Showing 21001 words to 24000 words out of 82431 words

Chapter 8 - Kana Naka Book 2 Hausa Novel Complete

Janafty   

07 Dec 2024

189

Fadin"Saudatu ta fadamin Ummansu ke musu karatu agida sosai na yaba miki kin yi kokari kuma hakan da kike yi ya kara taimakon yara wajen hazaka da maida Hankali da ace iyaye mata da maza zasu san amfanin koyar da yaro kad'an daga abunda ka sani agida da yara da yawa sun zarce Tunanin iyayansu"
Na jinjina kai ina yarda da mganarsa Saboda ban zauna ba ko na bangaran Bokon da ban iya ba ina sawa su koyama junansu na addinin kuma da na kwarewa ban ta gajiyawa ba domin shi kadai gareni da zan basu su godemin watarana.
Sai wajen Tara na Dawo gidan na iske Rigima acikin gidan Tsakanin Zainab da Yaya Ishaq,Allah ya taimaka Hafsah bata nan na aiketa kasuwa ammh Badariya na gidan,Suna Dakinsa ne ammh fad'an nasu yayi kamarin da gabadayansu suke daga muryoyin su,da na dawo na kasa karisawa Dakina kamar zan shiga na gani wata zuciyar ta kwabeni tana fadin"Ke fa'iza ina ruwanki.?
Aiko sai na kama kaina na kama Sabgan gabana dakin yaran na fara gyarawa na fito falo kenan Sai ga shi ya fito har yana Tureni bai sani ba nayi Saurin yin gefe kamar kububuwa haka ya shige Dakin Mama itama sai gashi ta fito tabi bayansa tana fadin"Wlh baka isa ba Ishaq"
Itama tabi bayansa Fuu kamar zata tashi sama,sai gani rike da baki ina binsu da kallo ina nanata sunan Ishaq din da naji ta ambata, tunda nake ban taba jin ta kira sunansa gatsal ba sai dai Honey, ashe su Honey an jiki yau din nan.
Domin duk rashin karfin jina haka na rika jiyo tashin muryoyin su Mama nayi suna yi kamar ta kasa tsawarta musu ne sai ga Badariya ta shigo da Fadil tana Lallashinsa yana ta kuka na ijiye tsintsiyan Hannuna na karbesa ina fadin"Me ya same shi?
Badariya sai ta koma ta zauna tana fadin"Rudewa yayi da hayaniyar iyayan.Ni kaina barci nake yi sai da na tashi a firgice"
Kamar zan tambayeta sai kuma na fasa,Daman nasan zata koramin yadda akayi Kitchen na shiga na Dauko Purewater nazo na zauna ina basa yana karba da sauri alamun kishi yake ji cikin alamun Tausayi nace"Allah sarki bawan Allah kishi yake ji"
Badariya tace"Komai ma zai ji tun safe an fara fada,Daman ni nasan sai haka ya faru yadda Yaya Ishaq ya gina auransa ba kan turba mai kyau ba ne Anty Fa'iza"
Sai na kalleta ina fadin"Hala me ya ke faruwa..?.
Sai ta gyara zama tana fadin"Nima ban san kan mganan ba ina dai jin Kan tafiyar Anty zeey ne.Babanta ya Turo mata Mota tuni Direban ma ya iso zata koma Abuja to ina ga shine Yaya yace wlh bazata tafi ba sai dai in ta tafin ta fara shirin dawowa nan gabadaya ku zauna tare. shi bazai rika binta ba tunda baya aiki achan yanzu ita kuma ta Daka Tsalle tace bai isa ba sai ta tafi kuma bai isa ta ijiye aikinta ta Sauya rayuwarta Saboda shi ba,in bazai Bita ba sai dai ya bar shi"
Sai na jinjina kai jikina duk yayi sanyi Badariya tace"Ta wani fanni fa tana da gaskiya abunda ya zaba mata ne Tun farko rana tsaka ba shi da Hujjan da zai ce a'a duk wanda ya siya rariya yasan zata zubda ruwa"
Kafin nayi mgana Zainab ta shigo Dakin tana kiran Badariya ta kawo mata Fadil na mike na mika mata shi ta fita dashi nima sai na bita Daidai Zainab din ta fito da karamar akwatinta ta kalli Badariya tana fadin"muje mota da shi"
Taci gayunta ta yafa mayafinta abun nasa ya shafeni ko sallama batamin ba ta juya ta fara tafiya kenan Ya fito Daga Daki cikin Daga murya yace"Wlh Zainab in kika saka kafa kika fita daga gidan nan batare da izinina ba kin tafi kenan"
Dam!naji mganar nasa na d'ago ina kallonsa ita ma sai ta tsaya cak kafin ta juyo tana kallonsa Mama ta fito daga Daki hannunta a saman kai tana fadin"Na shiga uku ni Saudatu me zan ji haka..?Don Uban ka ka janye kalaman ka ko ranka ya baci"
Idanuwansa sun sauya launi yace"Bazan janye ba Mama haka nace.Wlh bazan zama jani talau ba..Ni ke auranta ko ita ke aurena..?
Mama ki duba fa wannan mgana taya za'a kafa min sharadin zuwa Abuja ina naga ko kudin mota.?zirga zirgan kansa ina naga kudin yinsa..?in a baya ina da aikin yi na dauki wannan Dawainiyar yanzu ta sani bani da shi To meyasa bazata zo ta zauna da ni a inda nake da shi ba in dai har da gaske tana so na?
Yafad'a cikin bayyana bacin ransa,Mama kuwa ta kasa mgana Ni kaina ban ce komai ba ni da Badariya muna tsaye cirko cirko,kamar wasu zakaru,ita ko Zainab sai batayi mgana ba ta jawo akwatinta ta shige Falona ta fito da waya tayi kira sai ta sauya Harshe turanci da Fillanci.
Shi kuma Mama ta shigar da shi Daki bansan me take fadamai ba,chan kuma sai ga Anty Binta suka sake kulewa Daki itako Zainab tana falo na kafa d'aya kan daya tana girgizawa karamar akwatinta na gefe sai hura Hanci take yi bini bini ana kiranta a waya tana mgana yadda batamin mgana ba nima sai na kama kaina na fito ina harkan gabana.
Zuwa azahar ina waje ina Dafa zobo na sai ga Mahaifin Zainab ya fad'o gidan kamar daga sama ashe jirgi ya shigo ya iso kano,Direban da yazo daukan Zainab yaje ya Daukosa Kai tsaye ya shigo cikin Hanzari ina gaishesa ko amsani bai yi ba cikin Kaushi da Dagawar murya yace"Ina Ishaq din..?
Muryansa ya fito da Zainab Daga dakina tana ganinsa ta nufesa da Sauri ta fada jikinsa ta fashe da kuka tana Fadin"Daddy wai ni Ishaq zai ce in na fita a bakin aure na..?ni Daddy Ishaq fa..?
Sai ta kara saka kuka,Cikin Kakkausan murya yace"Shi..Am here bai isa ya fad'a miki wannan mganar ba,Who is he.?
Mganarsa da kukan Zainab ya fito da Ishaq da Mama da Anty Binta suna ganinsa suka fara kame kame Mama ke fadin"Alhaji sai da ta taso ka?
Kallonta kawai yake yi bai yi mgana ba Ishaq ne ya nufesa yana fadin"Daddy k.."
Hannu ya d'agamin cikin tsawa kafin yace"Kayi min shuru Butulu kawai."
Sai ya tsaya ya kasa gaba ballatana baya Su Mama sai ido yayi kasa,Hannun Zainab ya kama kafin yace"Ina son mgana da kai domin ba zama nazo yi ba"
Da Sauri Mama tace"Mu shiga daga ciki Mana Alhaji"
Wani kallo ya watsa mata Lokaci d'aya yana fadin"Ba ni da wannan lokacin.Nazo ne Ishaq ya maimaita abunda zeey tace ya gayamata.."
Yafada yana bin su da wani kallo ni dai ina gefe ina kallon ikon Allah.
Ishaq ya sausauta murya yana fadin"Daddy da ka shigo ciki don Allah"
Cikin Tsawa yace"Ina da Lokacin shiga ciki ne ballatana naji shirmenka?nace ka maimaita abunda ka fad'amata so nake naji da kunnena"
Ishaq sai ya gyara Tsayuwa yana fadin"Daddy gaskiya na fada mata nace baan iya juran binta Abuja ba sai dai ta dawo nan mu zauna tare"
A wulakance yake kallonsa kafin ya nuna gidan cikin Yatsina yace" A wannan kejin gidan zata zo ku gamutsu da iyayanka da matarka..?
Yafad'a yana masa wani kallo lokaci daya yana kare ma gidan kallo a wulakance,Gabadaya su Mama sun daskare sun kasa mgana Yaya ishaq kuma sai ya sunkuyar dakai ya kasa mgana cikin kakkausan murya ya cigaba da fadin"Na ce a wannan a kurkin gidan kake tunanin y'ata ta bar komai nata ta dawo ta zauna dakai saboda kai ne autan maza ko?
Yaya Ishaq ya dago yana fadin"ammah Daddy.."
"Dakata min shashasha butulu a irin wannan gidan ka ganta ka aureta..?
Nace a irin wannan gidan ka ganta ka aureta da zakace hakkun Dole sai tazo ta zauna da kai a haka..?
Ya fada bayan ya katsesa,cikin Fusata da Bacin rai.
Ya nuna Zainab cikin Daga murya yana fadin"Lokacin da ka y'ta kace kana sonta acikin rayuwar hutu da jin Dadi ka ganta.cikin iliminta da tarin gata ka ganta kaji sha'awanta ka nemi auranta na aura maka ba domin ka chanchanta ba, sai domin nayi maka alfarma ina kallon ka kamar D'ana ashe baka da mutumci ban sani ba..?yar tawa kake so ka saka ka maidamin ita bazawara..?
Yaya Ishaq yace"ni ban ce zan saketa ba"Ya taresa da fadin"Ba ka ce ba kalaman ka me suke nuni..?kace in ta fita kada ta dawo..?so kake ta ijiye rayuwarta da Aikinta da komai nata tazo ta tare a wajen ka, to ka ba ta mene..?Kada kaa manta ko da ka ganta chan ta fara gudanar da rayuwarta bazata iya zama a ko'ina sai a inda ta saba.Bazan lamunci wannan rainin da iskancin ba,in ba ma kana Butulu ba an dauke maka nauyin ya'yanka na Dauke ma nauyin gida da zirga zirgan ai duk hakkin ka ne sannan na Dauke maka nauyi ita kanta Zainab din hakan ma baka gode ba kawai naka ka shiga mota ka rika zuwa kana dubasu ne zai zame maka matsala..?batulci zakamin ko kuwa zafin Talaucin ne yasa ka fara Nuna min akan ya'ta..?
Ya fad'a yana kallonsa cikin fusata,Sai wajen ya Dau shuru Mama bakinta yayi nauyi sai Anty Binta ta rika ma alama da tayi mgana itace tayi karfin Halin cewa"Alhaji ayi hakuri duk mganar bata kai haka ba a zauna a warwareta"
Ko kallo bata ishesa ba yace"Zan iya warware mganar ko wata iri ne ba sai na zauna ba,Kan ya'yana zan iya shari'a da ko waye na lura D'anku baisan  mutumci da Hallaci ba,duka abunda nayi mai bai gani ba in na barsa da Dawainiyar Zainab din zai iya Dauka ne..?to bai isa ba ku fadamasa bai isa ba.ba haka na aura masa yata ba kuma bai isa ya dawo min da ita haka ba, zan tafi da ya'ta kuma ya zama Wajibi ya janye kalamansa a kanta,Domin shima yasan hakan bazai taba yuyu ba ni ba sakaran Uba ba ne kan ya'yana sai nayi shari'a dakai wlh."
Abun mamaki Yaya Ishaq sai gashi ya kasa mgana Har da mama,Anty Binta ne ke bada Hakuri yace sai Ishaq ya janye kalamansa,Mama ta kallesa tana fadin"Kana ji ana mgana kana banza da mutane shashasha kawai"
Ransa bace yace"Na janye kalamai na"
Da sauri Mama tace"Ya janye Alhaji don Allah kayi hakuri Zainab kema ki yi hakuri don Allah"
Bai ko saurare su ba ya kalli yarsa yana fadin"Ina fadil.?
Sai ta juya tana neman Badariya ita ko daman tana dakin Mama tana ji ta fito da Sauri yako karbesa ko kunya yaja hannunsa yarsa ya dago yana kallon su Mama da suka yi Tsumu tsumu,Lokaci daya yana fadin"Zan tafi da y'ata zata kuma zauna ta jiraka.Hajiya ki gayamsaa duk bayan Sati biyu zai rika zuwa yana ganin matarsa da yarsa in kuma yaki jin mganata wlh tallahi zan saka Hukuma aciki saboda tun farko yasan Da Tsarin ya amince da haka sai yanzu zai sauya mganaa..?ina ruwan aikin Zainab da rashin aikinsa..?da zai wuce a kanta..?to zan kai kararsa bai isa ya tozartamin ya' ya zauna lafiya ba.in kuma bai ji mgana ba zan nuna masa waye lawal bako dan mutanen Adamawa"
Daga haka yaja hannun yarsa ita kuma ta dauki Jakarta suka fice Daga gidan,Sai aka rasa tsakanin Mama da Anty Binta ko Yaya Ishaq wanda zai motsa ni ko Allah ya kyauta nace araina na cigaba da duba dahuwar zobo na,Mama da ranta ya gama baci da Ishaq ta kallesa tana fadin"Ka kyauta ga abunda taurin kanka ya jawo ma ka nan, kaje in ya cire hannunsa a kanka sai ka duka ka Dauka."
Anty Binta tayi tsaki kafin tace"To me ma ya kawo mganar ta ijiye aikinta ta dawo nan ta zauna..?in ta Dawo kana da wajen da zaka ijiyeta ne..?
Sakarci kawai achan ya baku gida ya Dauki dawainiyar su Farhan da komai nasu ammh baka gode ba sai ka Tsiro da wata mgana Saboda kada a zauna lafiya.?
Idanuwansa jajir ya dago yana fadin"Don Allah ya isa.Ya isa nace.."
Mama ta saki baki tana kallonsa Anty Binta tace"To dake ni don na fada maka gaskiya Ishaq dake ni nace"
Gefe ya koma yana numfarfashi Kafin yace"Bazan dake ki ba ammh bazan fasa fad'a muku wannan ba gaskiya muka taka ba.Ta yaya wannan abun zai yuyu Mama duk bayan fa Sati Biyu ina naga kudin motar..?
Bude bakin Mama sai cewa tayi"Ba ga matarka nan na sana'a ba. tana da kudi sai ta rika baka Lokacin da kake da shi taci gajiyanka yanzu sai ta rama ma kura aniyarta"
Ina duke ne sai da na dago ina kallon mama tako zabgmin harara tana fadin"Munafuka ta saka shegen kurman kunnuwanta tana ji tana Dariya"
Sai na maida kaina kasa na cigaba da aikin Gabana shiko a fusace yace"Sai kawai saboda ina jani talau saboda zuwa na ganta sai na rika karban kudin mota wajen fa'iza wannan wani irin mutuwar zuciya ce?Haba Mama ki ma bar wannan mganar bazai yuyu ba wlh na jawo ma kaina bansan haka abun yake ba"
Yafada cikin kosawa Mama tace"Da auran Zainab din ka jawo ma kanka..?kada ka manta sun maka komai..?
A fusace ya katse Mama da fadin"Basu min komai ba Mama don Allah ki Daina fad'in haka me suka min.?da girma na ya ganni aikina Bashi ya nemamin ba,Auran yarsa da nayi nawa ya yafe min komai sai nayi Mama Dawainiyarta da yake mgana yaushe ya farayi..?ko da take aiki duk watan duniya 100+ nake tura mata nata da na Hidiman yara in adalci zan yi kudin zasu isheni..?nawa nake turo miki ke da Fa'iza da Dawaniyar yara sai kuma don yanzu Kaddara ta hau ni sai afini nuna iko Kan matata da ya'yana wannan wani irin kaddararran aure ne..?
Ya karishe fad'a kirjinsa na Dagawa alamun bacin rai ganin ya birkice yasa Mama ta fara lallabasa tana fadin"Taho mu shiga ciki"
Kin shiga yayi ya cigaba da fadin"Meyasa kuna ganin gaskiya bazaku bi bayanta ba.?In adalci zai yi bazai min uzuri ba..?ko bai san bani da aiki ba ne yanzu zaune nake nima lalurorina Dauke min su ake yi bai taba Duba Lokacin da nake wata biyu har uku a Abuja ya taba  ko sau d'aya ya yi min fad'a cewa na rika zuwa gida akai akai ina da wata matar da ya'ya..?bai taba ba yana jin dadin haka sai yanzu don kaddara ta fad'amin na rasa aikina sai yace Dole duk bayan sati biyu sai naje na Duba yarsa..?bazan iya ba Mama wlh bazan iya ba gwara na zauna anan ko banza ina ganin gilmawar ya'yana da mahaifiyata tare da Matata,achan kuwa ban ma ganta ba yaran kuma basa yini a gidan ni kad'ai kamar maye ina musu gadin gida.wlh ban taba jin abunda nake ma Fa'iza Laifi ba ne sai yau kuma na Tabbata Hakkinta ne ya fara Bibiyata, na Danne mata tarin hakkokinta daya rataya a wuyana, ko da sau daya ban taba duba hakan ba nasani akwai hakkinta dake Bibiyata na sani har da Hakkin Fa'iza Mama"
Ya karishe fad'a kamar zai yi kuka ban taba ganinsa cikin rauni haka ba inaji ajikina kallona yake yi ni kuma sai naki Dagowa sai ma na mike na Sauke tukunyar zobon na shige Daki Hawaye suna cika kwarmin idona.
Rana ta farko da Yaya Ishaq ya taba Furta ya zalunceni ashe yana sane da abunda yake aikatawa..?
Maganganun sa ya sanyaya ma su Mama jiki shi dai ina ji ya shuru takalmansa ya fice daga gidan, su mama kuma suka shige Daki jiki ba kwari.
Ranar gidan haka ya yini ba walwala nice ma na dinga zirga zirgan girki da Hada zobo har na gama abincin na zuba ma su mama na sakamai na kai Dakinsa bai shigo ba,yara suka Dawo makaranta kusan Lokaci da'ya suka shigo da Hafsah daman aiki aka basu taje kaiwa sai kuma na fara Damuwa da rashinsa suna ta tambayan ina Daada sun leka baya dakin mama haka ma baya Dakinsa sai nace musu ya fita.
Wasa wasa Yaya Ishaq bai shigo gidan nan ba sai Dare,kafafunsa Futufutu daga gani tafiyar kasa ya sha abunda yasa ya warware da ya dawo Jamal ya iske ya dawo shiyasa ya saki ransa.
Ruwan wanka ma Amir ya aiko yace wai Daada yace don Allah Umma ki saka mai ruwan wanka.
Sai ya bani Tausayi na tashi na saka mai na kai mai har Tiolet din dakinsa na aika Amir ya kirasa,sai da na baro  ya shiga wankan nazo na gyara Dakin da Matarsa ta gama bata sa ammh bata gyara ba,araina in naji kamar tausayinsa zai yi min tasiri a raina,sai nayi Saurin na kauce ma haka sai wata zuciyar tace saboda su Amir bazan bar Babansu a wulakance ba.
Koda ya fito dakin Tsab ya ganshi  ga abincinsa a gefe,sai ya zauna gefen katifarsa yana fadin"Anya ban yi wauta ba..?
Ko dai dai bakin Baba ne ya fara kamani..?.
Ya tuna Baba yasha fad'amai ya rike Fa'iza Amana in ya wulakantata bai yafe masa ba,sannan yana tausayamasa ranar dazai san amfaninta lokacin kuma tayi masa nisa..'
Tuna haka yasa yaji hankalinsa ya tashi bayan fitansa bai san ina ya nufa ba shi dai yasan yayi ta gagari a gari inda yaga masallaci ya tsaya yayi salla yasha a ruwa karon farko da ya tsaya ya fara Tunanin kuskuran da ya tafka a rayuwarsa tun farkon auransa da Fa'iza har zuwa yau..?sai a yau yake jin tabbas zai iya yuyuwa girman hakkin Fa'iza ko Bakin Baba ne sune suka yi Zaren Dabaibayi suka fara taba Rayuwarsa. lalle ko in hakane ya zama Dole ya fara gyara mu'alamansa da Fa'iza ya roketa ta yafe masa kila Furucin Baba zai sake sa.
Yana cin abinci hawaye sun cika kwarmin idanuwansa Ya tuna burinsa na auran Zainab da ra'ayinsa sai gashi Burinsa bai masa komai ba, yau ta kawo Fa'izan da ya raina ya hantara ya wukalanta itace komai nasa ta dauki laluransa har da ta kannensa da ta mama daman Laluran ya'yansa tun yana da aikinsa ya bar ma Fa'iza ragamar komai kaicon sa"
Cokalin hannunsa ya sauke abincin kamar yana cin mgani kansa ya Dafe dake juyamin cikin Fitan Hayyaci yace"Innalillahi yanzu ya zan yi..?ta wata Hanya zan gyara kuskurena..?duk da tarin laifukana a wajen Fa'iza zata iya duba na ta yafe min..?
Tuna haka yasa yaji hawaye masu duni sun zubo masa yayi wauta rud'in duniya da Irin Tarbiyan Mama sun kai shi sun rabo duniya da mutanen cikinta sun saka ya hau keken bera ta kaisa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login