Showing 153001 words to 156000 words out of 158267 words

Chapter 52 - Dan Adam Book 1 Complete Hausa Novel

daya."
  Fadin Hajiya Mama kenan don wannan karon banda manyan iyaye a zuwa. Da haka Ummi ta fita ta na cigaba da gwada kiran Faruk wanda ya kashe wayoyinsa kaf. Takaici ya isheta, a waje ta tsaya tana waige-waige, motoci masu tsada sun cika farfajiyar gidan wasu kuwa da basu samu shigowa ba suna daga waje, to biki ne bana mutum daya ba, Hajiya Lubna itama yan uwanta na Maiduguri sunzo da yawa don bata ta6a aurar da diya ba, hakanan Hajiya Binta wacce rabin yan uwanta a Kano suke, su dinma duk hallara. 
  Tana nan tsaye anata tafiya ta hango Gidado na kokarin shiga mota da sauri ta karasa gareshi.
"Yaya Gidado." Ya waigi, yana ganinta ya karaso ya cimmata ganin yanda ta ke tafiya da sauri.
  "Yi a hankali mana Ummi, za ki je dinne?"
  Ta gyada kai gami da yin narai-narai da fuska. 
  "Eh, ina Yaya Faruk?"
  Ya yi murmushi. 
"Yana kofar gida amma nasan yanzu sun wuce, taho mu tafi kawai."
   Ba musu ta bi bayansa, kafin ta kai ga shiga wayarta ta dauki k'ara, Abubakar ne. Ya tambayeta ko tana ina, ta sanarmishi gatanan za ta bi Gidado, ya ce ta jira tare zasu wuce. Ta amsa da toh gabanta na faduwa, kada fa ya zamana Faruk bai yi na'am da zuwannata bane, to amman ai Abubakar bazai mata karya ba tunda ya ce ya amince ta je. 
  Aikuwa motar Ango da Amarya ta hau, gidan gaba ta zauna, Kb ne matuk'in Abubakar da Ihsan. Ihsan ta ci magani ganin Ummi k'ame a gaban mota, har akaje ba ta ce uffan ba sai kuwa Abubakar da Kb ke kwasar hirarsu, jefi-jefi sukan sanyo Ummi da Ihsan, motocin Amare a jere haja suka isa. 
   Gaban Ummi ya fadi ganin Faruk zaune saman mota a farfajiyar wajen tare da Jafar abokin aikinsa suna hira. Ya yi kyau har ya gaji da haduwa. Tun shigowar motocin idanunsa suka hangomishi matarsa a gefen mutumin da har gobe bai mance abinda ya so aikatawa ga iyalinsa ba, wato Kb. Wani abu ya soki kirjinsa, kishi mai tsanani ya turnuk'eshi x ya dauke kai fuskarsa kamar an aikomishi sak'on mutuwa, wannan ba karamin firgita yan hanjin cikin Ummi ya yi ba, ta hau karanto adduo'i cikin ranta har motar ta daidaita fakin, har Amarya da Ango saida suka rigata fita, sannan a karshe ta daure ta bude mota ta fito, nan masu hoto suka yi musu ca, da sauri ta samu ta bar wajen ta nufi wajen mijinta, saidai babu shi babu dalilinsa, can ta hangeshi wajen Angwaye suna gaisawa da Abokai, jiki a sanyaye ta koma ta shiga ciki, saidai me? Zaman namiji da mace ne, ga mai aure da matarsa, marar aure kuwa budurwarsa. Intisar ana k'ame gefen Haidar, hakanan su Jidda, ta yi shiru ta kasa karasawa ciki dole ta juya da zummar fita saidai ta ji an riko hannunta. Da sauri ta dago kanta, Faruk ne saidai fuskarnan tasa babu digon walwala ya ja hannunta zuwa ciki, ta kasa cewa uffan ga uban tsoro da ya cikata kamar ta saki fitsari a wando, ya dan saki fuska gudun kada a dagosu, itama ganin haka ta saki nata. Haka suka karasa mazauninsu kusa da su Ridwan. 
  "Madam daga nan sai Asibiti ko?" Cewar Ridwan cikin zolaya. Murmushi kawai ta yi. 
"Kema dai Ummi, ai da kin hakura kin zauna gida." Fadila wacce ta sauko yanzu ta fada da murmushi saman fuskarta. 
   "Ina zata zauna wata ta yi mata kwace? Da gaskiyarta ai."
  Haidar ya fada yana yar dariya, hakan yasa Ummi fadada fara'arta wanda duk yak'e ne ganin gogannata bai wani sakarmata ba, sai murmushi da ya ke wanda ya zamto yak'e. 
   "Au Madam ashe kinga ogannaki ina can ina nemanki naga kamar ba ki shigo ba." Suka tsinci muryar Kb daga gefe, ta yi yar dariyar yak'e tana fargabar abinda zai biyo bayan amsawarta. 
   "Um, na shigo yanzu."
"Yauwa." Daga haka ya maida akalar hirar da Haidar dake tambayarsa ko da wa zai zauna.  Ya nunamishi wata cikin kawayen Ihsan wacce a ganin farko ta kwantamishi. 
    Can kuwa Gidado na tare da Ikram kamar su hadiye juna don so. Party ne na yan boko, komai bisa tsari aka yishi, ba'ayi wani raye-raye sosai ba, sai ko (step-dance) da dangin Ango Abdullatif suka shirya suka yi wanda ya k'ayatar sosai. 
     Anci an sha, an kuma yiwa Angwaye da Amare lik'i kwarai. 
   Kafin akai ga tashi ta soma buga uban hamma don ta gaji ga bacci dake cinta, ta dubi Faruk da hankali kwance ya ke kur6ar lemu abinsa, lokacin su kadai ne saman tebur su Babban Yaya da sauransu an tafi daukar hoto. 
  "FAR HAS na gaji wallahi bacci nake ji."
Ko kallo bata isheshi ba, kamar ba da shi ta ke magana ba haka ya nuna. Jikinta ya kara sanyi, ta lalubo hannunsa na dama ta matse cikin nata. 
  "Don Allah ka yi hakuri na yi maka lai..."
Kallon da ya watsamata ne yasa ta hadiye maganarta babu shiri, har lokacin hangota ya ke zaune kusa da Kb a mota.  Ya zare hannunsa cikin nata.
   "Ai ba ni na kawoki ba, ki nemi wanda ya yi miki iznin zuwa da wanda ya kwasoki a motarsa har ku ke hira da dariya su yafi dacewa ki je su maidaki."
   Hawayen da ta ke rikewa suka zubo.
"Amma Yaya Abubakar cemin ya yi ka amince."
  "Tunda shi ki ke aure ai ya miki izni kin zo, shikenan kuma, komawa kuma ni ba yanzu zan tafi ba sai na gama abinda ya kawoni."
Daga haka ya mike ya soma tafiya a kasaitance, tafiya mai cike da aji, babu budurwa da bata kyasa ba, ya wuce gurin Angwaye, yana zuwa ya fiddo rafar yan dubu-dubu ya hau lik'i. Nan wuri ya chanja, kida ya chanja, Mai wak'a ya tambayi sunansa aka sanarmishi habawa tuni ya hau wak'eshi yana mishi kirari da yayan Amare kuma Abokin Angwaye. 
   Ummi hawaye ta ke na bakinciki da tsananin kishin yanda yan mata ke faman zubamishi lik'i shima, ji ta ke kamar ta dora hannu akai ta kwara ihu, ga bakincikin fushin da ya ke da ita, ga kuma na kishin mijinta. Mamaki ta ke na yanda yau bai damu da zubar hawayenta ba. Mikewa ta yi jiki a sanyaye, ji ta yi fatin ya fice a ranta, ita kuwa ko tasi ne zata hau ya maidata gida da dai ta zauna ta shak'i wannan kayan takaici. Tana jinta wani iri, Faruk bai kamata ace ta bak'anta mishi rai haka ba, idan da alk'awari sam Faruk bai kyautu ta musgunawa zuciyarsa ba, ya cancanci komai daga gareta. Haka ta ke faman tunani har ta fito farfajiyar dakin taron. Nan kuma ta shiga rarraba idanu, to ina zata nufa? Waya ta ciro da zummar kiran Abubakar sai ta tuna abinda Faruk ya ce kawai ta fasa, ta maida wayar jaka ta soma tafiya tana fatan ganin direban gidan su Mami ko Hajiya Mama don ya maidata gida, saidai akwai mutane da motoci sosai babu damar gane hakan. Takalmin yana da tudu, ya isheta, hakan yasa ta zuwa daidai motar Haidar ta tsaya gamicireshi sannan ta soma kokarin dauka, saidai durkuso ya yi wuya agareta, ta kara kokarin durkusawa ta ji an rike kafadarta, a razane ta dubeshi, Faruk ne, ya durkusa ya dauki takalmin ya rike mata, kai tsaye ya wuce ya bude motarsa ya tayar, ya yo ribas ya saita kafin ya budemata gidan gaba. Sauke gilashin motar ya yi yana dubanta batare da ya ce uffan ba. Hawayenta suka zubo ta soma tafiya, ya kuramata idanu cike da tausayi, tabbas ya kula a gajiye ta ke, abinda ya gujemata kenan shine babban dalilinsa na dagewa kan ba zata zo ganin anyi kamu anyi yini duk tana faman zirga-zirga. Ta shigo ta zauna ta rufe kofar, ya soma ja a sannu-sannu har suka fita, saida ya hau titi kafin ya dan k'ara gudu. Ta dubeshi saidai ta kasa magana, a hankali ta soma kuka sosai harda sheshsheka, duk yanda yaso ya basar, ya kasa, dole ya sauka daga saman titi ya yi fakin a gefe. Dubanta ya yi na yan mintoci kafin ya soma magana cikin sanyin murya.
"Meyafaru kuma?"
Ta dan matso kadan ta dora kanta saman kafadarsa gami da rungume hannun gam. 
  "Don Allah FAR HAS ka yafemin, na fito bada izninka ba kuma na yi abinda kishinka ya motsa, don Allah ka yi hakuri."
  Wani so da tsantsar tausayinta ya cikashi, shima yana cikin dakin taron ya dawo daga lik'i ya ga batanan hakan yasa shi fitowa a rude, karshe ya hangeta jikin mota. Ta ya ya zai iya fushi mai tsawo da Umminsa? Ya sanya hannunsa na hagu ya dafa kanta. 
"Kinmin laifi Ummina, saidai duk iyakar laifin da za kimin bazan iya rabuwa da ke ba saidai wata kaddarar da bana fatan ta rabamu idan har ba mutuwa dayanmu ya yi ba, ina kishinki Ummi musamman da Kb wanda ya kusan cin rabona."
  Ta dago kanta cikin marairaicewa ta ce.
"To ka yi hakuri bazan k'ara ba."
Murmushi ya yi ya ka karan hancinta.
"Haka ake bada hakuri?" 
Ta yi murmushi.
"A hanya muke fa."
Ya share mata fuskar.
"Muje ki huta, daman nasan bebina bazai jure wannan Dinner ba shiyasa na hana ki zo amman Abubakar ya nunamin ke yar uwarsa ce."
Ya karashe da dariya, ta tayashi kawai. Haka ya cigaba da tafiya, ta koma kujerarta ya kwantar mata da kujerar kadan ta yi filo da hannunta tana dubansa yana tuk'i, a haka bacci ya yi awon gaba da ita don sosai ta ke jinsa. 
  A waya Faruk ya sanarwa Abubakar sun taho Ummi ta gaji don ba wanda ya sani. Koda ya yi fakin, saida ya karemata kallo don ba don baccin ta ke ji ba da bai ci ace ta yi ba don tafiyar ba wata tafiya ce sosai ba. Ya shafi gefen fuskarta, hakan ya sanyata bude idanunta. Kyakkyawan murmushi ya jefeta da shi.
"Mun iso."
  Ta mike, ya zagayo ya budemata, da taimakonsa ta zura takalmi ya rike fos dinta suka shiga ciki. A falon Mami duk an ragu babu kowa, wasu sun yi bacci, har daki ya kaita, nan ma yaran su Jidda ne duk sun yi bacci, ya dubeta.
"Ko za ki dakin Fahad? Kinga nan ma a cike."
  Ta dubeshi ta girgiza kai.
"Aa zan kwanta gefensu karka damu."
Bai bar dakin ba saida ya tabbatar ta rage kayan jikinta ta chanja zuwa na bacci ta kwanta, ya sumbaci goshinta.
"Goodnight."
Ta lumshe idanu tana murmushi.
"Kaima ka kwanta fa."
"Aa, zan koma wajen budurwata." Ya fada a wasance, ta kai mishi bugu a kirji sukayi dariya. 
"Bakasan na ji haushin yanmatan nan masu yi maka lik'i ba ko?"
Ya ja karan hancinta.
"Na fiki kishi Madam, karki damu ke kadai zuciyata ke so da kauna. Oya kwanta."
Ta muskutawa ya rufeta, sannan ya kashe musu fitila ya fice, Allah Ya taimakeshi babu wanda ya ganshi balle tsoffin su ce ya yi rashin ta ido....!
  Washegari da safe ya koma bakin aikinsa Abuja, a ranar aka kai Amaren biyu, Iklima da Hassana, ita kuwa Ihsan Adamawa zasu wuce washegari.
   Bayan Magriba Mami ta yi kiran Ihsan da Ummi zuwa sashen Abba ta rufe don samun damar yin maganar da ta ke so....!
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

129-130

Kowaccensu ta yi shiru tana mamakin wannan kiran, Ummi zata zauna k'asa Mami ta nunamata kujera.
"Zauna nan Ummi kada ki takura."
Ba musu ta zauna kujerar da ke fuskantar Mamin hakanab Ihsan ta zauna gefenta saidai nesa da ita. Tsaf Mami na lura da yanda Ihsan ke faman cin magani, ta numfasa ranta babu dadi kafin ta soma magana. 
   "Abinda yasa na nemi da na ganku bai wuce fahimtar irin rashin jituwar da ke tsakaninku ba har zuwa wannan lokacin da ya ci ace komai da ku ka sanyawa zuciyoyinku ya kau. Matsalar ba daga Ummu ta ke ba sai daga ke." Ta nuna Ihsan wacce ta kara tamke fuska. 
   "Na lura kin sanyawa ranki kiyayya, muguwar kiyayya ta Ummi alhalin banga wani mugun abu da ta ta6a yi miki ba har ta cancanci hakan. Ihsan kina wasa da addininki, wannan ba d'abi'ar musulmin kwarai bane, ina mamakinki, ba ki da rik'o akan kowa sai akan Ummi, yarinyar da gatanan zan shaidi cewa takan yi kokari matuk'a wajen kulaki saidai ba za ki amsamata ba, ko sau daya ban ta6a ganin kin bita da kallon arziki ba. Anya kina son gamawa da duniya lafiya?"
  A razane Ihsan ta dubi mahaifiyarta har idanunta sun ciko da ruwan hawaye saidai ta kasa cewa uffan. Mami ta jinjina kai cikin tabbatarwa.
"Hakika wannan hali ba inda zai kai ki a rayuwa, ke duk abinda ya faru bai zame miki ishara ba? Ni na haifeki, ni nasan halinki saidai ban ta6a saninki da nunawa mutum kiyayya ba sai akan Ummi."
  "Ni Mami me ta yimin da zan k'i ta?" Ta fada cikin rawar murya idanunta cike da ruwan hawaye. A fusace Mami ta ke dubanta, Ummi ta dubi Ihsan kadan saidai ba ta ce uffan ba ta maida kanta k'asa. 
   "Shi nakeson a yau ki bude zuciyarki ki sanarmin, me Ummi ta yi miki ki ke k'in sakin jiki da ita kamar yanda sauran yan uwanki ke yi? Ko kinsan cewa nasha kamaki kin harararta? Fuskarki na nuni da tsantsar kiyayya gareta koyaushe. Annabinmu s.a.w ya hanemu da zurfafa kiyayya ga dan uwa musulmi. 
  Abu hurayrah ya ruwaito Annabi SAW ya ce "Na rantse da wanda raina ke hannunsa mutum ba zai shiga aljanna ba har sai ya mika wuya,  sannan ba zaka mika wuya ba har sai kunso junanku. Ku yaɗa alkhairi zaku so junanku. Sannan ku guji kiyayya don kaifi gare ta,  bance yana aske gashi ba amma yana aske addini."
Wannan kadai bai isheki hujjar da za ki yi watsi da makamanki ki rik'i Ummi yar uwa ba? 
  
  Mami ta cigaba da magana, ta inda ta shiga ba tanan ta ke fita ba har yanda ta fusata ya tayarwa Ihsan da Ummi hankali, musamman ma Ihsan wacce ke son mahaifiyarta ta sosai, kokadan batason abinda zai 6ata ranta, kuka sosai ta ke yi, ta mike ta nufi wajenta ta durkusa gami da riko hannunta.
"Ki gafartamin Mami, wallahi na daina, zan riki Ummi duk yanda ki ke so, Ummi don Allah ki yafemin abubuwan da na aikata gareki, bazan k'ara ba in sha Allah."
Ummi ta share hawayenta tana murmushi a hankali ta mike ta tako har wajen da suke, zama ta yi gami da riko hannayen Ihsan.
"Ban ta6a rikeki a raina ba daidai da rana daya, na yafemiki tun kafin ki rok'a, karki damu, nima ki gafartamin idan akwai abinda na yi miki da bansani ba."
  Kunya ta rufe Ihsan, ta sauke kanta jiki a sanyaye.
"Ba abinda kikamin, idan ma kin yi to na yafemiki duniya da lahira."
Mami murmushi kawai ta ke yi, ko babu komai tana alfahari da Ihsan a fagen jin maganarta, da wuya ta sa6a umarninta.
   Ta riko hannuwansu ta sanya cikin na juna.
"Allah Ya muku albarka, Ya kara hada kanku."
  Ummi da Ihsan suka dubi juna suka yi murmushi alokacin da suka amsa da amin. 
   Tun daga wannan lokacin, suka dinke, idan ana zaune ana hira, Ihsan ta daina barin wajen idan ta ga Ummi, har takan tsokani Ummi cewa ita fa yayarta ce yanzu. Ummi dariya ta yi saboda rashin sabo da hakan daga gareta. 
   Su Intisar gaba daya sunyi mamaki.
"Ko kefa." Cewar Aisha yayar Ihsan a saitin kunnenta, ta dubeta kawai suka yi murmushi. Hatta Amina, saida Ummi ta kira a wayar ta sanarmata batun shirinsu don ranar yini kawai ta zo wanda shima Bellon dakyar ya amince don acewarsa bai isa ace ta soma fita ba.  
   Babu wanda bai yi murna da shirin Ihsan da Ummi ba. 
  "Wallahi kinsan me Ikram? Yanzu jin zuciyata nake wasai babu ko digon damuwa, ashe kiyayya babu dadi? Ni sai yanzu ma na ke kara fahimtar Ummi mutum ce, halayenta abin so da sha'awa." Abinda Ihsan ta fadawa Ikram kenan sadda suka shigo falon Mami bayan ta raka Ihsan din wajen mijinta da ya bukaci ganinta. Ikram murmushi ta yi.
"Kwata-kwata gaba bata yi ba ai, Allah Ya k'ara nisantamu daga shaidan."
  "Amin."
  Washegari aka yi shirin tafiya Adamawa tun karfe takwas na safiya, Ihsan nan ta shiga kuka sosai dakyar aka 6an6areta daga jikin Maminta, nan kuma ta kama hannun Fahad gam ta rike, shi kansa kuka ya ke kasancewar sun shaku da ita. 
   "Ya kamata ki samarwa Fahad k'ani."
Mami ta tuno furucin Mijinta a daren jiya, kwarai da zata kara haihuwa tasan ba karamin dadi zaiji ba, saidai kuma likita ya tabbatar mata cewa tsarin iyali na shan magunguna da ta yi ya janyomata matsala a mahaifa, abu ne mai wuya ta kara haihuwa sai ikon Allah, ya yi mata wannan bayanin ne sadda ta ga 6atan watanta kwanakin baya da har Hajiya Mama ta shawarceta da zuwa ganin likita ko ciki ne da ita. 
  Kwarai ta yi da na sanin yin tsarin iyali musamman ma da ya kasance ba da iznin mijinta ba. 
    Haka kukanta ya kasance biyu, da jimamin rabuwa da diyarta wacce kusan tafi kaunarta duk a yarannata idan an cire Adnan wanda Abban ke so sosai, sun shaku da ita yau ga aure ya raba. 
  Aka wuce gaba daya har su Hajiya Babba, Ummi kuwa a ranar suka wuce da su Jidda zuwa Abuja. 
                 ***    ***    ***
  A farkon zamantakewar Ihsan da Badiyya, sun sami matsala na kishi, saidai da ikon Allah komai ya zo ya wuce suke zamansu lafiya, ga Abubakar ya na takatsantsan sosai don ya rage kula yanmata musamman da ya ke 6arje Angoncinsa, hakanan ya rage hira a waya a gaban matansa gudun 6atawa wata cikinsu, yanmatan ma duk sai ya ke ji suna ba shi haushi, watan Ihsan biyu a gidan, ta samu ciki, murna wajen iyayen Abubakar ba a magana, shi kansa har kuka ya yi don tsananin farinciki. Ya zamana hankalinsa kacokam ya koma ga kula da Ihsan, Badiyya ta shiga tashin hankali matuka saidai ta yi jarumtar 6oyewa bata nuna ba. Da ita aka hadu aka yi ta kula da Ihsan.
              
     Ummi cikinta ya shiga tara cif, a wannan lokacin sosai an soma shirye-shiryen bikin Ikram da Gidado, bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login