Showing 69001 words to 72000 words out of 158267 words

Chapter 24 - Dan Adam Book 1 Complete Hausa Novel

na gaba daya layukansu hudu masu tsada da ba wata diya mace da ta ta6a mallakarsu haka. 
    Bayan ya kammala ya mik'amata kwalin.
  "Mun gama da wannan Ummina, yanzu maganar aurenmu ce ya ragemana."
Ta lumshe ido tana mai jin kamar ta saki ihun kuka, ya matsa yana fuskantarta. 
   "Gobe juma'a nakeson bayyana ki ga su Hajiya matsayin wacce nakeso da aure."
     Ido waje ta ke dubanshi, hawayen da ta ke dannewa tuni ya fito ya soma sauka saman fuskarta.
    Ji ya yi wata iriyar kasala ta saukar masa, ya runtse ido cikin kasalalliyar murya ya ce. "Please stop it mana, na tsani ganin hawayenki ya zuba Ummi akan kuma dalilin da bai taka kara ya karya ba. Idan ke kin kasa jarumtar jure koma menene zai zo wanda bana fatansa ma, ni ya kikeson nayi ne? A'a Ummi, wallahi Faruk bazai iya daukar wani tsawon lokaci batare da Hasiya ba. Na soma gajiya, ni ban iya wannan rayuwar ta 6oye abinda zuciya da gangar jikina ke muradi ba. Bazan iya ba, gobe ki shirya, ina zuwa."
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

66

A fili kuwa don ta kwantar mata da hankali. Ta nunamata bawani abu bane, ya dace ta koyi jarumta tun daga yanzu. Ta k'ara bata shawarar tashi tsaye da addua, inda ta tabbatar mata itama zata tayata. Ummi ta yi godiya sannan ta jawo ledar suka bude. Wani hadadden Atamfa (pink) ne mai turuwa, a wani 6angaren mai dan haske-haske, anyi dinkin riga da zani, koda Ummi ta daga rigar ta girgiza kai.
"Anya rigar nan zata yimin?"
"Tsaf ma kuwa, tashi ki gwada kedai."
Ba musu ta gwada, ai kam ba karamin kyau ya yi mata ba. Ta cire suka cigaba da duba ledar, harda dan kunne da sark'a fashion mai kyau da agogo, harda turare kala uku da kayan kwalliya, abin bai tsaya anan ba har dasu takalmi fari kalar mayafin da ya sanyomata. Binta banda washe baki babu abinda takeyi, ita kuwa mai abin jikinta sanyi ya k'ara yi. Wayar ta k'ara dagawa tana juyawa.
"Kai Ummi ki godewa Allah, kin samu mijin da ya iya kula da matarsa wallahi."
  Murmushi Ummi ta yi.
"Kai Binta, har ya zama mijina?"
  "Haka nake miki fata 'yar kanwata, nidai nasan gudunmuwar da zan baki a wannan lokacin idan ya zo."
  Dariya kawai Ummi ta yi gami da girgiza kai, a ranta fatan hakan ya ksance takeyi.
Sun dan jima tare da Binta kafin ta mik'e ta yi mata sallama don ta soma hamma na jin bacci. Bayan fitarta ta maida kayan cikin ledar ta yi gefe da su. 
   Alwala ta d'auro ta gabatar da nafila, ta jima tana addu'o'i kafin ta shafa ta koma makwancinta. Wayar ta k'urawa ido tana jujjuyawa, ta yi nisa cikin tunani wayar ta dauki k'ara. 
'Hubbyna.' Shine sunan da ya fito, wani ajiyar zuciya ta saki gami da yin murmushi. Kafin ta dauka kamar yanda ya koyamata yacce zata yi.
   Sallama ta soma yi mishi ya amsa.
"Ba ki yi bacci ba, meyasa?"
Ta ji daddadan muryarsa har cikin jini da bargonta.
  "Bakomai." Shiru ya dan biyo baya can kuma ya yi magana.
"Ina fatan ba kuka kikayi ba?"
Da mamaki karara akan fuskarta ta girgiza kai.
"Ni..ni banyi kuka ba."
Ya yi murmushi mai sauti.
"Ni kuma jikina ya bani kinyi kuka Ummina, amman dai shikenan. Ya kika ga kayan, sunyi miki ko a chanja?"
  'Ni na isa nace basuyi ba?' Ta fada a zuciyarta batare da sanin ya fito fili ba.
"Har kin yi yawa indai awajen Umar Faruk ne. Ni ban ajiyeki nan kusa ba fa. Amma yanzu duk bazaki gane hakan ba sai bayan aurenmu."
  Ta lumshe ido tana mai jin wani kaunarsa sabuwa fil a cikin ranta.
"Inama hakan zata faru Yaya Faruk."
Furucin ya yi mishi dadi, ya fahimci ta soma sakin jiki da shi.
"Zai faru in sha Allahu Ummina, ki kwantar da hankalinki har zuwa ranar da Umarul Faruk zai mantar da ke dukkan bakkan ciki da iznin Allah, ranar da zamu kasance mata da miji abin so da alfahari. Matukar ni ne mijinki, bazan k'ara barin ki cikin hali na damuwa ba. Watakil sai kin gaji da ni, don daga ranar da na aureki, na daina zuwa aiki."
  Dariya sosai ya bata, sai gashi ta shiga yinta kwarai. Ya lumshe ido gami da k'ara rungume daya daga cikin kananun filon dake saman gadonsa. Shi kadai yasan yanda ya ke jin dariyarta. Ta tsaida dariyar cike da jin kunya. Murya kamar na wanda baya son magana ya ce.
"Naso ace kina gabana kike dariyar nan Ummi, yana daga cikin abinda ban ta6a gani ba daga gareki, kuma zanso na ganin."
   Ta sunkuyar da kanta tamkar yana ganinta ta hau wasa da igiyar hular t-shirt din dake jikinta. 
  "Saida safe Yaya Faruk, bacci nake ji."
  "Ko na zo?"
Ta zaro ido kamar yanda ganinta, ya yi 'yar dariya.
"Matsoraciyata, na tabbatar kin tsorata. Shikenan saida safe, kiyi mana adduar fa."
  "To."
Daga haka sukayi sallama. Ta bi wayar da kallo tana murmushi. A karshe ta ajiyeta gefe, mikewa ta yi ta yi nafila sannan ta karanta istihara tana kallo a takarda kafin ta shafa ta kwanta.
                 WASHEGARI....!!!!
 
Cikin ikon Allah ta tashi da jin kwarin gwuiwa a zuciya da gangar jiki, kaso sitti na damuwarta ya ragu.
   Bayan Magriba ya shigo gidan, kai tsaye sashensa ya soma nufa. Bayan ya yi wanka ya nemi Ummi a waya, tana zaune tana harhad'a kayanta sanin da ta yi cewar gobe Asabar kuma a ranar Hajiya ta sanarmata shine na komawarta Kano, wayar ta katseta. Hannu tasa ta dauka, tasan ko waye mai kiran, gabanta na dukan tara-tara ta dauka da sallama. Ya amsa sannan ta gaisheshi.
  "Ki shirya Ummi, na dawo ina sama, da zarar na kammala abinda nakeyi zan sauko mu je."
  Ji ta yi kamar ta saki fitsari, ta daure ta gyada kai don bakinta ya yi mata nauyi. Shaf ta mance ma waya ce suke yi.
  "Ummi, meyafaru kuma?"
Ya tambaya a sanyaye. Sai lokacin ta dan samu ta yi magana.
"Bakomai, zan shirya."
Ya yi murmushi mai sauti.
"Ko kefa."
  Daga nan sukayi sallama. Ta yi k'uri tana duban wayar kafin kuma ta ajiyeta.
"Allah ka saukaka mana." Ta fada a fili, tana mai amsawa kanta. 
     Shigowar Binta ya katseta, ta amsa sallamarta. Binta ta k'araso.
"Naga fa Yalla6ai ya dawo."
Ummi ta yi murmushin karfin hali. 
"Munyi waya yanzu, yana nan kan bakansa, yanzun ma cewa ya yi na shirya."
  Binta ta jinjina kai.
"Sai ki tashi, hakanan za ki je kedai kiyita addua a ranki."
  Ta saka kayan, Binta ta gyaramata fuskarta, ta yi mata daurin dankwali mai hawa-hawa irin na zamani. Ta taimaka mata da sanya dan kunne da sark'an. Sai kuma ta saki baki tana kallonta.
  "Masha Allah, wallahi Ummi na k'ara ganin abinda Yalla6ai ya hango wajenki, Ummi bakiyi kalar 'yan aiki ba."
  Ummi ta girgiza kai bata iya cewa komai ba don a yanzun ita kadai tasan yanayin da ta ke ciki. 
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  65
  Mik'ewa ya yi ya koma daki ta bishi da kallo cikin jin wani shauki na kaunarsa.
  'Kaico, Yaya Faruk an kusa rabamu.'
Ta fad'a a ranta, jikinta yana bata cewa komai ya zo karshe, watakil harda zamanta cikin zuri'ar tasu gaba d'aya, tasan maganar Antinta ya kusa tabbata wanda ta ce.

'Karki manta matsayinmu awajen mutanen nan, mu 'yan aiki ne, ba su daukemu komai ba face wannan Ummi. Bar ganin suna mana dariya, duk sadda muka bari wasu lamura suka afku ranar zasu tunamana cewar mu kaskantu ne awajensu, ranar zasu tunamana matsayinmu na marasa galihu.'
   Hannunsa ta ji saman fatar fuskarta yana sharemata ruwan hawaye. Ta dubeshi, fuskarsa kai ka rantse bai ta6a dariya ba. 
  "Kinaso muyi fad'a kenan, na tsani nayita nanata magana d'aya. Karki so ki ji yanda nakejin zuciyata idan kina kuka, amma ke naga kamar kin fison damuwata."
  Karo na biyu da ta ji tana son fadamishi damuwarta.
"Kayi hakuri Yaya Faruk, saidai gani nakeyi kamar an kusa yimin katanga da kai."
   Ya zubamata ido baice uffan ba, hannunsa tuni ya sauke daga saman fuskarta. Can kuma ya soma magana.
"Fata nagari lamiri, ki saka a ranki in sha Allah babu wani abu da zai yanke alak'armu har ya zuwa aurenmu da rayuwar auren. Banaso kina kawo komai a ranki. Yau idan da dama, kada ki rage bacci ki tashi mu yiwa junanmu addua akan Allah Ya za6amana abinda yafi alheri. Kin iya karanta istihara?"
  Ta girgiza kai.
"Ban iyaba, saidai ina da Hisnul muslim." 
  Ya gyada kai.
"Ki yi adduar istihara a yau Ummi, in sha Allah zamu ga daidai a lamuranmu. Ga wannan."
  Ya mik'amata wata leda, ta sa hannu ta kar6a. 
   "Shi nakeso ki saka gobe idan na kiraki a waya, kinji?"
Ta gyada kai.
"Yauwa."
Daga nan ya sallameta ya yi mata rakiya har suka sauka daga matattakala sannan ya tsaya ta wuce.
"Zan kiraki." Ya fada da muryar rad'a. Ta dubeshi ta murmusa ya yi mata alamun (kiss) da baki, a kunyace ta wuce da sauri. Daga haka ya koma sama.
   Bayan ya kammala dukkan wasu ayyuka, ya soma duba kyaututtukan da yan uwa da abokan arziki suka ba shi, sai a yau ya samu wannan damar. Turaruka sunfi komai yawa, agogo kuwa kusan biyar ya samu, wasu kuwa kayan kwalam ne har da katina kala-kala. Hankalinsa ya kai ga na Ihsan, yasa hannu ya dauka ya bude. Kamshi ya soma ziyartar hancinsa....!

  Wani hadadden agogo ne sai kuma zobe na azurfa. Murmushi ya yi sadda ta ci karo da kati mai dauke da kalaman so. Ya bude ya karanta. 
   
 "My friends told me that falling in love would be the most beautiful feeling in the world. After I fell in love with you, I realized that even the most beautiful feeling in the world would look ugly against your love. Frm Ihsan Modibbo."

   Ya ta6e baki kadan, ya cigaba da daga sauran katinan, duk kalamai ne na nuna soyayya. 
   'Ya tabbata tana sona din kenan?' Ya ayyana a ransa kafin ya lumshe ido. Baya fatan shiga matsala saboda ita, a rayuwarsa bai ta6a shaawar kasancewa da kowace mace ba face Umminsa, ta makaro, bayajin zata samu wani gurbi a zuciyarsa, saidai kuma ta dan ba shi tausayi.
Ya dan ja guntun tsaki sannan ya mik'e ya tsallake kayan ya shiga harkar gabansa.
     
Ummi kuwa tana shiga daki ta tarar Binta na zaman jira. Binta na ganinta ta mike ganin yanda jikinta ya ke duk a sanyaye.
  "Lafiya?" Ba ta ce uffan ba, sai kayan da ta ajiye saman katifa ta zauna, batasan lokacin da kuka ya kufcemata ba. Binta wacce ta sandare tana kallon waya hankalinta ya komo ga Ummi.
"Me ya faru wai? Ki gayamin don Allah mana."
   Ita dai Ummi kukanta ta ke, ji takeyi inama yau ace mahaifiyarta na raye, ta rungumeta ta rarrasheta ta kuma bata shawarar da zai taimaki rayuwarta. 
  "Allah Ya ji k'an ki Ummana, Allah Ya yi rahma agareki,  na taso ban ta6a jin dumin uwa ba, na taso cikin wahala da tsanani na rayuwa har zuwa sadda aka maidani 'yar aiki. Babu wani mahalukin da ya ta6a rungumeni ya ji matsalata ya rarrasheni ya min addua acikin shak'ik'aina, Babana bai ta6a tarana ya yimin fad'a akan rayuwa ba, ko sau daya bai ta6a sakarmin fuska ba, asalima kyamata yakeyi, bai ta6a tambayar Ummi ko kin ci abinci ba, Ummi zan saki makaranta, Ummi ki kula da kanki, Ummi ki tsare mutuncinki, ko sau daya babu wani cikin yan uwana da suka ta6a nunamin kulawa ko k'auna. Babu, babu su Ummana, Ummana nasan da kina raye da wasu lamuran zasuyi sauk'i agareni, ayau ga wata rana babba da nake bukatarki Ummana, saidai kinmin nisan da bazan iya kamoki ba, kin koma ga Ubangijinmu da ya fini kaunarki, babu wani da ya ta6a ban cikakken tarihinki da kyawawan dabi'unki, asalima saidai ayita aibatamin ke, ana miki kazafi. Nayi rashinki Ummana, Allah Ya yi rahma agareki."
  Daga haka ta k'ara sautin kuka mai tsanani, ta cukuikuiye jikinta wuri guda, a rayuwa koda a gaba wata sila tasa Antinta Amina da yar uwansu juyamata baya, koda shima Faruk zai juyamata, bazata ta6a mance da tarin kaunar da suka nunamata ba. Sun nunamata itama DAN ADAM ce. Faruk ya gwada mata cewar itama ta cancanci komai a rayuwa, ya dauketa a mutum, haka nan danginsu gaba daya, banda matsala ta Ihsan da kishiyar Mami, babu wani abu da ta ta6a fuskanta na cin zarafi cikin zuri'arsu. Watakil a gobe zama da su zai k'are. Ta daga kai tana mai duban dakin, sheshshekar kukan da ta ji ne ya tunasar da ita cewar bafa ita daya bace a dakin. Ta kai duba ga Binta, kuka takeyi kwarai. Ta share hawayenta tana mai dukar da kanta k'as.
  "Meyafaru Binta?"
  Binta wacce zuciyarta ta cika da dumbin tausayinta ta dago kai tana dubanta.
"Shakka babu ke abar a tausayawa ce Ummi, saidai ki yi hakuri, komai na rayuwa mai wucewa ne, babu abinda ya ke dauwamamme a duniya. Wataran sai labari, Ummi akwai wadanda idan kika ji matsalarsu sai ki gane naki ba komai bane, za ki gane ke lallai kina cikin rufin asiri, ina wadanda suke kare rayuwarsu a wahala babu ko digon jin dadin rayuwa? Ummi akwai matsalolin da suka sha gabannaki, wata ma iyayenta na raye uwa da uba, amma bata ji dadinsu ba ko kusa, kuma tana gabannasu. Ina ji a jikina za ki auri Yalla6ai in sha Allahu, kuma za ki ji dadi a rayuwa. Ki cigaba da mik'a lamuranki ga Allah, in sha Allahu zai magance miki. Nima ina so ki sanyani cikin layin masu kaunarki, har abada bazan cutar dake ba, wanda mukayi a baya ma, ina neman afuwarki, ajizanci ne na DAN ADAM."
   Ranta ya dan yi sanyi da jin zantukan Binta masu dadi. Haka ta cigaba da yi mata 'yan nasihu da misalai da wandanda suka fita shiga matsala kuma cikin ikon Allah ya wuce kamar baayiba. A karshe Ummi ta labartamata yanda Faruk ya ce na ta shirya gobe zai kaita gaban iyayensa matsayin wacce zai aura.
  'Tirk'ashi!' Shine abinda Binta ta fad'i a ranta
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
   
67

Ji takeyi kamar ta gudu tsabar rud'ani. Binta na sambatu tana feshe mata jiki dq turare, hakanan mayafinta shima ta bi ta fesheshi sannan ta yafamata akanta. Takalmin ta mik'omata ta sanya, banda Masha Allah babu abinda Binta ke kira don iyakar haduwa ta hadu, kai ka rantse dinkin aunata akayi. 
  "Ni ganinki nakeyi kin saje da mutan gidan, babu wani bambanci."
  Anan ne Ummi ta murmusa don gani takeyi kawai zolaya ce don Binta ba laifi akwai barkwanci. Suna nan zaune Binta ta bata baki wayarta ta dauki k'ara. Ta yi sakato tana dubanta, ganin zata katse yasa Binta mik'amata.
  "Ki d'aga mana."
Ta kar6a hannunta har rawa yakeyi ta d'auka. A kunnenta ta kara, bai bari ta ce komai ba sai cewa da ya yi.
  "Fito."
Ji ta yi cikinta ya bada wani sautin k'ululu. Tuni ya katse kiran, ta mik'awa Binta wayar sannan ta dubeta idanunta har sun ciko da kwalla.
"Don Allah ki tayani addu'a."
Tausayinta ya kama Binta, Binta ta rik'e hannunta.
"Allah Yana tare da ke, na tabbatar zai taimakeki, ki saki ranki. Komai na Allah ne."
  Ummi ta mike jikinta a sanyaye ta fita. Ido hud'u sukayi da shi yana tsaye a bakin matattakala ya sanya kafarsa daya jikin bango yana danne-dannensa a waya. Ya yi mata kyau kwarai dagaske haka kuma ya bata mamaki, sai kace wasu Amarya da Ango duk yasa su yin shigar kaya masu kyau, shi dinma wani boyel fari k'al yaa sanya da hula wacce ta dace da kayan.  Tunda idanunsa suka sauka akanta, ya kasa daukesu, daskarewa ya yi a wajen kawai don  ya yi kamar zuciyartasa ma tsayuwar ta yi. Haka har ta k'araso wajenshi ta tsaya gefe tana wasa da jelar mayafin. Yasa hannu ya dago ha6anta, idanunsu cikin juna sannan ya kauda hannunsa.
  "Kinyi kyau matuk'a."
  Ta lumshe ido gami da kauda kanta cikin bugun zuciya mai sauri. To Faruk ina wani kyau a wajenta idan aka had'asu? Gaba daya ganinta ta keyi wani tsami akansa, ta k'ara raina ajinta kwata-kwata, har ta hangowa kanta irin kyamar da za'a nunamata yau. Watakil ma su Ihsan su yi mata dariya. Idanunta ya yi kwal-kwal. Hannu ta ji yasa ya janyo mayafinta ya dan rufe kusan rabin fuskarta da shi.
  "Muje." Ya yi maganar cikin dusashshiyar murya. A hankali suka soma takawa, Faruk shi kansa dakewa yakeyi don ba shi da yak'inin samun goyon baya, yana dai ji a jikinsa kawai zai yi nasara idan Allah Ya so.
  Haka har suka shigo falon Hajiya, babu kowa, daman hakan yafi buk'ata, yasan a wannan lokacin Hajiya na sashen Daddy, kai tsaye kofar zuwa sashen Daddy ya shige. Anan kofar falon ya dakata gami da umartar Ummi da tsayawa anan. Ba musu ta tsaya, ta bishi da kallo har ya shiga da sallamarsa, kirjinta ta dafe jin irin yanda ya ke bugu fiye da baya, addu'o'i kawai ta ke karantowa. 
  Daddy da Hajija suka amsa sallamar dan nasu fuska a sake. 
    Ya karasa yana taku a kasaitance ya zauna a gefen kafafun Daddy ya gaishesu. Suka amsa suna k'are mishi kallo. Daddy ya kasa hak'uri ya tofa.
  "Wai ni kodai wajen surukartawa za ka tafi ne? Wannan ado haka?"
  Ya shafi k'eyarsa da murmushi saman fuskarsa, Hajiya na dariya.
  "Daddy na je na dawo, kuma tare muke da ita ma yau za ku ganta."
  Sai Hajiya ta hau salati.
"Kai Sadaukina, haka kuma akeyi babu sanarwa? Maimakon ka fad'amin a shirya?"
  "To yanzu dai ai magana ta k'are tunda daman ya sanarmana a satinnan zai kawota, kinsan halin d'annaki komai nashi daban ne."
  Cewar Daddy yana duban matarsa kafin ya maida dubansa ga Faruk.
  "Tana ina ne?"
Faruk ya dubesu, su dinma shi suke kallo fuskokinsu a sake. Hakan ya k'ara mishi wani k'arfin gwuiwa, ya mik'e tsaye ya nufi hanyar waje. 
  Ya dubi Ummi wacce ya tabbata a rud'e ta ke. 
  "Addu'a zakiyi, Allah na tare da mu."
Ya fada cikin muryar rad'a. Ta gyada mishi kyau kafin ya bata hanya.
"Bismillah."
  Dagowa ta yi ta dan bude fuskarta ta dubeshi kamar zata yi kuka, ya jefeta da kallo mai sanyaya jiki, dole ta maida ta rufe fuskarta sannan ta saka k'afa da sallama, shima ya biyo bayanta. Iyayen suka amsa fuskarnan a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login