zuciyarta, tambayar da tasan amsar bai wuce na ta shiga uku ba. 
   Lokacin da Haidar ya kammala addu'oin fatan alheri shi da budurwar da ya ke so, aka soma mikewa da kadan kadan ana mik'a mishi kyautuka. Ihsan ta so barin wajen don ita kadai tasan yanda ta ke ji, saidai Ikram ta lalla6ata gami da nunamata kada ta sake ta yi wasa da wannan damar, shi kadai ya yi mata saura, haka ta daure ta karasa gami da mik'a mishi kyautar da ta tanada domin shi wanda a ciki sak'on da ta ke son isar mishi ya ke. Ya kar6a yana mai dubanta, ko baa fada ba, idan ka kalli idanunta kasan ta yi kuka. Bai nuna ya gane komai ba, godiya ya yi mata sannan ta bar wajen da saurinta. 
   Haka kawai sai Ummi ta ji tausayinta, tana son maso wani, son wanda ta ke yi don shi baisan tana yi ba. A sanyaye ta juya ta bar wajen ta koma daki. Bata yi mintuna uku da shiga ba ta ji an murda kofar da sallama an shigo. Ai batasan sadda ta mik'e tsaye ba tsabar kidimewa. Murmushi ya sakarmata sannan ya tura kofar ya rufe. Karasowa ya yi yana dubanta.
  "Matsoraciya Ummina."
  Ta yi raurau da ido, ya girgiza mata kai.
"Kar fa kice kuka zakimin."

   Ta yi k'asa da kanta. Yasa hannu a ha6anta ya dago fuskarta suka dubi juna ido cikin ido. Ta lumshe idonta don ba zata jure kallon kwayar idanunsa ba. Ya saukr hannunsa gami da sakin ajiyar zuciya. Allah kadai yasan irin wutar kaunarta da ke ruruwa a zuciyarta a kowane dak'ik'a.
Hankalinsa ya kai ga kayanta da rabinsu ta sanya a jaka ga wasu a k'asa.
  "Menene wannan?"
Ta dubi kayan sannan ta tuna ashe fa guduwa ta yi shirin yi. 
  "Bakomai, linkesu nake yi."
Ya durkusa gaban kayan ya soma dagasu, duk ba wasu kayan kirki gareta sosai ba, ya girgiza kai kawai ya mike tsaye. Ta dubeshi kadan.
"Domin Allah ka tafi Yaya Faruk, kada a je nemanka."
   Ya rungume hannunsa a kirji.
"Wai kuwa Ummi kina kallon kanki a madubi kuwa?"
  Bai bari ta yi magana ba yasa hannu ya dauki hodarta dake gefe ya bude gami da juyamata, ta dubi dan madubin na hodar, kafin ta sauke idanunta kasa. Ya numfasa da murmushi saman fuskarsa.
  "Shikenan dai."
  Shiru ya biyo baya, tana ji Haidar na cigiyarsa ta lasufika akan ya zo sallamar bak'insa. Ta daure ta yi magana.
"Ina tayaka murnar wannan rana, Allah Ya k'aro shekaru masu albarka, Ya taimaki rayuwarka."
  "Amin. Allah Ya nunamana na aurenmu haka. Thanks my Ummi, zo muje ki rakani mu sallami bak'inmu."
   Ya kai hannu da zummar riko nata, ta ja baya da sauri tana girgiza kai.
"Ke na soma gajiya da 6oyon da muke yi, aurenki fa nakeson yi. Amma dai..."
  Ya jinjina kai kawai sannan ya juya ya fita, a kofar sukayi kici6us da Binta ta gaisheshi, fuska a daure ya amsa gami da fadin.
  "Ki kiyaye bakinki." Shi ne abinda yace, ta amsa da to cikin sauri, daga nan ya yi gaba. Da sauri ta fad'a dakin wajen Ummi. Ummi na ganin itace ta sauke numfashi don a farko da ta ji maganar da Faruk ya yi duk ta dauka ko da Ikram ya ke. Binta ta kama ha6a bakinta a washe.
    "Ke Ummi, abu fa ya soma zafi, anya kuwa nan gaba Yalla6ai bazai daukeki daga sashen yan aiki ya maida cikin gidansu ba, kafin daga baya ya daukeki cancak zuwa gidan aurenku?"
   Ummi ta yi dariya, maganar Binta ta karshe ta yi mata dadi. Ita kuwa Binta k'irr ta tsayar da ido tana duban fuskar Ummi kafin ta doka tsalle ta rungumeta tana ihun murna.
"Kece, daman nasan ke ce wallahi."
Ummi ta kwaci kanta tana kokarin rufewa Binta baki.
"Ki rufamin asiri kiyi shiru kada wani ya ji."
  Binta tana dariya ta yi mata nuni da tabon dake a saman hancinta. 
  "Wannan tabon nayi mamakin yanda Yalla6ai ya ganoshi, naga sai an k'ura miki ido ake ganeshi."
   "Shiyasa nake gudun ranar da asirina zai tonu."
  Guntun tsaki Binta ta ja.
"To menene? Ke saifa kin zama jaruma wallahi. Ni kizo muje kaya aka bani na kai dakin Yalla6ai, ki zo ki tayani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login