Showing 126001 words to 129000 words out of 158267 words

Chapter 43 - Dan Adam Book 1 Complete Hausa Novel

a cigaba har dai a karshe ya fita sakamakon Daddy da ya yi kiransa ta waya yana nemansa, wannan ya sanyashi tafiyar dole.


Kwance ta ke tana faman juyi, can kuma idan ta gaji ta ja tsaki, wai meyasa haka ne? Ina ita kamarta ina kuma wani dan kauye? Meyasa ta kasa daina ganin hotonsa a kwayar idanunta, ta mike zaune gami da jingina da katakon gadon, batasan sadda hawaye ya zubomata ba, ba don komai ba sai don takaicin wannan lamari, abin kunya ne babba agareta, ta ja wawan tsaki cike da jin haushin kanta, wannan kuwa abu ne da bazata ta6a bari ya yiwu ba, wai ta ce KO A MAFARKI....! Ta yi adduoi ta shafa sannan ta kwanta, har dai bacci ya yi awon gaba da ita.

Washegari tun Asuba da Ummi ta farka bata koma ba, karfe bakwai zasu wuce, kai tsaye wanka ta fad'a ta sanya leshinta ruwan hoda marar nauyi.
Karfe bakwai kuwa aka fidda akwatinta, bayan sun kammala karyawa, Faruk har dakinta ya zo kafin ya wuce ofis suka yi sallama, haka ta wuce cikin kewarsu da kuma d'okin zuwa ga mahaifinta da kakanninta...!!!


      
   DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

    110

Sai wuraren karfe daya suka isa Gombe, kai tsaye Tudun Wada suka nufa, da yaran gidan ta soma tozali a kofar gidan, da gudu suka shiga ciki domin sanarwa jama'ar gidan, dariya kawai ta yi sannan ta ja jakarta ta hannu ta yi ciki, a zaure suka yi kici6us da Anti Halima wacce ta taho ganin ko dagaske suke, ai kuwa ta rungumeta suna murna gami da lale marhabin da Amarya. Suka karasa ciki, ganin Dada tsaye tana rarraba idanu na son ganin ta inda zata 6ullo yasa ta k'arasawa a guje gami da rungumeta, Dada ta dan tureta cike da farinciki. Kafadarta ta dafa.
"Use Hasiya, kun sha hanya."
Dariya ta yi. Haka suka yi ta nan da nan da ita kamar wannan ne ganinsu na farko da ita. 
   Saida ta gabatar da sallah sannan ta isa dakin Malam, yana kishingide yana gyangyadi saman darduma, sallamarta ce ta sanyashi wartsakewa yana mai amsawa fuska a sake. Bayan sun gaisa ne ya ke tambayar mutan Abuja. Bata jima sosai ba ta koma ciki. Sai yamma iyayensu maza suka dawo daga kasuwa, alokacin har direban da ya kawo Ummi ya juya bayan ya gabatar da sallah ya ci abinci. Malam Balarabe ya yi farinciki da ganin diyartasa. 
Sai bayan Magriba suka samu ke6ewa da Malam Balarabe, anan ta ke jin labarin zuwansa Ringim bayan tafiyarta, inda ya sanya gidansa a kasuwa, ya hada kan kudadensa ya sallami Haruna yaronsa mai tayashi aikin balangu a kasuwa sannan ya taho da zummar idan an siyar Malam Yahuza zai aikomishi da kudaden. Hakan ya yi mata dadi, shikenan sun rabu da Ringim kenan. Ya shiga bata labarin kiran da ya samu ta waya daga Daddy cewar kada ya yi komai na kayan daki shi zai yi don shima diyarsa ce, ya sanarmata koda ya ji hakan, ya ji abin banbarakwai, ya so tambayarta ta waya saidai yasan ba lallai ta samu labarin, koda ya sanarwa yan uwansa, su kansu sunyi mamaki, Malam da kansa ya sanya suka kira Daddy. Bayan an gaisa ya ce. 
   "To kai Alhaji ayi haka? Kwa daukarwa kanku nauyi har haka?"
Dariya Daddy ya yi ya nuna zai iya yiwa Ummin haka koda ace ba dansa za ta aura ba, acewarsa itama diyarsa ce." Jin haka har Malam saida ya yi kukan farinciki, ya yi mishi godiya da binsa da kyawawan addu'o'i, Daddy ya nuna bakomai, tunda har suka bawa dansa aurenta sun mishi komai a rayuwa. 
  Ummi jin dukkan lamarin ta ke yi wani iri, jikinta ya yi sanyi, ko kusa bata da masaniya kan abinda ake ciki a Abuja. 
  "Kada ki bani kunya Hasiya, ki yi kokarin bin mijinki tsakani da Allah, tabbas Umar yaro ne nutsastse, ki godewa Allah don kuwa kin yi babban sa'a, yana sonki kuma iyayensa suma suna sonki, ki zauna da su da zuciya daya, wanda zai yi maka haka a rayuwa lallai bai kamata ka yar da shi ba."
Har da hawayensa alokacin da ya ke fadin haka gareta, ita kanta saida ta share ruwan hawayen, acan kasan ranta kuwa, adduo'i ta ke ta jerowa ga Daddy da iyalinsa. 
    Kwanan Ummi biyu a Gombe, su Hajiya sun wuce Adamawa gaba dayansu har Modibbo. Saidai banda su Ihsan da sauran yaran masu zuwa makaranta da kuma surukansu. 
   Ita kuwa sosai su Abida suka shiga gyarata, duka-duka bikin a wannan lokacin bai fi saura kwanaki goma sha biyar ba, a bakin Dada ta ke jin cewa har mutanen Adamawa suma zasu zo. Dattijuwa Binta, tsohuwa mai ran karfe kenan Yaya ga Dattijo Manu(kakan Ummi) da zuri'arta wadanda rabonsu da Gomben tun rasuwar Inno.
    Gaba daya sai ta k'ara ji ta d'okantu da son ganinsu. 

    Duka-duka su Hajiya kwanansu biyar a Adamawa suka dawo har da wasu cikin yan uwansu wadanda sai bayan biki zasu koma, wasu kuwa sai dab da biki sannan zasu iso. 
  Shirye-shirye sosai akeyi, ba ga nan Abuja da mutan Kano ba, ba kuma ga can Gomben ba. 
    Amarya Ummi ta murzu iya murzuwa, idan ka ganta sai kace bata ta6a shiga rana ba tunda ta zo duniua tsabar kyau da murjewa da fatarta ta yi, ga shi kuma daman lokaci ne na damuna ba ranar ake yi sosai ba. Kayan gyara mace kuwa, har gajiya ta ke yi da sha, don Dada bata barta ba, haka suma surukan Dadan, (Anti Halima da Abida), daga sun ke6e da ita suke duramata. Kusan kullum sai sun kai ukun dare suna waya da ango wanda ya nuna gaba daya kewarta ya isheshi, har rantsuwa ya yi mata akan wani lokacin ji ya ke kamar ya yi tsuntsuwa ya biyota Gombe. Dariya kawai ta ke yi wani lokacin, wani lokacin kuwa tausayi ya ke bata. 
  Amina kuwa, tun kafin tafiyarsu Hajiya Adamawa ta kirata akan ta dawo.  Ana sauran kwana biyar biki da yamma tana zaune ta gama yin sirace na gyaran fata, hannunta rike da kofi wanda aka kad'a madara da wani gumba, su Abida sun sanyata gaba har da wasu yayyunta daga Jar Kwami akan sai ta shanye, kiran Amina ya shigo wayarta, dakyar suka bata wayar don da fari sun k'i wai sai ta shanye, wayar duk ta koma yaluwa, aun gaisa ta ke sanarmata cewar ta iso Gombe tana tasha wai ta yi mata kwatancen unguwarsu, ai Ummi daskarewa ta yi a zaune don mamaki, gani ta ke wasa kawai ta ke yi, saida ta rantse sannan ta saki dariyar murna.
  "Bari na bada a yi miki kwatance."
Ta mikawa Abida wayar, nan ta kwatantawa direban Adaidaitan. 
  Ummi kasa zama ta yi, zata mike suka dakatar da ita, batasan sadda ta kwankwade maganin ba don hankalinta ya tafi ga Antinta. Dariya suke mata saidai bata ko sauraresu ba ta sanya dogon hijabi ta yi sashen Dada cike da mamakin yanda akayi Hajiya Mama ta barta ta zo.
  "Dada! Dada!!"
Suka yi kici6us a kofa.
"Lafiya Boddo?"
  Ta rungumeta.
"Ga Anti Amina nan zuwa, ta Kano wacce na baki labarinta."
Itama Dadan ta hau farinciki.
"Kai Alhamdulillah, shiga ki yi wanka kafin ta karaso, bari na hadamiki ruwan dumin."
Ai da gudu ta shige ciki ta dauki roban sabulunta, sosanta shanye a saman igiya ta ja, Dada da kanta ta hadamata ruwan wanka ta fad'a. 
Tana daga bandaki ta ji muryar Amina na gaggaisawa da mutanen gidan dake mata lale. Ai sauri-sauri ta shiga yi, tana fitowa ta ajiye bokitin sabulun anan kofar dakin Dada, hannunta rike da soson ta fada ciki sai jikin Amina, suka hau dariya. Dada ta kai mata dundu a baya.
"Ke kam Allah Ya sauwaka miki, kai Boddo, a jik'e fa ki ke."
Ummi na dariya ta mike zaune,
"Wallahi murnar ganinta ne, ta yimin bazata." Dada ta kar6i sosannata ta fita tana dariya. 
   Amina wacce ke dubanta fuska a washe ta kamo hannunta ta zauna gefenta.
"Wai kece kodai mafarki nake yi?" Cewar Amina.
"Ai Anti ni zan ce ina mafarki ma wallahi, ban ta6a zaton za ki zo Gombe [truncated by WhatsApp]
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

111

  "Asiri ya tonu, bayan dawowar su Mami daga Adamawa da kwana biyu Abban Adnan cikin dare idanunsa ya gane mishi Hajiya Binta na tone-tone bayan windon dakinsa, bai ma gane kowacece ba, Mami ce a dakinnasa ita dinma idanunta biyu, ganin ya fita da sauri ta mara mishi baya, saida suka zagaya suka isketa tana kokarin binne wasu layu, ke wallahi idan karshen mugunta ya zo babu mai iya tserar da mutum idan ba Allah ba, kuma daman shi Allah ba Ya zalunci, mata ta rude, har kusan sakinta ya yi, itace har da durkusawa neman alfarma wajen Mami akan ta taimaka ta tayata rokar gafararsa. A daren bai sauraresu ba, kiris ya rage a saketa saidai ta ci darajar 'ya'yanta, dakyar da sudin goshi ta samu ya yafemata, saida Mami ta sanya baki sosai. Amma fa nima ina daga kicin ina aiki na ji Mamin suna hira da Hajiya Mama don gida ta zo ta sameta. Tun daga lokacin kuwa jikin Hajiya Bintar ya yi sanyi, har sashen Mami ta je ta fayyacemata mugun kullin da ta yi mata Abba ya juyamata baya da kuma yanda ta so had'e baki da ke amma ba ki bata goyon baya ba, tana kuka ta nemi gafarar Mamin, yanzu ba ki ga idan kin je gidan ki ka shiga sashenta yanda zata kar6eki ba, wallahi sai kinyi mamaki, duk ta yi sanyi har sashen Mami ta biyo Hajiya Mama suka gaisa, Iklima itama yanzu duk ta chanja kodayake ance ita wani saurayi ne ya yaudareta ya kaita gidan masu zaman kansu zai yi mata fyade, kinsan Iklima yar son zuwa party, dakyar Allah Ya kwaceta a hannunsa sakamakon zuwan yan sanda kame, aka hada har ita, saida ta kwana biyu a kaso Abba ya ce babu inda zai taka ya je belinta, sai fa can cikin yan uwan Ummanta ne suka je suka yo, ranar kuwa ta ci duka wajensa don har  makaranta ya hanata zuwa yanzu ya ce aure zaiyi mata."
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

112
Sanye ya ke da shadda kalar sararin samaniya sai hula shima bulu, sai murmushi ya ke bugawa yana gaisawa da yan uwa har da mikawa Dada hannu suna gaisawa gami da dariya.
Ummi bata iya motsi ba hakanan ta kasa cewa uffan saida ta tsinci muryar Amina na fadin.
"Wai daman *ABUBAKAR* dan uwa ne gareku?"
  Ta girgiza kai sannan ta maida dubanta ga Amina kamar wata doluwa. 
  "Wallahi bani da masaniya nima."
Basu kai ga tsinkewa da lamarin ba saida suka ga shigowar Alhaji Kabiru Jimeta da sallamarsa. Mamaki, rud'ani da tsananin faduwar gaba duk suka tararwa Ummi da Amina, aka rasa mai magana cikinsu har wasu cikin mutanen Jar Kwami suka shigo wasu rirrike da jakunkunan kaya. 
  "Wai ina Amaryar?" Cewar wata mace da zata kai shekaru arba'in a duniya. 
   Da sauri ta ja baya daga jikin windon tana sussunne kai, wata gwaggonta ta riko hannunta tana dariya.
  "Oh 6uya ki ke? To fito nan ga uwarki da ba ki sani ba, Safina, sannan kuma (ta nuna wata doguwa mai rike da bebi a hannunta, bazata wuce talatin da tara ba) itama uwarki ce Nafisa sunanta, duk yaran gwaggonki ce Binta."
Sukayi dariya, wacce aka kira da Nafisa ta ce.
"Maza fito na kaiki ku gaisa da Innarmu ta ga Innonta ta dawo."
Amina ta hau janyo musu ita don ta mak'ale a bayanta, ita kanta dauriya kawai ta ke yi saidai jikinta ya yi mugun sanyi, tambayar da kowannensu ke yiwa zuciyarsa bai wuce na son sanin dangantakar Alhaji Kabiru da mutanen gidan ba. 
  Ummi na kallo suka ja ta har rumfar Dada inda ake zazzaune ana gaisawa, kan Ummi a k'asa yayinda aka zaunar da ita gefen wata dattijuwa wacce shekaru suka ja saidai garas tana gane mutane sannan tana fahimta. Da harshen fulatanci ta ji wacce ta zaunar da ita ta yi magana. Abinda ta fada ne ya janyo hankalin sauran bak'in duk suka dubeta, Abubakar da hankalinsa ke kan wayarsa yana kokarin turawa uwargidansa sak'on isowarsu lafiya, shima ya dago kai yana duban wacce aka kira da Amarya kuma jininsa mai kama da Innonsa. 
  Mamaki k'arara ya bayyana saman fuskarsa, a yayinda shi kuwa Alhaji Kabiru ke kallon Ummi cike da al'ajabi na kamanninta da Antinsa Inno wacce a girme ma ya girmeta saidai duk da hakan kanwa ce ga mahaifiyarsa GWAGGO BINTA babbar Yaya ga Manu Lamido uba ga marigayiya Hasiya...!
    Hannun Gwaggo Binta na rawa ta kamo na Ummi tana mai rike kafadarta da hannun damanta.
  "Sannu Hasiya, shakka babu wannan jininmu ce diya ga diyata Hasiya, ashe da rabon mu k'ara sanyaki a idanunmu?"
Sai ta janyota jiki tana hawayen farinciki ga kuma bakinta da ya k'i rufuwa don murna.  
   "Ke ce?"
Cewar Abubakar da mamaki yana nunota da yatsa, hakan yasa duk wanda ke fahimtar hausa sosai ya kalloshi don ba kowa cikinsu ne ke jin hausa ba, Malam Balarabe da Alhaji Kabiru har suna hada baki wajen fadin.
  "Ka ta6a ganinta ne?"
Ya jinjina kai yana murmushi mai bayyana hakora.
"Tabbas Dad ita nace maka na gani fa a gidansu Abban Kano mai kama da Inno. Saidai..."
Sai kuma ya yi shiru, har lokacin bai bar mamaki ba. Kallon Ummi kawai ya ke yi kamar Innonsa, Innonsa Zahra mai matukar kaunarsa, sun shaku sosai, ayi wasa ayi dariya, yana mata kallo kamar wata sa'arsa kuma kanwa gareshi don koda zata girmeshi ba da wasu shekaru na azo a gani bane sannan gajeriya ce bata da jikin girma. Sune har guje-guje, komai na shawararsa idan ya dauko to fa da Inno zasuyi ta, sau da yawa kafin iyayensa su san wani abu nashi, Inno ta sani don gaba daya tare suke zaune har Gwaggo Binta a gidan Baffansa Kabiru.
   Bai mantawa ana shirin bikinta ta yi bankwana da duniya, mutuwar da sosai sun ji ta a zukatansu don har kwantar da shi ta yi, hakanan mahaifiyarsa Hajiya Salma ita kanta saida ta yi kamar ba zata rayu ba tsabar razanar da ta shiga sanadin mutuwarta. To me ya kaita Kano? Me kuma ta ke yi gidan su Ihsan? A ina Faruk ya ganta ya ce yana so?
   Wannan shine tambayoyin dake  yawo a kwanyarsa da ba shi da mai amsa mishi. 
  Kowa a wajen ya cika da mamaki banda wadanda sukasan silar zaman Ummi a Kano da Abuja.

    Bayan gama gaggaisawa mazan suka fita, itama Gwaggo daki ta koma.  Ummi ta ja Amina suka koma sashen Anti Halima.
  "Kinga ikon Allah ko Anti?"
"Allah kenan, ashe duk firiritar Ihsan kuma danginku za ta shigo? Wannan lamari saidai Allah, ya dangantakar ta ke?"
  "Gwaggo Binta kakarsa uwa ce ga Ummana. Nima tana matsayin kakata."
  Amina ta hau gyada kai sai kuma ta soma dariya Ummi na tayata tana tambayar ko lafiya.
Girgiza kai ta yi.
"Wallahi Ihsan gwanar wulakanci ce ta ban tausayi kawai, yanzun ko da wane idon zata kalleki? Shiyasa a duniya ba'ason ka dunga wulakanta DAN ADAM don bakasan mai yi maka rana ba gobe."
   Murmushi Ummi ta yi kawai tana kokarin goge wayarta wacce ta koma yaluwa saboda kurkum.
    Sai dare Abubakar ya samu damar ke6ewa da Ummi sadda ita da Amina suka je kai mishi damammiyar fura inda ya je zaune tare da Gidado (wanda shima bai jima da zuwa ba daga Jar Kwami) suna hira. Kusan ma a kyau har Gidado ya tsere Abubakar saidai shi zai nunamishi wayewa da hutu sosai da kuma zurfi a ilimin boko don kuwa shi Gidado iyakarsa sakandire ya watsar ya fada kasuwanci, Kano ya ke zuwa saro kayan sawa na mata ya ke siyarwa, sosai yana samu don asirinsa a rufe. Matarsa daya Aisha wacce sukayi auren soyayya sai dansu da baifi shekara daya ba don duka-duka aurensa ko shekara biyu baiyi ba saidai idan Gidado ya sanya sutura sai ka rantse ba mazaunin Jar Kwami bane musamman idan Abubakar ya mishi aiken suturu daga Adamawa. 
    Da sallama suka shiga suka ajiye furar kafin su gaishesu, suka amsa. Ummi ta dubi Gidado da murmushi saman fuskarta.
   "Yaushe ka zo?"
Shima murmushin ya mayarmata.
"Ko awa biyu cikakku banyi ba."
Ta gyada kai sannan ta mike zata bi bayan Amina wacce daman suna ajiyewa ta fito, Abubakar ya dakatar da ita.
"Ummi."
"Naam." Ta amsa tana dubansa gabanta na dukan tara-tara.
"Please ke ce dai wacce na sani a Kano gidansu Ihsan?"
  Ta gyada kai a sanyaye. 
"To meya kaiki can?"
Gidado ya cafe.
"Au ka ta6a ganinta acan kenan? Ai ta zauna can."
Jin haka Ummi ta mike da sauri, tana jin Gidado ya soma labartamishi yanda lamura suka kasance ita kuwa tuni ta soma zura takalminta, suka kama hanya da Amina tana sanarmata yanda akayi, Amina murmushi ta yi.
"Allah Sarki." Shine abinda ta ce kawai. 
                  ***   ***   ***
                     ABUJA
 Tun bayan sati da kwanaki da tafiyar Ummi, Ikram bata cikin nutsuwarta, gaba daya ta rame ta koma wata shiru-shiru, koyaushe bata da aiki sai na kuka ga wani ciwon so da ya addabi zuciyarta har tana ji idan bata samu cikar burinta ba zata iya rasa rayuwarta. Har mutanen Kano suka iso Abuja bata da walwala sosai, kowa sai ya tanbayeta damuwarta amman ta nuna ba komai kawai bata jin dadi ne, Ridwan har dubata ya yi ya kuma gano damuwa ce kawai ta sanyawa kanta, tanbayar duniya ya yi mata amman babu amsa. Daidai da dinkin ankon da sukayi kala biyu ya yi mata yawa sakamakon ramar da ta yi. 
  Yau ma babu kowa a gidan, Hajiya sun fita tare da su Mami ganin gida, ita kuwa Ihsan da su Maryam sun tafi gidan Baraka can zasu wuni har da wasu cikin bak'in Adamawa, manyan kuwa suna can kwatas suna hira da Hajjah wacce ta zo ko don jikanta. Tana kwance daga ita sai shimi da dogon wando wanda da kadan ya wuce gwuiwa, wuf ta mike tsaye, kai tsaye kofa ta nufa, babu kowa a falon, hakan ya bata damar zarar mukullin kofarta wanda ana iya amfani da shi wajen bude kofar dakin Baraka inda ya zama na Ummi a yanzun. Ta bude dakin ta shiga gami da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login