Showing 30001 words to 33000 words out of 82431 words
kashewa bazan iya da sababbin kalaman da Yaya Ishaq ya koya a kaina ba,Bani da wajen sauke su ballatana su samu muhalli sai ga shi ya kara kira sai na kwalama Amir ya kira yana zuwa na mika masa wayar ina fadin"Baban ku ne,jeka ku taru da yan'uwanka zai yi mgana da ku"
Da Murna ya karb'a suka fita falo ina jinsu suka Dauki wayar suna ta Bidirinsu gajiya yayi ya kashe wayar ko kudin ne kila suka kare, tunda ya Fahimci ni din ne bana bukata jin mganarsa sai ya shafa ma kansa lafiya.
Bai dawo ba sai da ya kwashe kwana Goma tsakanin miji da mata daman sai Allah,har ga Allah bana son auran Zainab ya kare saboda haka,ance ba'a son kishiya ammh ni Fa'iza ina kaunar Zainab da zuciya d'aya ta karbeni ta mutumtani fiye da yadda wanda ya ijiyeni ya mutuntani,bawai don tana ma ya'yana Hidima ba a'a ance Halin mutum ka fad'esa bata da wulakanci bata da girman kai,tunda nake da ita bazan ce ta taba min wani abu da ya sosa min raina ba. tana kaunata tana kaunar ya'yana nima shiyasa nake kaunarta da ya'yanta bana fatan kuma auransa ya samu matsalan ina addu'an ya kauda dukkan Fitina ya Dauwamar da su har abadan saboda sun fi dacewa da juna.
Zainab ta aiko ma da yara Tsaraban kayan sallar da tayi musu yan kanti harta Amir yan kanti ta siya masa ni kuma sai ta aiko min da Takalmi da Jaka da mayafi,Mama kuma Atamfa da leshi har da kud'i Badariya ma da nata Jamal ma boyel da takalmi shima uban gayya sabbin kaya ya Dawo da su fin kala Biya Mama an samu Duniya sai washe baki take tana jin dadi fadi take yi"Kaga to in da abun arziki yake zaune da digadigansa Ishaq ammh ka zauna kana wani shirme,in da ka zauna wazai biyo ka da wannan kayan arzikin..?
Shuru yayi bai mata mgana ba,yasan shi da Zainab akwai kauna da Fahimtar juna matsalan ilmin addininta Ragagge ne batasan miji yafi ubanta iko da ita ba, gani take yi da ita da miji duka suna karkashin ikon Mahaifinta ne shi kuma Daman haka yake so,kada ikon ya'yansa ya tashi Daga Hannunsa har Abada yana son komai ya'yansa zasu yi cewarsa ne da ikonsa,Ko wannan zuwan ya sake zuwa ya basa hakuri sai da ya gama gayamaasa mgana har yana fadin bai kai ba,bai kuma isa ba, kaunar da yake masa ne yasa ya aura masa Zainab ammh shi ai ba sa'an auranta ba ne Daganan yasan Allah ne ya kai shi inda za'a koya masa Rayuwar duniya indai bai santa ba.
Mama nata mgana ko jinta bai yi ya fada kogin Tunani sai da Jamal ya tabashi sannan ya dawo Hayyacinsa Mama tace"Ka daina wannan zurfin Tunanin fa"
Anty Hure da bata koma ba har Lokacin tace"Kuma hawan jini yafi kama yara yanzu ba".
Shi dai shuru yayi bai yi mgana ba Sai da Mama ta tambayesa ya mganar aikinsa sannan yayi ajiyar zuciya yace"Mganar aiki ana ta nema Mama ni ma ban zauna ba in da naji ana neman masu karatu irin nawa ina Tura Cv dina ko za'a dace.."
Mama tace"Yanzu shikenan ka rasa wanchan aikin naka.?.
Kai tsaye yace"Sai dai fatan samun wani Mama ammh wanchan sai babban Rabo kad'ai ne zai iya dawo min da aikina, shima bayan Hukuma ta wankeni daga wannan zargin"
Mama ta jinjina kai kafin tace"bakomai muna gayama Allah ko waye ya yi maka sanadin barin ka aikin ka da ikon Allah shima bazai taba samun kwanciyar hankali ba"
Aransa ko sai yace"Ba wani bane Hakkin Fa'iza ne. Allah ne yaso ni ma da Rahma ba sai na mutu ranar lahira na tashi da bari d'aya na jikina na Rinjaya na ba.Subhanallah Allah ya Tsaremu"
Sai jikinsa ya dau d'imi ya tuna wa'azin da yaji lokacin dayaje Abuja na wani malami ya na fadin azabobin da Allah ya Tanadar ma mai kuntata ma matarsa da wanda ya kara aure bai kwantanta adalci a tsakanin matansa ba ,sai yaga kamar malamin yasan shi,kamar da shi yake yi wa'azin jin wannan wa'azin ya sa tsoron Allah ya kara kamasa.
wannan azumin ya Dawo da kudirin niyar bama Fa'iza hakuri su Fuskanci Sabuwar rayuwa ammh ya kasa kwarjini Fa'iza take yi mai,sannan bata sakar mai fuska, kuma bata yadda su kebe inda ba Mutane kamar bata son ma taji dame yazo ya Lura da ita tana da'ri da'ri da shi.
Ni ko ta bangare na bansan yana yi ba, duk da ai ya fad'amin in ya dawo zamu yi mgana ammh sai na rika kauce ma haduwa dagani sai shi ko bana wani abu,in Hafsah na makaranta da yara bana yarda nayi zaman daki ina Tsakar gida ina tsiro aikace aikace sanda Sakon Zainab ya iso da kaina na kirata nayi mata godiyan Dawainiyar tayi yawa sai ta yi dariya kafin tace min"'Haka Honey yace. Ammh sai da yayi korafin ban siya ma Uwargida nata Leshin ba"
To na dai ce a bini bashi zan biya in sha Allahu"har muka gama waya ina mamakinsa wai uwargida..?lalle abunda ya baka dariya wata rana shi zai saka kuka gashi ina gani akan Ishaq kabir karofi.
Duk neman Hanyar da zai samu kaina yayi bai samu ba,na kauce ma wannan haduwar tamu,kwatsam sai ya Tsiri shigewa dakina ya kwanta saman gadona Hake hake Allah na tuba ko a zamanin baya, baya shigowa Dakina iyakarsa in kira ne ko mgana daga bakin kofa ballatana yanzu da komai ya sauya.
Ni ban ma san yana shiga ya kwanta ba,Saboda in yara sun tafi makaranta ni kuma ina waje ina aiki Dakina sai dai in nazo daukan wani abu nakan shigosa,ranar ma Zobo aka zo siya na Dubu d'aya naje neman ledojin da nakan tara acikin dirowa ta, har ga Allah ban gansa ba ina ta duba ledan sai ji nayi kafa daga bayana tana zungurin Bayana na tsorata na juyo a firigice sai kawai naga Namiji kwance a kan gadona ban ko ga fuskarsa ba saboda ya rufe kansa a tsakanin Filo gefe nayi gabana na fadi jikina ba inda baya rawa ammh bakina bai yi ihu ba sai naji nace"Subhanallah waye anan..?
Ashe yana ji sai ya Dago kansa yana Dariya ido na zaro ina kallonsa kafin nace"kai ne..?
Mikewa zaune yayi yana fadin"To da waye zai shigo miki daki ya kwanta in ba mijin ki ba..?
Sai na jinjina kai mamaki ya cikani,Ban ce masa koomai ba na koma na cigaba da neman ledata,Saboda yanzu kuma sha'aninsa nasa yafi karfin Tunanina kawai ban ankaraba sai ji nayi ya chachumeni ta baya ya rumgumeni ya hadani da kirjinsa,tudun kuguna na dukam bayansa Hannayensa Cak ya dadumo kirjina kamar ya samu wani abun har da sauke ajiyar zuciya nan da nan jinin jikina ya daina aiki ya Tsaya cak! sai na rasa ina zani tun ballatana da Bakinsa ke saitin wuyana ya na fesar min da Numfashi ko a lokacin da rabon ya'ya ke giftawa tsakanina dashi bai san wadan'an abubuwan ba. shi dai bar sa ya biya bukatarsa in ya Damesa. Ba domin ya damu da ni ya nawa Bukatan ba.?shiyasa tun a wanchan Lokacin bazan iya dora komai akan bukatawata ba, na dai san ni bakuwa ce a harkan bansan komai ba.
Yanzu da yake yi min wad'anan salon sai nake neman rasa hankalina, a yanzu ma Hannayensa suka fara kasa zuwa wajen cikina yaraf na saki hannayena jikina na rawa ban dawo Hayyacina ba sai da ya daga riga ta,ya dafa haannunsa saman marana Fatar Hannunsa ta had'u da nawa lokaci daya muka gwama Numfashi Hmmmm!!!!!"
Bai kyaleni ba,sai ma bakinsa da ya kai saman kunnena ya lasa sai da naji ji kamar na shid'e na sake dawowa,Lokaci d'aya da ya yi amfani da wata irin karuwar murya yana fadin"Fa'ii...ki zo ki tayani barciii..'"
Lokaci da'ya yana matseni a jikinsa inaji ta baya abu na dukan bayana na rikice iya rikcewa kamar wata gaula,Yana shirin ya kai hannunsa akasan zanina na shammacesa nayi kasa bai zata ba sai ya koma kan gado ya zauna Dabas ni kuma kamar wata yarinya sai na saka gudu na fice Daga Dakin, Allah yasa masu siyan zobon suna tsakar gida da sun sha kallon yadda na fito a razane,Kitchen na shiga ina Sauke numfashi har Lokacin Salon sa da Sautin muryansa basu bar jikina ba sai da na Huta sannan na samu ledan Aya na juye cikin wani Bokiti na zuba musu zobon na fita na mika musu shima ganin na gudu sai bai biyoni ba,Ranar wasan buya na rika yi masa bana son ma mu had'u,Da daddare dukkanmu muna falo shi yake koyama Amir lissafi ni kuma ina Rubuta ma Ahmad Huruful Hija'iya a wani Takarda inda zai ta maimaitawa Saboda ya iya rubutawa da karantawa,Dagowa goma sai naga idonsa kaina Lokaci da'ya yana dagamin gira da na Fahimci haka sai na daina yarda ina dagowa na yi kamar bashi ma afalon da zamu kwanta yayi ta tsiro da sani aiki ni kuma sai na saka ya'yansa daga karshe sai ya kalleni yana fadin"Fa'iza ina jin zafi ina so nayi wanka"
Ban kallesa ba nace"Amir tashi kaje famfo ka tarar ma baban ka ruwa in ya cika Hafsah sai ta Dauko"
Sai ya bata rai har Amir ya mike sai yace"Kai koma ka zauna. ke na saka in kuma baki yi shikenan"
Ina kallon rubutun gabana nace"To Abban Anum baka ga aiki nake yi ma yara ba..?
Amir ko sai ya mike yana fadin"Daada bari na cika maka"
A chunkushe ya mike yana fadin"yi zaman ka zan yi da kaina"
Dariya ta kusa kamani sai na Danne da kansa ya fita ya Debi ruwan yazo ya kai tiolet din Dakinsa, chan kuma ina Murnan na rabu da k'aya sai ga shi ya leko yana fadin"Baki shimfid'a zanin gadon da kika wanke ba ne Fa'iza..?daman yasan nayi wanki jiya kuma har da kayansa na wanke da zannuwan gado saboda bana so na shiga Dakin ya Ritsani ne yasa naki shiga na maida zanin gadon, sai kawai na kalli Amir ina fadin"Yana nan saman Dirowa dauko ka kaje ka shimfid'a masa"
Ai ban gama Rufe baki yace"Bar shi bana so'
Daga haka ya koma Daki sai da nayi Dariyan data kawomin Amir ya kuramin ido ina Dagowa muka had'a ido sai na Dauke kai ammh yaron nan sai cewa yayi"Umma Daada ne ya saka ki aiki fa..?
Sai na ware mai ido ina fadin"Eh Daadan fa sai akayi ya ya..?
Sai ya kasa mgana araina nace ji yaro da iyayin tsiya to dai har muka shiga barcin ban kara ganinsa ba ni kadai in tuna yadda ya yi jiya sai naji Dariya tazo min,Washegari da safe da ya fito na gaishe sa a dake ya amsa kayan karyawansa kuwa yana fita rakasu makaranta na shiga na ijiye mai na fito. sai da ya dawo ya iskeni ina karyawa a falo yana ganina sai ko ya zo ya zauna karshe dai tare muka ci ni dai ban sake ba sai da muka gama ne ya kalleni yana fadin"Yanzu abunda kika yi jiya kin kyauta kenan..?
Ido na waro kafin nace"Me nayi..?
Sai ya yi wani kamar maraya kafin yace"Au baki ma sani ba ko..?jiya nace ki gyaramin shinfid'a kika saka Amir ko..?
Sai na dukar da kaina ina fadin"Ai lokacin ina ma yara a karatu ne"
Ban dire ba ya tareni da fadin"Ko kina menene in na kira ki na sakaki aiki zaki ijiye kizo ballatana gyaran Shimfidar miji. Kin ga jiya kin kwana mala'iku na fushi da ke"
Mamaki ya bani na kallesa sai yace"Eh mana ai kin fini sanin haka tunda Lokacin kina gaban Mama a kwai ki da son zuwa islamiyan nan ta la'asar"
Araina sai nace ashe ya sani ganin ya nace da mganar ne yasa nace"To kayi hakuri"
Nan da nan yaji dad'i ya washe baki yana fadin"Yauwa ko kefa yar albarkata. Ina fatan in nakara kiran gyaran Shimfid'a baza'ayi min gaddama ba ko?.sai na gyada mai kai saboda ya kyaleni aiko bai barni ba. sai ya rika jana da Hira yana shigemin ni ko ina baya baya labarai har da wad'anda basu Shafeni ba abun mamaki har yana tambayata yaushe zamu je karofi mu gaida su Goggo..?
Sai kawai nace ranar da ya shirya sai yace sai weekend saboda yara.
Ban ko tsaya mamakin sa ba domin yanzu ya daina bani mamaki in dan yayi wata mganar ko ya yi wani abun.
Jamal ya yi shirin komawa makaranta acikin kayan abincin mu na dibar mai Taliya da shinkafa da man girki sai na bashi Dubu goma, biyar yayi pocket money, biyar yayi na mota nace in na samu zan bama yayansa ya Tura masa ya karba yana ta godiya har yana fadin"Allah ya kawo babban Shago Matar bro.'
Ina yar dariya na amsa mai da Ameen haka ya tattara ya tafi to yayan bai da ko sisi yana nema nema. itama kanta Maman bata da shi kawayenta duk sun gajeta ba wacce tafi bani mamaki sai Hajiya Barira bata zo ba tun bayan da Yaya Ishaq ya fito Sannan Mama ta shirya taje gidanta bata sameta ba,Kuma bata biyo sahu ba kuma bata Hakura da binsu ba shine da yagaji ya yi mata mgana fadi yake yi"Mama yanzu rayuwar nan ba irin da ba ne. In kana da shi ayi dakai daga Lokacin daka rasa bamai son rabarka ka zame masa wahala Mama.ni kaina alokacin da nake dashi abokai har da na banza kuma ai mun taimaka musu ammh yanzu ko kare bana gani ballatana kira an san bani da shi kowa Tsoron haduwa dani yake yi kada na gayamasa matsalata"
Ko nace ya taimakeni"
Mama ta gyada kai tana fadin"Uhm nagani,ammh na Dauka ko kowa zai gujeni ban Dauka harda Hajiya barira ba, ta bani mamaki kamar mafa blooking dina tayi fa"Dariya yayi yana fadin"Shi yafi komai sauki Mama bazata yarda ku hadu ba, tasan baki da shi yanzu zaki yi Tunanin samun wani abu daga barayinta, a baya kina da shi kuna nima ina dashi kinga dole ta rab'eki ki kama kanki da kowa kawai ki Rumgumi kaddaranki Mama kina gani ko a yan'uwa sai wanda yaga Allah ne yake tunawa dakai in ka shiga Halin babu, sai kuma wanda ma kake tsammanin zai tsaya maka ranar da baka da shi, sai kiga shine ke baya baya dakai. wanda ka gujema Lokacin da kake da shi shine in ka shiga Halin Rayuwa zai taimake ka"
Mama na hawaye tace"Hakane wlh nagani Ishaq"
Tana tuna Hajiyar Dala ko wayarta bata son dauka yanzu. Ammh Goggo ko bata zo ba zata aiko da Sakonta tabbas Lokacin da suke da shi basu mu'amalance ta da kyakyawan mu'amala ba,ammh ita bata rike su ba ta Duba zumunci ta kuma bi Umarnin Ubangijinta..
Nan ya fice yana fadin"to haka halin mutanen duniya yake Mama Lokacin da kake da shi ayi da kai, in kuma baka dashi ayi da wanin ka"
*Janafty*
*KNKB2009*
*Ki biya ki karanta cikin salama,Kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta min littafi,Sannan kada ki yad'amin shi,Pay N500 regular ko kuma VIP N1000, Via Jamila Umar Gt bank 0552179550,ban da tsarin kati wannan karon, a turo ta POS, Shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*
Haka muka cigaba da lallab'a Rayuwarmu yau fari gobe Tsumma. abunda aka samu aci agode ma Allah ba domin ina samun,masu son Turaruka ba,da tuni jarin Zobo da kunin aya sun Dargane da Hidiman gida na yau da kullum,To riban da nake samu na turarukan,sun fi
na su auki. da shi nake had'awa muna rufa ma juna asiri sannan Allah ya sanya ma kasuwancina Nasibi komai na yi sa sai ya kare kuma ana nema,Shi kan shi Yace min ya gaji da zaman gida ba abunda yake yi ranar har ce min ya yi ko zan fara doramai zobon da kunin Aya ne yana zuwa tasha ya zauna min..?
Sai da naji kwallar Tausayinsa na kallesa yana bakin kofa zaune duk ya rame ya lallace ba wannan farin ba kyau ba fafa ba,kwanbo rayuwa kenaan.
A lokacin ban ce mai komai ba sai da ya karamin mgana sannan nace mai"Ko fita da shi baka ga inayi ba, a gida ake siye shi. Kai ma da wata mgana ka ke"
Cikin bayyana yanayin dayake ciki yace"Bazaki gane ba ne Fa'iza wlh na gaji ne ko Dako zan je na fara ne..?
Na kallesa ina maimaita"Dako..?
Sai ya gyad'amin kai yana fadin"Shima sana'a ne kuma akallah zan rika samun wani abun da zan rika taimaka miki da shi"
Da sauri nace"Aa ka bari dai mu yi Tunanin wata sana'ar tukunnah"
Da haka ya bar mganar tunda muka yi wannan mganar sai ta Dameni sai naga yana da gaskiya shi magidanci ne,zama agida kad'ai ya isa yasa bawa Damuwa na yi ta tunanin sana'ar da zai fara ban samu mafita ba, yanzu fa ko wata sana'a ta kudi ce sai kana da shi,ni kuma d'an jarin nawa kad'an ne Riba kuma agida muke cinye su don ma yan'uwa suna ta tallafawa.
Babban sallah tazo tana matsowa bani da matsala tuni na wanke ma yara kayan su na goge ga kuma na wajen Zainab, daman basu saka ba,ni daman bani da matsala in dai ya'yana zasu saka su fita cikin tsara Allah ya gama min komai Mama bata nan ta tafi Yamai da Hure zata koma sai ta bita,tafi wata achan ina jin Yaya Ishaq na fadi'n kila chan zatayi sallah Sai kuma naji gidan ba Dadi ba Mama ko yaya mutum yake Rahma ne haka ma yaran su yi ta fadin"Daada yaushe Mama zata dawo..?sai yace"Zata dawo in sha Allahu"
Ga Hafsah ma sun yi Hutu ta koma korafi tayi ma su Goggo Hutu, Badar kuma tana gidan Anty Binta suna ma Jarabawar Fita ne bayan sallah zasu gama makarantar gabada'ya ita da Raliya tun nesa da kofa tazo ta sameni tace min"Anty Fa'iza zamu gama makaranta akwai kudin riga da zamu yi na graduation din mu, wajen dubu ashirin ake so kowannen mu ya bada kinsan ba ni da shi Mama bata da shi ko da ta na nan Yaya ne kuma kina gani kece komai nasa yanzu,Anty Binta kuma bata ta kaina da na fara mata mganar kudi zata fara masifan itama bata da shi ke kad'ai gareni Anty Fa'iza don Allah ko rabi kika ragemin bakomai nagode".Sai ta bani