Showing 78001 words to 81000 words out of 82431 words
mamaki"Bangane a'a ba ki bude baki ki yi min mgana Fa'iza"Bana son mgana alokacin sai kawai nace"Sai dai nazo"
Da sauri na katse kiran,ina jin kaina yana saramin ban zauna ba na mike na rika fito da jakunkunan kayana na zuwa falo,Sai ledan kayan da ba cikin kayana zan hada shi ba.
Ina cikin aikin ne sai ga shi ya shigo yana ganin haka sai yace"Yauwa daman mganar da na shigo nayi miki ne,bari naje tasha na yo tashar Ko Sharon ne yadda zasu daukemu da kayanmu duka"
Kai na gyad'a mai kafin nace"ni ma ka yo min tashar Ko karamar Golf ne don Allah"
Cikin mamaki ya juyo yana kallona lokaci d'aya yana fadin"bangane ba..?sharon fa zata ishemu in na yo tashar ta"
Kai tsaye nace"Aa ina so zan aika ma Goggo wannnan Frezer din karofi ne, in na barsa anan ba'a amfani da shi zai lalace. shiyasa nayi mgana da ita zan aika mata da shi"
Kamar zai yi mgana sai ya fasa ganin zai fita yasa nace"Kayi ma su Amir mgana su zo su fitar da kayan su"
Ya amsa min da toh ina ji ya leka Dakin Mama yana musu mgana,sai da suka zo nace su fito da kayan su tsakar gida daman tun jiya nagama duka kaye kaye muka kwashe komai muka adana cikin rawan jiki suka fara fito da kayan suna murna suna jin Dadi kallon su kawai nake yi ina zaune ko wanka ban yi ba Anum ce tace"Umma ke bazaki shirya ba ne..?
Sai na Rausayar da kai ina fadin"Zan yi wanka yanzu Anum"
Nan suka fice suka barni,ina sake sake ganin zaman bazai amfaneni ba yasa na mike na shiga daki,tubewa nayi na shiga wanka,kokarin daidaita kaina nake yi saboda in na rasa kwarin gwiwa bazan iya aiwatar da kudurina ba.
Na fito wankan kenan ina Shafa mai,naji dawowar Yaya Ishaq da maganan su Mama sai hayaniyar yara kamar suna fita da kayan ne waje da Sauri na Zura Doguwar rigar leshi,daman kwalliya ba aikina ba ne,Dankwali kawai na dora na zura Hijabi,na fito da sauri duk suna Tsakar gida har su Mama yana ganina yace"Ga motar chan a waje."
Nasan wanda nayi masa mgana ne kai Tsaye nace"akwai yara a waje ne..?
Juyawa yayi yana fadin"Bari na duba"
Ba jimawa ya Dawo,da wani Saurayi tare suka kama suka fita da Babban Frezer din da Starplezer,Anty Binta da ta shigo kenan ta ci karo da su suna fita da shi shine ta shigo tana fadin"Ina za'a je da wannan frezer din.?ba dai Lagos ba..?
Dayake na gayama su Mama karofi zan kaisa sai itace ta bama Anty Bintan amsa ni dai muna gaisawa na koma daki na shirya a gurguje saboda kada na bata Lokaci,hijabina na saka Dogo har kasa ni na kulle sauran Dakunan gabad'aya na fito da jakar hannuna na,karama na duba duk sun gama fita da kayan suna jidan sauran zuwa waje ne, har da Baban nasu ina kulle dakin na juyo ina kallon Amir da zai Dauki karamar ledar da na fito da ita da Sauri nace"Kai bani ledan nan"
Ba musu ya mikamin na karba ina fadin"ina kayana.?kun kai waje ne..?
Cikin natsuwarsa yace"Daada ya saka a mota"ina shirin mgana sai ga shi ya shigo yana fadin"Ku hanzarta fa Goma ta wuce mu isa kano akan Lokaci,ke kuma ga mai motar nan yana mganar lambar wanda zai kira in ya isa karofin..?
Anty Binta har ta fice,Mama ce da Anty Hure ban damu ba nayi karfin halin yi masa mgana ganin zai sake fita cikin Dakiya nace"Ina son mgana dakai"
Ba shi kad'ai ba har Mama sai da tayi mamaki gabad'ayan su suka kuramin ido,Sai nayi saurin Kauda kai ina juyawa na koma na bude dakin na shige daidai Lokacin da yake fadin"Fa'iza zamu makara fa kinsan jirgi ba jiranmu zai yi ba"
Ina kokarim daidaita yanayina nace"In sha Allahu bazaku makara ba"
Biyo bayana yayi muka Tsaya a Tsakiyar falon,na juya bayana ina maida hawayena a bayana ya tsaya yana fadin"Kin kuma juya.?wata mgana ce..?
Sai na juyo cikin karfin hali,idona yake son kallo saboda ya Fahimci yanayina ni kuma sai naki basa Dama,jikina ne ya kara yin sanyi Sabida ba jimawa mun yi mgana da Anty Fadila tace ita da mijinta zasu zo Filin jirgi daukan mu sai min je gidanta mun huta sannan su rakamu Sabon muhallin mu,da ita taje jiya ta kara gyara shi bayan kamfani yazo ya saka kayan Furnitures.
Har muka gama waya ban samu abunda na gayamatabba, ina jin kunyar gayamata cikin masu sauka a Lagos ba Fa'iza a ciki.
Ledan hannuna na mika masa sai ya saki baki yana kallona cikin sanyin jiki yace"Meye wannan kuma..?
Kai Tsaye nace"Duba ka gani mana"
Sai ya amsa ya bude yana gani Lokaci d'aya yana kallona da mamaki da alamun karin bayani da sauri nace"Kayan ka ne. Tun daga lokacin da ka jingine aurena da kai na daina amfani da duk wani abu naka,Abinci dai naci sannan ka bani wajen kwana Darajan ya'yana nagode kwarai Ishaq."
Na fad'a ina kallonsa ido cikin ido yadda ya kafeni da ido ne yasa nasan karin bayani yake so sai na yi ta Mazan cewa"Kayi hakuri Ishaq. Bazan iya binka Lagos ba."
Cikin Daga murya yace"What..?wannan wata irin mgana ce Fa'iza don Allah ki bar wannan wasan bana so.."
Ya fad'a har yana d'agamin hannu,sai nayi mirmishin takaici kafin nace"Ba wasa nake yi ba. Da gaske nake yi, daman na fad'a maka ka bani Lokaci naga ko zan iya bama auran mu wata Dama ko ba haka ba..?
Kamar gaula haka ya gyad'amin kai sai ya bani Damar cigaba da mgana ina fadin"To abunda na Dad'e da yankewa kenan,rasa aikin ka da abunda ya faru yasa na dakatar da kudirina,ammh yanzu tunda ka samu aiki komai ya wuce zama na dakai ya kare daman auran ka jingina ne, shine nake rokom ka ka karisa ballesa daga wannan jinginan ma'ana ka Furta min SAKI da kan ka"
Na gama fad'a ina maida hawayena lokaci daya ina jin karfin gwiwa na shigata shi ko ledan hannunsa ne ta kubce ta fadi kasa cikin Tsananin Firgita kamar kiftawan ido na ji sa ya Damki kafaduna duka Biyu yana fadin"Fa'iza ki daina irin wasaan. Wani irin saki.?ki yi tunani mana kina tunanin zan iya sakin ki ne.?so kike na rabu dake wai Fa'iza..?
Kai Tsaye na gyad'a masa kai cikin idonsa nace"Kwarai haka nake nufi ka Sauwake mun auran ka domin bazan so ka cigaba da zama da matar da baka so ba. Ka auri zab'inka a wanchan Lokacin kace nayi maka adalci in barka ka yi rayuwa mai Dad'i da matarka. ni ma a wannan karon ina neman wannan adalci nima a wajenka kayi hakuri ka sakeni, daman a jingine nake kamar yadda ka fad'a"
Ban ko gama mgana ba kawai naga ya sakeni da karfi yana fadin"Ina. Wasa kike Fa'iza har fa mun shirya jirgi na jiranmu fa ?kowa yasan yau zamu tafi sai yanzu ki sauya mgana..?ga yara chan na murna sai na fita nace musu me..?su Mama na Tsakar gida me zan gaya musu..?to wai kina nufin na tafi ni kad'ai dagani sai yara.?wa zai kula damu Fa'iza rayuwar mu ta fara tare dake kuma Dole mu karisa tare Fa'iza har Abada babu saki ko yaji Tsakanin aurena da ke"
Nima cikin Tsawa da Daga murya na taresa da fadin"Ammh akwai jingina acikin auran namu ko..?sannan akwai Tozarci da wulankanci duk aciki ko.?kayi hakuri na riga na yanke hukunci bazan iya cigaba da zama dakai ba.."
Sai ya juyo yana kallona cikin Fitan hayyaci yana fadin"In sake ki na Lalace Fa'iza?kin manta abunda Baba ya fad'amin?yace in na rabu dake na rasa mata tagari sannan bazai taba yafemin ba in na barki,don girman Allah ki bar wannan mganar ki bari in muka isa chan na yarda mu zauna da Mama ki fad'a mata komai tayi mana Sulhu, ammh zuciyata bazata iya Daukan wannan mganar ba. plz ki bari don Allah"
Ya fad'a har yana hada hannayensa alamun roko gabadaya tsoro da firgici sun bayyana a saman fuskarsa gabadaya,jikinsa kuma sai rawa yake yi,ina kallonsa kamar zan yi rauni sai kawai na tuna da irin zaman Tozarcin da nayi da shi na Tsawon shekarun auran mu,kuka ya kwace min na juya baya na ina fad'in"Kayi hakuri ba zan iya ba.."
Sai kuka shabe shabe,Ban sani ba ashe duk'amin yayi sai ji nayi yana jan Hijabina Lokaci d'aya yana fadin"Ki yi ma girman Allah Fa'iza ki yi hakiri ki bar mganar nan. Hankalina tashi yake yi in naji kina fadin saki da kuma cewa bazaki bimu ba.?Ta yaya kike so na fara rayuwa a in da baki..?
Bansan Lokacin da na juyo,har ina bangajesa cikin daga muryan da bansan ina da shi ba nace"Zaka iya. Nace Ishaq zaka iya.."
A baya ka zauna da wata macen inda bani kuma baka mutu ba. Na fuskanci Kaskantattaciyar rayuwa a gidan auranka,na fuskanci tozarci a wajen ka da wajen dangin ka a karkashin auran ka,ka rabani da kowa nawa ciki har da mahaifiyata ka rabani da yan'uwana duk wani mai so na baka kaunarsa,baka son ganin Dariyata sai kuka na Ba a macen aure ka Daukeni ba,ka Daukeni a baiwa,mara gata,jahila wacce bata da ilimin zamani,sannan mummuna baka wacce ka ke zaune da ita Saboda alfarma,wacce tayi ma rayuwarka karan Tsaye Fa'izar dai da tayi ma mafarkin ka kutse, Fa'izar da ka zaunar da ita kana rokonta da ta taimaka tayi maka adalci ka zama na mace Daya,Matar da ka fifita a kan Amaryan ka,Fa'izar da baka san ciwon ta ba,baka san cikin ta ba,baka san zafin nagudar haihuwar ya'yanka da ta dinga yi ba, itace dai wacce ahaka ake kiranta kamar akuya ta cika Haihuwa Fa'izar da ka nemi datse mata Haihuwa saboda baka kara kaunar Zuru'a da ita,Ni ce dai Fa'izan da kasa nuna ma duniya ni matsayin matarka kana jin kunya,Nice Fa'izan da ka ke barina wata da wattani Saboda wata mace ni ce Fa'izan da na dauki dukkan Tozarcin yan'uwan ka har da na Dangin matarka saboda Fa'iza bata da gata,Fa'iza ba kyakyawa bace. Sannan bata da ilimin zamani ba wayayyiya bace ba kuma yar gayu ba ce,sannan ita ba fara bace bata kuma iya haihuwan Fararan ya'ya ba,ni ce Fa'izan da kake kirana mara amfani Fa'izan da auran ta bai amfana maka komai ba ni ce dai Fa'iza nan wannan mai raunin jin,wacce ka ce ka tsani mgana da ita saboda tana saka ka ihu ko ka manta ne..?
nice fa nice fa kake kiran bazaka iya Rayuwa a inda bani ba..?karya ka ke yi..Wlh karya ka ke yi.."
Na karishe fad'a cikin Tsawa Lokaci daya da kuka sai kawai na zube saman Cafet din ina wani irin kuka mai cin rai ban sani ba ihu na da mganata yasa su Mama rugowa Dakin,duk a gabansu na rika amayar da abunda ke cikina.
Su kansu jikinsu yayi sanyi sannan sun kasa gane wasu abubuwan
Shi bai ma gansu ba sai ya rarrafa cikin Fitan hayyaci ya na kokarin rikoni nayi maza nayi baya da jajayen idanuwana ina fad'in"Kar ka kara tabani. Kar ka kara in ba haka ba wlh zan sharara maka mari"
Na fad'a ina nuna sa da yatsa cikin bacin rai da bai taba ganina aciki ba
Sai ya kasa karisowa gabana,cikin rawan baki da na murya yace"Fa'iza ba kin ce kin yafemin ba..?
Me ya sa..?
Kai Tsaye nace"Eh da gaske na yafe maka,.ammh ba shi zai goge tabon da kayi ma rayuwata ba.
Dalilinka aure ya fita kaina na Tsani duka maza sannan nake Tausaya mata ire ire na da Tunanin wata irin Rayuwa su kuma suke fuskanta a gidan nasu auran..?ka taba Tunanin ko sau d'aya kayi min adalci?
Nace ka taba wannan tunanin.?
Sai kawai na kara fashewa da kuka ina fadin"A gabana ka kori yar'uwata uwa d'aya uba d'aya,Har kana ikirarin in ka kara ganinta a gidanka zaka had'a ta da Hukuma?ashe ko bata ci darajan aurena da kake yi ba, bazata ci Darajan zumunci ba Ishaq..?
Mahaifiyata ta rasu bata san Dadina ba. Har ta koma ga Allah ban taba zama da ita na yini d'aya ba.
Ranar da zata rasu ma baku barni na kwana da ita ba,ta rasu ban sani ba.
Na rasa uwata ammh ko gaisuwa baka zo min ba, kana wajen wacce ta fini muhimmanci a wajenka.Sai da ka dawo baka iya ce min Fa'iza ya hakuri ba sai Duba na kayi kana ce min ashe wai kuma babarku ta rasu..? Wai ne ma baka Tabbatar ba.?shine kake so na manta..?ko kuwa yadda ka ware ni daga cikin sauran mata a dalilin auranka yasa nayi shekaru ina fama da Gulit din mata masu kyau da gata ne suka chanchanci ado da kwalliya,a gidan ka na fuskanci mata ire irena basu dace da samun soyayyar miji irin Ishaq kabir karofi ba. Shiyasa na yanke shawaran karshen zama na dakai yazo daga yau.Na rantse da Allah bazan bika ko'ina ba. Daganan karofi zan koma daman ranar da Baba yace zai had'a aurena dakai Mama ta koreni sannan tayi alkawarin bazan koma mata gida ba,Karofi na koma wajen Goggo kuma chan aka daukoni nan duniya bani da gatan da ya fi gaban Goggo gabanta zan koma na zauna Domin Fuskarta Sabuwar rayuwata"
Na karishe Fad'a ina share hawayena lokaci Daya na mike da Sauri ina fadin"Zainab zata iya kula da kai. Yara kuma Amir da Anum sun yi girman da zasu iya kula da kansu. Ahmad da mutsy ba su da matsala zasu kula da su.
Ba lalle ba ne don na faro rayuwata dasu na karishe ta da su ba..Haka Allah ya kaddara Labarin ya kare daga wannan Lokacin"
Na fad'a Lokaci daya ina Daukan karamar jakata,Mama na gefe sai sharan kwallah take Anty Hure ta sha gabana tana fadin"Haba Fa'iza ku ba yara bane. yi hakuri mu tafi in mun je chan sai a zauna a fahimci juna'
Kallonta nayi kafin nayi mirmishin takaici na tuna har da ita a masu biye ma Mama suna cin zarafina,sai kawai na kad'a kai ina fadin"Bakin alkalami ya riga ya bushe Anty Hure.."
Na kad'a kai na zan fita waje,Ishaq ya yi kukan kuran shan gabana yana rike Hijabina na balla masa harara ina fadin"Cikani kafin raina ya baci"
Yaki ko sakina fad'i yake yi"Fa'iza ina zaki.?Fa'iza kada ki yi min haka..?me zan ce ma yaran chan..?
Fa'iza..Fa'iza"
Sharr sai kuka abunda ban taba gani ba,kai na kauda abubuwan suna dawomin kamar yanzu komai ke faruwa,kwace hijabina nayi ina fadin"Na fada maka kuma zan kara fad'a maka na gama zaman aure da kai. Na tsani aure na tsani kowani zamantakewa,Ka sauwak'e min Ko kuma ka k'ara Turgud'e shi daman jinginanne ne"
Na turesa zan wuce sai ya makale kafafuwana yana fad'in"Kada ki yi min haka Fa'iza,Kada ki yi min haka"
Kasa kwace jikina nayi sai kawai na juya ga Mama tana kuka nima ina Hawaye nace"Mama ki fad'a masa ya cikani don Allah"
Sai Mama ta sunkuyar dakai shi ko,sai alokacin yaga su Maman sai ya sakeni ya Rumtuma wajenta ni kuma sai na kwashi Sauri na fita Daga Falon ina Fitowa sai nayi Turus ganin yaran duk Tsaye suna jin abunda ke faruwa ga Anty Binta itama.
Cikin mamaki tace"Fa'iza meke faruwa ne har kofar gida ana jin Hayaniyar ku..?
Ban bata amsa ba Ishaq ya fito rike da Hannun Mama ya kawota gabana yana fadin"Mama ki gaya mata wlh nayi nadama.bKi gayamata abunda Baba ya sha fada'min,Yace in na rabu dake zan lalace Fa'iza ko so kike kada nayi albarka..?
Komai ban ce ba kaina na kallon kasa ina Digar kwallah,Mama ma sai sharan hawaye take yi Anty Binta ta kalli Anty Hure tana fadin"Anty meke faruwa ne..?
Anty Hure cikin Damuwa tace"Fa'iza ce tace bazata bisa lagos ba. Tana neman saki ne da wasu mganganun da ban gane ba.."
Sai ta waro ido kamar yadda yaran suka yi cikin wani yanayi tace"Fa'iza yanzu kuma?kika ma zauna dashi a bai da shi sai kuma yanzu da Dadi yazo sai kice haka.?aa ku bari muje chan sai mu zauna mu tattauna kin ji ko..?tafad'a gabanta na fadi domin bata san ya wannan al'amarim zai kare ba.
Jallonata nayi ina tuna Yadda tayi Tsawon shekaru tana Tozartani har da ita masu saka bakin na zauna sai kawai na share hawayena ina fadin"lokacin da bai da aiki wannan yanayin da mata ire iren Fa'iza ya Dace shiyasa ban tafi ba tun a wanchan Lokacin,sai yanzu kuma da komai nasa ya dawo sai nayi Tunanin Lokacina ya kare daman kema kin sha Fad'a jin dadi bai dace da mata ire irena ba,wahala ce da bauta ta Dace dani kamar yadda Mama ta sha fada. Shiyasa zan tafi zainab itace ta Chanchanci zama da shi Tunda ita ta tako kashin arziki sannan bata yi kama da matan bauta ko wahala ba.."
Dukkansu Tsaye suka yi an kasa mai mgana ina gani Anty Binta na zaran ido sai kawai nayi Dariyan takaici kafin nace"Na kwashe fin shekara goma ina bautar aure kuna ganin komai ammh baku taba zaunar da shi kin fad'amasa bai kyauta ba..?sai ni yau don a shekaru goma sha Biyar da auran mu na yunkuro sai ku nemi Danne ni.?wannan karon ba wanda ya isa ya hana Fa'iza tafiya.
Zan tafi kuma tafiya ta har abada"
Ina gama fad'in haka na ratsa Mama zan wuce sai ta riko Hijabina tana kallona,yanayinta zai sakani rauni sai na daga kaina sama cikin wata murya tace"kiyi hakuri Fa'iza.
Ba domin na isa ba..Ki yi hakuri ki Duba yara nan kada ki bar su yi maraicin uwa"
Ta fad'a tana nuna su Amir,Anum har ta fara kuka da su Ahmad zuciyata ta karye ammh ban damu ba Hawayena na Shatata saman fuskata nace"Ke kan ki shaida ce Fa'iza bata dace da D'anki ba.,yaran nan kuma rabo ne Allah ya sa na same su,maraici kuma baza su yi maraici ba Mama kina nan ga Zainab,sannan shi ma babansa zai kula da su tunda ya'yansa ne sune Dolensu bazan ce a zama da shi bai Tabamin wani abun alheri ba,yayi min Tunda dalilin sa yasa yau nake amsan sunan uwa,ammh mganar na Duba yaran nan bai taso ba. Nima a lokacin da yake tozartani ko sau d'aya bai tab'a Duba darajan ya'yana ba.."
Na fad'a ina kallon su, bana so na cigaba da mgana a gabansu kada su ji,kamar ma Amun da Amir tunda suna da wayan su.
Na